Sashe 68
Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe bakinta tayi cikin murna tace"wanka zan fara yi tukunna saina jirashi muci abincin tare, ko ya kika gani?"
Murmushin farinciki mama tasake tana share hawayen fuskarta tace"yauwa yar albarka muje!"
Yusayrah kenan! Fitarta daga gidan Dakhil a wannan daren tasamu hatsari wanda sanda tasamu tsagewar kashi akafa har yau kuma kafar baidawo daidai bah! gakuma bugawa datayi akai wanda yakusa juyar mata da kwakwalwa inhar ka ganta a hanya dole ka tausaya mata soboda tadawo abar tausayi....
Anje anyi tambaya agidansu Zuly inda akamusu kyakyawan tarba, nan take aka sanya aure nan da 2months, Mourad baiji dadin jin al'amarin bah! Shi dayaso ace nan da sati 1 Amma shine har watanni 2 gaskiya ba'a mishi gentle bah!.
Suna barin Azare sukayi cikin Abuja gidansu Maram dayake an San da zuwansu, sukam ma cewa sukayi inso asamu neh ayi komai da wurwuri, tambayan Fakhih akayi akan yafadi lokacin da yamishi ai ko kunya babu yace wani wata hakan ma baya son ace yacika zumudi neh!, nan kuwa suka amince , cikeda murna yadinga zuba musu godiya Kaman ya ari baki!
Mourad ma ya tayashi murna yana mai jin da ma shine Amma ba komai! Watanni hudu Kaman gobe neh Allah yakaimu da rai da lafiya...
"Taya za'ayi kibar yen gidansu subuce miki cikin sauki bayan kinsan kafin kisamu kamarsu saikin shawuya!
Baga Fakhih yana sonki bah?why not kije kifadawa babanki kema kinasonshi iyaso saiki aureshi gudun kiyi biyu babu!"Shine tunanin dayake kai kawo a kwalwalwarta Karar wayarta neh yadawo daita daga duniyar tunaninta yamutsa fuska tayi hade da daukan wayan
"Wayyo Allah kawata lefe na yaiso!"Shine abinda aka fada da karfi daga dayan bangaren , cikin sauri ta cire wayan daga kunnenta tareda maka wa wayan harara tana ya mutsa fuska
"Toh sainayi Yaya?tafada cikin isa da takama
"Cewa nayi kizo kigani"Maram tafada cikin sanyin murya jin yanda Mom tayi magana saikace ba kawarta bah
"No! Gaskiya bazan iya zuwa ganin kayan takaici bah! Soboda nasan raina neh kawai zai baci kawai soboda haka basai nagani bah!"tafada tareda kashe wayan batareda tajira jin abinda Maram zata fada bah
"nine zanje ganin kayan matsiyata? Allah ya sauwaka wlhy"tafada tareda ajiye wayarta akan gado sannan tafice zuwa dakin babanta.... Kallonsu Mysha dake zaune Maram tayi hawaye na ciko mata a idanuwa
"Dallah matsa! Yanzu kuka zakiyi soboda tace bazata gani bah?"Mysha ta tambaya tana jefa mata harara
Hawayen daya silalo mata tashare tace"banji dadi bane kawai"
"Chill Maram! Amarya agidan Balarabenta"Mahrosh tafada tana share mata hawayenta murmushi Maram tasake cikin jin dadin abinda Mahrosh tafada...
'''RANAR DAURIN AURE...'''
Sosai ake shirye-shirye a duka side din Amarya da Ango inda Kuma har yanzu Mom bataje ganin Lefen Maram bah! Kuma Daman Fakhih yace bayason a daura hoton Lefen a media soboda makiya!
Zaune suke su uku adaki, Maram tayi Wani irin kyau na ban mamaki sai sheki kawai takeyi ga farinta yasake fitowa inka ganta dole kasake kallonta,shigowan Zuly da Fakhiha neh yakatse musu hiran dasukeyi
"Amarya bata laifi!"Zuly tafada tana zama akan kujera likewise Fakhiha ma Gaishe da Fakhiha sukayi cikin ladabi soboda daman Sun San itace twin din Fakhih
"Sannunku da zuwa!"Maram tafada tana yafa gyalenta akan dogon gashin kanta
"Yauwa Amarya!"Fakhiha tafada tana gyara zamanta "Miye za'a kawo miki?"ta tambaya cikin ladabi irin ga surukan nan
"Haba karki takurawa kanki"bata gama rufe baki bah Mom tashigo da sallama dauke abakinta,turus ta tsaya tana binsu da kallo daya bayan daya cikin mamakin abinda yakawo su Fakhiha
Karasa shigowa tayi tana yamutsa fuska hade da fadin "shiyasa bana zuwa irin wa'inan bikin,! Yen kauye duk Sun cika gida , Abu ko tsari babu"
Kallon mamaki suke mata inda Maram tasake murmushi tareda basar da zancen tana fadin"kawata yana ga kin rame haka Kaman wacce tayi ciwo"
Ajiyar zuciya tasauke tace "ba dole na rame bah dady yabani Sati daya na fito da miji in ba haka bah wai zai aura min koma waye!"
Kallon juna suka hauyi kowa na kokarin danne dariyar daya ciyoshi!
Fakhiha neh tace"toh samarukan ki fah?"
Tsaki taja tace "ai ni nafi karfin wainan talakawan! gashi Kuma Fakhih sai juyani yakeyi Kaman waina acikin kasko!"
Dariya Zuly tasake jin abinda tafada Amma tace"yanzu ya kenan Mom "
Sanda ta harareta tukun tace"Yaya kuwa? Lallabashi kawai zanyi ya aureni awuce wajen"
"Waye zai aure ki din?"Maram tafada cikin Kishi
"Waye kuwa in ba Fakhih bah!"tafada tana hararanta tareda lallibo numbernshi ta danna mai kira, cikin sauri Maram ta fauce wayan tareda katse kiran!"
Kafin Mom tayi magana har wayan Fakhiha yadau Kara!
Kallon juna suka hauyi kafin Fakhiha tadauki wayan, ji sukayi tace"wow Alhmdllh bro Allah yasanya Alkheri"
"Andaura!"sukaji Fakhiha tafada da karfi cikin hausarta mai Kama da larabci Ai sai duka gidan yadauki guda, zaro idanuwa Maram tayi tareda gyara zamanta soboda jitake kaman faduwa zatayi daga kan gadon
"Ayiriri!! MARAM TAZAMO AMARYA AGIDAN FAKHIH!"
Garam taji wani abu ya buga acikin kanta sai maimaita abinda aka fada takeyi acikin kwanyanta ,ganin yanda aketa tsokanar Maram da sunan Fakhih neh yasata kwala Kara tana rike kanta dake barazanar rabewa
Tsit sukayi Suna binta da kallon mamaki cikin rawar murya tace "Wani Fakhih? Amma Inace bah Fakhih na bah?"
"Fakhih dinki kokuma nawa?"Maram tafada tana kafeta da idanuwa, girgiza kai Mom tafara yi tana fadin
"Calm down Momina wannan duk mafarki neh ba gaskiya bah!" Mintsinetan da akayi neh yadawo da ita hankalinta aikuwa ta chakume Maram tana fadin
"Karya kikeyi yarinya! Ai ke bah kallar Fakhih bane soboda Fakhih yafi karfinki Kuma dani yadace ba dake bah!"
Banbare hannunwan Mom tayi daga jikinta tana fadin"tin lokacin dayake binki kaman jela kisoshi kika ki kina fadin ke kinfi karfinshi shine sai yanzu kikasan cewan dake ya dace? Inma mafarki kikeyi ki farka soboda yanzu Fakhih yamiki nisa irin na sosai dinnan, yazamo nawa! Nawa nikadai soboda yanzu babu wata Momina acikin zuciyarshi saidai Maram!kingane koh?"
Daskarewa Mom tayi cikin mamaki tana mai bin Maram da kallon kaskanci da raini, nunata tayi da yatsa tace"nasan bahaka kawai kika barshi bah soboda nasan bayanda za'ayi yakula irinki"
Murmushin takaici tayi tace"ayyerh, anfada miki sai irinki zasuna samun abubuwa masu kyau? Mukuma ya'yan talakawa mukare ayanda muke? Tirr Wlhy da masu irin halayenki kije ma banson sake ganin fuskarki!"
Tana gama fadin hakan tafice daga dakin abinta tana mai share hawayen fuskarta, zubewa Mom tayi akasa tana mai fashewa da kuka mai cin rai, ganin ba mai rarrashintane yasata mikewa itama tafice cikin sanyin jiki...
'''BAYAN KWANAKI BIYU!"...
_Manage please, not feeling too well_
*DanAllah wattadians ina bukatan Followers dakuma votes🙏*
#team Zuly
#team Mom
*Vote,comment&share*
*ZULFA*
@MHIZZPHYDO
A Sweet and pitious Romantic love story
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
*Page 95*
_Arrogance_
'''BAYAN KWANAKI BIYU!"
Kwance take akan gadon asibiti banda ruwan hawaye babu abinda takeyi sai sannu ake zuba mata, karan notification din wayarta taji cikin sauri ta janyo wayan hade da dubawa
Hannu tasa ta rufe bakinta cikin son danne kukan dake shirin kufuce mata sanadiyar ganin haddadiyar dinner event dinsu Maram da Fakhih, ga manyan mutane harda larabawa duk sun hallarci bikin.
Kuka tafashe dashi tana fadin "Sun yaudare ni! Yanzu ni waye zai aureni (nace so maza basu kare bah!) Wayyo Allah nah! wlhy ban yafe bah! Allah zai saka min"
Bata gama rufe baki bah taji Zuly dasuka shigo yanzu nafadin"ke kika yaudari kanki basu bah!"
"Ya za'ayi nayaudari Kaina?"TA tambaya ahasale batareda ta lura da sauran wa'inda suka shigo cikin dakin bah!
"Girman kai! !"Zuly tafada tana zama agefen gadon Mom
Tsaki taja tace"ai nakai nayi girman kan neh shiyasa nakeyi"
Murmushin takaici Zuly tayi tana girgiza kanta hade da fadin "shin kinsan miye ake nufi da girman kai kuwa? kinsan hadisai da suka zo kan girman kai kuwa?
Kinsan abubuwan dasuke Haifar da girman?
Kinsan illolin girman kai? Kinsan karshen masu girman kai?
Nasan baki sansu bah amma bari na fada miki; Yadda Malaman Aklaq suka yi bayani shine:Mutum ya dunga shu’uri a ransa cewa yafi wani ko wasu,to idan wannan tunanin ya tsaya a zuciyar mutum kawai wato bai bayyanar da shi ba, to a is]ilahin ilimin Aklaq ana ce ma haka Kibr,to amma idan ya bayyanar da girman kan ta hanyar walakanta wanda yake ganin yafi shi a zantukansa ko ayyukansa to haka shi ake ce ma Takabbur.
To minene banbanci tsakanin Kibr da Ujub? Ujub shine jiji dakai da wata ni’ima da Allah Ta’ala ya yi ma mutum misali dukiya,mulki,ilimi da dai sauransu.
Girman kai nau’in shi ya kasu kashi ukku:1-Akwai girman kai ga Allah wanda shine mafi muni,misali irin yadda Fir’auna yayi,ta yadda ya siffanta kan sa amatsayin ubangiji.ko yadda Namarudu yayi cewa shima yana kashewa yana rayawa.
Akwai kuma girman kai ga mutane.
Akwai kuma girman kai ga gaskiya,shine mutum ya ga gaskiya ko a fada masa amma yaki bi...
Hadisai da suka zo kan girman kai:Akwai hadisai masu yawa da aka ruwaito daga Manzon Allah(SAW) da kuma Aimma na Ahlul bayt kan abin da ya shafi girman kai,ga wasu daga cikin hadisan:
Manzon Allah(SAW) yace, “Kashedinku da girman kai,domin Iblis girman kai ya kai shi ga KIn yin sujuda ga Adam.”
An ruwaito hadisi daga Imam Ali[AS] yace, “Ku lura da karshen Iblis,yalalata ayyukansa da yayi tsawon lokaci sakamakon girman kan da yayi a lokaci guda.”
An ruwaito daga Imam Sadik [AS] yace, “Ba zai shiga Aljanna ba wanda a cikin zuciyarsa akwai kwayar zarra na girman kai.”
Haka kuma a wani hadisi da aka samo daga Imam Bakir[AS] yace, “Girman kai komin kankantarsa ba zai shiga zuciyar mutum ba face sai ya samu raguwar hankalinsa dai dai gwargwadon abin da ya shiga.”
Manzon Allah(SAW)yace, “Wadanda nafi ki daga cikin ku,kuma suka fi nesa da ni ranar qiyama sune masu girman kai.”
A wani hadisi kuma yace, “Duk wanda ya kasance mai girman kai to zai hadu da Allah yana mai fushi da shi.” Da dai sauran hadisai akan haka....
Abubuwan da suke haifar da girman kai:Sun kasu kashi biyu,akwai sabubba na duniya da kuma sabubba na addini,misalin sabubba na duniya da suke haifar da girman kai akwai dukiya,mulki,kyan halitta da dai sauransu.