← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 98

Sashe 50

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Umma da kanta ke sunkuye yayi tareda matsawa wajenta, hannu yasa ya dago habanta tareda Kura mata idanu, saiyanzu ma yaga takara mai haske,murmushi yasake yace" ashe ajiyata neh yakesamiki zazzabi"

Sake sunkuyar dakai tayi tana sakin murmushi a b'oye shikuwa yawani. Kura mata ido yana sakin murmushi,

Karan camera neh yadawo dasu, cikin sauri takarasa wajensu tace " wlhy yayi kyau sosai"

"Banson shashanci fah" Umma tafada tana kokarin kamo Zuly,gudu Zuly tasa  tana dariya.

"Umma nah takusa haifo min kanwa ko Kani"tafada tana tsalle kaman ba mai ciki bah

Tsawa taji Umma tadaka mata cikin sauri ta tsaya tana zare ido

"Bakida hankali neh kike tsalle da yanayin dakike ciki?" Umma tafada cikin yanayin tashin hankali

Idanuwanta neh yakawo ruwa cikin i.i.na tace" Allah Umma mantawa nayi " soboda cikinta a shafe yake luff ko irin dan tasowan nan baifara bah

Malam neh yace"Lallai yarinyar nan a gaisheki, yauwa daman mijinki neh yace gobe zaizo daukarki"

Gabanta neh yayi mugun bugawa ai batasan sanda tazauna bah zufa na karyo mata cikin rawar murya tace " DanAllah Malam yabari saina haihu tukunna"

Dangwalan ta Umma tayi shikuma Malam baki sake yake kallonta

"Bakisan miye kike fada bah" Umma tafada tana mikewa

Kuka tafashe dashi tana fadin ita babu inda zataje, Malam ma tashi yayi yana mata kallon yarinya kina hauka neh soboda gani yakeyi kaman raina musu hankali take son yi.

Sallama yamawa Umma yafice abinshi ranshi fess.

Ganin Umma tashige daki yasata sake fashewa da wani kukan harda su majina, ganin kukan yaki karewa neh yasa Umma fitowa daga daki, cikin sanyi jiki takarasa waje Zuly tareda dafa kafadarta,

Buge hannun Umma tayi tareda tashi tafice daga parlourn dagudu,

Girgiza kai kawai Umma tayi tana mai mamakin abinda yasa take kuka akan ance zata koma gida.

Sai dare Zuly ta koma bangaren su idanuwanta duk sun kumbura har wani zazzabi takeji tsantsan tashin hankali.

Muryanta chan ciki tayi sallama, amsawa Umma tayi tana mikewa

Ko kallon inda Umma take batayi bah tashige cikin daki, jikin Umma neh yayi bala'in sanyi , ahankali tabi bayanta.

Abakin kofa taja ta tsaya tana kallon Zuly dake hada kayayyakin ta acikin trolley,

Tana gama hadawa tashiga toilet tayi alwala sannan tazo ta tada Sallah , Umma ma gajiya tayi da tsayuwa itama tashiga toilet tadauro alwala , kafin tafito har Zuly tafice daga dakin.

Zuciyarta babu dadi ta tada Sallah, ta dade tana mawa Yar ta Addua soboda ta tabbata ba'a mata daidai agidan aurenta.

Fitowarta kenan daga daki tasami Zuly natattara abubuwan zanenta,

Zama tayi agefenta tace" yar Umma kinada wacce tafini neh?"

Idanuwanta cikeda kwalla takalle Ummanta sannan tafashe da kuka tana kwanciya ajikin Umma

Shafa kanta Umma tayi sannan tadago ta tana mai kallon kwayar idanuwanta cikin muryan dake Muna tsantsan damuwa tace " muzguna miki sukeyi neh?"

Runtse  idanuwanta tayi tana cizan labba soboda yanda Umma ta Sosa mata inda yake kaikayi,jan hanci tayi tareda yin murmushin yake tace" taya za'ayi ya muzguna min Umma nah? Mijina neh fah kuma sirrina kawai dai banson rabuwa dake neh"

Kallon rashin yarda Umma tamata tana maimaita mijina neh kuma sirrina acikin zuciyarta, badon zuciyarta ta yarda da abin da Zuly ke fad'i bah tace" yayi kyau daman ba'ason mace na bayyana sirrin zaman aurensu amma in kinga kina cutuwa kifada mana kinji?"

Gyada kai Zuly tayi tana kwanciya akan cinyar Umma, sosai taji takaicin rashin fadawa Umma damuwanta dabata yi bah amma kuma wani bangare na zuciyarta na fada mata abinda tayi daidai neh soboda tasan mudin suka san abinda yake mata zasu ceh sai sun rabu gashi only hope dinta Yay Mou gashi shidin ma yayi aurenshi cikin salin halin gashi ta tabbata yana cikin kwanciyar hankali abinshi kuma ya yarda da kaddara toh why not ita? Daman kuma ance gidan aure gidan tarbiya neh kuma kowa da irin tashi kaddaran saidai nawani yafi wani tabbata in taji labarin rayuwan auren wasu to lah shakka sai tayi kwana tana mawa Allah godiya daya jarabce ta da kalan nata...

Share hawayenta tayi tana Adduan Allah yakawo mata mafita kuma Allah ya Alkheri neh wannan dinnan mah...

_Washe Gari..._

Zaune take akan kujera tana shan koko dakuma rogo kaman bazata ci bah  sai wani shan-shan kamshi take , jefi-jefi kuma ta yatsine fuska,

Duk abinda takeyi Idanuwansu akanta yake especially Iqbal daya kasa dauke idanuwanshi daga garets soboda yanda tasake kyau dakuma cika kaman ba ita bah tawani yi fresh harda su kumatu

Ture tray din tayi tana kwantar dakanta a bayan kujera,

"Kina bata mai lokaci fah" Umma tafada

"Toh Umma nah bazan dan huta abinci na yayi digest bah" tafada cikin shagwaba

"Ahh toh huta abinki yar' Umma" murmushi tasake tana lumshe idanuwanta

Haushi duk yagama turnuke shi soboda gani yakeyi tana raina mai hankali neh.

Tashi yayi yace "Bari nafita da kayayyakin ta saimu wuce"

Gyada kai Umma tayi kawai tana kallon shi kasa-kasa...

"Jeki jirashi Amota zamuyi magana" Umma tafada tana kallon Zuly bayan Iqbal yadawo daga kai trolley

Tashi tayi tafita, Iqbal kam zuciyarshi neh yafara bugawa dasauri-sauri soboda fargaban abinda Umma zatace

Gyaran muryan da Umma tayi neh yadawo da hankalinshi gareta

"Iqbal in mai rokon ka da riketa da hannu biyu soboda samun irinta wahala yake dashi kuma na tabbata dakasan rawan ganin data taka arayuwarka wlhy koda kuda bazaka bari ya tabata bah DanAllah ka kiyaye karka zo kana danasani nan gaba kasan kuma danasani keya ceh, koda bazaka iya sata amatsayin dakasa uwargidan ka bah toh ina gargadin ka da karka kaskantar daita na roke ka" tafada cikin sanyi murya tana mai hada hannayenta waje guda

Kaman wanda maganar yayi tasiri azuciyar shi yace " Ayyerh Umma dagaske babu abinda nake mata asalima daidai nadauke ta da Yusayrah amma zan dada kiyayewa"

Murmushi Umma tasakar mishi tareda mikewa tace" muje karmu daddar daita"

Shima tashi yayi yabi bayan Umma yana tabe bakinshi,

Fitowa Zuly tayi ta rungume Umman ta duk jikinta asanyaye, Sallama suka sake da Iqbal sannan yashige bayan mota soboda driver neh ya tukoshi.

Hannunta tasa tana shafa tumbinta " gani ga Dadynku fah babies"

Tafada ahankali tana sakin murmushi, duk abinda yakeyi yana kallonta da jefen ido,

Tabe baki yayi azuciyarshi yana fadin basai kiyi tayi bah mahaukaciya kawai...

Baifi sauran mintuna talatin su isa gida bah yadauko juice din gora yanasha,

Abinka da mai ciki dukta gama hadiye yawu, gani tayi kaman inbatasha bah zata iya mutuwa ahankali tace" DanAllah kasanmun kadan koda kuwa kurba daya"

Murmushi yasake azuciyarshi yana fadin anzo wajen, daure face yayi yace " ban bayarwa kwadayayya kawai"

Narai-narai tayi da ido hawaye na taruwa cikin rawar murya tace" ai badaga ni bane soboda wlhy in tanine kadaisan abinka bazai burgeni bah, amma danAllah dan darajan cikin twins dinka dake jikina kabani nasha"

Dasauri kaman baisani bah yace" twins kuma??"

Murmushi tayi tana sake shafo shafaffen cikinta tace" erh mana yanzu watansu 4"

"Alhmdllh" tafurta yana rungumarta ajikin cikin son nuna erh yana murna da labarin cikin data fada amma daza'a bude zuciyarshi dakunga yanda yake konewa kaman wanda ake cilla ashana a gas.

Cirota yayi daga jikinshi sannan ya sumbaci Lip dinta sannan yasa hannu akasa ya dauko ledan daya ciro wanda yake sha daga cikin ta,

Bude mata yayi dakanshi yace" ga wannan ni bana shan abu rabi"

Karba tayi sannan tayi Jim tana kallon goran hannunta,

Shindin ma takalla taga hannunshi akan cikinta yana murmushi, haka kawai taji zuciyarta bata yarda dashi bah amma yanda yakeyi yasa ta karyata abinda zuciyarta ke fadi,

Kafadunta tadage kafin ta lumshe idanuwanta tahau kwankwadan juice,

Wani boyayyen murmushi  yasake tareda kallon agogon hannunshi sannan ya kwatar dakanshi a bayan kujera.

Ko minti 15 basu karaba suka iso gida, dakanshi yashigar mata da trolley dinta,

Da mamaki take bin dakinta da kallon ganin yanda yayi fess cikin rad'a yace"wancan dakin neh kawai ban samu daman gyarawa bah,

Cikeda mamaki take mishi kallon DanAllah Kaine kuwa?

Ko damuwa da irin kallon datake mishi baiyi bah yace" barina jeh na watsa ruwa"

Gyada mishi kai tayi tana Adduan Allah yasa ya chanxa kenan.

Wanka tayi tafito sannan ta sa kaya, tin kafin tagama sawa taji cikinta na kullewa.

"Wayyo Allah wannan wani irin kashi zanyi neh haka" tafada tana nufa toilet da dan sauri,

Taje tana kirawo kashin amma baizo bah saima kara kullewa da cikin yayi.

Ai kaman Jira yakeyi tamike nan kuwa wani azababben zafi ya ziyarceta a lokaci guda.

Kara tasake tana mai tsugunawa a kasa,

Wasu zufan wahala neh yake keto mata gakuma hawaye,

Kokarta rarrafe tazo yi taga ji....

_DanAllah wattpadians ina bukatan Followers dakuma votes🙏_

#team ZulynMourad
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 76*

Kokarta rarrafe tazo yi taga jini wani azababben kara tasake wanda inada yakinin cewan duk mahalukin dake cikin gida yajishi.

Kuka tafashe dashi hawaye na kwaranya daga idanuwanta, ganin hakan bashine mafita bah yasa tafara rarrafowa daga cikin bayan gidan...

Iqbal dayake kokarin shiga cikin bayan gida yaji ihun ta amma soboda rashin tausayi yasashi yin kaman baiji bah yashige wanka abinshi yana murmushi...

Dakyar take rarrafawa harta kai tsakiyan parlourn ta duk jini yagama b'ata mata daki, wajen center table ta nufa dakyar tareda daukan wayarta,

Numbern Iqbal tafara gwadawa amma harya gama ringing bai daga bah.

Hannunta na rawa tayi dailing numbern Lutfiya, bugu daya tadauka

"Maman baby harkin dawo n..."

Nishi dataji Zuly nayine yasa gabanta faduwa kafin tayi magana har Zuly tace"jini..jini yana fitowa wayyo Anty kizo karna mut.."

Bata gama magana bah wayar hannunta ya subuce, idanuwanta neh suka fara rufewa tin tana budesu dakyar harsuka rufe ruff sannan taidda kwantawa akasa...

Khimar kawai Lutfiya ta dauka tareda ficewa da gudu.

Sanda yagama shirin shi tsaf kaman mai fita anguwa tukunna yafito yana mamakin inda Yusayrah taje.

Sauka yayi kasa tareda nufan fridge don shan ruwa, daidai yakafa cup abaki daidai shigowan Lutfiya.

Da mamaki yake kallonta ganin yanda duk tabi tarude,

"Lafiya kuwa?" Yatambaye ta

"Zuly ceh takirani yanxu, inaga ba lafiya bah"

"Bangane bah?" Yafada looking a little bit confused

"Muje!!" Tafada tana hawa stairs din dagudu ya mara mata baya.
Chapter 50 · 0% Book details