← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 98

Sashe 41

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tasake Jin yafada, cikin zaro ido tace"Daman lokacin da Yay Mou ya ajiye ni sai ya tafi massalaci shine fah naga bai dawo bah, danazo fita sai yace in har nafita abakin igiyar aurena guda daya azaton shi Zan ji tsoro nakoma  nikuma kawai sai nafita kuma ina dawowa ya miyar dani"

Sarai Umma tasan karya Zuly keyi soboda her eyes says a lot, wajen Zama Malam ya nema yana mai cire hulan kanshi soboda zafin dayaji dukda akasan bishiya suke

Shikam baisan miye zaice bah cos gabadaya kwalawar shi tadau zafi

"Yah Salam miyesa baku fadamin bah?" Yatambaye Umma

Cikin sanyin murya tace"ai tace ya miyar daita neh shiyasa"

"Ya miyar daitan banza bayan alokacin babu iddan shi akanta"

Gaban Umma neh ya yanke ya fadi , itafa Sam wannan tunanin baizo mata bah,

Kallon Zuly dake binta dana shanu tayi wanda alokacin jikinta bari yake yi cikin rawar murya tace"bangane bah"

"Erh mana ai sai mijinki yasake biyan rabin sadakin ki kuma asake daura muku aure kafin ki maidu"

Kuka Umma tafashe dashi tace"nashiga uku nah kunyi zaman haramci "

Zaro ido Zuly tayi zuciyarta na zafi wani tunani neh yazomata cikin sauri tace"ba abinda yataba shiga tsakanin mu dashi"

Dagowa sukayi dasauri suna kallonta cikin mamaki, Malam neh yace"kina nufin duk watannin dakuka kwashe tare babu abinda ya shiga tsakanin Ku?"

Ganin yanda Malam yamata tambayan neh yasata cewan"ce mishi nayi yakara min lokaci shine ya yarda"

"Kenan babu matsala atsakanin Ku?"yasake tambayan ta

"Erh babu matsalan komai"

Ajiyar zuciya Malam yasauke kamin yace"Daman yafarka neh"

Ai kaman jira takeyi tayi cikin Hospital din dagudu, kallon Umma Malam yayi ganin yanda jikinta yayi sanyi yace" yanzu da banzo nan bah saidai yaran nan su cigaba da Zama a hakan?, Miye sa bazaki manta da baya bah mu zauna kaman yanda ko wasu ma'aurata ke zaune?"

Rungume Malam tayi cikin kuka tace"kayafe min DanAllah"

Cirota yayi daga jikinshi ya goge mata hawayen ta...

Kaman wanda ake bi aka tashiga cikin ward wanda yayi sanadiyar razanan mutanen cikin ward din ciki kuwa harda shi Iqbal din,

Murmushi shimfide asamar fuskarta takarasa shiga ward din batareda ta Lura da kallon dasuke binta dashi bah

"Oh you scared me abokina, you left me restless" tafada tana shafa fuskar shi tareda samun mazauni a gefen shi

Murmushi yaskar mata cikeda jin dadin ganinta dukda yana jin jiki,

"I miss you" tafada kaman yayi shekaru basu hadu bah,

Sororo sukayi suna kallonta, sosai suka sha mamaki cos harda mamanshi azaune amma ko kunya bata ji bah,

Malam neh dakuma Alhaji wato baban Iqbal suka shigo Umma nabinsu abaya,

Ido akamusu dukkansu suka fita cikin kuwa harda Yusayrah amma banda Zuly,

Sannu da jiki suka mai inda Malam yace" shin kana son ka cigaba da Zama da Zulfa?"

Akidime dukkansu suka dago suna kallon shi,hadiye wani yawu Iqbal yayi cikin muryan marasa lafiya yace

" Erh mana"

"Amma dai kasan ayanxu haka babu aure atsakanin Ku tinda ka riga da ka saketa?"

Atsorace yake kallon Malam cikin rawar murya mai nuna tashin hankali yace"na miyar daita tin alokacin"

Girgiza kai Malam yayi tareda koro mishi bayanai daga karshe yace"yanzu dai rabin sadakin daka bawa Zuly kawai muke bukata sai asake daura sabon aure"

Cikin rawar jiki yace Zuly taje gida ta dauko mai Check book dinshi, itama kaman wacce aka tsikara tayi waje da gudu,

Daidai kofan fita tayi kicibus da Doctor dakuma Awad zasu shigo, gaishe su kawai tayi tareda wucewa abinta...

"Sakamakon test dinda mukayi mun ga cewan Kidney dinshi duka biyu sun lallace sakamakon tara spam din dayakeyi a marar shi don haka inson asamu neh amishi transplant acikin wannan satin" Doctor yafada wa su Malam bayan sun zauna a kujeran cikin office dinshi

Wasu gumi Malam da Alhaji suka hau sharewa cikin tsananin tashin hankali, kallon juna suka hauyi ,

Malam neh ma yayi jarumtan fadin"akwai Kidney din siyarwa neh?"

"Maganan gaskiya babu Kidney sai dai wani daga cikin Ku Familyn shi ya taimaka"

"Toh mungode"suka fada tareda barin wajen...

Samunta sukayi har tadawo daga dauko check din cos har ya rubuta yana jiran dawowan su,

Suna karasa shigowa Zuly ta mikawa Malam check cikin Zumudi,

Karba Malam yayi yana bin Iqbal da kallon tausayi, muryan Iqbal sukaji yace"tinda yau jumma'a neh DanAllah a miyar mana yau A massalaci"

Alhaji zaiyi magana Malam ya katse shi da fadin"inshaAllah yau za'a miyar da auren"

Yana gama fadin haka yace Zuly taje gida, badon taso bah ta tafi bayan tayi pecking dinshi a goshi...

"Yanzu kuna nufin babu wanda zai taimaka mishi da Kidney guda daya acikin nashi"Malam yafada cikin takaici

Ai duk palourn babu wanda yasake tari , kowa kagani sai zazzare idanuwa sukayi banda Yusayrah da Zuly dakuma Mamanshi dake ta kuka,

Sallaman su akayi kowa yakama gaban shi cos ko asibitin wasu daga cikin yen uwan Iqbal basu koma bah,

A mazan neh mah wasu suka hallarci daurin auren da aka sake wanda dubbanin mutane suka shaida shi...

Banda sautin kukansu babu abinda kakeji adakin gashi kuma alokacin ammawa Iqbal maganin bacci soboda yanda yake shan wuya,

Share fuskarta tayi tareda ficewa daga ward din, daidai kofar consulting room ta tsaya gabanta na wani Irin bugu,

Shahada tayi tareda knocking tareda shiga, cikin sa'a kuwa Awad dakuma wani doctor daban tasamu babu patients acikin,

Gaishe su tayi tace"daman akan maganar Iqbal neh"

Gyada mata kai sukayi suna tunanin abinda yake tafe daita, cikin sanyin murya tace"yanzu we're friends nida Iqbal and Zan iya mawa friend dina komai in har inada daman yi, from the buttom of my heart nake jin taimakon shi ,shiyasa kawai na yanke hukuncin bashi...

_hmmmm_

#team ZulynMourad 
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*
[19/09, 11:42] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO 

A Sweet and pitious Romantic love story 

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 63* 

Shiyasa kawai na yanke hukuncin bashi nawa guda daya"

Arazane suke kallonta,gyaran murya Doctor yayi yace"are you sure you wanna do this?"

Dasauri ta gyada kanta alaman eh

"Zuly!!!"Awad yakira ta in a serious tune

Kallon shi tayi tareda kureshi da ido tana jiran abinda zai fada cikin sanyin murya yace

"Kindai San Mourad abokina neh koh?....Gyada Kai tayi ya cigaba... Kuma kinsan ni mijin kawarki ceh kuma ina matsayin Yayanki cos baki fi sa'ar kanwata bah?... Sake gyada kanta tayi... Why not kibar Kidney naki matarshi Yusayrah tabashi cos ita tasa shi acikin matsala kuma natabbata zaifi son nata akan naki"

Girgiza kanta ta hau yi kafin tace" nasan dai kasan cewan burinshi baifi ace yaga MISS ZULFA bah?... Shima gyada mata kai yayi tacigaba da fadin...kuma na tabbata zaifi son na MISS ZULFA akan na Yusayrah, pls amatsayin MISS ZULFA zanyi filling din form din I know he will be so happy"

"Kina ganin hakan bazai zamo matsala bah?"Awad yatambaya cikeda tausayin ta cos ya tabbata da Zuly tasan yanda Iqbal yake kinta da bazata taba kawo wannan tunanin aranta bah.

Muryanta yaji tace"inshaAllah babu wata matsala"

"Toh shikenan zamu fadawa musu ansamu kidney donor"dayan Doctorn yafada cikeda Sha'awar samun irinta

Murmushi tasakar tareda gode musu sannan ta fice...

"Bangane tace zata bada Kidney dinta bah?" Umma ta tambaya a kidime

"Erh haka yarku tace"nan yazayyane musu yanda sukayi daita, 

Zufa neh ke gangarowa wa Umma, she's totally out of words,da taimakon maman Iqbal tasamu suka fice daga office din doctor cos ko tashi bata iyayi daga kan seat dinda take zaune.

Neman Zuly suka hauyi a hospital din amma ko alaman ta basu gani bah, Yusayrah ceh ma tace musu taganta tafita,

Ba bata lokaci sukayi gida sudin ma cikin sa'a suka hangota zata shige cikin gidan cos harta kai rabin shiga da alaman abu tazo bayarwa awaje.

Ganin anbude gate yasata tsayawa tana jiran ganin suwaye acikin motan,

Ganin su Malam neh yasata gyara tsayuwarta,

"Sannunku dazuwa mushiga ciki kafin ace ban iya tarban bak'i bah"tafada tana kafe maman Iqbal da idanuwanta bayan duk sun sauko daga motan, sunkuyar dakai maman Iqbal din tayi tana jin dacin abinda tamawa Zuly ranan...

"Basai mun shiga bah"Alhaji yafada

"Ohk bari na kawo chairs achan" bata jira cewarshi bah ta dauko su tareda ajiyewa kowa,

Ita tafara Zama kamin tace"please seat"

Zama sukayi takara fadin"1 minute pls" kaman wasu dolaye suka gyada Kansu

Wani number ta latsa cikin harshen turanci tace"inada bak'i  kiyi kaman yanda kika saba"

Shiru neh ya ziyarci wajen amma kuma sai wayan Malam yayi ringing  adaidai lokacin,

Isowar Christine neh da kayan motsa baki yasa suka miyarda hankalin su kanta ganinbaturiya.Gaishesu tayi cikin harshen turanci suka amsa mata,

Umma neh tace" why is she here?"

Kallonsu suka miyar wajen Zuly suna jiran jin abinda zatace bayan Christine ta ajiye musu kayan motsa baki tareda tsayawa agefen ta

"Nina kirata cos nasan zaku bukace ta nan gaba"

"Bangane bah"Umma tafada cikin rashin fahimta

"Erh cos lokacin dakika jeh Hajj banda lafiya sosai har spot suka fito min shine Yay Mou yakaini asibiti anan aka tabbatar mana da cewan jini na bashi karfi kuma bakowani Irin magani da Allura bane zai karb'e ni" tafada hankalin ta kwance

"Are you sure you're doing this?" Umma tafada cikin rawar murya

Ahankalin ta kwance tamika wa Umma cup din juice tace"calm down ai it's nothing,kuma kusha ruwa"

Bayan sunsha neh tace"inason na nimi Alfarma awajen Ku DanAllah"

"Ai kinfi karfin neman Alfarma awajen mu just say duk abinda kike so"Alhaji yafada

"DanAllah banason yasan cewan nice na bashi"

"Why" Umma ta tambaya

"Just"

"Amma dai kinsan zai nemi sanin waye ya bashi"

"Erh shiyasa nace zanyi signing da sunan MISS ZULFA" tafada, gyada sukayi inda suka dinga zuba mata ruwa godiya...

Duk abinda akeyi Yusayrah batasan waye zai bada Kidney bah itadai abu daya tasani batason Mourad ya margaya kuma Allah yagani baxata iya bashi nata bah,

Kwatsam taji wai ansamu Donor abin yabata mamaki amma jakan bata nemi ganin waye donor din bah balle tayi godiya

Ansamu anyi operation din lafiya  bayan tarin Adduo'in da aka bisu dashi,

Daki daban daban aka kaisu inda doctor yafada musu cewan 3 days shine tsananin lokacin farkawan su...

Itadai Yusayrah bataga Zuly kuma bata damu data ganta bah...

_6 days later_
Chapter 41 · 0% Book details