← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 98

Sashe 69

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Misalin kuma sabubba na addini akwai ilimi,Nasaba mai daraja wato shi Dan wane ne ko kuma jikan wane,aikata addini misali ace shi mai yawan ibada ne ko ba da gudunmawa a wani fage na addini misali mai yan infaki ne,sai dai fa a lura anan mujarradin mutum na da wadannan ni’imomin ba ya nufin girman kai ga mutum.Abin da ake nufi shine ire-iren wadannan ababe da aka ambata galibi idan zuciyar mutum ba tsarkakakkiya  bace,to su suke sabbaba ma mutum girman kai ta hanyar jin cewa ya fi wadanda basu da shi ko kuma basu aikatawa kamar na shi.

Daga cikin abubuwan da suke haifar da girman kai akwai jahilci da kuma gafala.Wato idan mutum ya jahilci hakikanin naf’s dinsa ko kuma ya sani amma ya gafala to haka zai iya sabbaba masa girman kai,akwai hadisi da aka ruwaito daga Imam Ali[AS] yace,

“Ina mamakin dan Adam farkonsa digon maniyyi,karshensa mushe,tsakiyarsu kuma yana dauke da najasa amma kuma yana girman kai.”Daga cikin abubuwan da suke sabbaba girman kai akwai rashin tazkiyyar naf’s.Wato idan mutum yayi mujahada ya tsarkake naf’s dinsa to zai kasance duk irin wadannan ababe masu halakarwa zai ku~uta daga gare su...      

Illolin girman kai:Girman kai yana da illoli masu yawa a duniyar mutum da addininsa da kuma lahirarsa.Idan mutum ya duba a duniyance idan mutum na da girman kai za ka ga mutane suna kinsa.

Akwai ma hadisi da aka samo daga Manzon Allah(SAW) yace, “Mafi Kin mutane shine mai girman kai.”Daga cikin illolin girman kai ya kan haifar ma mutum da kaskanci a duniyarsa da lahirarsa wato idan bai tuba ba.Imam Ali[AS] yace, “Duk wanda ya yi girman kai ga mutane to sai ya kaskanta.”

Daga cikin illolin girman kai yana jawo ma mutum rashin son Allah gareshi wato dai kamar yadda yazo a cikin Al-Qur’ani cewa Allah baya son masu girman kai,kuma ranar Qiyama mai wannan mummunar dabi’a zai hadu da Allah yana mai fushi dashi.

Haka nan daga cikin illolin girman kai shine yana hana amsar gaskiya.Idan mutum ya lura da mai girman kai zai ga bai cika amsar gaskiya ba, wanda wannan ko ba karamar hasara  bace ga rayuwar mutum wato yaga gaskiya amma ya ki binta saboda girman kai!.Daga cikin illolin girman kai yana sa mutum ya dinga walakanta mutane a zuciyarsa ko zantukansa ko kuma a ayyukansa,alhali wanda ka walakanta ba ka san yadda yake a wajen Allah ba..... (Allah yasa mudace)

Wani irin kuka Mom tafashe dashi dajin bayanan da Zuly tayi "Ashe girman kai ba abin takama bane! Ashe bakomai bane girman kai face muguwar cutar Ruhi mai hallakarwa! Wayyo Allah, Allah natuba kayafe min"

Tafada tana kwantawa ajikin Zuly jikinta na wani irin sanyi she's so ashame of herself

"Shin kinsan Hanyoyin magance girman kai? Kinsan Fa’idodin nisantar girman kai dakuma karshen masu girman kai?" Taji muryan Wanda bazata tab'a mantawa bah yatambayeta

Dago kanta tayi sukayi ido biyu da ustaz, cikin sauri ya kawar dakanshi daga gareta soboda daman bai zata zata dago bah, cikin shakekiyar muryarta tace"a'a!"

Gyaran murya yayi yace"Akwai hanyoyi masu yawa da malaman Aklaq suka yi bayani yadda mutum zai yi ya tsarkaka daga girman kai.

Daya Daga cikin wadannan hanyoyi shine mutum ya fahimci cewa Kibr, wata siffa ce wadda ta ke~anta ga Allah wato kamar yadda yazo cewa Walahul-Kibriya’u.Saboda haka wannan wata siffa ce wadda bata cancanta ga kowa ba face ga Allah Ta’ala.

Daga cikin wadannan hanyoyi na magance girman kai shine mutum ya yi tunani a kan cewa dukkan abin da yake tinkawo da shi wadda har ya kai shi yana girman kai ga wani ko wasu da abin,to Allah ne fa ya ba shi,in yaso zai iya kwacewa,saboda haka idan Allah Ta’ala ya yi maka wata ni’ima,abin da ya hau kan mutum shine ya gode ma Allah ya kuma kasance mai tawadi’u.

Daga cikin wadannan hanyoyi shine mutum yayi dubi da kuma tunani kan ayoyi da hadisai da suke suka da kuma bayanin  mummunan sakamako na mai girman kai,da kuma wadanda suke nuna yabo da sakamako mai kyau na mai tawadi’u.

Daga cikin wadannan hanyoyi na magance girman kai shine mutum ya yawaita tunanin Akibarsa wato karshensa a fagen addini,ba mamaki wanda kake ma girman kan shi yayi kyakkyawan karshe kai kuma wa’iyazu-billahi kayi mummunan karshe.

Daga cikin wadannan hanyoyi shine lizimtar addu’a musamman ma ta Makarimul-Aklak,mai son ganin ta yana iya duba littafan addu’oi kamar mafatihul jinan,in  mutum zai iya ya kasance ko wane dare bayan sallar tahajjud dinsa ya karanta ta, ko kuma akalla ko wane daren jumma’a ko ranar.Haka nan kuma  mutum ya dinga rokon Allah ya ba shi lafiya daga dukkan cututtuka na ruhi,shi yasa idan mutum na addu’a na Allah ya ba shi lafiya to ka da ya tsuke tunani ga neman lafiya ta gangar jiki kawai, A’a har da ta ruhi,domin mutum zai iya kasancewa ga shi da lafiyar jiki amma kuma ruhinsa bai da lafiya.Haka nan idan mutum na rokon Allah ya wadata shi,to ya roka har da wadatar zuci,saboda mutum zai iya kasance ga shi da dukiya amma kuma bai da wadatar zuci....    

Fa’idodin nisantar girman kai:Yana da fa’idodi masu yawa daga ciki akwai jawo ma mutum son Allah da kuma son Manzon Allah kai har ma da son mutane.Yana haifar ma mutum wanzuwar ni’imar da Allah yayi masa,sa~anin girman kai da ke janyo ma mutum gushewar ni’ima.

Yana daukaka mutum  awajen mutane da kuma wajen Allah Ta’ala.Akwai hadisi da aka ruwaito daga Imam Sadiq[AS] cewa,wani mawadaci ya zo wajen Manzon Allah da tufafinsa fes-fes,sai ya zauna gaban Manzon Allah,can kuma sai ga wani talaka ya zo da tufafinsa ya yi datti,sai ya zauna kusa da wannan mawadacin,sai mawadacin ya tattare tufafinsa.Sai Manzon Allah  ya ce masa kana tsoro ne ka da ya shafamaka talaucinsa? sai mawadacin yace A’a,yace to kana gudun ka da ya sa maka datti a tufan ka ne? Ya ce A’a.Sai Manzon Allah yace masa to mi yasa ka yi haka? Sai yace aikin shaidan ne.To nan take sai mawadacin yace na bashi Rabin dukiya ta.Sai Manzon Allah ya tambayi matalaucin akan zai amsa? Sai yace A’a.Sai mawadacin ya tambaye shi miyasa ba zai amsa ba? Yace ina tsoron abun da ka yi mani nima in yi wa wani.A takaice dai nisantar girman kai ya na haifar ma mutum da kyakkyawan sakamako a duniyarsa da kuma lahirarsa....        

  {issoshi na karshen masu girman kai:Mu duba saboda girman kai yadda karshen shaidan ya kasance.Mu duba tarihi zamu ga yadda girman kai ya haifar da  mummunan karshe na wadanda suka ki bin Annabawan Allah da kuma Aimma[[AS].

Haka nan mu duba sakamakon girman kai yadda ya haifar da mummunan karshe ga wadanda suka Ja da wadanda Allah Ta’ala ya yi amfani da su wajen jaddada  addini misali a zamanin Shehu Usman dan Fodiyo da kuma Imam Khumain.

Atakaice dai girman kai yana haifar ma mutum da mummunan karshe a duniyarsa da lahirarsa,kuma mutum ya lura da mai girman kai ko a rayuwarmu ta yau da kullum za ka ga daga karshe sai ya walakanta har ma ya zama abin tausayi.Kuma irin wadannan munanan siffofi na girman kai,Riya,Hassada,munana zato ga juna,son matsayi da sauransu sune suke dabaibaye mutum daga ayyuka na da’a,misali ka ga mutum da yana ibadodi kaza da kaza amma yanzu ya yi rauni a kai ko ma bai yi.

Haka nan kuma irin wadannan zunubai su suke hana mutum samun istikama a tafarki na Allah Ta’ala,ka ga da yana tafarkin Allah amma yanzu ya barshi.Saboda haka yana da muhimmanci mutum ya yi mujahada domin ya samu tsarkaka daga wadannan munanan siffofi,wato ka da ya bari mutuwa tazo masa alhali yana tare da wadannan munanan dabi’u,domin in ya tafi da su lahira to zasu zama masa matsala babba.Muna rokon Allah Ta’ala ya tsarkake mu da tsakakewarsa,ya kuma samu cikin tsakakan bayinsa...."

*DanAllah wattadians ina bukatan Followers dakuma votes🙏*

#team Zuly
#team Mom

*Vote,comment&share*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 96*

"Ameen" suka sake fada atare inda Mom tadinga sauke ajiyar zuciya akai-akai, gyaran Murya Maram tayi cikin sanyin murya tace

"Kawata kiyafe min! Amma kisani bawai don na bata miki rai na aureshi bah na aureshi neh soboda son danake mishi" Dago kai Mom tayi har zata harareta saikuma takawar da kanta tana mai gyada kai alaman ba damuwa, murmushi Zuly tayi soboda sarai taga abinda Mom tayi amma tabar hakan amatsayin dabi'rata ma'ana yanda tasaba yi kunga kuwa ba alokaci daya abin zai barta bah!

"Toh Allah yakara karfin jiki!"ustaz yafada tareda ajiye ledar hannunshi sannan sukayi musabaha da mazajen waje yafice hannunshi nacikin na Raees. Da ido suka bi bayansu kafin kowa yayi jugum ana tunanin abin duniya.

Matsowa yayi kusa da Zuly tareda dan zungurinta da hannunshi make kafadarta tayi tana turo baki alaman bazata juyo bah, murmushi yasake kafin ya dan tsuguna daidai kunnenta yace "Haba ustaziyata Kuma Malamata!"

Murmushi tayi soboda yanda yayi maganan tana dan kawar dakanta cikin turo karamin bakinta, mikewa yayi yana shafa laulausar suman kanshi duk abinda sukeyi idanuwan Mom nakansu, ajiyar zuciya tasauke tana maimaita Kalman istgfari acikin zuciyarta, Maram ceh tace

"Toh muntafi kawata Allah yakara karfin jiki"

"Ameen"tafada cikin sanyin murya tana danne hawayenta,fita sukayi inda yarage sauran Zuly, Mourad, Mom dakuma yen gidansu!

"Toh muma mun tafi Allah yakara karfin jiki"yafada yana mikar da Zuly wacce sai zumburo baki takeyi, Suna fita daga ward din ta fauce hannunta tareda cikawa bujenta iska!

Cikeda damuwa yabi bayanta ganin yanda tadauki zafi alokaci guda, bude mata gaban mota tayi tashiga ko kallonshi batayi bah ta koma owners corner din motan wato gidan baya tazauna tareda slamming kofa, Dayan bangaren yakoma yabude bayan motan tareda zama agefenta, matsawa tayi ganin yanda ya matsota Kaman zai shige mata jiki Gani kawai tayi yadaura kanshi akan cinyarta, cikin rawar murya yace

"Zulynah yanzu akan abinda nafada dazu kike fushi dani?"

Hankalin ta bakaramin tashi yayi bah jin muryanshi kaman na mai shirin yin kuka, hannun tasa asamar kanshi tana shafa sumarshi

"bakai bane!"tafada cikin shagwaba

"Toh shikenan bazamuyi honeymoon dinmu a Nigeria bah sai ki zaba mana inda zamuyi ko bahaka bah?"yafada yana dago kanshi tareda shafan gefen fuskarta Kura mishi idanuwa tayi kafin tasaki murmushi tace
Chapter 69 · 0% Book details