← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 98

Sashe 93

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kan cinyar Ammi Zuly ta d'aura kan ta inda Ammi  tafara aikin shafawa tana kuma jin gaban ta na fad'uwa nan ta fara Kara to Addua a cikin zuciyar ta, ba da jimawa ba bacci ya d'auke Zuly....

Nishi da Ammi ta  ji ne ya farkar da ita daga baccin da ya fara d'aukan ta a zaune saboda bata jima da fara baccin ba, cinyan ta ta hau shafawa saboda a nan ta bar kan Zuly

Caraf ta ware idanuwan ta jin kaman babu kowa a kan cinyar ta, bata tashi saukar da idanuwan ta ko Ina ba sai a kan Zuly  dake kwance a ta kofan toilet

Mikewa ta yi da Sauri tana fad'in Adduoin sa da suka xo bakin ta

"Miye faru? " ta tambaya cikin tashin hankali, Zuly na jin muryan Ammi ta fashe da kuka saboda daman daurewa ta keyi don kar ta tasar da Ammi

"Ammi cikina! Zan mutu Ammi! "Cikin kuka da zafin ciwo ta fad'a wa  Ammi da ta yi mutuwar zaune a gefen Zuly

Hannu Ammi tasa ta shafo abin da ta ke gani kaman jini saboda gabadaya tunanin ta ya gama gushewa

Hannun Ammi ta riko zata yi magana kenan ta ji damshi a hannun da ta rik'e, kasancewan akwai full light a wajen ya sa Zuly ganin abin da ya ke hannun Ammi

Cikin tashin hankali Zuly ta zaro idanuwan ta tare da fasa ihu wanda ya dawo da hankalin Ammi, kafin ka ce me har numfashin Zuly ya fara kokarin fita daga jikin ta saboda yanda ta ke ji

Dakyar ta ke fuzgar numfashin ta sai so take ta yi magana amma gabadaya bata iya wa saboda ko kalmomin ma kasa had'awa a cikin kwakwalwar ta tayi

Kafin ka ce miye wasu irin zufa suka tsatsafo mata dukda uban sanyin da aka yi, fizge fizge ta soma cikin radaddi da zafin ciwo

Ammi ce ta riko hannun ta cikin tashin hankali sai kokarin nusar da ita take yi amma ina.. Zuciyar Zuly ta yi nisa daga karshe ma numfashin ta Tsayawa ya yi chak kaman d'aukewar ruwan sama...

_Tirkash....._

_Hey 👋 lovies💞! Show me some love by following me on my Instagram *Mhizzphydo*_ I will really appreciate it if you do!.

_*Vote,comment&share*_
*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A sweet and pitious Romantic love story

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 122*

Birkice wa Ammi ta yi gashi kofan proof ce babu daman a ji su, jijjiga Zuly ta hau yi tana kiran ta cikin tashin hankali

"Waya...! "Ta fad'a had'e da mikewa da sauri, dube dube ta fara tsaban tashin hankali ma bata hango sa ba kuma a fili ya ke daga karshe ma fita ta yi daga cikin dak'in

Wani button da ke manne a jikin bango ta hau dannawa babu kaukautawa nan yen aiki suka soma fitowa da sauri saboda yanayin da ake danna  bell din kaman babu lafiya

Ammi suka hango tsaye tana tana kai kawo ga zufa ya jik'e ta, wajen ta suka nufa da sauri suna tambayan ta abinda ya faru cikin ladabi

Bata iya magana ba sai nuna musu d'akin ta ta keyi nan suka shige suma...

Taimakon gaggawa aka hau bawa Zuly lokacin da suka isa asibiti din, Ammi ta sha kuka har ta gode Allah kuma har lokacin bata kira kowa ba a takaice di kwana Ammi ta yi a kan sallaya tana sallah da Addua mai tarin yawa wa Zuly...

Washe gari...

A mugun gajiye da fargaba ya koma gida saboda jiya da kyar ya iya aikin sa a asibiti saboda gabansa da ke ta fad'uwa wanda ya haddasa mai rashin sukuni adaddafe ya gama komai na sa ya dawo gida gashi Sam basirar kiran gida bai zo mai ba barin ma da Qudsiyah ta ce mai komai kalau.

Gabansa bai gama fad'uwa sanda ya shiga cikin parlour dafe kirjinsa ya yi yana ajiye wayar sa a hannun kujera, juye-juye ya fara yana neman inda Zuly zata bullo saboda a yanda ya san ta in har ba'a gida ya kwana ba to lah shakka ba zata koma bacci bayan rana ya fito ba har sai ta ga dawowan sa

Haurawa ya yi sama cikin rashin jin dadi, straight d'akin Ammi ya nufa, bud'e kofa ya yi wani kamshi ya bugi hancin sa a hankali ya lumshe idanuwan sa,

Wani irin bud'ewa ya yi saboda ganin kaman ya ga datti a d'akin Ammin sa, a hankali ya fara takawa wajen da stain din jinin Zuly ya ke

Chak ya tsaya yana jin kwakwalwar kan sa na tsincewa "Ammi! " ya fad'a cikin rawar murya had'e da bude kofan bayan gida ganin babu kowa ya sa ya fita daga d'akin cikin tashin hankali,

Yana sauk'a ya hadu da wata yar aiki d'auke da basket din abinci a hannun ta ji ya yi gabansa ya fi na ko yaushe fad'uwa cikin sanyin jiki ya tambaye ta abin da ya ke faruwa

Nan ta fad'a masa Zuly ce babu lafiya abinci ma zata kai musu asibiti yanzu, bai tsaya tambayan miye same ta ya cesu tafi saboda yana fargaban abin da zata ce...

Zaune ta ke a kan gado Ammi na bata baki saboda irin kukan da ta keyi, kuka ta keyi sosai kaman ranta zai fita saboda abin da ta ji doctor ya ce musu

Shigowar su Mourad ne ya sa suka kalli kofan lokaci daya da, idanuwan sa bai fad'a ko ina ba sai akan idanuwan su daya yi mugun kumbura

Wani irin kuka mai tsinka zuciya Zuly ta fashe da shi lokacin da ta ga Mourad, cikin sauri ya Karaso wajen su yana kallon Ammi da ta kawar sa fuskarta saboda bata son ya fara jin mummunan labari daga bakin ta

"Our babies! "Ta fad'a cikin kuka had'e da rik'e shi gam, dan runtse idanuwan sa ya yi kafin ya bud'e su wanda a lokacin har sun sauya Kala zuwa ja saboda ya gane abin da ta ke nufi da hakan

Hawayen fuskarta ya soma share mata saboda kukan ta ya fi komai d'aga mai hankali"its ok Allah zai bamu wani kinji? "

Ya fad'a cikin kwantar ma ta da hankali, girgiza kai ta soma yi ya rungumeta a jikin sa wanda hakan ya yi daidai da silalowan hawaye daga idanuwan sa wanda hakan ya sa Ammi sauke ajiyar zuciya saboda tasan rashin hawayen sa zai iya jawo mai matsala gwanda kawai ya yi hawaye din

Goge hawayen ya yi da sauri tare da cire ta ajikin sa yana sakar ma ta da Murmushin yak'e

"Doctor ya ce azo kuma bazan iya barin ta ita kadai a nan ba so ka je! "Ammi ta fad'a a hankali, mikewa ya yi tare da jan hancin Zuly ya ce

"Ki daina kuka kinji? Kin san bana son kukan ki koh?  Kuma kar ki damu in Allah ya yarda next month zan sake baki wani cikin kinji? "Ya karasa in a funny way wanda hakan ya sa Ammi murmusawa amma Zuly kam kallon sa kawai ta keyi saboda ita kadai tasan ya ta ke ji a cikin zuciyar ta kuma tasan Mourad din ma ya fad'a ne saboda ya kwantar ma ta da hankali , ya fad'a ne kawai saboda yana son ta d'auke maganan a ranta while she can hear kukan zucin da ya ke yi!  tana jin yanda ya ke hawaye acikin zuciyar sa

Mikewa ya yi tare da ficewa da sauri,  kasancewan babban asibiti ne yasa ya je wajen counter ya tambayi waye doctor in charge din case din Zuly nan aka yi directing din sa...

Shuru ya yi yana kallon yanda bakin doctor ke motsi, murmushin takaici ya sake tare da mikewa cikin harshen larabci  ya ce"gabadaya maganan da kake fad'a shirme ne saboda matata bata tab'a yin ciki ba balle har azo ga maganar zubarwa! "

Mikewa ya yi yaje wajen wani computer da ke cikin consulting room din tare da kunnawa ya ce"Excuse me!  Hala dai bata fad'a maka ba saboda binciken mu ya nuna cewan har sau uku matar ka tana yin ciki kuma suna kaiwa 4th months daidai ta ke zubarwa and the most baffling thing among it shine wannan karan ba ta sha ba amma kasancewan ta sa ba yasa maganin sticking a mahaifar ta gashi kuma jikin ta ba kowani magani ya ke karb'a ba, you ought to understand everything saboda kai ma doctor ne dukda ya ke ba a wannan fannin ka yi specializing ba amma nasan ka gane! "

Gabadaya tinda doctor ya soma bayani komai nasa ya tsaya chak! Ji yake kaman ya d'ora hannu a kai ya dinga rusa ihu ko zai ji saukin abin da ya keji a zuciyar sa

"But... "

"No thank you! "Ya fad'a tare da ficewa ba tareda ya jira jin abinda doctorn zai sake fad'a ba...

Ko cikin asibitin bai koma ba ya wuce gida saboda yanda zuciyar sa ke mai suya, so kawai yake ya je ya sha maganin sa inba haka ba zuciyar sa zai iya fashe wa kuma baya son ya mutu yanzu har sai ya hukunta Zuly akan kashe rai da take yi...

A chan asibiti kuwa tin suna sa rai ga dawowan Mourad har suka cire rai, ba karamin damuwa Zuly ta yi ba saboda tasan by now ya san komai

Ammi ce tasa aka kawo mata wayarta sannan ta kira su Fakhih ta fad'a musu halin da ake ciki, cikin tashin hankali suka iso asibiti, Qudsiya da Fakhiha kam kuka suka dinga yi barin ma da suka ga yanda Zuly ta dawo lokaci guda sosai ta basu tausayi Fakhih ma san da ya yi kwalla ita kuma Maram jikin ta ya yi sanyin sosai she also couldn't hold back her tears barinma  da ta ga yanda suke ji da cikin, kowa ka tab'a "babies din mu suna hanya..., Allah sarki ashe ba nasu bane tinda har  sun  koma... "

"Ku dubo mun pumpkin dina? Ku ce mai inason magana da shi! DanAllah ku kira mun shi!  I really need to talk him! " Ta fad'a cikin kuka sosai
Chapter 93 · 0% Book details