← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 98

Sashe 56

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusayrah da idonta ke rufe ta bude da sauri tana kallon abinda yafaru, cikin tsananin tashin hankali Yusayrah tafara takowa da frying pan a hannunta kwakwalwarta nason tariyo abinda take gani volume din kukansu dayakaru neh yasata sakin frying pan mai zafi akafan Zuly da idanuwanta ke waje kaman zai fado kasa

Kuka Zuly tafashe dashi tareda daukan frying pan dinta data kawo daga part daga wajen kafarta wanda hakan yayi daidai da shigowan Iqbal cikin gidan

Cakk yatsaya yana kallon abinda yake faruwa awajen, wani ihu Yusayrah takurma daidai lokacin da numfashin Fareeda yadauke cakk while Fareed nakukan Azaba kasancewan mangyadan yafi tab'a Fareeda

"Nashiga uku takashe mun y'a!"Yusayrah tafada tana daura hannunta akai duk zufa yagama wanke mata fuska ga hawaye dakuma majina,

Ai Iqbal baisan sanda yakarasa wajen Yusayrah bah yana kallon Zuly dake rikeda frying pan tana kuka mai tsuma zuciya saikace itace ta watsa mai mangyadan.

Daukan Lifeless Fareeda yayi wasu Hawaye na zubowa daga idanuwanshi,

Hanyar waje yayi da gudu da Fareeda ahannunshi, itakuma Yusayrah tadauki Fareed sai waje

Sakin pan din hannunta tayi tareda binsu waje damugun gudu don karsu tafi su barta

Zata bude kofar gaban motan taji Iqbal nacewa"Zulfa indai aka tabbatar dacewan Fareeda nah tarasu toh nasakeki saki Uku"

Zaro idanuwa Zuly tayi cikin tashin hankali cos itafah ganin datake mawa Fareeda babu arai atare daita

"Bata mutu bah tukunna Zuly kibisu asibitin ayi komai agabanki"tafada wa kanta tana nufan gate din waje cos gani takeyi inhar takoma dauko key to akwai matsala.

Jitayi cikinta na murdewa haka dai tadaure tafice daga gate din tana uban kuka dukda uban tambayan da baba maigadi kemata

Taxi tashiga tafada mai asibitin su, kai tsaye yawuce daita inda sai kuka kasa-kasa takeyi...

_4hours later..._

Zarya sukeyi a bakin kofan emergency room din da'aka shiga da yaran,

Zuly bata minti biyu bata tsuguna bah soboda azabar ciwo dake cinta amma hakan take daurewa, yanzu kam tadaina risgar kuka saidai kuma uban unstoppable hawayen dake silalo mata.

Yusayrah kam tindazu tahada kanta ta bango tana kuka mai tab'a zuciya jefi-jefi kuma Iqbal dake cikin tension na rarrashin ta

Gefe guda kuma en gidansu Iqbal neh dakuma en gidansu Yusayrah wanda aka fada musu abinda yafaru.

Wani irin mugun faduwar gaba Zuly taji lokacin da taga jan wutan gaban operation room din yamutu.

Likitoci neh suka fito sannan aka fito da Fareed da jikinshi ke nannade da bandage,

Girgiza kai Doctorn yayi yace"saidai kuyi hakuri fah cos tin kafin akawo su macen ta rasu"

Wani ihun daya razana duk wanda yake gurun Zuly tayi tareda rike kasar mararta tana zaro idanuwa dayan hannunta kuma tana rike hannun Maman Iqbal dake gefenta

"Take heart!" Likitan yafada tareda wucewa yana jin tausayin Zuly cos azatonshi itace mahaifiyarsu

Jitayi kaman wani abu nazuba ta kasanta, cikin tsananin tashin  hankali take sauke kanta ahankali don ganin miye neh ai basu farga bah kawai suka ga tazube akasa summamiya...

_wayyo!! Allah yajikanki Fareeda_

*DanAllah wattpadians ina bukatan Followers dakuma votes🙏*

#team ZulynMourad
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 82*

_My wattpadians wannan page din naku neh... Much love_

Cikin tashin hankali Maman Iqbal ta tsuguna agaban Zuly tana jijigata tareda fashewa da kuka, nurses ta hau kwalawa kira.

Iqbal Kan Kaman karamin yaro haka yake kuka cos bakaramin so yake mawa yaranshi bah, dubanshi yamiyar wajen Yusayrah, zaro ido yayi ganin yanda duka jikinta yasake

"Nurse!!"yafada yana daukan Yusayrah data shiga biggest shock of her life dalilin jin mutuwar yarta, ahanya yahadu da nurses din cikin sauri aka directing dinsu ward dinda aka shigar da Zuly tareda fara bawa dukkansu biyu taimakon gaggawa.

Zama yayi yahada kanshi da guiwa yana sauke ajiyar zuciya chan Kuma yafashe dakuka tinawa dayayi Zuly neh takashe mishi y'a batareda tunanin komai bah yamike yanufi reception....

   _3 hours later_

Ahankali tafara bude idanuwanta tana Adduar Allah yasa duk mafarki takeyi,runtse idanuwanta tayi tasake budewa ganin Kaman ceiling neh instead of P.O.P, salatin datayi neh yamiyar da hankalin Maman Iqbal dake zaune kanta "Sannu koh."

Tafada cikin tausayawa Gyada kai tayi tareda shafa cikinta tana sakin murmushin wahala, hawayen dasuka zubo mata tashare tace"ya jikin Fareeda"

Ajiyar zuciya Maman Iqbal tasauke cikin sanyin murya tace" ta riga mu gidan gaskiya"

Runtse idanuwanta tayi hawaye na zuba sosai chan Kuma tasake kuka mara sauti tace"Allah sarki Fareeda Allah yajikan ki yasa ke mai ceto ceh"

"Ameen" ta amsa Mikewa tazoyi Maman Iqbal ta tayata

"Nagode" tafurta Kaman ance ta juya karaf idanuwanta yasauka akan bedsheet dinda ya baci da jini, kallon fuskar Maman Iqbal data kawar dakai tana rufe bakinta da khimar, zama tayi abakin gadon cikin sanyin jiki, muryarta narawa tace"yasake fita kenan?... runtse idanuwanta tayi tareda fashewa da Wani irin kuka mai ban tausayi... Allah sarki Iqbal am sorry for not giving u baby"

Mama zatayi magana kenan Iqbal yashigo jijiyoyin goshin shi duk Sun fito rad'au, har gabanta yatako sannan yasa hannu a aljihu yazaro well folded white paper sannan ya damka mata ahannu, "Miye wannan" mama ta tambaye shi kawar da kai kawai yay inda Zuly tayi shiru tana tina kalman daya fada mata lokacin da tazo shiga mota, cikin sauri tahau bude papern abinda tagani neh yasata sakin gigitacciyar Kara tana fadin

"cikina babu yanxu! Aurena ma yamutu, Wani irin rayuwa nazo neh , Iqbal baka min adalci b.."

Kafin takarasa magana yadauketa da wata zaffafiyar Marin dayasa gefen bakinta fashewa "ban miki adalci fah kikace? KI kashe min y'a kice ban miki adalci bah, kina kirana da murderer koh? Yanzu acikin mu waye murderer, you killed my daughter fah my Fareeda"

Yafada cikin kuka Itakuwa sai girgiza kai takeyi tana zaro idanuwa, cikin tashin tace" Wlhy bani nakashe ta bah , Yusayrah ceh Wlhy kayarda dani bazan taba cutar ka bah "

Bango ya nausa sannan yajuyo dasauri yana nuna mata yatsa yace "taya za'ayi uwa da takashe diyarta? in kika sake cewan matatace takasheta Wlhy bazanyi la'akari da cewan kinsamu miscarriage bah zan nada miki najakin da bazaki Kuma daukan Wani cikin bah! Zulfa you're a great misfortune! nayi tunanin baki second chance arayuwa nazama dani har abada , nayi cherishing dinki sosai naso duk abinda kika nuna kinaso Amma gabadaya ke tsanan duk abubuwan danake so kikayi, kina yawan cewan kin tsane ni ashe kiyayyar ma tawuce tunani na tinda har kika kashe min y'a, I regret marrying you , I regret knowing you!!!"

"Stop!! Wai miyeke damunka neh? Tinda nasanka baka tab'a amfani da kwakwalwarka bah, miyesa zan kashe innocent girl kaman Fareeda kawai kayanke hukunci batareda bincike bah, thank God ma yanzu am a free bird tinda har kamin saki har Uku and Wlhy bani nakashe maka y'a bah kaje kayi bincike dakyau and kuma I never regret anything av done to you kobah komai mu family and friends neh, amma karubuta ka ajiye wlhy daga yau kafara dana sani kenan!"

Tana gama fadin hakan tadauki wrappern dake ajiye sannan tashige toilet tareda slamming kofa

"Miyesa ka saketa batareda kayi bincike bah?"Mama tafada cikin takaici bah

"Mama what we see is what we believe! Ahannunta nasamu frying pan din. Ita takashe min y'a" yafada yana yin zaman dirshan akasa

Girgiza kai mama tayi tace" is not all what we see that we believe cos some maybe fiction."

Tin lokacin daya shigo tadawo hankalin ta amma the guilt inside her yahanata bude ido.

Ta tsane kanta sosai yanzu, she can't believe ita takashe diyarta da hannunta ga dayan ma rabin jikinshi yakone,

Runtse idanuwanta tayi hawaye na gangaro wa lokacin data tina Dakhil,

"Nashiga uku nah" tafada dakarfi dayasa sukayi kanta dasauri

Fizge-fixge tafara yi akan gadon tana kuka sosai kaman ranta zai fita tsantsan tashin hankali datake ciki na tinawa da Dakhil har mantawa tayi dacewan akwai mutane adakin tayi tafara fadin"wayyo Allah! Tawa takare nakashe ya'ta da hannu nah adalilin kishin banza wayyo Allah Fareeda na tatafi"

Sororo Iqbal ya tsaya gabanshi na dukan uku-uku, mama neh ma ta tabata tareda kiran sunanta,

Tsit Yusayrah tayi tareda bude idanuwanta fess tasauke su akan Zuly data fito daga toilet rike da leather a hannunta, cikin sauri tamike zaune ko lura dasu mama da Iqbal batayi bah

Takowa Zuly tayi har gabanta kafin tasaki murmushin takaici tace" yanzu Iqbal is all yours Allah yajikan Fareeda"

Chakumo wuyar Rigarta tayi cikin tashin hankali tace" miyesa kika kauce? Miyesa baki bari mangyadan ya tabaki bah? Kinsa nakashe ya'ta miye kikeson nafadawa ubanta?"

"Ce mishi zakiyi kishin mijinki neh yajawo hakan"tafada tana cire hannunta daga wuyarta

"Wlhy kin shiga uku a wajenshi" tafada

"Bayan sakin daya dankara min?" Tafada kaman batasan akan Dakhil take magana bah soboda talura kaman Yusayrah ba acikin hanyacinta take bah

Yusayrah zata sake magana Zuly tafada kafadarta kafin tajuya wajen Iqbal da notin kwakwalwar shi yake barazanan kuncewa jin cewan Yusayrah ce takashe Fareeda bah Zuly bah, murya Zuly yaji tana fadin

"Toh Iqbal kaji koh bani nakashe maka y'a bah, zargina dakayi dafari nayafe maka soboda matsalolin dazasu kunno maka ma ya isa, nabarku lafiya" tana gama fadin hakan tafice daga ward din tana share hawayen fuskarta da hannun da babu komai,

Zama tayi awajen kujera domin hutawa tana kuka kasa-kasa jin kukan yarinya yasata zaro Ido tareda mikewa tana yin hanyar waje sai cewa take "wayyo Babynah!!"....

Kaman wanda aka zarewa laka ajiki yakarasa wajen Yusayrah datake zaro ido cikin tsananin kidima jin katobaran data gama yi yanzu

"You killed her don't you?" Yafada cikin rawar murya yanajin kafafuwan shi narawa

Girgiza kai tafara yi tana matsawa baya hawaye na malala daga idanuwanta

Cikin tsawan da baitaba mata yace"answer me!"

Rike hannushi mamanshi tayi tana murzawa alaman yakwantar da hankalin shi

Fizge hannun yayi yakama kafadar Yusayrah yana jijigata dakarfi, ai kuwa saita sume mai soboda tashin hankali

Yana cire hannushi daga jikinta ta zube akan gadon da bayanta

"Heartbeat!!" Yafada cikin sabon tashin hankali yana rungume kanta akirjin shi tareda sakin wani kuka again.

Mamanshi neh ma taje takirawo doctor aka zo aka fara dubata duk kanta nakan cinyar shi yana shafan kanta sai ajiyar zuciya yake saukewa kaman wanda yayi gudu saukin abin ma har sunkai Fadeela makwancin ta...
Chapter 56 · 0% Book details