← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 98

Sashe 91

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Ammi kam ji su ke kaman su yi tsuntsu su gan su a gaban pregy Zuly,  sai tambaya suke a kan yaushe zasu dawo ya ce musu sun kusa,  gashi sai so suke suyi magana da Zuly amma ta ki yin magana ko kunya ta ke ji ko kuma miye ne ban sani ba!

Har suka isa _Rojenny Tourist Village_ Zuly ba ta yi magana ba amma gabadaya bai lura saboda tsananin murnan shima zai zamo uba da yake yi

Sauk'a ta yi daga cikin motan lokacin da suka isa daidai bakin apartment na su da ake bawa couples , wajen so silent sai irin karan tsuntsu da ba za'a rasa ba kuma jefi-jefi ka kan hango masoya masu shan iska a waje suna zaune a bin su wasu kuma suna irin guje-gujen masoya dinne kuma komai a cikin class da nutsuwa suke yi ba bu wani hayaniya saboda akwai wa'inda ba su son ana takura musu, in ma kana son enjoying din wajen sai daddare saboda akwai entertainers Kala Kala sai wanda ka zab'a.

Da gudu ta shige cikin apartment din su inda shi kuma ya zaro ido cikin tsoro tare da mara ma ta baya da saurin yana mai cilla wa wani key da alaman shi zai d'aga motan daga wajen

"Miye haka ki ke gudu baki san yanzu ba ke kadai ba ce? "Ya tambaya cikin lallashi, bai hankara ba dai ji yayi ta fashe da kuka kaman wacce aka daka

Cikin tashin hankali ya karasa inda ta ke tare zaunawa a gefen ta ya ce"Subhanallah! Miye same ki? "

Rumgumesa ta yi da sauri cikin kuka ta ke cewa"dama zan sake yin wani cikin? Dama nima da rabon zan ga kwai na? Wallahi na cire rai da samun ciki a rayuwata"

Cikin rashin fahimtan abin da ta ke nufi ya ce"miye kike fad'i ne haka! Ko farin ciki ne yake saki fad'in abubuwa? "

Gyada kai ta yi da sauri har lokacin kuma hawaye bai bar fitowa da ga idanuwan ta ba, hannun sa ta daura a maran ta cikin muryan kuka mai had'e da farinciki wanda daga gani a kwai abin da ya ke cin ran ta  ta ce" our babies! "

"Babies? "Ya tambaya yana goge hawayen fuskarta , gyada kai ta yi tana jan majina ta ce

"Eh mana Babies! "

"Ya aka yi kika san ba guda biyu ne a ciki? "Ya tambaya yana d'aura ta a kan cinyar sa, zaro idanuwa ta yi tare da girgiza kan ta kaman taga abin tsoro ta ce

"Guda uku ne ba biyu ba! "Wani irin dariya ya fashe da shi saboda sosai ta ba shi dariya,  turo baki ta yi tana tana kokarin mikewa daga kafan sa ganin kaman ya miyar da abin da ta fad'a abin dariya

Dawowa da ita ya yi ya ce"am sorry Mine amma kin san ba za ki iya haifan uku ba ko!? "

Kallon sa ta yi ta ce"why!"

"Saboda sun miki yawa? "

"What Allah ko guda.... Tsayawa ta yi tana lissafi da hannun ta kafin ta ce.... Ka ga uku sau uku tara sai kuma ga wani ukun... Ta fad'a tana tab'a cikin ta tace.... Duka sun zamo sha biyu, kaga ko sha biyu zan haifa a lokaci daya bazan girgiza ba! "

Zaro idanuwa ya yi ga kuma dariyan da yake cin sa ya ce"ban da sha biyu a lokaci daya yarinya! Kin d'auka haihuwa shan ruwa ne ko kuma love making ne? "

"Dagaske fa! "Ta fad'a looking so serious saboda da za'a ce wa'inan lost babies din ta na gidan Iqbal ta haifo su to baza ta k'i ba

"Wait, tukunna ma uku sau uku tara da kika lissafo a ina kika samo su?"ya tambaye ta yana mai tsura ma ta idanuwa

Ya mutsa fuskar ta ta yi alaman ba ta son maganan ta ce"na fara jin yunwa fa! "

Mikewa ya yi da saurin tare da zaunar da ita ya ce" wani abinci ki ke so? "

Murmushi ta yi cikin jin dadi ta ce"ni fa wallahi Masa da kuma Kunnun gyada na ke so!"

"Masa da Kunnun Gyad'a kuma?"Gyada kan ta tayi tana zama a kan kujera ga ajiyan zuciyan da ta ke saukewa kaman wacce ta yi gudun race

"Toh ki taimaka ki ci wani abu tukunna! Just name anything da kaina zan dafo miki! "

Lumshe idanuwanta ta yi tana tunanin abin da za ta ce,chan ta bud'e idanuwan ta ta ce"zan ci tuwo da miyan kuka kuma kaman yanda ka ce kai zaka dafa mun da kanka! "

Zaro idanuwa ya yi jin abin da ta ce, cikin sanyin murya ya ce"Mine, kinsan ban iya dafa irin wa'inan abincin ba! Please ki fad'i wani abun"

Hannu ta d'ora a kai tare da fashewa da kuka mai tsuma rai kaman wacce a ka mawa mummunan abu....

_Hey 👋 lovies💞! Show me some love by following me on my Instagram *Mhizzphydo*_ I will really appreciate it if you do!.

_*Vote,comment&share*_

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A sweet and pitious Romantic love story

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 121*

A tsorace ya ke kallon ta har yen dube-dube ya fara irin yana neman abin da ya sa ta kuka dinnan, volume din kukan ta ta kara cikin sauri ya zauna a gefen ta tare da jawo ta jikin sa cikin taushin murya ya ce

"DanAllah mine ki yi shiru! "

"Oho! "Ta fad'a a shagwabce har da make kafada tana mai cigaba da kukan ta, rasa abin yi ya yi aikuwa caraf ya chapki bakinta

Tirjewa ta fara yi saboda right away ba shi ta ke bukata ba, ganin yanda ta keyi ya sa shi sakin ta ba don ransa ya so ba!

K'awar da fuskarta ta yi saboda yanda ya kure ta da jajayen idanuwan sa, hannu ya sa ya juyo da fuskar ta nan ta runtse idanuwan

Dariya ya yi yana jan karan hancin ta "wayyo yunwa! "

Ta fad'a kaman zata yi kuka, ajiye ta ya yi a kan kujera tare da tsugunawa a gabanta ya ce"mine please na had'a miki wani abun daban? "

Mak'e kafada ta yi"toh muje ki taya ni! "

"Ni bacci na ke ji"ta fad'a tana kokarin kwanciya akan kujera, mikewa ya yi , cikin mutuwar jiki ya fara tafiya ganin ta rufe ido

Tana jin ya tashi ta bud'e idanuwan tana kallon bayansa, gani kawai ta yi ya tsaya, cikin sauri ta rufe idanuwan ta, karasowa wajen ta ya yi yasake tsugunawa, a hankali ya ce

"Fruity!" Dum gaban ta ya fad'i saboda tasan miye ya ke nufi in ya kira ta da hakan

"I miss you fa! Please in kin gama cin abinci ko round daya ki bari muyi! "Ya fad'a cikin sanyin murya yana shafa sliky fuskar ta

Wani tausayin sa ta ji ya kama ta saboda rabon su da suyi making love yanzu kwana hudu kenan ko rage zafi kuma bata bari ya yi saboda gabadaya yanzu bata son yana ko tab'a ta ne amma tasan abu ne mai wuya hakan ya yiyu barin ma da ta da ri ga ta saba mai da jikin ta, tana jin lokacin da ya mike a hankali ta sake bud'e idanuwan ta tare da raka sa dasu, ajiyar zuciya ta sauke tare da gyara kwanciyan ta lokacin da ya shige kitchen.

Da taimakon Google ya samu ya tuka ma ta tuwo din har da miyan kuka duk da ba karamin wuya ya sha ba amma ya ya iya tinda shi ya sata a condition din da ta ke

Yana tsaye ya hard'e hannayen sa a kirjinsa yana kallon yanda ta ke shan baccin ta, a cikin baccin ta ta ji kamshi ya cika ma ta hancin a hankali ta hau bud'e idanuwan ta,  caraf ta sauke su a kan sa

Da sauri ta mik'e tana dada bude sleepy eyes na ta da kyau "kar dai baka gama dafawa ba? "

Ta tambaya tana Adduan Allah yasa ba mafarkin hadadden kamshin tuwo da miyan kuka ta keyi ba

"Kalli nan! "Ya fad'a yana nuna mata stool da ya ajiye abinci, wani irin yawu ta had'iye tana lashe labban ta cike da kwad'ayi

Jawo stool din ta yi gabanta sannan ta fara bud'e rufeffen plate din gaban ta, wani irin lumshe idanuwa ta yi saboda kamshin da ya bugi hancin ta

"Ruwan wanke hannu! "Ta fad'a kaman an fixgo maganan daga bakin ta

Dan zaro idanuwa ya yi tare da juyawa da sauri yana fad'in "Oh sorry! "

Chan sai gashi ya dawo da bowl a hannun sa, mik'a ma ta ya yi ta wanke hannun ta sannan ta yi bismillah

Zama ya yi a gaban ta tare da kura ma ta idanuwa cike da dunbin sha'awarta sanda tayi kusan loma uku kafin tasan ta mai tayi

Murmushi ya yi yana fad'in"ke dai ki cigaba da cin abinki"

Bata ma wani ci dayawa bah ta ture sauran, dole shi ne ya ci sauran saboda daman na cikin mutum daya ya yi googling

Kallon sa ta yi ta ce"but I thought ka ce baka iya dafawa ba! "

Phone din sa ya mika ma ta, cikin rashin fahimta ta karb'i phone din ta yi tare da duba screen din nan ta ga ashe searching ya yi

"Thank you so much Pumpkin! "Ta fad'a tana mai murmushi, gyada kai ya yi kawai saboda ba halin magana a lokacin dalilin abincin dake cikin bakin sa

Yana gama cinyewa ya kai plates din kitchen nan ya ga ashe bai gyara in da ya b'ata bah ai nan ya hau gyara wa wanda hakan ba karamin bata mai lokaci ya yi bah

Zuly da ya ji shurun ya yi yawa ta bi bayansa nan ta tarar ashe gyara yake yi, tsayawa tayi daga bakin kofa tana kallon sa

Sanda ya gama kafin ya juyo ya ganta, ware hannun sa ya yi alaman tazo gare sa, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta nufi wajen sa tare da rungumesa
Chapter 91 · 0% Book details