← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 98

Sashe 45

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana idarwa Lutfiya tashigo da cup a hannunta, wajen ta takarasa tareda zama agefenta tana Mika mata Cup din,

Kawar da kanta tayi tace"yau bah ranan shan tea bane,kihado min _cappuccini chiaro_"

"Pardon?" Ta tambayeta cikin neman karin bayani cos tinda take bata tab'a Jin wannan sunan bah

Yamutsa fuska tayi tace"_wet cappuccino_"

"Aww sai yanzu naji zance"tafada tareda barin tea din akan stool

Kwanciya tayi akan sallayan tana sauke ajiyar zuciya...

Bayan tadawo neh ta Mika mata tareda balla mata pain reliever,

Dakyar Zuly ta yarda tasha nan da nan bacci ya kwasheta, kara karfin AC din dakin tayi takoma parlour abinta,

Sai wajen Azahar Zuly ta tashi kuma har lokacin Lutfiya na nan kuma lokaci zuwa lokaci take zuwa duba Zuly dake bacci...

Wanka tasake yi tareda gasa jikinta dakyau cos dazu taji dadi sosai.

"Nagode Anty"Zuly tafada cikin sanyin murya, shafa kanta tayi tace don't worry dear,

Sosai Zuly taci abincin da Lutfiya ta girka tana mai tunanin irin abinda zata saka wa Lutfiya dashi, chan ta nisa tace

"Wai nikam Anty kinsamu anmiki wannan zanen kuwa?"

Girgiza kai tayi tace"a'a munajiran muji ance Miss ZULFA ta warke neh saimu sake komawa"

"Ohk, DanAllah akwai wani daki tawajen parlour in kika shiga zakiga drawing board da wasu tarkace kidan kawo min"

Batareda Lutfiya tayi magana bah ta fice , sai gata tadawo da drawing board din ajiyewa tayi agaban Zuly tana tunanin miye Zuly keyi da drawing board kaman wata architect,

"Bari nayi wanka Sweetheart dina yakusa zuwa dauka na" tafada tana shigewa toilet.

Kafin tafito har Zuly tagama zanawa ta nade shi tareda sawa acikin jakan Lutfiya din kafin takwanta abinta,

"Ji tsiya kinsa na dauko miki abu kuma bakiyi komai dashi bah" Lutfiya tafada lokacin data leka board din

"Yamutsa fuska tayi tace"Anty wai wannan turaren aina kika samo shi?"

Mikewa tayi zuwa wajen wani trolley din dake ajiye agefen wardrobe"Har kin tinamun ma naganshi dayawa in zan tafi zaki bani aciki cos yamin dadi sosai...kardai bakisan dashi bah?"

"Wlhy Anty narasa awani trolley yake neh shiyasa"tafada da murmushi afuskarta cos saitaji kashi 60 na damuwarta yakau,

"Anty kidauka duk yanda kikeso Ammi neh tabani lokacin da mukaje Dubai" tafada cikin farinciki

Dauko trolley din Lutfiya tayi tayi har gaban Zuly sannan suka fara fitowa da abubuwan dayake ciki,

"Siyah!!!"tafada da murmushi afuskarta tareda daukar cute paper bag din,

Dan portable Jewelry pack tafara cin karo dashi, budewa tayi kusan atare sukace Wow

"Wlhy yamin kyau"Lutfiya tafada tana daukan wayanta domin daukan shi hoto

"Basaikin dauka a hoto bah nabaki shi"tafada tana sa pack din akan cinyar Lutfiya tareda zura hannunta cikin bag din soboda papern data hango aciki

"Ai bazamu yi haka dake bah" tafada tana kokarin miyar mata

"Soboda miye Anty? Soboda banda abinda zan baki?"tafada tana kureta da Ido

"No kawai dai naga kema kinaso neh"

Dariya tayi tace" lahh inada irinshi fah amma yafi wannan cin tuwo"

"Miye kuma cin tuwo?"

"Yafishi jiki toh ma'ana yafi wannan kato"

"Toh nago..."

"Shihh kin fi haka awaje na"ta katse da fada tana warware papern hannunta,

Zaro Ido tayi da tsananin mamaki tana kallon abun dayake cikin papern,

"Pls duba min wannan abun miye aciki cos I think idona yafara samun matsala"tafada tana nunawa Lutfiya papern hannunta...

        ★★★★★★★★★

_German Heart centre Bremen: cardiologist. Building 39 Dubai Healthcare city- 3rd floor_

Anyi nasarar operation din Mourad,yanzu mah haka anfito dashi yana bacci,

Shafa kanshi dake kan cinyarta takeyi cikin shaukin so da kauna, she can't wait Mourad ya tashi ta nuna mai true love,

Wayar dake cinyarta neh yayi kara,cikin mamaki take kallon numbern dake yawo akan screen dinta

Sanda ta bari wayan ya katse tashiga Google domin duba code din wata k'asa ceh take kiranta

"Nigeria!!!" Tafada tana lumshe idanuwanta 

Karar da wayan yasake neh yasata rike saitin zuciyarta soboda yanda bugun shi ya changa ga wani tsoro tsoro data fara jih dukda tasan waye ke kiranta,

Wani yawu mai daci ta hadiye kanta nadaukan chargi shahada tayi sannan ta runtse idanuwanta tareda daga wayan hannunta na karkarwa

Cikin sanyin murya tayi sallama tareda aza jarumta a muryar ta tace....

_toh fah who's calling Siyah neh??manage, still recovering..._

#team ZulynMourad 
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*
*ZULFA*

@MHIZZPHYDO 

A Sweet and pitious Romantic love story 

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 68* 

Cikin sanyin murya tayi sallama tareda aza jarumta a muryar ta tace"sai yanzu kika ga daman congratulating dinmu?"...

Kallon Lutfiya tayi kafin tace"kina lafiya" domin ita batasan akan miye zatayi congratulating dinta bah

"Ai dole ki gaishe ni tinda ina auren Mou dinki"

Wani irin faduwan gaba Zuly taji nan da nan idanuwanta suka kawo hawaye cikin rawar murya tace"ina yake"

Dariyar rainin hankali Siyah tayi tace" dama kidaina damun kanki akanshi cos yanzu baya yinki ,yanzu yadaina sonki shiyasa kikaga ma ko neman ki bayayi so focus on your husband not someone else husband kinji Zuly?"

Izuwa yanzu Zuly tasake kuka mara sauti tareda rike hannun Lutfiya gam kaman her life depends on it,bakinta har karkarwa yake tace"kidaina cewan yadaina Sona Siyah"

"Taya za'ayi nadaina fadin abinda shine gaskiya? Yanzu ma don yana wankan sunnah bah dakinji muryar shi cos kaman chewing gum haka yake agareni, wlhy he's one in a million cos ya iya soyyaya,making love, the sweetest part is that he's so sweet in be..."

Jefar da wayan Zuly tayi har yana tarwatsewa da karfi tace"No...." tareda kama kanta dake barazanar fashewa cos jitake maganganun Siyah na kokarin tarwatsa mata kwakwalwa...

Ajiyar zuciya Siyah tasauke Jin ta rikita mata lissafi, tsaki taja tareda lumshe idanuwanta tace" Shegiyar yarinya ai daga yau babu ke babu shi cos _he's mine_"

Bude idanuwan dazatayi idonta yafada acikin na Mourad nan da nan jikinta ya dau b'ari ,

Da jajayen idanuwan shi yake kallonta kafin ya mike daga kan kafarta dakyar,

Hannu yamika mata ahankali yace"bani wayan"

Hannunta na rawa tabashi wayan , call log dinta ya buda cos tin lokacin data Kira sunan Zuly yafarka kawai Jira yake tagama haukarta yamata magana amma kuma kalmar Shegiyan da Siyah tafada neh ya bata mishi rai shiyasa ma yabude idanuwan shi,

Numbern Zuly yayi dailing amma cikin rashin sa'a ko shiga bayayi,

Mikawa Siyah wayan yayi yace"get lost and don't you ever in your life show me your face again"

Cikin sauri Siyah ta tsuguna tace" am really sorry sweet bazan sake bah, kaga ma bari na kirata nabata hakuri" tafada tana danna numbern ta ga hawaye duk ya wanke mata fuska

"Don't let me repeat myself" yafada yana lumshe idanuwanshi cikin son b'oye bacin ranshi akan abinda tayi cos yasan dole yanzu Zuly tana chan tana rizgar kuka akan karyar da Siyah ta shararo mata, tashi tayi jikinta asanyaye tana kallon shi ganin idanuwanshi a lumshe yake yasata jan yenmatan kafafun ta zuwa waje a hakan ma tanayi tana waiwayowa.

Tana tuki tana kuka harta Isa gidansu Mourad din,tana shiga tafashe da kuka mai tsuma rai,

Cikin sauri su Ammi suka sauko jikinsu na rawa , cikin hada baki sukace "miye sameshi?"

Wani kukan daya sake rudar dasu tasake fashewa dashi tana mai Jin haushin abinda suka fada cos ita anata tunanin cewa yakamata suyi _Siyah miye sameki bah miye sameshi bah_

"Wai miye neh in-law" Fakhih yatambaya yana daukan car key dinshi

Cikin shesheka tafada musu duk abinda yafaru,tsaki Ammi taja tace"shine kika daga hankalinki?, Amma kuma maganar gaskiya abinda kikayi bai dace bah amma zan san nayi.... Bari na dauko khimar dina saimuje hospital din"

Gyada kai sukayi Fakhih yakalleta yace"sister in-law you were too fast wlhy"

"Am sorry" tafada murya asanyaye, girgiza kai kawai yayi tareda ficewa...

        ★★★★★★★★

Kuka takeyi sosai kaman ranta zai fita, cakk ta tsayar da kukanta tana dube-dube,

Tashi tayi dasauri ta jeh inda wayarta yake cos harta manta da wani ciwon datake dashi tsantsan tashin hankali, dauka tayi tana kallon yanda wayanta ya tarwatse , wajen kunnawa tahau dannawa ko zaiyi amma ko alaman kunnuwa baiyi bah,wani kuka tafashe dashi tafara kokarin sim dinta tana fadin

"Wlhy karya takeyi!!!"

Riketa Lutfiya tayi tareda rungumeta tana bubbuga bayanta , 

"Wlhy karya takeyi bai manta Dani bah nasan yanada uzuri"tafada tana kallon Lutfiya

Gyada kai Lutfiya tayi idanuwanta na kawo kwalla tace" erh karya takeyi"....

      ★★★★★★★★★

_DUBAI_

_A week later_

Zaune suke akan sofa bayan ansallamo su daga Asibiti, kowa da abinda yake sak'awa acikin zuciyarshi, shigowan Siyah neh yadawo da hankalin su,

"Get out"yafada cikin sanyin murya

"Am sorry sweet,wlhy kullum sainayi dailing numbern ta amma baya shig.."

Bata karasa bah yace" I said you should get out"

Kallon Ammi tayi tana hawaye ,gyada mata kai Ammi tayi alaman taje, fita tayi tana jin kunci acikin zuciyarta,

"Mourad zamuyi magana"Ammi tafada fuska ba wasa

Kallon Ammi yayi kawai tareda jinjina bayanshi ajikin sofa tareda kurb'an ruwa 

"Akwai aurenka akan Qudsiyah"

Wani irin shakewa yayi da ruwa nan da nan yafara tari kaman ba gobe, dasauri Ammi takarasa wajen shi tana buga bayanshi, matsawa yayi daga wajenta alamun bai bukatan sympathy dinta,

Zaman dirshan yayi akasa bayan tarin ya lafa yana sauke ajiyar zuciya gakuma hawaye na zubo mishi, har wani Jiri Jiri yakeji daga zaunen dayake,

Zama Ammi tayi agefen shi tace" soboda kai muka aura maka ita"

"Ni nace inasonta?"yatambaya yana runtse idanuwan shi cikin tsananin bacin rai

"A'a dear, you were sick kuma kanada bukatar hakan shiyasa babanta yace adaura muku aure tinda yar uwarka ceh... She loves you tinda kake jinya itake kula dakai, tayi maka kokari sosai , she quit her job soboda kai, bata da lokacin kanta duk soboda kai amma yanzu kace ta tafi?... I  don't think ka mata adalci.... Pls move on with your life, Yanzu Zuly is no longer yours try to... To forget her"

Arikice yake kallon ta yace"bazan iya mantawa daita bah,itace rayuwata Ammi .... Am such a fool Ammi , nice najawo komai cos bantaba cemata ina kaunarta bah saidai nace inasonta, I thought wannan kalman duk daya neh ashe bahaka bane, Ta fadamin cewa SO is LIKE while KAUNA is LOVE, natabbata da cewa nayi ina kaunarta da yanzu tana Matsayin Zulyn Mourad dinta, Ammi am hating everything wlhy bansan yazanyi bah"

"Addua zakayi"
Chapter 45 · 0% Book details