← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 98

Sashe 16

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"InshaAllah Sai na mawa Yay Mou dina wannan abinci inyazo"tafada tana kwashe plate din tareda ficewa.

"Umma bari nashiga cikin fadan ko Malam yafito" ya fada hade da tashi,hannunshi yasa a aljihu sannan yayi ficewarsa, daman kuma Umma tashige cikin daki...

```1:50pm```

Fitowarta kenan cikin Erin Embellished Denim Mini Skirt da Missoni Wave Textured Top kafanta cikin Miu Miu Crystal Detail Skate Sneaker Ga kamshi Sai tashi daga jikinta yakeyi.

Iya haduwa fah ta hadu.

Kallon ta yakeyi daga balcony yana mamakin yanda akayi yanzu tadaina kunya, yanzu da irin wannan kayan take yawo daga inda ta taho kenan.

Sosai ranshi yabaci kuma ya daura duka laifin akan Umma wai itace bata taka mata birki amma InshaAllah yakusa yin maganinta.

Cikin motar ta tashiga akayi gaba daita, kallon koina takeyi cikin nutsuwa wani dadi takeji yana ziyartar zuciyar ta.

Daidai wani katon industry din cikin garin ta kafe da ido.

Lumshe idonta tayi cikin son tariyo abubuwan da bazata  taba manta da yanda komai yafaru bah.....

*Asalin su*...

*ZULFA*ya'ce ga Malam Abubakar Umar wanda yakasance Kani ga Alhaji Muhammadu Kabir Umar(Malam,wato sarkin Azare) sunan Mamanta Salamatu neh wance takasance yaya ga Ramatu(Umma kenan).

Ramatu da Salamatu sun kasance  yaya da kanwa kuma babansu abokine ga Babansu Malam.

Suna mugun son junan su sosai hartakai ga babu inda zaka ga daya baka ga dayan bah.

In daya na rashin lafiya to makawa dayan mah bata da lafiya.

Tin suna yara Umma takamu da matsananci son Malam Abubakar amma zurfin ciki ya hanata sanar da yar uwarta dukda basu boyewa juna sirinsu.

Ashe awajen Salamatu mah suna chan suna soyewan su da Malam Abubakar amma itama ta boyewa dayarta harta kai ga bashi izinin turo magabatan shi.

Yana turo magabatan shi akace anbashi ita kuma atake aka sa ranar aure.

Lokacin da Ramatu taji wannan zance bakaramin kaduwa tayi bah.

Taso tasanar da yayarta abinda ke zuciyar ta amma ganin irin murnar da Salamatu keyi yasa jikinta yin sanyi tareda barin komai ahannun Allah cos tasan ko banza masoyinta nason abinda take so.

Sai karewa takeyi kaman kudin guzuri ta rame sosai duk alokacin da aka tambaye ta abinda ke damunta toh amsan ta daya zatayi kewar yayarta.

Har daki tasa araba musu wai tin yanxu take son tasaba da rashin yayarta din sosai suka tausaya mata.

Itakuwa Salamatu bata wani damu sosai bah tinda zataje gidan masoyinta amma kuma in taga yanayin kanwarta saitaji jikinta yayi sanyi sosai.

Umma kam dalilin sawa araba musu daki bai da nasaba kukan daren datake yi.

Har kwantawa rashin lafiya takeyi, sosai mamansu ta lura ba zallar tafiyan Salamatu bane yake karar da yarta amma da ta tuntube ta amsan ta daya.

Sosai lokacin biki ya yanko kwana inda sauran kwana uku daurin aure.

Amarya tayi kyau takara cikowa sosai itakuwa Umma banda ramewa babu abinda takeyi duk tafice hayyacinta ta rage walwala,ta rage fita fara'an mah tadaina yinshi inkaganta saika tausaya.

Kwatsam ranar daurin aure labari yazo mata cewan andaura aurenta mah, abin ya mugun daga mata Hankali soboda da bata tsanmaci hakan bah.

Bata gama kaduwa bah saida taji wai da Muhammadu Kabir aka daura aurenta(Malam).

Sumewa tadinga yi tana farfadowa soboda daman chan basuda jituwa  atsakanin su.

Sosai iyayensu suka nutsar daita akan sunyi akane soboda su zauna kusa da kusa da yar uwarta tinda daman soboda rabuwan su tazamo mara walwala...

Aranar Salamatu ta tare inda suka sha amarcin su batareda damuwan komai bah.

Adaren ranan akayi asibiti da Ramatu soboda rikicewan da jikinta yayi sosai.

Asibiti aka tabbatar musu da Ramatu na dauke da ciwon zuciya sosai hankalin iyayenta yatashi.

*A month later*

Zaune take akan tabarma tana shan kunu cos yanzu tafara jin relief azuciyar ta dukda haryanzu babu abinda ya rabu acikin kaunar shi datake yi.

"Kije ku gaisa da Mijin Salamatu" wani irin bugawa kirjin ta yayi nan ta hau Tari ba kakautawa.

Sosai mamansu ta rikicewan  da yanayin datake cikin.

Jin tari acikin dakin Kanwarta neh yasa hankalin ta yatashi cikin sauri ta nufe kofa domin fita,daidai kofar dakin Ramatu din tayi turus SAKAMAKOn abinda taji inda Ramatu tace

"Mama ya zanyi da rayuwata neh wai??,miyesa Sai alokacin danafara wartsakewa zasu zoh?? Ko sunzo su tasar minda ciwo na neh??, Umma kice su tafi kar shaidan yasa na aikata abinda ba shine bah" tafada cikin kuka

Sosai jikin Mamansu yayi sanyi numfasawa tayi sannan tace"bangane abinda kike nufi bah"

"Umma nah tinkafin nasan kaina nakeson  mijin Yar uwata, ina mugun sonshi mama"

Jitayi kafafun ta bazasu dauke ta bah ,cikin sanyin jiki tabar wajen tana mai jin kishin yar uwarta acikin ranta.

Daidaita nutsuwar ta tayi kafin tashiga cikin inda yake, murmushin daya sakar mata neh yasa ta sune kanta kasa cikin kunya tana jin sabon sonshi na huruwa cikin kohon zuciyar ta.

Bayan Umma tagama mata nasiha tafito cikin sanyin jiki tana mai jin tausayin Ramatu sosai acikin ranta soboda itama tasan Zafin so.

Cemusu tayi Ramatu tayi bacci , cikin jin haushin mama Salamatu tace"bacci ko munafurci??"

Akidime mama take kallon ta cos tinda take bata taba jin daya ta fadawa daya irin wannan kalman bah koda kuwa acikin wasa.

"Ayyerh in ta tashi ace ina gaishe ta"Abubakar yafada cikin sakin fuska.

Murtuke fuska Salamatu tayi jin abinda yace cikin sauri tace wa maman su sun wuce.

Mama kam ta kasa magana don mamakin chanzawar halin yar tata...

Kowani jumma'a sai Malam yazo wajenta amma daga gaisuwa Sai kowanne su yayi shiru wai soboda yanxu mah don tana dan jin nauyin shi.

Kwanaki sunja inda ake neman wata uku amma haryanzu Ramatu bata tare bah...

Sosai tadan miyarda jikinta kyawun ta yafara dawowa mama kuwa bata fasa bah don kullum saita mata nasiha mai ratsa zuciya ga gyaran jiki da ake mata soboda sauran kwana biyu ta tare...

Abin mamaki in Salamatu tazo ko gaisuwan ta ma dakyar take amsawa shi din ma da hanci.

Sosai ta damu hartana tambayan ta ko laifi tayi amma amsar dayace"nace miki kin min wani abu neh??"

Fadawa mama tayi akan sabon halin da Salamatu ta tsiro dashi.

Nan kuwa babansu ya aika aka ki....

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 29*
         *Zulyn Mourad*
Nan kuwa babansu ya aika aka kirawo ta daga gidanta daddare kuwa saigata tazo.

Kamar kodayaushe yauma haka ta kasance Ramatu ta gaisar da Dadanta amma usual da hanci ta amsa yaukam ma harda tsarabar harara kuma agaban mamansu.

Zuwan babansu neh ya nutsar da su inda baba yatambaye Salamatu "wai koda akwai abinda Ramatu ta mata"

Cikin kuka Salamatu tace"baba wai don wannan yarinyar bata da hankali har ta iya fadin cewan mijina takeso!!"

Afirgice suke kallon ta inda baba ya cika da mamaki cos kokadan baida wannan labarin.

Miyarda kallon shi yayi ga Ramatu Wanda take kallon cikin idon Salamatu.

Sosai ranta ya baci ace ita dayakamata tadaina mata magana batayi bah sai ita.

Gyaran muryan da baba yayi neh yadawo da ita daga tunanin da tashiga.

"Baba danAllah amata iyaka da zuwa wajena dakuma wajen mijina"

Bacin rai dabata shiga irin bah tajita aciki bata San lokacin da tace" wlhy kin bani kunya,yanxu akan namiji ki gaba da yar uwarki wanda kuka fito ciki daya daita.

Kinsan Allah da inada niyar aurenshi wlhy da yanzu an wuce wajen cos nafiki Sonshi!!!

Wani irin mari Salamatu ta kwashe ta daita dukda marin yashigeta ba hana ta daina magana bah.

"Nadauka zamu iya sadaukar da farincikin mu wa juna in daya yanuna yanaso. Bansani bah Ashe ni kadai nake wannan tunanin,

Kin bani mamaki sosai ace soboda namiji kika mare ni??  Nagode adda  amma in har maganganu nah sun bata miki rai kiyi hakuri bada niya nayi hakan bah kuma ni har abada bazan iya yin gaba dake bah soboda son danake miki,zan Na gaishe ki kaman da amma kisani kin zubda girman ki  a wajena.

Tana gama fadin hakan tayi cikin gida dagudu.

Sosai jikin Salamatu yayi sanyi takuma ji kunyar abinda ta aikata sai dada sune kanta takeyi akasa(daman Salamatu akwai kunya sosai ita kuwa Ramatu hmm saidai Allah ya shirya zamuce).

Baba neh yayi gyaran murya sannan yamata nasiha cikin rashin kwarin jiki cos shima jikin shi yayi sanyi kallau.

Tana tashi tayi cikin gida itama, abakin kofa ta tsaya tana karewa yar uwar ta kallon cikin tsantsan tausayi.

Jin alamun ana kallon ta yasata miyarda jajayen idanunta wajen.

Da murmushi asamar afuskarta take fadin"ya kika yatsaya abakin kofa? kishigo mana adda"

Cikin sanyin jiki ta karasa inda kanwarta take, ba kazo ba tsammani kawai saitaji ta ajikinta.

Rungumeta tayi tsam ajikinta tareda sakin kuka.

Itakam Ramatu zuwa yanzu bata iya kukan cos har ta gaji dayin kukan.

Shafa bayan ta tadinga yi ahankali.

Cikin shesheka tace"ki gafarce ni kanwata karki daina ganin girmata, bansan miyesa na miki hakan bah kiyafe wa Addan ki"

Hannu Ramatu ta sa mata abaki ta girgiza mata kai alaman tayi shuru cos harga Allah batasan abinda zata iya fada mata bah...

Ranan da aka kai Ramatu dakinta aranan Malam ya angwance batareda yayi la'akari da irin kukan da takeyi bah...

*Three months later*

Laulayi sosai Salamatu keyi dukta zabge ta yamushe kaman cinyeyen slippers sosai take shan wuya inda Ramatu dakuma Rumaisa'u dakuma danta mai shekaru 12 suke kula daita.

Sosai Dan Rumaisa'u yakeson cikin jikin Salamatu harya kai ga yace in mace ta haifa zata zamo matarshi.

Dayaga Salamatu ta share zancen saiyaje wajen su Malam yace musu shikam yanason abinda Salamatu zata haifa cikin dariya irinta manya akamishi alakawarin hadasu aure nan gaba.

Rumaisa'u ta girme su sosai kuma ta kasance mata ga Abdullahi wanda yake aboki ga Malam dakuma kaninshi Abubakar soboda gabadaya kusan sa'ani neh amma Abdullahi yadan girme su (dayake Malam da Abubakar yen Uba neh).

Abdullahi yayi auren wuri cos ya kasance mabukaci gudun karya fada ga Halaka shima Malam baiyi kasance aguiwa bah yace yanaso bah bata lokaci suka mawa babansu Malam magana wanda ya kasance babban abokin babanshi.(kafin su rasu kenan)

Tsoffin sun yaba da kokarin dasukayi ganin sun yakice kunya. Nan aka tambaye su kosuna da wanda sukeso nan sukace sunadashi.
Chapter 16 · 0% Book details