← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 98

Sashe 46

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sau nawa kuma Ammi?, Kullum saina tashi sallar dare namikawa Allah bukatuna, kullum Addua shine Allah ya mallaka min Zuly, nagaji Ammi"

Yafada yana kuka sosai kaman karamin yaro, ganin yana rike kirjinshi neh yasa Ammi jijiga shi tace"keep quit inada solution"

Tsit kakeji yayi shiru harda goge hawayenshi,

"Addua zamu cigaba dayi cos Addua baya yawa kuma Allah maji rokon bayinshi neh kaji koh?"

Gyada kanshi yayi yana runguman Ammi,

"Qudsiyah!!!....dagowa yayi yakalli Ammi datayi magana cigaba tayi dafadin.... Inason ka dauke aurentan da aka maka amtsayin kaddara amma in bakaso bana maka dole zaka iya sauwaka mata"

Numfasawa yayi yana jin tukikin bakin ciki yana taso mai cikin dakewa yace...

_manage_

#team ZulynMourad 
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*
*ZULFA*

@MHIZZPHYDO 

A Sweet and pitious Romantic love story 

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 69* 

"Bazan sauwake mata bah! Allah yasa hakan shine mafi alkheri" yafada tareda mikewa cikin layi kaman wanda yasha giya ya kama hanyan stairs,

Cikeda tausayinshi tabishi da kallo, Siyah lab'e(nace sana'a) takaraso cikin parlourn zuciyarta wasai.

"Nagode Ammi"tafada cikin farinciki tana runguman Ammi...

         ★★★★★★★★★

_Abuja,Nigeria_

Papern dake hannunta take kallo cikeda mamaki cos tasan ita bata ajiye tarkace acikin Jakarta,

Tsaki taja tana nufan wajen dustbin din dakinta dashi kasancewanta mai tsabta

"Lafiya ko My Lut?"taji antambaye ta daga bayanta

Juyowa tayi takalle shi kafin tasaki murmushi tace"wlhy datti nagani acikin jaka nah shine zan yasar"

"Datti kuma dear?"yatambaya yana karasowa wajenta

"Erh kaganshi"tafada tana nuna mai clean papern da aka mishi nad'i mai kyau

"Kardai abu mai muhimmanci neh aciki cos baiyi kama da datti bah"yafada yana karban papern daga hannunta

Sakin mishi papern tayi tana wucewa wajen bedside mirror tareda jan stool tazauna

"What!!!" Taji yafada daga bayanta,juyowa tayi takalle shi yanda ya wani zaro idanuwan shi

"Miye faru"tafada atsorace

"Aina kika hadu da MISS ZULFA?"

Dariyan karaina min hankali tayi tace"wacce kenan?"

"Su nawa kika sani?"yatambaya yana karasowa wajenta

"Nikam ko a hoto ban tab'a ganinta ba balle kuma azahiri"ta bashi amsa tana mai shafa cleanser afuskarta

"Then wannan fah?"yafada yana Mika mata papern

Zaro Ido tayi tana tashi tsaye har towel din dake jikinta na kokarin kuncewa

Hannunta daya tarufe bakinta dashi cikin tsoro,juya papern tayi taga an rubuta

_"Nagode sosai Bansan da miye zan saka miki bah Anty, amma ga wannan hope baiyi kadan bah?"_

"Zuly ceh!!!"tafada cikeda mamaki tana kallon mijinta 

"Wacce?"

"Zulyn dakasani"

"Unbelievable!!!"

"No wonder ranan damuke asibiti da aka kirani akace MISS ZULFA bah lafiya tace min itace amma sai nakaryata " tafada cikin sanyin murya

"Shiyasa akace don't underestimate anybody" yafada yana kama ta zuwa jikinshi,

Wayarta tadauka takira wani number babu dadewa aka daga cikin farinciki tace"dady you won't believe what happened"

Banji miye akace daga dayan bangaren bah tace"it's a surprise amma sai gobe zan fada maka"

Suna gama magana ta kashe wayan tace"yakamata nakirata na mata godiya koh?

"No ai godiya akan waya yayi kadan kibari gobe saimuje mu mata godiya har gida"

"Yauwa ka kawo shawara"tafada tana komawa zaune...

          ★★★★★★★★

Sosai Zuly tarame tayi duhu tsantsan damuwa kuma tin ranan da Iqbal yayi raping dinta bai sake shigowa koda dubata bah itama kuma bata damu bah acewarta abinda yake damunta mah ya isheta kuma itama bata sake lek'a koda bakin kofan part dinta bah...

Yanzu ma haka zane takeyi a dakin zanenta cos yanzu duk kwangilan da aka kawo karba takeyi tayishi duk soboda kar Iqbal yasamu,

Iqbal ma sosai abubuwa suka chakube mai ganin baya samun kwangila yanzu dadin abinma yanada business amma zuciyarshi fal mamaki soboda ya tabbata MISS ZULFA bazata tare mai cigaba bah...

Ringing din wayarta neh yakatse ta daga abinda takeyi cos tasa Christine ta siyo mata wani amma ba irin wanda dah take amfani dashi bah,yar tsaki taja tareda nufan inda wayar yake,

Sunan datagani yasata daukan wayan dasauri tareda karawa a kunne duk paint ya b'ata mata gefen fuska

"Anty na kina lafiya?" Tafada cikin sanyin murya, banji miye aka fada bah naji tace 

"Kibani 5 mins zan kiraki"katse wayan tayi tana jan tsaki tareda yamutsa fuska tana kuma danna wayarta kafin takara k'arawa a kunne, har yagama ringing ba'a daga bah,

Wani tsakin takuma jah sannan tayi yar danne-danne awayar kafin ta sake dailing numbern tace

"Ohk Anty saikunzo"ajiye wayar tayi tacigaba da abinda takeyi...

Fitowar shi kenan daga wakan yaga missed call dakuma message, 

Budewa yayi yana karantawa kaman haka

_Hi Mr! Nakira baka dauka bah daman cemaka zanyi zuwa nan da awa daya zanyi bak'i wato Anty and her Husband so kuma nabasu go ahead din zuwa,inkuma baka yarda da zuwan su bah kayi gaggawar sanar dani,frm Zuly_

Murmushi kawai yasake cos tin ba yau bah ya lura bata mawa mutum miss call dayafi daya,shafa kanshi tareda ajiye wayar shi yacigaba da abinda yakeyi.

Saukowa takeyi ahankali daga stairs din da zumbulelliyar khimar dinta har k'asa mai hannu, ko gyara fuskarta batayi bah cos bata san color paint ya b'ata mata bah,

Saukar ta yayi daidai da fitowar Iqbal daga cikin kitchen da cup a hannunshi,

Cakk yatsaya yana kallonta, sati 1 daya kwashe bai ganta bah sai yaga ma takara mishi kyau,

Tana lura dashi ta k'awar da kanta daga bangaren shi tana mai cigaba da tafiya

"Ke!!!"yafada cikin kausassar murya, tsayawa tayi cakk ta runtse idanuwanta gabanta na wani irin bugu tsantsan tsoro, 

Ai bata farga bah sai sanda taji numfashinshi awajen fuskarta,

Matsawa tayi baya tana kokarin ratsawa ta gefenshi still bata bude idanuwanta bah,

Fizgota yayi ya matseta da jikinshi yana sakin ajiyar zuciya dakuma murmushin da ni kaina Phydo baisan namiye bah,

Muryan shi taji yace"baki iya gaisuwa bane??"

Shiru tayi hawaye na gangaro mata jikinta sai rawa yakeyi

Sake matseta yayi ajikinshi yace"uhmmm?"

Bakinta na b'ari kaman wacce ruwan sama yamawa shegen duka tace" iii.. ina kw..wana?"

Sausauta rikon yayi yana karewa fuskarta kallo,hannunshi yakai daidai wajen da paint ya b'ata yace" nayi missing dinki sosai my friend amma kuma naga alaman ke bakiyi missing dina  bah, kodai nayi laifi neh"

Lura da yanda take motsa bakinta alamun zatayi magana amma takasa yasashi sakin dariyan mugunta yana mai shafa bayanta zuwa waist dinta 

Bakinshi yakai saitin nata yana lasan lips dinshi yace"bari na saki maganan dole".

_manage_

#team ZulynMourad 
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 70*

Waro idanuwanta tayi dasauri tace"ana Jira nah awaje neh"

Saketa yayi yana kallon fuskarta yace" zanyi tafiya yau and sai next month zandawo! Zaki iya zuwa duk inda kike so amma banda yawon dare akwai driver sai kimishi magana kuma kituromin account numbern ki"

Yafada tareda yin wajen dining table, hawayen ta tashare tace"ni bana bukatan komai naka"

Cakk yatsaya chan ya dage kafadunshi alaman ko ajikinshi,

Fita tayi tana aza murmushi asamar fuskarta, wajen su Lutfiya takarasa tana fadin"amun afuwa na tsayar daku"

"A'a wlhy amarya"mijin Lutfiya yafada,murmushi kawai tayi tareda musu jagora zuwa cikin gida,

A parlourn k'asa tasauke su tareda haurawa sama tadauko musu abun motsa baki,

Duk abinda sukeyi Iqbal nazaune a dining yana kallon su kuma basu ma lura dashi bah,

"Sister irin wannan kyauta haka? Mun gode sosai Allah yasaka da alkheri"

"Haba Anty ai babu komai wlhy kuma kinfi karfin hakan wajena"

"And kuma kiyi hakuri wlhy bansan ke...kece..."

Muryan Iqbal neh yakatseta inda yake musu sannu dazuwa yana bawa mijin Lutfiya hannu sukayi musabaha kafin ya musu sallama ya fice.

Mijin Lutfiya mah tafiya yayi yabar mata Lutfiya...

         ★★★★★★★★

Kwance yake akan Sofa idanuwan shi arufe da frame rungume akan kirjinshi,

Tindazu take mishi magana amma ko bude Ido baiyi bah abin bakaramin bata mata rai yayi bah,

Kuka tafashe dashi tareda zaunawa agabanshi , ahankali ya bude idanuwanshi dasukayi jah yasauke su akanta,

Yamutsa fuska yayi tareda gyara zaman shi akan kujeran,ahankali ya dagota tareda daurata akan cinyarshi yace

"Miye kike kuka?"

Shiru tayi tareda rungume shi tana sauke ajiyar zuciya,lumshe idanuwan shi yayi tareda lashe busassun lips dinshi yace

"Nagode kinji"

Gyada kai kawai tayi tana dada shige mishi jiki,ahankali tace"ni ba mace bace da bazaka soni bah?"

Cireta yayi daga jikinshi yakalle cikin idanuwanta yace" ki daina magana haka"

Hawaye neh ya gangaro mata tace"miyesa bazaka koma yanda kake dah bah? Bakasan miyesa Allah yayi hakan bah kuma fah karka manta ba duk abinda mutum yakeso bah yake samu, DanAllah kacire komai aranka Sweet"

Share mata hawayen yayi shima idanuwanshi cikeda da kwalla yace" ina kokartawa amma kema ki tayani da Addua"

Fuskarshi take kallo kaman maison dauko wani abu aciki ai ban hankara bah kawai sainaga bakin Mourad acikin na Siyah,

Sosai take sumbatar shi tana shashafa shi, ahankali ya janye bakinshi tareda kawar da fuskar shi gefe yana runtse idanuwanshi tareda shafa suman kanshi

Hannu tasa tana juyo fuskarshi gareta tace"miye faru kuma"

Girgiza kai kawai yayi tareda dagata daga cinyar shi yace"zanje na huta"

Da kallo tabishi tana sakin murmushi...

       ★★★★★★★

Sanye take cikin doguwar Arabian Riga kalan sararin samaniya wanda aka mishi adon duwatsu wato stone work,

Kanta yasha nad'i da gyallen  hannunta daya rike da basket wanda yake cikeda flask din ruwan zafi dakuma hadaddun coolers,

Dayan hannun kuwa wayarta ce saikuma makullin motan data tusa acikin yatsar hannunta,sai faman sauri takeyi kaman zata tashi sama,

Yusayrah tasamu a parlourn itada kawarta Nihal, ko iskar data kwaso su bata Shaka bah tayi hanyan ficewa abinta,

"Sai kindawo second option"

Cakk ta tsaya tana tunanin maganarta ,zatayi magana kenan wayarta yayi kara,

Cikin sauri ta fice abinta, tafawa sukayi tareda sa shewa.

Tuki takeyi ahankali tafice daga cikin gidan baba mai gadi namata saita dawo,

Wayarta neh yasake ringing, jonawa tayi da speaker taji muryan Lutfiya na fadin

"Kin bar gida neh?"

"Erh Anty nakusa zuwa kofar gidanki mah"

"Toh ki karaso inajiranki sai mu tafi tare"

"Ohk Anty"tafada tareda katse kiran tana kara volume din favorite wakanta(perfect).

Abakin gate tasamu Lutfiya tana jiranta, horn ta danna Lutfiya takaraso ta shiga sannan suka kara wuta...

_Hospital_

Sallama sukayi suka shiga cikin dakin, cikin sauri Zuly ta ajiye basket din hannunta tareda karasawa wajen gadon babyn dake wajen,

Daukar babyn tayi cikin kulawa tana santin baby ga wani murmushi shimfide asamar fuskarta

"Babu magana neh Zuly?"
Chapter 46 · 0% Book details