← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 98

Sashe 6

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah yasa Ammina, kullum wallahi zuciyata karaya yakeyi kaman zuly batawa bace kuma wani amma inaji ajikina koda wani ya aureta toh daga karshe wajena zata dawo amma Ammi na bana son ta subuce min" yafada cikin sanyin murya  hade da kwantarda kanshi akan cinyarta, Allah sarki tausayin danta ne ya ziyarce zuciyarta cos tasan maganan dacikin zuciyarshi take fitowa… muryanshi dataji ne yasata miyarda hankalin ta wajen ta inda yake cewa

" Ammi na kidinga min Addua soboda nasan in bansameta bah zaku iya rasa ni, kiji fah yanda zuciyata yake bugawa soboda daita" yafada yana mai sa hannunta akirjinshi, jin yanda zuciyarshi yake bugawa yasata firgita ahankali take fadin

"Mourad kayi hakuri kasawa zuciyarka salama kacire komai azuciyarka cos kafini sanin illar hakan kuma inshaAllah zulyn Mourad takace har abada"

Murmushin da shi kadai  yasan ma'anar ta ne ya subuce mai tareda fadin" Ameen Ammi na"

Sannan yacigaba da fadin" Ammi bansan miyesa nake sonta dayawa bah Ammi inasonta sosai sosai fah"

Dariya kawai Ammi tayi sannan tace" toh mr love katashi katafi hospital cos na tabbata kanada aiki agaban ka"

Dasauri yadaga kanshi daga kan cinyarta yana fadin" ya Salam Ammi inada theater by 10 Allah yasa wannan QUDSIYAHn tagama shirya komai kafin na isa"

"Ayyerh Qudsiyah yarinyar kirki kowani jumma'a  saitazo ta gaishe ni kuma harda hidima take zuwa"Ammi tafada cikin dariya tana mai kallon shi

Yamutsa fuska yayi sannan yace"kyaleta Ammi yar wahala ce, wai inbanda shashanci irin na Siyah wai ni tace tana so"

Murmushin kan fuskar Ammi ne ya fadada sannan tace " ga shawara mana tinda tace tana sonka"

Ahankali yamiyarda hankalinshi kan Ammi sannan tacigaba fadin"why not ka aureta kafin zulynka takai na aure"

Azabure yatashi haryana hankade daya daga cikin yen matan dake zaune dasauri ta matsa daga wajen gashi ba halin su bar wajen cos dukkansu babu maijin Hausa…

"What are you saying ammi? Kina nufin inyi ma zulynah kishiya tin bata shiga bah"wani dariyar ranin hankali tayi sannan ya cigaba dafadin

"That can never happen,nifa Ammi bani nace inson Siyah bah ita tace tanasona,ohk nama gane wato hala tana samiki wani abin tsafi acikin abubuwa da take kawowa ne dazakiyi wannan tunanin Ammi"

"Bazan iya auren siyah bah Ammi" yafada agajiye

"Why?" Ta tambaye shi cikin mamakin chanzawan shi

"Cos ban taba jin son wata ya' mace aduniya bayan ke bah sai zulynah and kuma natabbatar harna koma ga mahallici na bazan so wata inba keda zulynah bah,so it's better mubar maganar wata Siyah"

"It's ohk Allah yabada sa'a"

"Ameen Ammi saina dawo"

"Adawo lafiya" tafada asanyaye,shikam ko kula da yanda tayi maganar baiyi bah yasa kai ya fice daga gidan…

Hospital mai suna
German Heart Centre Bremen  yanufa yana isa straight Cardiologist · Building 39 Dubai Healthcare City - 2nd Floor - 26th yanufa cos anan yake da aiki…

Wanda tagani ne yasata sauke ajiyar zuciyar mai karfi tareda fadin Ya Allah ka mallaka min wann…

*Inkun ji dadin shi share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

Wannan page din nakine *Zainab Zakari(nima yar gata ce)* inajin dadin comments dinki...Allah yasaka

*Page 13-14*

Wanda tagani ne yasata sauke ajiyar zuciyar mai karfi tareda fadin Ya Allah ka mallaka min wannan bawa naka...

Murmushi shimfide asamar fuskarta take fadin" barka da zuwa my sweet Mourad"

Tamke fuskarshi yayi domin wani mugun haushinta yakeji,maimakon ya amsa saiyace"ina fatan angama komai da komai??"

Ganin yanda yamata magana fuska adaure kaman an mishi dole neh yasa jikinta yin sanyi ahankali tace "eh sir nagama"

Batareda Ya kalleta ba ya gyada kai sannan yayi gaba itama kaman gela tabishi abaya

"Sir Ammi tana lafiya dai koh?" Ta tambayeshi cikin dar dar

"Lfy take"ya amsa adakile still bai kalleta

"Ya kabaro zulynka?ina fatan kabaro ta lafiya?"

Wani irin sanyi neh ya lulube shi ga wank shegen murmushi ne ya subuce mai cike da kulawa yake fadin"zulynah tana nan lafiya wlhy"

Allah sarki ganin fara'an dake kan fuskarahi neh yasa tadanne abinda takeji aranta tareda kirkiran murmushi sannan tace"kadan kira min ita mu gaisa kafin mushiga theater din"

"Lah kinma tinamin tin jiya nakashe wayata bari na kunna"

"Toh" tafada tana mai jin dadin wannan hiran tasu amma kuma tadanji mamaki jin yace wayarshi akashe tin jiya kenan basuyi waya bah,sharewa tayi tana maijin dadi aranta dukda wani bangaren kishin Zulfa ne acike dam amma tinda asanadiyar ta Mourad yamata magana harda fara'a...

Yana kunna wayarshi sako yashigo amma ganin ba suna neh a numbern yasashi sharewa, numbern Zulynshi yashiga danna wa kira amma jin akashe ne yasashi shiga tashin hankali cos asanin shi sai batada lafiya kokuma tayi tafiya ne take kashe waya...

Cike da rashin jin dadi ya jatsaki , tsakin shine yasata dan matsawa kusa da shi cike da kulawa da nuna jimami duk da batasan miye ke damun shi bah cikin sanyi tace" sir lafiya dai ko?"

"Wayan zulyna akashe kuma wlhy nayi missing dinta " hadiye wani abu mai daci tayi sannan tace

"Allah yasa dai tana lafiya"

"Ameen" yafada hade da fadin "haryanzu lokaci baiyi bane?"

"Sauran 30minutes"

Tsaki kawai yaja cos gabadaya sai yaji zaman nasu ya gundareshi, gallery yake son dannawa domin ganin hoton masoyiyarshi amma mistakely hannunshi yadanna message

Har zai daga sai kawai yadanna kan numbern da aka turo mai da message, abinda ya gani ne yasashi tashi dasauri har sanda Siyah ta tsorata

"Ta yafe min!" Shine abinda yake fadi cikin murna,harda sujadda yayi...itakuwa Siyah kafeshi tayi da ido tana mamakin sauyin yanayinshi cikin dakikun da basu wuce 5bah amma saitace

"Sir kaida waye haka"

"Infada miki zulynah ne muka samu matsala daita wlhy, barina kirata naji ya take" yafada hade da dailing numbern da tayi mai message

Ringing daya biyu tadauka sannan tayi shiru bata yi magana bah ,cikin doki yace

"Amincin Allah yatabbata agareki ya ke sarauniyar zuciyata"

"Yay Mou dina!!!" Tafada daga dayan bangaren

"Am so sorry zulyna, bazan sake bah...wlhy na horu haka" yafada cikin kwantarda murya

"Stop saying sorry yay Mou"

"Zulynah nayi kewar ki sosai"

"Nima haka masoyi"

"Inasonki inasonki inasonki zulyna kuma har abada ke zan so daga ke babu wata inshaAllah"

Dariya tayi daga dayan bangaren sannan tace"yay Mou wannan soyayyan baiyi yawa bah?"

Zaro ido yayi tareda fadin" wayace miki so yana yawa,tab ashe anbar wannan yarinyar abaya"

Dariya tasake yi sannan tace"inji waye anbarni abaya bayan inada kai?"

"Ashe haka neh kinada nih"

Allah sarki Siyah har hawaye yagama wanke mata fuska tin tana gogewa har tadaina, kukan daya kufce mata neh yasashi dawowa daga duniyar soyewan dasuke

"Zulynah zankiraki kinji"yafada

"Ohk yay Mou dina ayi aiki lafiya kuma Allah yasa ayi a sa'a, inasonka sosai bye" tafada batareda taji miye zaice bah ta kashe wayan,dariya yayi kafin yace

"Ameen zulynah" miyarda hankalinshi yayi zuwaga Siyah wanda ahalin yanzu har tana rike kirji...

Ahankali yamatsa kusa daita tareda riko hannunta sannan yakirata

" Siyah!!!"

Ahankali take dagowa sannan takalleshi idanun ta dakuma kan hancinta sunyi ja abinka da balarabiya

Kawarda fuskarshi yayi daga gareta sannan yace" bazan hanaki kuka bah amma zan fada miki wani abu, kinsan shi so Allah ne yake daurawa bawan shi.

"Kaman yanda Allah yadora miki sona haka Allah yadora min son Zulynah,wlhy ba laifi na bane laifin zuciyata ne dayakasa sonki tin kafin Zulynah tashigo rayuwata nasan there's someone out there for me and inada tabbacin cewan kema akwai wanda yake mutuwar sonki, pls Siyah kicire ni aranki wlhy da inada yanda zanyi nafara sonki toh tabbas sainayi "

Shiru yayi kafin yacigaba da fadin" DanAllah Siyah kiyi aure,ke ba yarinya bace pls duk wanda yake aon shigowa rayuwanki kibasu dama and inshaAllah zan tayaki da addua kinji Siyah"

Ahankali ta gyada kanta,share mata hawaye yashiga yi sannan yace"Siyah din danasani 23yrs back ba haka take bah, wancan Siyah din bata kuka ko kadan amma ji wannan she cry easily, oya my sweetest Siyah kindly wipe off this tears okay,kinsan har abada you will be always be my good frnd nothing can change that and Allah yabaki miji nagari"

Wani dadi tadanji aranta cos sosai taji relieve azuciyarta ahankali tace"Ameen my sweet Mourad nagode"

"Good girl, oya jeki sha ruwa sai muje mushiga theater room dinko?"

"Erh" tafada hade da ficewa,ajiyar zuciya yasauke lokacin da tafita tareda daura hannunshi asaitin zuciyarshi sannan yace

"My heart beats only for you zulynah,daga ke babu wata"...

*Day 2*

*LBS Rd, Kamani, Kurla West, Kurla, Mumbai, Maharashtra 400070, India*

*Phoenix mall...*.

Hankali take tafiya inda wasu ke mara mata baya kaman wata sarauniya, ga wani annurin dake fita afuskarta sanadiyar farincikin datake ciki yau kwanan
*Zara at phoenix marketcity* suka karya wajen assossaries wani agogo mai shegen kyau tagani mai suna*Tourbograph"pour le mèrite na companyn lange&söhne*kudinshi sunkai $508,900(183,204,000.00naira)

Ahankali tace "yay Mou dina zaiso wannan agogon" cemusu tayi suyi mata packaging sannan tabasu ATM card dinta tareda cemusu inta gama abinda takeyi zata juyo ta karba...

Haka tagama zagayewa amma har lokacin bata gama bah,komawa tayi takarbi agogon sannan tafice...

*Inkun ji dadin shi share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 15-16*

*Pregnancy*

Haka tagama zagayewa amma har lokacin bata gama bah,komawa tayi takarbi agogon sannan tafice...

*Two days later..*

Shirye shiryen komawa gida takeyi cos harta kammala abinda yakawota, siyayya kam tayi su kaman ba gobe kuma abin mamaki koh kaya daya bata siyawa kanta bah duk na Umma neh dakuma Mourad ...

Abangaren Mourad ma yagama aikin daya kawoshi kuma Alhmdllh an samu nasara, shima tsaraba ya siya Zulynshi wanda yakashe kimani 7million azallan siyayya amma abin mamaki bawai sunyi wani yawan azo agani bane a'a tsantsan tsadan su neh yasa kudin yayi yawa...

★★★★★

*ROOM 5 SHERATON HOTEL, WUSE ABUJA NIGERIA...*

Kwance take akan gado while kafanta nakasa santala santalan fararen cinyoyin ta abude dalilin karamin towel dindake jikinta...

Sai lum lumshe ido takeyi can kawai saita waresu akan P.O.P din dakin dalilin karan bude kofanda taji...

Fitowan shi kenan ya hangota akan gado batareda tashirya bah wani tsaki yaja acikin zuciyarshi tareda hararanta afakaice...
Chapter 6 · 0% Book details