← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 98

Sashe 15

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaishe shi tayi ya amsa cikin sakin fuska tareda bin jikinta da kallo wucewar shi yayi azuciyar shi yana fadin" yarinya babu ke babu sake komawa wata uwa duniya saida aure akanki!!!"(nace yehh munkusan shan biki)

```washe gari```

Kiran Kuwah neh yatashe ta daga baccin round two dinda takeyi daukan wayan tayi inda Kuwah  take fada mata sun kusa isowa...

Tashi tayi taje tayi wanka sannan tashirya tana jiran isowan Kuwah din cos ko karyawa bata yi bah tsantsan zumudi...

Sa yara tayi akan in Kuwah ta iso azo afada mata cos sosai tayi missing best friend dinta shekaru Hudu bah wasa bah(wallahi kam).

Zaune take agaban dressing mirror daga ita sai towel hannunta kuwa Jan baki neh shigowar Umma neh yadakatar daita daga kwalliyan datake yi...

"Inazuwa haka da irin wannan kwalliyan ko kuma ince duk wannan kwalliyan nawaye tinda nasan Mourad baya nan?" Umma ta tambaye ta cikin dariya

Kara gyara fuskanta tayi sannan tace" Kuwah nah takusa isowa shiyasa nayi mata"

"Nayi kyau kuwa Umma nah??" Ta tambaye ta cikin daga gira

"Ai ke kyakyawa ceh daman" Umma tafada tareda shafo gefen kumatun ta.

Murmushi tayi sannan tace"yauwa Umma nah kaya nakeson insa kuma banson sa wa'inda nazo dasu,ko zaki tambaya min en matan gidan??"

"Toh shikenan bari na karbo miki" Umma tafada cikin kulawa

"Yauwa Umma nah Allah yabar min ke"

"Ameen" Umma tafada tareda ficewa...

Tafiya yake cikeda kasaita Sai wani daddaga kai yakeyi bai hankara bah kawai yaga an bangajeshi da karfi...

Kiran Kuwah neh yasata fitowa daga cikin fada dagudu hartana bige wani...

Tsayawa tayi cikin son bada hakuri, ai bata hankara bah tayi wata wawiyar mari akan kumatun ta...

Zare ido tayi cikin tsananin firgici hade da Jah da baya, daga hannunta tayi sama kaman zata rama amma saiyaga tasauke

"Ke har abada ba zaki taba yin hankali bah,jaka mara kunya kawai" yafada cikin tsananin bacin rai cos ya dauka mah rama marin zatayi, har yafara hango irin kulikulin wanda zaiyi daita

Wani siririn kuka neh ya kufce mata sanadiyar hada ido datayi dashi...

Kallon ta yake sama da kasa cikeda tsanarta dakuma kyama tana sanye neh da riga da zani da dankawali wanda suka kasance daban daban fuskan nan amai kwalliyan yen kauye , bakinta shake da janbaki wanda ta danbara shi...

"Yar kauye kawai" yafada hade da barin wajen.

Taba kafadarta da akayi yasa juyawa tareda runguman wanda ta tabata cos tasan Kuwah neh.

Breaking hug din tayi while hawaye suna cigaba da gangarowa daga kwarmin idonta.

Share mata hawayen Kuwah tayi sannan tace"haba Zulyn Mourad karki bada mu mana akan dan wannan mari zaki tsaya ki asarar da hawayen Yay Mou dinki"

Dariyan da bata shirya yinshi bane ya kufce mata cikin shagwaba tace"Allah marin da zafi kuma wlhy ya yarda Yay Mou dina yasani toh kashin shi ya bushe"

Dariya sukasa dukkansu kawai saiga Awad yakaraso cikin dariya yace(dama tare suka taho, shi yariga su fita daga motan neh)" daga haduwa harkin sha tsarabar mari??"

"Kuwahnah ki taka wa mijinki birki fah"tafada kaman zatayi kuka

"Amun afuwa" yafada tareda rike kunne

Dariya sukasa dukkansu kafin taja hannun Kuwah suka shige cikin fada...

"Kuwahnah haryanzu Iqbal baisona fah"tafada bayan sun dawo daga gaisar da Umma

"Chan ta matse mishi"Kuwah tafada cikin ya mutsa fuska...

"Haka zakice koh?"

"Toh Zulyn Mourad miye kike son nace bayan kinada Mourad" tafada cikin kosawa

"Yay Mou Kuma??*Ai shi bah kaunarshi nakeyi bah,sonshi kawai nakeyi!!!shima Sona yakeyi kuma ni zuciyata Iqbal take kauna tinda dadewa kema kinsani*"

Kallon ta Kuwah takeyi cikin mamaki cos itafa batasan haryanzu Zuly tana shirme bah tadai San ita tana tsokanar tane kawai.

"Miye kina kallona kaman kinga wata sabuwar hallita??"ta tambaya cikin buge kafadar Kuwah

"Ke wace irin Shashasha ce wai??,ke baki ganewa neh wai? Wlhy koda kwana daya na tabbata Iqbal bai taba sonki bah, baki ga tsanar ki acikin idonshi bane?

Kinsan yanda yake tsananin son matarsa kuwa??"

Tsakin da Zuly taja neh yasata yin shiru

"Wai wancan jakan kike sawa a lissafi??" Wani tsakin takuma sannan tace

"Wancan dabbiyan??, wancan mayaudariyan?? I beg of you Kuwah in ana maganar mutanen arziki kidaina Sako ta aciki"

"Koma dai yaya neh yana sonta,yana kau..."

"Keep mute Kuwah natabbata inkika karasa wannan kalman Umma nah da Yay Mou dina zasu iya rasa ni"ta katse ta cikin rawar murya

Ajiyar zuciya Kuwah tasauke sannan cikin sanyin murya take fadin" ni dake neh kawai mukasan miye Yusayrah take aikata wa ,kuma mu din mah rahoto ake kawo mana ma'ana bamu da tabbacin gaskiya, Zulyn Mourad wlhy tausayin Iqbal neh kawai yacika ranki kike zaton kaunarshi neh.

Wlhy Bazan miki kaffara bah Mourad zuciyar ki take kauna bah Iqbal b...

Cikin daga murya tace"ya isa haka Kuwah ke bazaki gane abinda nake nufi bah cos bakisan abinda nakeji azuciya ta"

"Toh kisanar dani abinda ke zuciyar ki Zulfa'u"

"Zulfa'u kuma??" Ta tambaye ta cikin bacin rai cos kokadan batason acire Mourad acikin sunan ta

"Toh miye kike son ince tinda kince ba kaunar Mourad kike bah"

"Amma ai kuma bance banson shi bah, cos na tabbata ko Ammi bazata kaini sonshi bah kuma ni ko aure nayi *I will still be Zulyn Mourad*"

"Shirmemiya kawai" Kuwah tafada cikin bacin rai cos sosai Zuly tabata haushi.

Zuly zatayi magana kenan wayarta yayi kara, ganin mai kiranta neh yasata daidaita muryan ta.

Daga wayan tayi sannan tayi shiru, jin tayi shiru neh yasa gaban shi dan faduwa cos bah halinta bane yin haka cikin sanyin murya yace

"Me  yake damun Zulyn Mourad neh??"

Numfawa tayi cikin shagwaba tace"bah Kuwahnah bane ta bata min rai bah"

"Yah Salam" yafada hade da lumshe ido soboda yanda yaga yanayin jikinshi ya chanza ahankali yace bata wayan

Daman wayan a handsfree yake ma'ana Kuwah najin komai,gaishe shi tayi amma ko arzikin amsawa bata samu bah , cikin muryan dayake nuna ranshi abace yake yace

"Haba ke kuwa miye neh zaki bata wa Zulynah rai"

Tabe baki Kuwah tayi sannan tace"ka tabbata kanason jin ba'asin zancen??

"Ai shiyasa nace abaki wayan"

Gabanta neh taji yafadi cos haka kawai taji batason afada mishi kuma tasan Kuwah fada zatayi cos bata karya

Numfasawa Kuwah tayi sannan cikeda muryan tausayi cos tasan yana mugun kaunar Zuly dukda basu taba haduwa da juna bah,kuma Allah yagani bazata iya mishi karya bah gwanda kawai ayi ta fanjama fanjam

"Daman fah Zulynka ce tace ita...

*Toh fans ga Kuwah zata mawa Mourad Albishirin mutuwa fah😱😱*

Team: ZulynMourad
Team: ZulynIqbal

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 28*
*ZULFA*

"Daman fah Zulynka ce tace ita..."

Kashe wayan da Zuly tayi neh yakatse ta,da kallon mamaki take binta irin what da hell dinnan

"Yanzu fadamai zaki kenan"tafada rai bace

"Toh bazan fada mai bah ai inaga gwanda yasan baki kaunar shi"tafada azazzafe ( Kuwah akwai masifa da daukan zafi fah..)

"Ai shima Sona kawai yakeyi kuma mah ni yakamata nafada mai...

Karar da wayan ta yayi neh yakatse ta, daman tasan zai Kira...

Kara wayan tayi akunne, ajiyar zuciya yasauke cikin sanyi yace"miye ke faruwa neh Zulynah??"

"Yay Mou bah Kuwahnah bace takirani da Zulfa'u bah" tasamu bakinta da fada,cikeda mamaki Kuwah take kallon ta cos tazata Zulyn zata fada mai neh amma saitaga sabanin hakan.

"Yah Salam shine kikayi kuka"yatambaye ta tareda sauke ajiyar zuciya

"Erh mana ai abin kuka neh"

Lumshe idon shi yayi sannan yace" sorry Kinji ai ke Zulyn Mourad and you will always be *I promise*

"Yauwa Yay Mou dina inasonka sosai"

Murmushi yayi sannan yace" nima insonki"

Murmushi tayi Sannan suka fara hirar domin har ga Allah tamanta da wata Kuwah agefenta.

Kuwah ganin hirar namai karewa bane yasata gyara kwanciyarta akan gado abin ka da mai ciki nan da nan bacci yayi gaba daita.

Jin cikinta na waka neh yasata mishi sallama akan inta gama cin abinci zata Kira shi.

Ganin Kuwah na sharban bacci neh yasata ficewa zuwa wajen Umma.

Zaune ta tarar dashi akan kujera yana cin abinci ga Umma agefe suna hira sama sama cos bata saba bah idan harkaga Umma nah magana da wani cikin sakewa toh lah shakka da Mourad neh.

Share shi tayi dukda taji dadin ganinshi amma saita basar.

Karasawa wajen Umma tayi cikin shagwaba tace"Umma nah"

"Ya akayi neh Zulyn Mourad" Umma tafada tareda miyarda hankalin ta wajen ta.

Cikin sauri yakalle Umma cos Zulyn Mourad dinda Umma tace bakaramin dukan kirjin shi yayi bah, wanda shi Karan kanshi bai San dalilin hakan ba.

Dariya mai sautin da Zuly tayi neh yasashi saukar dakanshi kasa.

"Umma nah wai inji Yay Mou dina wai in gaishe k.."

Bata idda maganarta bah wayan Umma tayi kara, cikin sauri tadauko wayan daga wajen chargi.

Ganin wanda yake Kira neh yasata yin wata karamar dariya  cikin farinciki tafara magana " Yay Mou dina"

Kallon ta yayi tareda miyarda hankalin shi gareta yana mamakin waye garan dayake Kula wannan shirmemiyan.

"Wai nikam bayanxu kuka gama waya dashi bane" Umma ta katse ta.

Cikin kunkuni ta mika mata wayan"Har anfara mantawa damu neh??" Umma tafada

"Wlhy a'a Umma ai ko yaushe mukayi waya daita ina Miko sakon gaisuwata saidai in tadan sha'afa neh"

"Oh kafara kareta kenan??"Umma ta tambaya

"Na isa??, Yauwa Umma Zulynah bata ci abinci bah DanAllah ataimaka amatsa mata taci ta koshi" ya fada mata

"Toh naji za'a matsa mata taci ta koshi"

"Yauwa nagode Umma"yafada hade da katse kiran cos yasan muddin bai kashe bah toh Zulynshi zata manta da batun abinci su dora daga inda suka tsaya...

"Ya kashe neh Umma nah??" Ta tambaya cikin sanyin murya

"Cewa yayi kici abinci tukunna"Umma tafada tareda ficewa.

Saigata tadawo da tray a hannunta, dumame neh acikin plate mai shegen zafi cos har turiri yakeyi kamshin saitashi yakeyi.

Hadiye yawu tayi tareda karasawa wajenta ta karbi tray din tana fadin "ai da baki wahalar min da kanki bah"

Wani guntun tsaki neh ya kufce mishi jin abinda tafada.

Juyawa sukayi suka kalleshi saiyayi kaman bashi neh yayi tsakin bah.

Suma basarwa sukayi inda Zuly tazauna Sai narkan dumame takeyi sannan ta gama cinyewa harda tande kwano cos sosai abincin yayi dadi.
Chapter 15 · 0% Book details