← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 98

Sashe 76

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dumm taji gabanta yafadi soboda rashin sabo! Bata hankara bah kawai taji hannunshi ajikinta harwani matsota yayi sosai tareda rungume bayanta akirjinshi

Jikinta neh yadauki rawa Wanda hakan bakaramin mamaki yabawa Mourad bah, cikin rawar murya tace"Yay Mou dina bacci nakeji"

Daidai wajen kunnenta yakai bakinshi tareda cewa"na hana ki neh? "

Tsit tayi batareda tayi magana bah, shinshinarta yayi yace"wannan scent din yamun dadi" Shiru tayi zuciyarta na wani irin rawa soboda tsoro

"Kinutsu mana bawani abu zan miki bah kawai dai inason feeling dinki neh pls kibarni"yasake fada still hancinshi na manne da jikinta yana aikin sunsuna saikace bada turare daya sukayi amfani bah !

Jin wani abayanta yasata mikewa zumbur cikin firgita, akidime tanuna shi da yatsarta tana cewa

*DanAllah wattadians ina bukatan Followers dakuma votes🙏*

*Vote,comment&share*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 105*

"Miye kake samun abayana?

Mikewa zaune yayi yana kallonta dakyau  yace"ni babu abinda nasamiki kingani ma?"yakarasa fada yana ware hannayenshi, kallon sama da kasa tamishi kafin ta sake kwanciya cikin dar-dar sai wani kame jikinta kam takeyi

Shima kwantawa yayi yakuma sake matsota,firgita tayi jikinta nadaukan bari"Wai miye yake damunki neh? "Yafada a hasale cikin b'acin rai yana kuma zaunawa

Zama tasakeyi tareda kura mishi idanuwa wasu zufa na tsatsafo mata, ganin yanda take zufa bakaramin sake bata mai rai yayi bah

"Sai kiyi tayi ai"yafada tareda jan tsaki, gani kawai tayi yasauka daga kan gadon, kallon mamaki tamishi kafin tayi magana har yafara tafiya abinshi, a hanzarce tadiro daga saman gadon tana fadin

"Ai abun baikai na fushi bah kayi hakuri! "Ko kulata baiyi bah yafice zuciyarshi na kuna kuma harwani kuka-kuka yakijin yayi

Direct dakinshi yawuce tareda slamming kofa afuskarta soboda daman tana binshi neh, bubuga kofan tafarayi chan ta tina ashe basu kadai bane acikin gidan, ahankali ta silale awajen cikin jin haushin kanta

Ahankali tafara rero kuka har wasu vibrating takeyi kaman anjonata da ringing tone mai vibration...

'''WASHE GARI....'''

Jin karar alarm asaitin kunnenta yasata yamutsa fuskar tareda sa hannunta daidai  inda take jin karar, dauka tayi tareda cillarwa

"Taaass"shine karar da agogon alarm din yayi soboda daman duka jikinshi glass neh, kaman zatayi kuka ta yamutsa fuskarta tareda  lume kanta acikin pillow cikin rashin jin dadin katse mata perfect marfarkinta da Yay Mou da alarm din yayi

Ahankali tadago kanta tana kallon inda take, wani murmushi neh yasubuce mata, lumshe idanuwa tayi tareda yin wani irin juyi wanda yasa rigar jikinta kwayewa...

Banda tsaki babu abinda to take ja ganin tinda tafarka bata ga Yay Mou dinta bah! Zama tayi akan tiles tareda zuba wasu uban tagumi kaman wacce taci kudin banki

Cire mata tagumin da akayi neh yadawo daita daga duniyar tunaninta, ajiyar zuciya mai karfi tasauke tana mai kawar da fuskarta daga kallon da Qudsiyah take mata!

"Sister inlaw lafiya kika zabga wannan uban tagumin?"

Murmushin yake tasake tace"kaina neh yake Dan ciwo"

"Ayyerh bari nakawo miki magani saiki sha"tafada tana kokarin mikewa daga tsugunen datake, riketa Zuly tayi tace "dasauki fah sister!"

Ganin zatayi sake magana neh yasa Zuly cewa"amma jiya ba anan kika kwana soboda damuka dawo banganki bah!"

Zama Qudsiyah tayi akan chinese rug din dake gaban Zuly tace"anan na kwana mana amma ba dawuri na dawo bah! "

"Oops nama manta! Yay Mou dina yafada mun yanda kiketa shan mana wahala, mungode sosai Allah yakaimu naki kuma Allah yasaka miki da gidan Aljanna!"

Murmushi tasake tace "Aww sister in-law ai yiwa kaine karki samu damuw..."

Kafin takarasa magana har Sallaman su Ammi yadoki dodon kunnensu, amsawa sukayi inda Qudsiyah tamike itakuwa Zuly nazaune kaman wacce aka dasa sai kallon Mourad dayayi kaman baisan da wanzuwarta awajen takeyi

"Kekuma ya haka kin wani yi zaman dabbas akasa acikin sanyi"Umma tafada suna zaunawa akan kujera

"Kun iso lafiya?  Ya hanya? "Ta tambayesu cikin kulawa, kafin su amsa har Mourad dake tsaye yace

"Bari naje nahuta!"cikin mamaki suke kallonshi ganin yawani sha mur yawani hada rai kaman soja

"Sannu da dawowa Yay Mou dina!"tafada ahankali, atakaice yace

"Yauwa!" Ba Zuly bah hatta sauran dasuke wajen sanda sukaji wani iri aransu, ahankali tamike cikin sanyin itama tayi hanyan dakinta, da kallo kawai sukabi bayansu kowa da abinda yake sak'awa aranshi

Akan gado ta fada tareda fashewa da kuka soboda itafa data ga kanta akan gado tazata yadaina fushi daita neh balle ma ita bataga abin fushi acikin abinda tayi jiya bah!  ahaka bacci yadauketa ko sleeping dress bata sa bah balle azo ga shan magani,  sai ajiyar zuciya take saukewa akai akai...

Awajen Mourad ma bawai ya ji dadin sharetan dayayi bane a'a asalima wani irin zafi yake ji azuviyarshi na sharetan dayayi amma kuma in ya tuna yanda takeyi jiya da dadare kaman wacce bata taba yin aure bah sai yaji wani irin haushi da takaici ya turnuke shi!...

'''WASHE GARI...'''

Zaune kowannen su yake akan dining ana kokarin cin breakfast 🍳 suka lura babu Zuly akan dining

Ammi ceh tace"Wai Ina Zulyn Mourad neh? "

Wani irin boyayyen ajiyan zuciya Mourad yasauke soboda tindazu tunaninshi awajenta yake har wani rashin nutsuwa neh yake luguiguitan zuciyarshi amma sai yayi shiru

"Nikam Ammi bansan miye damunta bah dazu danaje dakinta naga idanuwanta sun kumbura alaman tayi kuka amma dana tambayeta saitace min ciwon idonta neh yatashi wanda ni nasan idanuwanta  basuyin hakan in yafara ciwo gashi kuma tin shekaran jiya rabonta da abinci"Maram dake shafa jam ajikin slice bread 🍞 din dake hannunta tafada tana b'ata fuska cikin takaici

"What kina nufin jiya bataci abinci bah? "Suka hada baki wajen fada, dakatar da abinda takeyi tayi tareda kallon dukkansu dauka kafeta da ido suna jiran jin amsan dazata bayar

"Erh agaskiya dai jiya bataci komai bah!  Kuma nayi duk iya bakin kokarina wajen ganin nayi forcing dinta amma abun yaci tura! "Tafada kaman zatayi kuka

"Wannan ma aikin banza neh!  Taya za'ayi mutum yaki cin abinci tun jiya kuma kiki fadawa kowa? Anya ma kinasonta kuwa? "Mourad yafada cikin b'acin rai yana ture plate din gabanshi hade da mikewa

"Kai da kake sonta miyesa baka tambayeta shin ko taci abinci bah kokuma akasin hakan! Zaka wani zo kana wani cika kaman ka damu daita! "Qudsiyah tafada itama cikin b'acin rai hade da mikewa tana kokarin barin wajen tareda jan tsaki soboda daman tin jiya take jin haushin shi akan abinda yamawa Zuly jiya kuma daga lokacin tagane something is wrong shiyasa tabi Zuly daki amma saita sameta tana bacci ga hawaye duk sun bushe mata, batareda ta tashia ta bah ta gyara mata kwanciya tareda rufa mata bargo!

Jitayi an riko hannunta, nan tafara kiciniyar kwacewa soboda tasan Mourad neh, da karfi yajuyo daita hade da zuba mata jajayen idanuwanshi yace

"Maimaita abinda kika fada last! " wafce hannunta tayi tareda watsamai wasu harara tace

"Dolo neh yake maimaita aji sau biyu"bata jira cewarshi bah tayi gaba abinta cikin sauri kaman wacce ake bi

Wani iska yafurzar hade da hargitse gashin kanshi, chan kuma shima yabi bayanta dasauri, sauran dasukayi zaune suna kallon abubuwan dake wakana suma suka bi bayanshi hoping all is fyn...

"Lafiya baki fito cin abinci bah!? "Qudsiyah ta tambayi Zuly dake zaune tazuba wasu tagumi

"Naci abinci fah! "Tafada cikin rawar murya

Murmushi yake Qudsiyah tasake tace"yanxu ke tindaga yanzu har kun fara samun matsala da Yay Mou dinki!  Gaskiya hakan baiyi bah"

Riko hannun Qudsiyah Zuly tayi hawaye na gangaro mata tace"Nifa babu abinda na mishi! "

Share mata hawayen tayi tace"Kokuma kice bakisan abinda kika mishi bah!"

Kafin Zuly tayi magana har Mourad yashigo, kallon shi ta tsaya yi da fuskar tausayi ganin ya kawar da kanshi tareda jinjinawa ajikin garu yasata mikewa da kyar zatayi wajenshi, koh taku uku batayi bah tayi luuuu zata fadi soboda rashin kwarin jiki,  cikin wani irin super Mourad yakarasa tareda taro ta sai gata ajikinshi

Rufe baki Qudsiyah tayi soboda bata zaci Mourad zai tari Zuly dalilin ganin yanda ya kame kaman wani soja,  tashi Qudsiyah tayi daga kan gadon takarasa wajen su Mourad wanda hakan yayi daidai da isowar su Ammi

Ahankali Zuly take bude idanuwanta jin bata fad'i bah, fess suka sauka acikin na Mourad dayake kallonta kaman yasamu TV

"Am sorry 🙇! "Tafada cikin rawar murya jikinta nadaukan b'ari, kallonsu yayi yace"DanAllah ataimaka mana da abincin mutane 2!"

Kallon juna sukayi gabadayansu kafin suka fice inda Zuly ta lumshe idanuwanta wasu Murmushi na subuce mata

Daukanta yayi in a bridal style ya kwantar daita akan gado tareda zaunawa ya juya mata baya, ahankali tamike sannan tadaura kanta agadon bayanshi tace"nifa bansanka da irin wa'inan halayen bah, wlhy hankali na yadaina kwanciya ka sa nafara tunanin cewa maybe yanzu kadaina sona kaman yanda kake fadi neh!"

Ganin yana kokarin juyowa yasata tashi daga bayanshi, yana karasa juyowa yace"kidaina sa irin wannan tunanin aranki!  Kidaina cewan kadaina sonki! Wlhy inasonki irín na sosai dinnan amma abunda kika min shekaran jiya dadaddare  yakasa barin mind dina! "

Runguman shi tayi tace"toh kayi hakuri bazan sake bah in Allah ya yarda"

"Shine kika bar mun kanki da yunwa koh? "Yafada cikin shagwaba tareda cirota daga jikinshi, turo baki tayi tace

"Toh waye jawo?"lakutar hancinta yayi tareda shafa fuskarta yace

"Ni na jawo!  Amma ai baikamata ace kin biyemun bah!"kafin tayi magana har Qudsiyah tashigo da abinci acikin tray, murmushi tasakar wa  Zuly tace

"Yanzu hunger strike yakare koh? "Gyada kai kawai Zuly tayi taka sa kanta akan kirjin Mourad daya dauke kai kaman baiga Qudsiyah bah

"Toh lover girl saikiyi sauri kugama ci soboda har bakinmu sun fara lodging a hotel kuma kinga bazai dace mubari suyi ta jiranmu bah!  Nan da 1hour Fakhiha zata iso soboda tadage sai ita zata miki kwalliyan! "Qudsiyah tafada tareda yin hanyan waje batareda ta kula da halin KO inkula da Mourad ya nuna mata bah!

Dago kai tayi ta kalli Mourad, zatayi magana kenan yarigata fadin"no surutu!  Muje nabaki abinci saimuyi first wankan mu tare kafin lokaci yakure

Rola idanuwanta tayi tareda fadin"kowa yayi wankanshi dai! "

Hada fuska yayi yace"bangane kowa yayi  wankanshi bah?"
Chapter 76 · 0% Book details