← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 98

Sashe 57

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwance tasamu babynta akan bench din baba maigadi

"Allah sarki Babynah"tafada cikin tausayawa ganin yanda take sauke ajiyar zuciya alaman tayi kuka ta koshi gakuma hawaye duk sun bushe mata

Daukan baby tayi tayi hanyar ficewa daga gidan taji muryan maigadi yana cewa" lafiya daiko?"

"Tarasu" shine abinda tafada tareda ficewa daga gidan gabadaya...

"Kayafe mun maisona "tafada cikin disheshiyar muryarta

"But why kikace Zuly ceh takashe ta? Gashi kinjawo nasaketa dakuma asarar cikin jikinta"yafada ahankali

Jitayi gabadaya tausayinshi yarufeta, cije lebban ta tayi tana tirr da halin irin nata "am sorry for everything"

Tafada tana share hawayenta, gyada kai kawai yayi yana fashewa da sabon kukan dabaisan na miye bah...

_5 days later_

Zaune take tasa Fareed dake kwance agaba saikuka take mishi, duk tarame tayi duhu kaman baita bah.

"So dagaske neh?"taji anfada daga bayanta

Dasauri tajuya tana kallon Dakhil dake shigowa cikin dakin fuskar shi Sam babu ko digon annuri

Mikewa tayi atsorace cos batayi zaton zaizo har asibiti bah...

Tafiya yakeyi amma kaman hankada akeyi soboda rashin karfin jikinshi, he feels restless

Ajiyar zuciya yasauke tareda nufan ward din da aka kwantar da Fareed yana dada rike basket din hannushi wanda abincin lunch din Yusayrah neh acikinta.

"Miye kakeyi anan?"tafada cikin karfin hali

Mari yakwasheta dashi yace"harkinada bakin magana? Kin kashe mun y'a kuma nazo duba jikin magaji na kicemun miye nazoyi, you must be mad"

Jikinta neh yadauki rawa kaman mazari bakinta sai rawa yakeyi cikin rawar murya tace

"Masoyi danAllah katafi kar babanshi yadawo yasameka anan"

"Waye kuma Babanshi bayan ni Sayrah? Aww kina nufin ATM machine dinmu? Yazo mana and so kinma ci sa'a ban karya wannan hannun dakika watsawa yarana mangyada bah" yafada tana riko hannunta da karfi

Kuka tafashe dashi tana mai tsinewa Dakhil acikin ranta kaman saukar aradu taji yace

"Nikam ma yau zantafi da dana"

"DanAllah kayi hakuri katafi zanzo muyi settling komai" tafada cikin rashin nutsuwa jin yace zai tafi da Fareed

"Ai in kinga natafi toh tareda yarona neh" yafada yana kokarin daukan Fareed

Cikin muryan tausayi tace" danAllah karufamin asiri mai sona karka min haka, kadaisan soboda kai nake irin wannan abubuwan pls katafi zanzo gida muyi magana"

Hannu yasa yashafo gemun shi da ko gashi babu yace" inzaki zo ki tabbata kwana zakimun kuma kitaho da jakan kudade"

Wani kukan tasakeyi tace" danAllah ka sausautamin wlhy gabadaya nayi broke gashi Iqbal na nan"

Hawayenta yashare yace" haba my sweet Sayrah kima daina bata hawayen ki soboda kaifi daya neh dani donhaka just kiyi abinda nasaki"...

Wasu irin zufa ke karyowa Iq...

*DanAllah wattpadians ina bukatan Followers dakuma votes🙏*

#team ZulynMourad
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 83*

Wasu irin zufa ke karyowa Iqal gawasu taurari sai tsere sukeyi a idanuwanshi, jiyayi kafafuwan shi bazasu iya daukan shi bah,long bench din dake dan nesa dashi kadan ya isa yazauna tareda ajiye basket din hannushi,

Zuciyarshi har wasu zafi yakeyi"miye suke nufi?"

Yafurta underneath his breath,kirjinshi na sama da kasa, hannushi yasa yarufe fuskarshi dashi hawaye masu zafi na silalowa har baisan sanda Dakhil yafice daga ward din bah,jiyayi an dafashi akafada

Dago kanshi yayi yakurawa Awad dake gabanshi jajayen idanuwanshi wanda yake daukeda unstoppable hawayen bakin ciki

"Take heart!!"Awad yafada cikin jimami ganin halin da abokinshi yake ciki,

Basket din gefen Iqbal yadauka sannan yashige dashi ward din da aka kwantar da Fareed...

"Inason aduba min ko dagaske Fareed bah dana bane!" Yafada ahankali

Zaro idanuwa Awad yayi cikin mamaki yace" badai kuma yanzu zargin heartbeat dinka kakeyi bah?"

"Just do as I say" yafada cikin tsawa amma trying to calm himself down

Gyada kai Awad yayi sannan yace" muje lab zansa adauko jinin Fareed"

Batareda yayi magana bah yabishi zuwa lab din yana Adduan Allah yasa karya Yusayrah keyi nacewan Fareed ba danshi bane...

"Unbelievable!!!" Awad yafada yana share zufan goshin shi bayan result din test din yafito

Batareda Iqbal yayi magana bah yamike cikin sanyin jiki dakuma tsinkewar Zuciya yayi hanyar waje

"Friend karka sake yanke hukunci cikin Fushi" Awad yafada cikin muryan lallashi

Gyada kai kawai yayi tareda ficewa daga office din, yajima abakin kofan ward din Fareed kafin kawai yafice daga asibitin gabadaya.

Tuki yakeyi amma hankalin shi baiwajen motan har yayi nasarar buge wata baiwar Allah kadan

Cikin sauri taka burki tareda fitowa daga motan duk zuciyarshi babu dadi

"Sannu baiwar Allah!!"yafada ahankali

Tsaki yaji taja tareda mikewa cikin muryan bacin rai batareda takalli waye bah tace"sannu? Ciwo nakeyi dazaka ceh min sannu? Daman ance direbobin birni neh suke tukin ganganci sobida rashin sanin zafin kudin da akasiya mota kuma Allah yasoka ban samu kwarzoni bah da Wlhy saika sha cizo shashasha kaw..."

Maganar neh ya makale lokacin datayi ido biyu dashi cikin sauri tajuya mai baya cikin tsananin tsoro" innalillah nashiga uku ni _Hibba_(Kun tinata? Hibban data ciji Zuly akan nono).... Buge bakinta tayi tace... Kaikam baka iyayin shiru arayuwanka"

Sake juyowa tayi takalleshi yawani kafeta da jajayen idanuwanshi Azuciyarta tace"kai daga gani wannan mijin Zulfan nan za'ayi jaraba"

Wani yawu ta hadiye tace" kayi hakuri Yaya bansan kai bane DanAllah karka mareni"

Sororo yayi yana kallonta kaman maison tino inda yasanta amma gabadaya damuwan dayake ciki yahana shi tino fuskarta

"Kema kiyi hakuri" yafada tareda barin wajen

Tabe baki tayi tace"Allah yasoni ban samu tsarabar mari bah" soboda bata mantawa da irin marin dayake bawa Zuly duk zuwanshi

"Komiye yake damunshi haka oho"tafada tareda tabe baki tana barin wajen abinta...

Banda kuka babu abinda yakeyi harda su shidewa he's finding it hard to believe cewan dagaske Yusayrahn shi Mazinaciya ceh" Ya Illah so all this while Zuly tasan komai"

Yafada yana buga goshin shi" tayi deceiving dina all this while, she betrayed me"

Yafada cikin dacin rai"arrrghh" yayi sighing lokacin daya tina da Zuly

"So Zuly tasan dacewan yaran banawa bane and lokacin data fada nasaketa"

Wayyo Allah nah" nazubar mata da ciki,nazubar da ya'yana na Sunna"

"Zuly!!!"yafada dakarfi tareda nufan part dinta kaman baisan bata gidan bah.

Wayarta idanuwanshi yafara hangowa asaman center table duk yayi kura, daukawa yayi yana kallo kaman itace Zulyn yace" am so sorry!!! Kiyafemun Zuly,kince zanyi dana sani and here I am"

Ahankali yashiga dakinta yaga komai agyare yake kaman tana nan sai kuran dasuka bade koina

"Zuly!!"yafada yana bude toilet,

"Nasan baki tafi bah tukunna danAllah kifito" yafada yana nufan kofan fita daga dakin

Kaman ance ya waiga kawai saiyaga kofa, cikin sauri yabude kofan kaman zai balleta tareda shiga cikin dakin.

Cakk komai nashi yatsaya yana son kwakwalwar shi yabashi amsa abinda yake gani

Zanenshi yagani katoto ajikin garu agefe daya, dayan gefen kuma itane da Mourad suna zaune dayan angle din itada babynta while angle din daya rage itada Mourad saikuma babynta atsakiya.

Kallo yakaiga frames din dasuke kasa yana kallon frames masu shegen yawa wasu kam ma har ansa su akwali wasu kuma an jiye dayawa akansu akalla frames din zasukai dubbanni he was looking so shocked

Wani art work neh yadauki hankalinshi har baisan lokacin dayaja Michael Jackson kafanshi zuwa wajen bah

"MISS ZULFA" shine abinda aka rubuta cikin wani design mai shegen kyau zai iya rantsewa koshi bazaiyi wannan beautiful artwork din bah cos it's extra ordinary.

Jiyayi gabanshi yayi mugun bugawa girgiza kai yayi yace"wannan mafarki neh Iqbal katashi kawai"

Faduwar wayar hannunshi neh ya fargar dashi firgit yayi yana sake kallon dakin dakyau ai baisan sanda yajuya da reverse bah yafice daga part dinta dagudu...

"Waye yabani koda??" Shine abinda yatambaye Awad cikin rawa murya

"Miss Zulfa mana"ya bashi amsa

"Waye ita?"yatambaya kaman baisan waye bah

"Wacce tabaka abinda matarka bata baka bah wato matarka Zuly!!"

"Don't tell me Zuly ceh MISS DINA!"Yafada akidime

Tabe baki Kuwah data fito daga cikin daki tayi tace" natabbata kaga shaida adakin Zanenta, Zuly itace Miss dinka!!!!"

Wani irin dishi-dishi yafara gani kafin Awad yasan miye yake faruwa kawai yaji karar fashewar center table.

*DanAllah wattpadians ina bukatan Followers dakuma votes🙏*

#team ZulynMourad
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 84*

Cikin sauri Awad yayi kanshi yana mai kiran sunanshi amma inaaa! Iqbal yayi nisa.

Ganin dayayi yana fidda jini ta hanci neh yasashi fita waje dagudu.

Itadai Kuwah ko motsawa batayi bah asalima tabe baki tayi daga baya takoma daki abinta wajen danta dake kuka.

Chan saiga Awad yadawo da Maigadi,da taimakon maigadi yasamu yafitar da Iqbal dake sume!

Bayan sun isa asibiti neh ya ari wayar daya daga cikin nurses dinsu yakira iyayenshi yafada musu halin da dansu yake ciki kafin yakira Matarshi Kuwah, tana daukawa yace

"Maigidan kine ke magana"

"Ai nagane muryarka"tafada hankali kwance

"Kitaimaka mana da abubuwan da ake bukata a asibiti mana"

"Bashida mata neh?"

"Haba matata ni basan ki da rashin tausayi bah please kice driver yakawo ki kinji?"yafada cikin lallashi tareda kashe wayar soboda yasan in bai kashe bah rigima zata tada mai.

"Mijinki babu lafiya fah" Awad yafada wa Yusayrah dake fitowa daga bayan gida

"Miyesa me shi?"tafada hankalin ta tashe

"Jita kaman mutumiyan arziki"yafada aranshi afili kuma yace

"Shock!"

Wani muguwar faduwar gaba taji yashige ta lokaci guda, cikin rawar murya tace" kozan iya ganinshi"

"Yanxu dai ba'a barin kowa yaganshi kibari sai anfara bari zanzo naje dake"yafada tareda ficewa daga ward din...

_BAYAN SATI BIYU_

Sosai Iqbal yakare kaman mai ciwon S , rame sosai kaman ba shi bah, inka ganshi saika zubar mai da hawaye, kullum bashida abinyi banda kuka da nadaman abubuwan dayayi, alokacin kuma har an sallami Fareed shiyasa Yusayrah take samun daman kula dashi dukda bawai yanzu yana sakar mata da fuska bah

Itakam bata damu bah cos atunanin ta zafin rabuwa da Zuly neh amma zaiyi yagama.

"Maisona danAllah inason zuwa gida yau"tafada cikin ladabi

"Allah sarki Zuly nasan dake ceh datin kafin satin fitan yayi zaki fadamin"yafada azuciyarshi tareda ciza busassun labban shi kafin yace

"Toh agaida su"

Murmushi takuma sakewa tace" DanAllah ina bukatar kudi"

Kallonta yayi na wasu mintuna sannan yace"dauko cheque book dina"

Washare baki tayi tareda hurawa sama cikeda farinciki ganin bai tambayeta miye zatayi dashi bah...

"5million Naira!" Tafada cikeda farinciki soboda bata yi zaton zai bata kudin dayakai hakan bah
Chapter 57 · 0% Book details