← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 98

Sashe 13

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sis nalura da wani abu"Fakih yafada lokacin da suka shiga mota dayake mijin Fakihah yazo(Wato tare zasu tafi)

"Miye fah" tafada cikin boye damuwar ta

"In kinason yaya yadawo kula ki sosai toh dole Sai kin ajiye kishi agefe kin nunawa abinda yake so soyayya"yafada tareda yin shiru

"Anya Zan iya kuwa??" Ta tambaye shi

"Zaki iya mana,just try to show that thing a fake love agaban shi"

"Ohk I will try"

"Yauwa sis,Allah yabaki Yaya"

Bakunya tace Ameen.

Suna isa wajen taro akafara shooting dinsu ta kowani bangare, kuma bakaramin dacewa sukayi da juna bah wasu mah sun dauka miji da mata neh...

Wata hadaddiyar tray mai dauke da scissors aka kawo mata ba bata lokaci suka yanka...

"Miye kike nema neh wai??" Taji yatambaye ta soboda waige waigen datake tayi.

Kirkiran murmushi tayi sannan tace"babu komai"

Amma aranta mamakin abinda ya hana shi zuwa take, ai kodan ita ta tura mai invite din dakanta yakamata yazo.

Dukda mah last dasukayi magana yace mata yana son su hadu,kenan mah karya yakeyi...

Sosai abin yamata zafi aranta amma babu yanda taiya danne duk abinda ke damun ta tayi gudun kar Mourad ya fahimta.

Wani tunanin da ya shige ta neh yasa tayi maza taciro wayarta acikin jaka.

Kiran numbern shi take yi amma harya tsinka ba'a dauka bah.

Hadiye duk wani abu tayi sannan ta miyarda wayarta cikin jaka cos aduk rayuwarta Mourad neh kawai take iya mishi missed calls dayawa amma sauran kam inta Kira sau daya ba'a dauka bah toh shikenan.

Yana Lura da yanda take yi ya danne zuciyar shi ya share tinda tace babu abinda take nema amma sosai nutsuwar shi ya koma gareta.

Suna hada ido tasakar mishi murmushi,mutane Sai congratulating dinta sukeyi.

Abinda yabata mamaki shine yanda Fakih da Siyah suke kaffa kaffa daita,sosai suke nuna kulawar su gareta wanda yasa ta aza ayar shakku akansu.

Ganin yanda suke mawa Zulynshi neh yasashi sakar musu fuska sosai harda darawa sukeyi.

Sosai abin yamawa Siyah dadi tinda gashi sanadiyar fake love dinda take nunawa Zuly yake kulata.

Angama taro lafiya, anci ansha sannan kowa yakoma muhallinsa, Siyah kamar karsu tafi cos rabon da tasamu care irin wannan daga wajenshi harta manta,itakam Zuly tasaki ranta tinda tasan yay Mou dinta bason Siyah yakeyi bah.

'''washe gari'''

Zaune suke akan dinning table zasuyi breakfast amma tsantsan gulma irin na Fakih da Siyah Sai suka sanya Zuly atsakiya cos su suka dauko ta daga daki.

Tinanin inda tashiga yake yi amma hangan ta dayayi atsakiyar su Siyah yasa shi sakin murmushi  tareda Adduan Allah ya bama Siyah din miji nagari.

"Yay Mou dina kashigo mana " tafada tana lumshe ido

Lumshe idon datayi neh yasasu tabe baki tareda juyawa baya suka kallo bakin kofa ga mamakin su sukaga Mourad ya harda hannuwan shi a kirji yana kallon su

Cikeda mamaki Siyah tace"ya akayi kikasan ya shigo bayan kin bashi baya

Murmushi tayi sannan tace" aduk lokacin da yay Mou ya bayyana awajen da nake toh ba makawa zuciya tace zata fara sanar dani isowar sa"

Mamakin irin wannan soyayyan su neh ya rufe su ,Sai Siyah tafara jin ashe son da take mishi mah bakomai bane(Kin fara Karaya kenan...hhh)

Tashi tayi daga inda take zaune sannan taje ta mishi iso cikin murmushin ta mai sace zuciyar mutane.

"Barka da safiya yay Mou" tafada dukda dazu bayan an dawo daga masallaci sun gaisa( muryan shi take ji last kafin tayi bacci,kuma shi take fara ji dasafe).

Jan kumatunta yayi sannan yace"ya  Kika kwana?"

"Alhmdllh gidan nan so sweet wlhy' tafada cikin murmushi

"Haka dai Kika ce"

"Muje kazauna kafin Ammi tafito"tafada tana janshi zuwa kan kujera ,yana zama kuwa saiga Ammi mah ta shigo.

Cikin sauri taje ta tare Ammi din tareda mata ina kwana, amsa mata Ammi din tayi cikin fara'a while bakin ciki gona sha biyu suka dabaibayi Siyah.

Zama sukayi suka ci abinci sannan Siyah tace tadan hada wa  Zuly karamin walima.

Sosai suka ji dadin abinda tayi Mourad kam ma harda rungumeta ajikinshi.

Wannan abu yamata sugar sosai itakuwa harda pecking dinshi tana shashafa mai kirji ,abinda take mishi bakaramin dadin shi yakeji bah sai lumshe ido yakeyi kaman Ammi bata wajen amma saidai abinda sukeyi da Mourad  neh yakona wa Zuly zuciya.

Nan da nan kuma annurin fuskanta ya bace wanda Ammi ta lura da hakan.

Excusing kanta tayi domin ganin yanda Siyah take shishigi mai, abin bakaramin dukan kirjin ta yayi bah kuma gashi Mourad dinta ya boye mata

Ganin tabar wajen neh yasashi bin bayanta cikin sauri cos yaga yanayinta ya chanza...

"Zulynah miye sameki??" Yatambaye ta daidai ya cin mata adaki.

Kawar da kanta tayi alamun batason ganin shi, nan da nan hankalin shi yatashi

"Miye neh wai??" Yatambaya
agajiye

"Why do you care??" Ta tambaya a hasale

Zaro ido yayi cos bata taba mishi magana cikin irin wannan sigar bah

"Wai miye kike magana haka"

"Karka takuramin min kaji, kaje kasame wanda kake ta rungumewa nasan tana chan tana jiranka"tafada tareda fashewa da kuka cos in tatina yanda Siyah take shishige mai saitaji zuciyar ta na zafi

Sosai abin yabashi dariya ai nan kuwa yahau darawa ganin kishin shi takeyi..

Dariyan shi neh yasake tunzirata nan kuwa zuciya ta debe ta batareda tasake yin magana bah ta wuce straight wajen sif.

Kayanta ta hau tattara wa  tana zubasu acikin trolley daman sunyi akan zatayi one week neh amma abinda yafaru yau yasa taji bazata mah iya ko kara kwana bah.

Ganin abinda takeyi neh yasa dariyan shi dauketa, cikin sauri ya isa wajenta.

"Haba Zulynah miye abin fushi anan" yatambaya cikin Sanyin murya

Ko magana batayi bah ta cigaba da abinda takeyi ganin tana niyar zuge trolley din neh yasashi finciko ta jikinshi.

Tirjewa tashiga yi ga hawaye sunki daina gangarowa daga kwarmin idonta.

Ganin zata bata mishi lokacine yasashi rungumeta tsam ajikinshi,itakuwa banda bugu babu abinda take kai mishi.

Tureshi tayi da duk karfin da Allah yabata nan kuwa suka rabu

Idonta arufe take fadin"karka sake rungumata kaje wajen wancan ka rungumeta,wlhy tafiyata zanyi bansake kwana daya agidan nan kuma daga yau karka sake min magana  nima bazan sake bah daman kuma tace min aurenta zakayi sbd haka nabarku tare"

Gabadaya ji yayi duniyar namai zafi, wasu zufa ce suka shiga tsatsafo mishi soyake yayi magana amma yakasa.

Kawai saiga hawaye sun fara zubowa daga idonshi, ga sautin kukanta bakaramin wargaza mai kwanya yakeyi bah.

Siyah dake labe abakin kofa tanajin komai tasake wani murmushin farinciki sannan tajuya tayi gaba, tasan ance babu kyau labe amma hakikanin gaskiya sosai abin yamata dadi tinda taji Alkheri,batareda ta gama jin abinda suke fada bah tayi gaba abinta.

Kuma tasha alwashin saita raba tsakanin su tinda ta lura Zuly akwai iya kishi.

Share hawayen shi yayi tare da tattara duk nutsuwar shi yahada waje daya sannan yace

"Zulynah so kike ki Kashe ni neh??" Cakk kukanta yadauke cos yanda yayi maganan muryan shi na rawa.

Cikin sauri tajuya wajen shi still hawaye na zubowa daga idonta.

"Zulynah wlhy Siyah is just my cousin and nothing else kinji na rantse"

"Really??"

Gyada kanshi yayi while zuciyan shi tafara rage tsallen dayake hoping zata fahimce shi.

"Shine tace kai zaka aureta??take kiranka da my sweet??"tasake tambayan shi

"I can explain" yafada

Kura mishi ido kawai tayi sannan tace"with that passionate hug??with that melting smile of yours??and you said you can explain?? Explain what in the first place?? I don't think i need your explanations you should keep that with you cos bazai min amfani bah illa bakin cikin da zai kara min.

Zaiyi magana ta katse shi dafadin" and yes I need some fresh air, I mean I need privacy you should excuse me, and tell Ammi anjima Zan tafi.

Tana gama magana tashige bayan gida tareda slamming kofa, yasan koya buga kofan ba lallai tajishi bah soboda ruwan data kunna.

Jiki asanyaye yafice zuwa dakin Ammi, dukkansu yasama adakin straight wajen Siyah tanufa ai baiyi wata wata bah yatsinka mata mari.

Agigice tamike cos zata iya rantsuwa tinda take arayuwar ta ba'a taba marinta bah.

Fakih mah mikewa yayi, yatsa yanuna mata tareda fadin"miye Kika fada wa Zulynah??"

Nan da nan jikin ta ya hau bari Fakih neh ya janye shi tareda fadin" haba yaya wannan wani irin abu neh?? Gwada ta fah mukayi yi koh itama tana sonka.

Wani tsaki yaja sannan yace"sa ku nayi ??

Girgiza kansu sukeyi, Siyah kam Sai tsine wa Zuly takeyi azuciyar ta.

Zai sake magana kenan Ammi takira shi,ai kaman jira yakeyi daman takira shi din.

Dasauri yanufe ta ,yana zuwa yazauna akasa tareda daura kanshi akafarta yana mai fashewa da kuka.

Gabadaya dukkansu mamaki neh yacika su  jin abinda yakeyi sunsan yana sonta amma basu taba zaton zaiyi kuka soboda ita bah.

Shafa kanshi takeyi tareda fadin"fada min abinda yafaru"

"Ammi nah tayi fushi dani" yafada cikin shesheka gabadaya Sai Siyah taji bah dadi aranta

Ajiyar zuciya tasauke sannan tace"saikuma miye??"

Shiru yayi sannan yace"tace tafiyanta zatayi anjima, tace karna sake mata magana,Ammi DanAllah kitayani bata hakuri kice mata bazan kara bah" yafada hade da tashi yana mai Jan hannunta.

Sai binshi takeyi harya kawo ta gaban kofar dakinta,suna isa ya share hawayen shi tareda bude wa Ammi kofa.

Zai shiga kenan Ammi ta dakatar dashi"excuse us koh soboda naji dadin tsara maka ita"

Gyada kanshi yayi tareda sakin murmushin dabai shirya yinshi bah.

Shiga tayi cikin dakin tasami Zuly akan gado, jin anshigo dakin neh yasata fadin" nace maka I need privacy koh"

Jin ba'a yi magana bah yasata sakin wani kuka

"Yah Salam!!!" Ammi tafurta asarari, jin muryan Ammi yasata tashi tana share hawayen fuskanta.

Murmushin yake ta aza asamar fuskarta tareda nufan inda take

"Sannu da zuwa Ammi, ai dakin min magana nazo" tafada kaman babu wani abin aranta

"Miye sameki kike kuka?" Ammi tafada cikin son jin abinda zatace

"Babu komai fah Ammi, yauwa Yay Mou yafada miki yau zankoma koh??"

"Haba dai??"ta tambaya kaman daman bata sani bah

"Erh Ammi zantafi, zuwa 4 pilot dina zai iso"

"Mun miki laifi neh kike son komawa yau??"

"a'a Ammi"

"Toh miye faru tsakanin ki da Mourad??"

"Babu komai fah Ammi"tafada with full confidence
Chapter 13 · 0% Book details