← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 98

Sashe 28

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fashewa da kuka tayi kaman wanda aka mata Albishirin mutuwa, kallon Iqbal Umma tayi wanda yake kallon Zuly cikeda takaici itama Yusayrah sakin baki tayi tana kallonta

"Kimin magana mana" Umma tafada cikin tashin hankali

Tsagaita kukan ta tayi tareda Jan majina tace"ya hana ni picking"

"Waye"

"Iqbal mana"tafada gatsal kaman yanda tasaba

"Ke shi sa'an ki neh da zaki Kira sunan shi babu ko respect" Yusayrah ta tsoma bakinta 

Wata harara ta zubawa Yusayrah kafin tace" naga dai bada wata elephant nayi magana bah anan"

Kallon jikinta ta hauyi Jin tace mata elephant dan murmushin takaici tayi 

"Zaki shigo hannu na yarinya" tafada acikin zuciyarta

"Ki bata hakuri" yafada yana nuna mata Yusayrah 

Ko iskan daya kwaso shi bata shaka bah tayi cikin daki abinta cikin jin haushin shi

"Umma?"yakira Umma ranshi a bace

Batareda ta kalle shi soboda itama abinda yayi baimata bah tace "Toh miye kakeson ince bayan kai ka tabo ta??" 

Jin abinda Umma tace yasashi ficewa cikin bacin rai, harara Umma ta watsa wa Yusayrah kafin ta shige cikin dakin itama

Cikin sanyin jiki Yusayrah ta tabe baki tareda cigaba da danna wayarta...

```2 days later...``` 

Zaune suke a palourn Umma inda Zuly tayi pillow da kafar Umma idonta lumshe kaman mai bacci ga wayarta akan kirjin ta as usual Jefi jefi Yusayrah dake shan juice ke kallon su tareda tabe baki.

Tarr ta bude idonta tareda tashi zaune tana dafe saitin zuciyar ta

"Lafiya koh" Umma ta tambaye ta

Wasu siraran hawaye neh suka zubo mata cikin sauri ta dauke su da yatsarta dariya tayi tace" Umma nah Yay Mou dina"

Ko jiran abinda Umma ke fada bata to bah tayi waje da gudu kanta ko dankwali babu

Mara mata baya Umma da Yusayrah sukayi da sauri ko Umma bata dago miye take nufi bah

Daidai kofar shigowa fadan taja ta tsaya wasu hawaye nasake zubo mata, sake sharewa tayi tayi murmushin farinciki shimfide asamar fuskar ta.

Jiyayi ana kallon shi ga kuma bugun zuciyar shi daya karu gakuma wani iska mai dadi sai shigar shi yake yi ta koina

Jikake timm sun zube akasa sanadiyar Runguman bazata data kai mishi 

Kowa awajen daskarewa sukayi suna kallon abinda Zuly tayi Iqbal kam tsantsan bacin rai baisan yaushe ya Mike tsaye bah

Dariya ta fashe dashi tareda tashi kafin shima ya tashi, cikin farinciki tace" nafadar dakai wlhy wayyo yau ni Zulyn Mourad nayi karfi"

Jinjinawa yayi ajikin motansu yana Jin kashi 50 acikin damuwar shi na tafiya

Jin baiyi magana bane yasata miyarda hankalin ta gareshi

Mamaki dukkan su suka shiga ganin ko wannen su a rame

Takawa tayi gabanshi tareda daura hannunta a wuyanshi  cikin muryan tausayi tace" Yay Mou dina miye neh haka naga ka rame"

Murmushi yasakar mata tareda rungumeta itama rungumeshi tayi harda lumshe ido

"Kema kin rame sosai" yafada hade da breaking hug din sake Rungumeshi tayi cos gani take tana sakinshi zai tafi

"I miss you" suka fada kaman hadin baki

Cikin kuka take fadin" you don't miss me Yay Mou , you don't kullum sainayi trying numbern ka kullum bana iya bacci mai kyau miye na maka to deserve such punishment"

Ammi ganin Zuly zata karasa mata d'a yasa tace" Zulyn Mourad"

Cakk ta tsaya tana zaro ido, kara Kiranta Ammi tayi sai asannan tajuya cikin Jin kunya tace" daman tare kuke?"

Dariya suka saka sannan Ammi ta rungumeta zuwa jikinta tace"daman taya za'ayi kisan tare muke?"

Ahankali tace" sannu da zuwa"

Ahankali yataka zuwa wajen su Ammi sannan ya rabasu tareda sa Zulynshi ajikin shi yace

"Har an fara karya min doka neh" 

Kallon shi tayi tace" am sorry"

Jan hancinta yayi yace" it's okay Zulynah"

"Manyan baki neh haka" Umma tafada da murmushi asamar fuskar ta

Ammi neh takarasa wajen Umma tareda rike hannunta kafin ta rungumeta suka gaisa cikin nuna jin dadi ganin juna dukda daman basu taba haduwa bah

Cikin larabci Ammi tamawa Mourad magana, Jan Zuly yayi yace" nagaji da tsayuwa Zulynah"

Cire hannunta tayi daga nashi tace" zo in goyeka to nawan"

Dariya yafashe dashi yace" Ina zaki iya Zulynah"

Tsuke fuska tayi tace" nayi karfi fah Yanzu"

Nuna ta yayi cikin zolaya yace"Da wannan uwar raman??"

Turo baki tayi tace"ba duk kai kajawo bah"

Zaro ido yayi yace" kiji tsoron Allah fah Zulynah"

"Wlhy duk kai ka da na rame tsantsan tunanin ka "

Jan kumatun ta yayi yace"Ayyerh sorry"

Gyada kai tayi cikin jin dadi tareda sakalo hannunta a kugunshi

"Keee!!" Yakira ta cikin kausasar murya, atsorace tajuya cos har tsakiyan kanta taji ke din

Su Ammi dake gab da kulewa suka dan dakata

Ahankali shima yajuya yana tunanin wani mahaukacin neh haka wanda ya firgita mai Zulynshi cos gabadaya ko lura da mutanen dake zaune baiyi bah

Karaff idanunsu suka sarke cikin na juna dumm sukaji azuciyoyin su zuciyan Mourad har wani zafi yakeyi

"Sakeshi ki wuce gida" yafada tareda takowa gabansu

Kankame Mourad tayi sosai kafin ta turo baki tareda dagun kafada alaman baxata bah

Ai bata farga bah tafara ganin stars , hannunshi bai gama sauka bah yaji wani irin naushi a hancinshi 

Take jini yafara zubowa kan kace miye har sun fara kokuwa dukda cewan Mourad bashi da wani karfi sosai hakan bai hanashi mawa Iqbal jina jina bah cos ran maza ya baci

Dakyar aka kwace Iqbal a hannun Mourad inda Ammi tarike danta tana mamakin karfinshi dukda ba lafiya gareshi bah

"Ammi ku barni nakoya mai hankali tinda bai dashi" yafada cikin huci

Kwace kanshi yayi daga hannun Ammi sannan yaja hannun Zuly zuwa gaban Iqbal yace" wlhy da mutum ya taba Zulynah toh gwanda mishi yaje ya rungume transformer"

Yana gama fadin hakan yayi cikin gida da Zuly, Zama yayi akan sofa tareda lumshe idanunshi 

Da sallama su Ammi suka shigo dakuma Yusayrah wanda akace ta wuce cikin gida za'a tafi da Iqbal asibiti 

Zama Zuly tayi agefen shi tana jin shakkan mishi magana cos bata taba ganinshi cikin wannan yanayin bah

Sai ta kai hannu zata taba shi sai ta janye cikeda tsoro, tashi tayi zata shige cikin daki taji ya fizgo ta zuwa jikin shi

"Wayyo Allah Umma nah ki bashi hakuri" tafada hawaye na gangaro mata

Hade rai yayi sannan ya bude jajayen idonshi nan da nan Zuly takara tsurewa tana kokarin zille mishi cikin tashin hankali

"Wai miye haka neh you're scaring me fah" tafada cikin kuka sosai 

Sakin fuskan shi yayi  sannan yasa dariya yana mai kura mata ido

Cakk ta tsaya da kuka sannan ta turo baki tace"wlhy bazan yarda bah ai wannan ma Jan alhaki neh"

Dariya duka palourn yadauka amma banda Yusayrah wanda take cikeda mamakin su

"Am sorry" yafada tareda rungumeta

"Mu shiga ciki cos inkika ce na wa'inan drama guys din zaki bi toh bazamu bar nan bah" Umma tafada tareda Jan hannun Ammi zuwa cikin daki

Gyara zaman ta tayi akan cinyarshi kafin tayi pecking din katuwar tabon sallahn goshin shi

Murmushi yayi kadan yana Jin kaman su dauwama ahakan

Dan juyawa tayi caraf idonta ya sarke ana Yusayrah data kafe su da ido 

"Kar mutum ya cinyemu fah" tafada tana yamutsa fuska

Sai alokacin shima ya lura ashe akwai mutum acikin palourn, cikin sanyin jiki Yusayrah ta mike hade da ficewa daga palourn gabadaya

"Ya naga jikin ki yasake wani fresh neh miye sirrin" yafada yana bin jikinta da hannun shi

"Gyara akemin"

"Ashe Zulynah zatayi aure " yafada cikin dauriya

Farr da ido tayi tace" yess ohh bride to be kake ji"

"I see but are you Happy??" Yafada gabanshi na faduwa

"Am so so happy Yay Mou dina wlhy bansan yanda zanyi da rayuwata bah in akace za'a...

_sick🤒🤒_

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo
*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 47*

"Am so so happy Yay Mou dina wlhy bansan yanda zanyi da rayuwata bah in akace za'a fasa aurena da Iqbal"

Runtse idonshi yayi yana maijin kaman ruwan dalma take kwarara mai acikin zuciya

Zuba mata jajayen idonshi yayi yaga yanda take nuna farincikin ta afili cikeda tausayin kanshi yasake runtsa idonshi zuciyar shi na wani irin nauyi

"Yay Mou inace gidansu budurwan ka sun shirya?"

Batareda ya bude idonshi bah ya girgiza kanshi

"Toh ya maganan alkawarimu na aure rana daya?"

Bude idonshi yayi cikin dauriya ya kwakulo murmushi yace"ai some promise are meant to be broken"

Cikeda rashin jin dadi ta turo bakinta tace"Allah yasa hakan shine mafi Alkawari"

Dan dagata yayi daga jikin shi cos sosai yakejin yanayin shi na neman chanzawa yace"Ameen Zulynah"

Murmushi tayi tace" 5 minutes Ina zuwa"

Batareda ta jira cewarshi bah tafita dugudu kaman yanda tasaba, tana fita ya fashe da kukan da yake rikewa tintini

Su Ammi neh suka fito cikin sauri , cikeda tausayin shi suka karasa wajen shi

"InshaAllah kai zata aura koda zan rasa raina akai" Umma tafada tana share kwalla

"No Umma tana farinciki da auren ki barta kawai daman haka Allah ya kaddara" yafada tareda fashewa da wani kukan 

Share hawayen shi yayi yace"pls karku fada mata bazan so ace ta sadaukar da farincikin ta soboda ni bah"

"Amma ai kakai ta sadaukar da farincikin ta soboda kai" Umma tafada mai

Zaiyi magana kenan Zuly tashigo da tray a hannun ta batareda ta kalle su bah tace ga ruwa

Cikin sauri suka hau share hawayen su don karta gani amma cikin rashin sa'a yanayin fuskan su ya bayyana halin da zuciyar suke ciki

Cikin sanyin jiki takarasa wajensu agefen Mourad tazauna tace" miye ke faruwa anan"

Jiyayi bazai iya cigaba da rike kukan bah ai kuwa yasake fashewa da kuka tareda rungumeta tsamm ajikin shi

Mutuwa jikinta yayi kurumus sannan tayi breaking hug din kwallan idonta neh suka yi nasarar zubowa daga cikin idanunta

Murya chan ciki tace"miye neh wai"

" Budurwata zatayi aure Zulynah  bazata aure ni bah bata kauna ta" yafada yana sa kanshi akan cinyar ta

Lumshe idanunta tayi hawaye suka zubo mata tana maijin zafi acikin zuciyarta 

"Waye ita" tafada cikin dakewar murya

Girgiza mata kai Ammi keyi tareda rufe bakinta da hannu
Chapter 28 · 0% Book details