← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 98

Sashe 78

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya suka sa gabadayansu saboda yanayin da tayi maganan"Umma kuyi hoto kafin naje na taho da Ammi"

Fakhiha tafada tareda ficewa dasauri ba tare da ta jira jin ta bakin Umma bah...

Hotunan da sukayi a d'akin bai kirguwa saboda harda na hauka sukayi kafin suka fita saboda daman su kadai aka jira...

Sanye yake cikin wani Black Tuxedo, Black bow tie, white tux shirt na Calvin Klein wanda ya mugun haska shi sai yakara wani irin kyau a ciki gakuma Patent leather takalmin dake kafarsa...

Sai wani irin murmushi yake sakewa kaman an mishi albishiri da gidan Aljanna, sai faman duba agogon hannunshi yakeyi,  tab'a shi da Fakhih yayi neh yadawo da hankalinsa jikinsa

"Yaya muje mu jirasu a waje sun kusa fitowa"Fakhih yafada gyada kai yayi tare da lumshe idanuwansa  kafin suka fice waje...

Kurr yayi da idanuwansa a bakin kofa yana jiran ganin fitowar annurin zuciyarsa, wayarsa da yayi Kara neh ya dauke hankalinsa daga bakin kofa

Daukan call din yayi yafara magana kaman haka" Gaskiya bazan iya making din shi yau ba saboda yanzu ma haka bride 👰 dina nake jira tafito mu tafi wajen event 🎫 din! "

Ban ji miye aka fad'a daga dayan bangaren bah Mourad yasake fad'in" Pardon me Mr Ben i... "

Maganan neh ya makale sanadiyar ido biyu da yayi da adorable Zulynshi wacce ta wani sauya lokaci guda bai san lokacin da ya mika wa Fakhih wayar hannunsa bah, ahankali yafara takawa har zuwa wajensu  inda su kuma suka ja jefe suna kallon sarautar Allah

Yana karasawa wajenta ya mika mata hannunshi, ahankali tayi submitting nata hannun a cikin  nashi, cikin nutsuwa da kware wa yakai hannunta bakinsa tareda sumbatar bayan hannunta

Kit!  Suka ji an daukesu a hoto, murmushi suka sakarwa juna nan ma Philia tasake daukansu, hannunshi ya sakale a nashi hannun tare da janta suka nufi wajen hadaddiyar motansu Wanda aka mishi adon ribbons....

Wani hadadden Hall suka dosa wanda daga nesa ma inka kalle wajen sai ka yabawa wedding planner dinsu(Qudsiyah), 

Kaman wasu stars 🌌 haka suka shiga cikin hall din da yake fitar da sautin romantic song mai ratsa cikin zuciyar mai sauraro, 

Zuly da Mourad dinta neh agaba hannunsu makale da na juna bayansu kuma Fakhih dakuma Maram sai Fakhiha da nata balaraben tukunna Qudsiyah dakuma Raees dinta.

They all are looking so cute and made for each others,  mutane sai kallonsu ake yi cikin sha'awa.

Sanda su Zuly suka fara zama akan royal chairs💺 wanda aka tanadar musamman saboda zamansu kafin sauran ma suka nemi wajen zama

Su Umma da Ammi ansha kwalliya,  gold dinnan da silvern nan sai magana sukeyi, maman Qudsiyah ma duk suna wajen kai gabadaya families dinsu mai martaba sarkin Dubai neh kawai baya wajen shidin ma saboda  bayanan neh kuma ya turo an wakilcesa

Yen Nigeria ma birgijib  na hangosu saboda musamman aka sa jirgi ya kwaso su batareda sun biya ko sisi bah an wani sha heavy makeup kaman zasu je gasar Miss world ko wacce sai feeling kanta takeyi irin anzo USA dinnan 😄

Ga turawa da labarabawa kaman ordern su aka yo saboda yawansu!  Donma hall din kato neh irin sosai dinnan da ansha cunkusu.

Cikin kalle-kallena na hango Momina achan nesa tayi kwalliya babu laifi saboda tayi kyau Amma kallo daya zaka ma ta kagane tayi sanyi sosai sai wani cute guy 👦  agefenta sai danne-danne yakeyi akan waya zanma iya cewa ya manta da cewan a wajen event yake saboda yanda yamiyar da hankalinshi gabadaya kan wayan,  agefenshi kuma wata babe ce sai kalle-kalle takeyi tana wani gyara rigarta takeyi itama ta hadu ba karya jefi-jefi kuma sukan hada ido da Mom data zama so silent...

Wata katuwar cake 🍰  suka fara yanka wa, cikin soyayya suka ciyar da juna, daga nan suka koma wajen zaman su Philia sai aikin daukansu pics takeyi ga sauran apprentice dinta suka barbazu a ko ina na wajen suna daukan masu bukata

Kiransu akayi a cikin filin wajen aka ce suyi rawa,  Mourad da kanshi yace a sa musu wakan perfect  aiko nan salon kid'i ya chanza!  A kugunta ya dora hannunshi tareda rike hannunta guda daya, itama batayi sanya bah ta dora nata hannun a kafadarsa nan suka fara rawa cikin nutsuwa da kware wa ,  nan kuwa wajen ya dauki sowa.

Manyan mutane  suka fara tasowa Ana musu liki da manyan kudi,  bakaramin kuka ya'yan banki suka sha bah, suna komawa aka Kira babban abokin ango wato Fakhih dakuma matarshi Maram don suzo su taka,  ko kunya babu  suka yi rawa iya son ransu wanda akan yasa hawaye silalo wa Mom dake kallonsu

"Ke kuma lafiya kike neman a raina mu? "Wannan gayen yafada cikin takaici, kai kawai ta girgiza mai tare da share hawayen fuskarta....

Rike yake da hannunta sai taku sukeyi ahankali kaman bazasu taka kasa bah, duk cikin wajen babu wanda ya lura dasu sai muryan shi dasukaji yace

"Happy married life! "

*Vote,Comment&Share*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A sweet and pitious Romantic love story

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 108*

Tsit wajen yayi kowa na miyar da hankalinsa kan su, Murmushi neh ya subuce mata, kallon fuskar Mourad tayi kafin takai bakinta dai-dai labbansa sannan ta sumbacesa, murmushi shi ma ya sakar ma ta kafin su ka miyar da hankalinsu wajen Iqbal da ke tsaye da Matarsa Hibba wacce yanayin ta ya isa ya tabbatar maka da cewan a tsorace take

"She has a beautiful face, she's innocent 😇, she has a pure soul, a forgiving heart, she's marvelous, she's amazing, talented,intelligent and a great chef! Mind you she's also a star ✨, she's one in a million" ya fada cikin murmushi yana kallon fuskar Hibba da ta kurasa da manyan idanuwanta

Kallonsa ya miyar ga su Zuly sannan yace" Ko kunsan waye mai wa'inan qualities din da na lissafa?"

Girgiza kai Mourad yayi yana Kallonsa shi ma inda hall din ya dauki shuru suna jiran jin amsan sa, hannun Hibba ya sake tare da takawa har wajen su Zuly sannan ya mika wa Zuly hannunsa alaman ta zo, kallon Mourad tayi sannan ya gyada ma ta kai alaman ta je kafin ta mika wa Iqbal hannunta da su ka sha zanen flowers 💐 💐, a hankali yasaukar da ita ta matakalar hawa, tsakiyar filin ya koma da ita dai-dai inda ya bar Hibba sannan ya saki hannunta tare da nuna ta da hannu yace

"She's the one" habawa nan kuwa wajen ya dauki sowa.

"How I wish zan iya dawowa da hannun agogo baya, Da na gyara kura-kurai na! Amma hakan bazai yiyu bah, kuma bazan gaji da neman yafiya a gareki bah, forgive me sis! " ya fada yana hada hannayenshi waje guda kwalla na taruwa mishi, girgiza kai Zuly ta hau abubuwan da ya ma ta na sake dawowa sabo fil a zuciyarta,

Ganin yanda Zuly ke yi neh ya sa Mourad saukowa tareda nufan wajen su, rike Zuly ya yi ta baya wanda hakan ya yi dai-dai da silalowar hawaye daga cikin idanuwanta

Wani iri Mourad ya ji a zuciyarsa har ya fara dana sanin gayyatar Iqbal wannan wajen saboda tunaninsa na ba shi cewan har yanxu Zuly na son Iqbal din!

Rungumanta yayi ajikinshi tare da patting din bayan ta alaman rarrashi, cikin style ya juya da ita suka koma wajen zaman su mutanen wajen kuma suka sa tafi

"Wlhy wa'inan ma'auratan sun burgeni sosai! "Wata yenmata tafada, juyawa Mom tayi gefen su tace

"Ai they are made for each other! "

Gyada kai suka hau yi suna miyar da duban su kan abinda ake yi, ahankali Mom tamike tareda barin wajen inda wancan yarinyar wato Izma ta bi bayanta da harara!

Ta baya ta bi har ta haura high table straight wajen su Maram da ke ta hiran masoyansu ta nufa tareda musu sallama ahankali yanda bazata janyo hankalin sauran bah!, juyawa Maram tayi adan tsorace ta juya, ganin wacce batayi tsammanin gani bane yasata zaro ido cikin mamaki, hannu Mom ta sa a baki alaman tayi shiru, gyada kai Maram tayi cikin farincikin ganin kawarta cikin koshi lafiya duk da raman da taga tayi, wajen Fakhih da suka fara magana da Mourad ta kalla tareda tab'osa tace

"Bari na je nadawo! " gyada kai yayi tareda sakar ma ta murmushi, ita ma murmushin ta miyar mai sannan ta mike ta bi inda taga Mom ta nufa.

B'ata rai Maram tayi tace"Ai kin kyauta kawata!!"

Murmushi Mom tayi "hakuri zaki yi wlhy kin san basan numbern ki na nan bah shiyasa ban Kira bah gashi ban san ta ya zanyi na tambayi Zuly numbern ki bah shiyasa kawai na ce na bari zamu hadu a wajen event! "

Runguman juna suka yi cikin farin cikin ganin juna kafin Mom tace"nayi missing din ki sosai babe"

"Nima haka kawata! Ya gida ya su Mummy? "

"Suna lafiya saboda bamu jima da yin Waya bah!Daddy na neh dai babu lafiya sosai, shi neh kawai zan bi jirgi gobe na koma KSA na basu letter a wajen aikina a kan zan je ganin gida! "

"Kina nufin yanzu kina wajen Mummyn Izma?? "Maram ta tambaya da mamaki

Cikin murmushi tace"Erh! "

"Amma Mr Ego yayi aure koh?"ta sake tambaya

"A'a tare ma muke da su Wasim neh kawai bai biyo mu bah"

Zaro idanuwa tayi tace"har da wannan Mr Ego din?? "

Dariya Mom ta saka tace" ke Seema fah yanzu bashi da Matsala da ma ni ceh mai creating rift a tsakanin mu shiyasa kika ga mu na samun sab'ani dashi"

Ajiyar Zuciya Maram ta sauke kafin ta Kanne idonta daya tace"Oya tell kun fara soyayya amma? "

Harara ta watsa wa Maram tukun tace"Allah ya kiyaye na so shi! "

Kafe ta da idanuwa Maram tayi tace"Soboda bashi da kyau ko kuma bashi da shares? "

Sunkuyar da kanta Mom tayi cikin rashin jin dadi, cikin sanyin murya tace"Allah ba haka nufi na bah!"

Tab'e baki tayi kaman ba ta damu da sauyawarta bah tace"Toh Miye?? "
Chapter 78 · 0% Book details