← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 98

Sashe 90

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune ya ke a kan kujera hannun sa riƙe da na Yusayrah da ke bacci hankalin ta kwance, kallon fuskar ta yake yi yana jin tsananin tausayin ta ga kuma sabon soyayyar ta na fizge sa daman an ce true love never die

A hankali ta fara motsa bakin ta kaman alaman tana yin magana, kunnen sa ya Kai wajen bakin ta

"Ɗana! DanAllah ku bani ɗana ba lallai na sake samun wani ba, nasan ma bazan sake haihuwa bah! Please ku bani shi! Narasa komai nawa DanAllah kar ka raba ni da abin da ya rage mun!. "

Wasu hawaye ya ji sun sauƙo mai cikin Sauri ya ɗauke hawayen da dayan hannun sa,

Da sallama Su ka shigo cikin Sauri ya saki hannun ta, shigowa Mourad da Zuly suka yi  a hankali suka karasa wajen harara ta balla mai tana cire hannun ta daga na Mourad tare da wucewa wajen Yusayrah

Murmushi Mourad ya yi yana girgiza kan sa, musabaha su ka yi, kallon Zuly ya yi yace

"Wai miye ne wannan ta ke wani share mutane? "Ya tambaya yana kallon Zuly

"Ai ni ba karamin mamaki ka bani ba!" ta fad'a tana kokarin ficewa,

Juyowa ta yi ta ce"Pumpkin! Ina jiran ka a mota kayi sauri"

Iqbal zai yi magana Mourad ya ce" zamu tafi honeymoon ne next month zamu dawo".

_Hey 👋 lovies💞! Show me some love by following me on my Instagram *Mhizzphydo*_ I will really appreciate it if you do!.

_*Vote,comment&share*_

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A sweet and pitious Romantic love story

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 120*

"Ya kamata muyi magana saboda gabadaya kai na ya kulle game da al'amarin Zuly! "Iqbal ya fad'a cikin damuwa

Shafa lausasiyar gashin kan sa ya yi tare da sakin murmushi ya ce"in aka ce nayi ma ka bayani game da chanzawar ta to wallahi karya ce zata fito daga baki na which bazan so hakan ta faru ba! Amma na baka izinin ka Kira ta ku tattauna amma fa that will be after mun gama cin amarcin mu! "

Girgiza kai Iqbal ya yi yana sakin dariya saboda sosai maganan sa ya bashi dariya, san da ya yi mai isar sa sannan ya ce"ba ka da dama wallahi amma na gode in Allah ya kaimu kun dawo zamu tattauna! "

Kafin Mourad ya yi magana har wayar sa ta hau Kara"Sai anjima kafin Zulynah ta yi fushi da ni! "

Ya fad'a yana nufan hanyan waje binsa Iqbal ya yi yace " haba dai ko ta yi fushi ba ta daddewa ta ke sauka saboda ba ta da wuyar sha'ani! "

Cak Mourad ya tsaya yana jin wani irin kishi na tokaro mai kirji, Iqbal da ke kallon  sa ya ce"lafiya kuwa? "

"Sai anjima! "Ya fad'a yana cika wa rigar sa iska, tsayawa Iqbal ya yi yana tab'e bakin sa kafin ya juya shima abin sa

Shiga cikin motan ya yi cikin b'acin rai, kallon sa ta yi tare da turo baki cikin shagwaba ta ce"shine ka je ka yi tsayuwar ka! "

Humming kawai ya yi yana murza steering din mota, hankalin ta gabadaya ta miyar kan sa ta ce "why the change of mood? "

"Please! " ya fad'a yana cigaba da abin da ya ke yi kasan zuciyar sa kuwa cike fal da kishi!" Yanzu abubuwan da ta ke mishi ta tab'a ma wa wani!? All those sweet romances? , those childishness things na ta?"

Shine abin da ya ke rayawa a cikin zuciyar sa, buga steering ya yi wanda hakan ya dan tsorata Zuly da ke aikin kallon sa tana tunanin mai ya b'ata mai rai cikin kankanin lokaci

"In ni ne nayi ma ka laifi a cikin rashin sani to Sorry I love you! "Ta fad'a cikin sanyin murya tare da kwantar da sit din motan...

'''BAYAN WATA DAYA...'''

Sosai suka gurji amarci iya son ran su, kuma kusan kullum sai sun yi waya da gida, Yusayrah ma ta warke sai dai yanzu da walker tanks tafiya saboda kafar ta kuma ko da yaushe Iqbal na hanyan gidan su wanda hakan bakaramin kina ran Hibba ya ke yi ba duk da ita yanzu tasan wace Yusayrah a rayuwar mijin ta, sosai ta lura da take-taken mijin ta da kuma rawar kafan da yake yi a kan Yusayrah!...

Sun je gurare da yawa irin su _Ikogosi warm spring resort,Abraka River resort, Oguta lake, LA manga Luxury Villas, LA champagne Tropicana Beach Resort, Eko Tourist Resort sai kuma Rojenny Tourist Village_ wanda yake Onitsha(Anambra State)

Sai a sannan Zuly tasan ba a kasar waje zalla ake yin honeymoon ba! Musamman lokacin da suka je _Eko tourist Resort_ wanda gabadaya ba shi da maraba da Miami!

Allah in zasu Kara zuwa honeymoon a 9ja zasu sa ke yi saboda it's more than fun! 

Yanzu ma zaune ta ke a kan cinyar sa sai cin kwakwa da dabino ta ke yi ga water melon a gefe daya shi kuma na aikin kallon ta kaman Tv.

"Mine,  gaskiya na iya kiwo ji kumatun ki yanda ya yi wani kato kaman cincin da ya tashi !" Mourad ya fad'a yana shafa kumatun ta

Dakata wa ta yi  da abin da take tukun ta ce"Ko kuma na iya kiwo ba? Ai Ammi na ganin ka zan sha ruwan Addua saboda yanda na miyar da kai! "

"Pumpkin! "Ta Kira sa a hankali tana miyar da hankalin ta kan sa, gira daya ya d'aga alaman ya ne

Fuskar sa ta shafa ta ce"Yaushe zamu koma gida? "

"Ki ce har kin gaji kenan? "Ya tambaya ya na kissing din wuyar ta, mikewa ta yi daga kan cinyar sa tana cewa

"Bari na had'a ma ka abin jik'a mak'ogoro"

Shafa kan sa ya yi yana bin backside din ta da kallo! Kwana biyun nan ba karamin chanza ma sa ta yi ba murmushi ya yi kawai yana godewa Allah da ya bashi muradin ran sa.

Five Alive ta d'auko cikin madaidaicin fridge din cikin apartment din su

"Pumpkin d'auko tumbler a kitchen!" Ta fad'a wa Mourad da ke kallonta

Tsura ma ta idanuwa ya yi ya ce"Ke miye sami kafar ki?"

"Dawowa ta yi ta zauna a kan chinese carpet ta ce"Allah na gaji ne! In kuma baza ka d'auko ba it's fine tinda ba ni zan sha ba!"

Mikewa ya yi yana murmushi sanda ya d'auko kafin ya ce" Allah ni ban ga aikin da ki ka yi yau ba! Daga kan gado sai bayan gida amma ki ce kin gaji?"

"To ban gaji ba ne? "Ta tambaya cikin shagwaba,  zama ya yi a bayan ta tare da matsota jikin sa sosai

Bakin sa ya kai wajen kunnen ta ya ce"miye ki ka yi? "

Zuba five Alive din ta yi a cikin tumbler  ta ce" gashi ka sha! "

Sanda ya sha rabi kafin ya kai tumbler din saitin bakin ta, cikin sauri ta matsar tana matsawa daga jikin sa, cikin mamaki yake kallonta, ganin zata mike ya sa shi rik'e ta

"Mine, kwana biyun nan na lura baki son cin abinci kuma kin chanza gabadaya! what's wrong!?"ya tambaya cikin kulawa

"Ai ina sha su watermelon 🍉 kuma ni bana jin yunwa! "

Cup din ya Kai bakin ta yana fad'in"Just one sip! "

Wani irin ture tumbler din ta yi wanda ya sa shi sub'ucewa daga hannun sa tare da zubewa a kasa tumbler din kuma ya fashe

"Na ce maka ba zan sha ba ka matsa gashi ka janyo fashewar tumbler! "Ta fad'a kaman za tayi kuka, kaman sab'aloto haka ya ke kallon ta

Mikewa ya yi  tare da riko hannun ta ya ce"miye ke damunki? You don't look normal! "

"Normal na ke... "Ta fad'a a hankali, girgiza kansa ya yi tare da cupping din fuskarta cikin damuwa ya ce

"Am worried! Allah you don't look normal ki fad'a mun musan na yi "

"Allah babu abin da ke damuna haka kawai na ke jin bani da appetite kuma wari su ke mun! "

"Miye ke miki wari? "Ya tambaya cikin kulawa

Kaman zata yi kuka ta ce"Komai ma!  har amai amai na ke ji amma ya ki fitowa! "

Zaunar da ita ya yi a kan sofa yana cewa"bari na d'auko miki kaya sai muje asibiti"

Gyada kai kawai ta yi tana lumshe idanuwanta saboda gabadaya bata jin dadin jikin ta kawai dauriya ta ke yi, ya na fitowa da kan sa yasa mata doguwar riga a saman karamin rigar jikin ta, taimaka ma ta ya yi suka fice zuwa asibiti...

Bayan ta gama ma wa Dr bayanai abin da yake damunta ya bukaci ta da suyi test, ba b'ata lokaci nurse ta zo ta wuce da su lab din asibitin...

Gwaje gwaje aka hau mawa Zuly wanda duk da taimakon Mourad ne saboda cewa ta yi ita baza'a ja jinin ta ba!

Zaune su ke a kan kujera suna jiran doctor ya gama duba papern result din ta, gyara zaman glass din sa ya yi cikin turancin sa ya ce"congratulation! your wife is a month pregnant!"

"Excuse! "Mourad ya fad'a cikin son fahimtan abin da doctor ke nufi

Cikin washe baki ya ce"Yeah your wife is pregnant! "

"You don't mean that! "Ya fad'a yana kallon fuskar Zuly da ta yi mutuwar zaune tsaban farin cikin da ke cin ta

"Alhmdllh! Thank you so much doctor "ya karasa fad'a cikin tsananin farin ciki yana bashi hannu, shima hannun ya mika mai cikin jin dadi

"Mine! Kina d'auke da ciki na a jikin ki! "Ya fad'a yana mikar da ita tsaye girgiza kai ta yi saboda gabadaya bata san a wani irin yanayi ta ke ba!

Card ya mik'a wa doctor ya ce"do call me please! "

Washe baki ya sake yi ya ce "OK sir"

Thumb up kawai Mourad ya ma sa sannan suka fice daga office din, tin a cikin mota ya fara kiran yen uwa da abokan arziki yana fad'a musu kyakyawan labari
Chapter 90 · 0% Book details