← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 98

Sashe 38

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Umma tayi tace"ai kullum cikin yi miki nake yar Umma"...

"Thank you"Iqbal yafada bayan tagama waya

Kuka tafashe dashi tace" bantaba mawa Umma nah karya bah amma kasa namata"

Jawota Lutfiyah tayi takwantar daita ajikinta tana bubuga bayan ta alaman rarashi, ganin Zuly take Kaman Kanwarta shiyasa tadau aniyar jawota jikinta domin jin matsalar ta...

Zaune take akan gado while Lutfiyah na hada mata tea wayan ta yadau Kara, kallon fuskar wayan Lutfiyah tayi tana tunanin a inda tataba jin sunan dayake yawo a fuskar wayan, mika wa Zuly wayan tayi...

"Yes Chirstine" tafada bayan ta dauki call din

Magana chirstine tayi daga dayan bangaren Zuly tace

"Kifada musu bazan samu yin aikin bah cos av been hospitalized su bawa Wani kawai"tana gama fadin haka ta katse wayan tareda karban cup a hannun Lutfiyah data kafeta da na mujiya

Da murmushi afuskar ta tace"nagode anty"

Shafa kanta tayi tace" ure welcome"

"Kinsan miye?" Tafada tana kallon Lutfiyah

Girgiza kai tayi tace"sai kin fada"

Lumshe idanunta tayi tana sakin murmushi tace"for the second time inajin dadi Kuma ta sanadiyarki and yanda kike kula dani reminds of my Yay Mou"

Gyara zama Lutfiyah tayi tace"waye shi?"

Juya bayanta tayi tayaye rigarta tace "wanda yabani wannan sunan"

Dan zaro idanu Lutfiyah tayi da mamaki ganin Wani well designed *Zulyn Mourad* rubuce da tattoo awajen

"Wani matsayi yake dashi azuciyarki da har kikayi tattoo da sunanku a hade abayanki"

Murmushi tayi tace " son juna mukeyi sai daga baya nagane ashe kaunar shi nakeyi amma it's too late alokacin"

"Miye kike nufi da it's too late?" Ta tambaye cikin rashin fahimta

"Erh ranan dana fahimci Ina kaunar shi shine ranan da aka daura mana aure da Iqbal"

"Kina nufin kinada aure kuma Iqbal mijinki neh? " ta tambaya cikin mamaki

"Erh amma a ranan da aka kawo ni a ranan yamin saki daya kuma yadawo dani" tafada tana share kwalla

Girgiza kai Lutfiyah takeyi cikeda tausayin Zuly "Yanxu shi Mourad din na ina"

Cikin rawar murya tace" Iqbal, Iqbal chased him away ranan da ya kawo ni, korarshi yayi batareda yabari ko Sallama munyi bah I hate Iqbal for that"

Takarashe maganar ta cikin kuka sosai, petting dinta Lutfiyah tayi tana shafa kanta

Wayan Lutfiyah neh yayi katse su jawo wayan tayi ta Kara akunne cikin sanyin murya tace" yanzu waye zai mana tinda tace bata da lafiya?"

Shuru tayi tana jin abinda ake fada daga dayan bangaren kafin tace"toh shikenan" sannan ta ajiye wayan,kallon fuskanta Zuly tayi tace

"Miye faru Anty?"

"Nothing serious daman fah munji labarin Miss Zulfa tana Nigeria neh Kuma daman akwai aikin mukeson yi shine muka kai Mata and yanzu wai bata da lafiya" tafada cikin rashin jin dadi

"Miss Zulfa?" Ta tambayeta cikin mamaki

"Erh mana wannan billionaire din bah maybe ma bakisanta bah"

Dariya tayi tace" nikuwa nasanta"

"Banson zolaya"

"What if nace miki ni ceh Miss Zulfa"tafada tana kanne mata ido daya

Dariya tayi tace"then I will say karya kikeyi"

Bata fuska Zuly tayi cikin shagwaba tace" shikenan tinda nine nake karya"

"Haba kanwata na isa incemiki karya kikeyi sorry kinji ai tatsuniya kike bani"

Zatayi magana Lutfiyah ta katse ta da fadin "pls karkiyi magana just rest kinji"

Gyada kai Zuly tayi tana dan murmushi...

_bayan an sallameta_

Sosai Iqbal yake Kula daita kaman wata kwai har yar aiki an yakawo yanxu Wanda zata nayin aikin gida dakuma girki kafin Zuly ta gama warwarewa, kullum cikin siyo mata kayan motsa baki irin su :chocolates,biscuit , sweet and so on...

Tsaye take akan stairs tana kallon Iqbal dake zaune akan kujera yana shan juice, kallo kwallin maganin hannun ta tayi sannan tafara saukowa , jin kamshinta yasashi dagowa yana kallon inda take

Murmushi tasakar mai tace"sannu da hutawa"

Gyada kanshi kawai yayi yana kallonta daga sama cos dressing dinta yamai sosai, hannu ya mika mata alaman tazo

Kundai San mutumiyar Ku akwai San jiki ba bata lokaci takarasa ta zauna agefenshi tareda dora kanta akafadar shi tana sakin murmushin dayake shidar da Yay mou kafin ta mika mai kwallin tace

"DanAllah wannan zaka siyomin a chemist"

Karban kwallin yayi yace"maganin miye haka?"

"Maganin Ciwon ciki neh, shi nake yawan sha"

"Ohk zuwa dare zanje" yafada tareda sipping juice dinshi

Tashi daga jikinshi tayi cikin shagwaba tace" taab wlhy ni yanzu nakeso dare yayi nisa"

Wani kallo dayasata mikewa yamata yace cikin daura fuska yace.....

_nace miye ke Shirin faruwa neh😎_

#team ZulynMourad
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 60*

Wani kallo dayasata mikewa yamata yace cikin daura fuska yace"ke kam ba'a iya miki gwaninta wlhy"

Bubuga kafanta tahauyi akasa tana turo karamin bakinta tareda matsawa gefe tace"nidai yanzu nakeso haka kokuma kabani izini naje nasiyo dakaina"

Harara ya wurga mata yace" driver baikusa yafita da Heartbeat Kuma nasan bayanzu zasu dawo bah kuma ni dinnan sai dare na fita"

Tabe bakinta tayi tace"toh kabani key ai naga na  iya mota"

Kallon kin raina minhankali yamata kafin yace"kin zata bacci akeyi a tuki?ki bacemin anan ko ranki ya baci"

Murguda bakinta tayi tareda yin gaba tana magana kasa kasa

"In na rikeki zaki sha mamaki" yafada daga inda yake zaune idanunshi nakan ta" Kuma karna rigaki isa dining"

Batareda tayi magana bah tayi sama abinta, itafa ko kadan bata son ace taci abinda yafito daga hannunshi kawai dai batada choice neh, straight Wani daki na  dabam tashiga , shima ya hadu iya haduwa Amma babu bed awajen,  su tarkacen abubuwan zanen taneh awajen wanda koda yaushe cikin yi take, wasu frames neh manne a garu wanda akwai Zane acikinsu , wajen wani katon frame tanufa inda ta yaye kyalen kai , wani haddaden zanen ta da Yay Mou  dinta neh ya bayyana wanda suke zaune alokacin da ta dafa mai tuwo a Azare, shafa fuskar hoton tayi cikin hawaye tace

"Ina mugun kawar ka Yay Mou dina, yaushe zaka waiwayo ni?, nadai San ba haka kawai zakaki nema na bah, Allah yasa dai kana lafiya"...

Saukowa takeyi ahankali tana ya mutsa fuska tareda rike ciki Alamun ciwo yake mata , dubansu suka miyar kanta Suna kallonta yanda take saukowa a yangace Kaman wata Miss world.

Karasawa tayi kafin ta zauna Iqbal yace "miye nafada miki kafin ki haura sama?"

Zama tayi akan kujeran cikin sanyin murya tace " Am sorry banjin dadi neh saikuma bacci yadauke ni"

Kawar da kanshi yayi yana mai cin abincin gabansu, kallon Yusayrah tayi cikin muryan raini tace" har kin dawo neh Sayrah? Toh ya gajiyan... "

Kallonta Yusayrah tayi tareda gyada kanta cikin tsoro gabanta na faduwa

"In mutum bai daina abinda yakeyi bah am afraid  to say what will happen next"

Yusayrah zatayi magana kenan Iqbal yariga ta da fadin" In kika sake magana awajen zan bata miki rai"

Tabe bakinta tayi cikin mouthful din abinci tace "kullum sai kadinga fadin zaka bata min ra...." bata gama magana bah ta kware, ai kuwa tadinga tari Kaman bah gobe cikin sauri Yusayrah ta taimaka mata da ruwa amma maimakon ta karba saita dauki ruwan gaban Iqbal daya ke zaune Kaman baisan abinda yake faruwa bah

Bayan tari yalafa neh ta kalleshi taga sai cin abincin shi yakeyi hankalinshi kwance wasu sirarun hawaye  neh suka gangaro mata soboda tunowa da Yay Mou dinda tayi yanda yake finta shiga tashin hankali  in wani abu yasameta acikin sauri tadauke hawaye tareda mikewa tabar dining din

Da gafen ido yaraka ta yana ya mutsa fuska tareda Jan Wani guntun tsaki, ture plate din gabanshi yayi don gabadaya jiyayi abincin ma ya ishe shi, kallon shi Yusayrah tayi tace" lafiya dai koh??"

Yake yayi yace " lafiya  kawai dai abincin ya ishe ni neh"

Murmushi tamai tace"ohk"

"Pls inkin gama kice mata tafito muje siyan maganin" yafada yana barin wajen

Ajiyar zuciya  Yusayrah  tasauke jin bai nemi Karin bayani gameda abinda Zuly tace dazu bah...

"Babu" shine abinda yafada bayan yashigo cikin motan, ahankali tadago kanta daga gaban mota cikin muryan jinya tace"yanzu ya kenan?"

"Nasiyo miki Wani daban"

"Wani Kuma?"

"Erh sunce wannan din babu shi a Nigeria only God knows daga Wani duniya aka siyo miki wannan"yafada yana murza steering din mota

"A chemist din uncle din precious muka siya" tafada tana miyarda kanta gaban motan while hannun ta daya akan cikinta

Tabe baki yayi yacigaba da tukinshi batareda ya sake kallon koda gefenta bah, Suna isa gida yayi parking tareda fita daga motan, har yakai bakin kofan shiga baiji ta daga bayanshi bah,

Juyawa yayi yaga ko saukowa daga cikin motan batayi bah, cikin bacin rai yakoma baya tareda bude motan Kaman mai Shirin ballawa

Afirgice tafarka jin anbude motan , bata gama  watsakewa bah taji anjawota daga cikin motan yajefar daita waje har sanda takusan faduwa kasa

Zai rufe motan kenan idon shi tahango mishi abinda yakusan sashi amai,  Wani sabon bacin rai yaji, he can't believe ace da wannan kazantan yake zaune acikin mota tin dazu,

Tafiya tafara yi taji anjawo gyalenta dakarfi daga baya,yana sakin gyalen tafadi tabaya ,kuka tafashe dashi acikin brain dinta kuwa searching din laifin da tayi mai takeyi amma amsa dayake bata shine _can't load search results_.

Bata gama saisaitawa bah taji an mikar daita tareda bata wata sweet Mari a fuska wata sabuwar kukan tasake sakewa wanda yajawo hankalin Maigadi ,

"DanAllah kayi hakuri" tafada cikin jinjiki cos ga Ciwon ciki gakuma Ciwon azaban dayake Shirin yimata,Kuma daman kalman hakuri baya mata Wuyan fadi cos habit dinta neh bada hakuri akan lokaci

"Ke wata irin kazama ce"tatambayeta cikin bacin rai yana nuna seat dinda ta tashi  wanda ya stain da jini dayan hannunshi rikeda bayan  wuyar riganta

Girgiza kai tahau yi tana mai runtsa ido cikin rawan murya tace "zuwa yayi, amma kayi hakuri zan goge"

Expensive Gyalen jikinta daya fadi kasa ya sunkuya ya dauko tareda jefa wa kan seat din yace"oya fara gogewa"

Bude idonta tayi ta kalli favourite veil dinta wanda Yay Mou yasiyo mata matsayin gift din success dinta na biyu akan jini, wani irin bakin ciki  taji ya ziyarci ranta, cikin sauri  ta dauki veil din ta duba,unfortunately har jini ya shafu kasancewan yana Mata rushing dalilin tea din datasha...
Chapter 38 · 0% Book details