← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 98

Sashe 22

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A ganinka bah??, Kabani mamaki Malam!ace agaban ka matan ka suka kirani da juya amma bakayi komai akai bah, shine yanzu zaka ce karna tafi??, Hmm tafiyata zanyi kuma ga Zulfan saiku yi yanda kuke so daita"

"Umma nah kiyi hakuri ki tafi dani danAllah karki barni anan bana son su ni ke nakeso"

"Kiyi hakuri Ramatu ki yafe mana" suka fada cikin hadin baki

Umma da zuciya tagama ciyowa tace" ku rike hakurin ku cinye ta ma, nabar muku ita kuma nagode"

Tana gama fadin hakan tayi hanyan fita daga cikin palourn timm sukaji akasa...

Cikin sauri suka kai hankalin su kanta, arikice Umma ta rugo, Mourad Kam numfashin shine ya dauke cakk ganin halinda Zulynshi tashiga...

"Wayyo Allah nah kitashi kinji y'a ta wlhy inasonki ki tashi kar ki barni, wlhy in babu ke arayuwata nima zan iya rasa raina soboda na tabbata banida wani sauran amfani"

Rungume Umma ta cikin murna tace "daman nasan bazaki tafi ki barni bah"

Ahankali Umma ta dagota daga jikinta tace" baki da kai neh dazaki nayin irin wannan shirmen,da zuciyata ta buga fah?"

"Kema kidaina cewan zaki barni" tafada a shagwabce

"Karki barni kinji??"

Hawaye neh ya gangaro wa Umma ta gyada kanta tace" tashi ki dauko kayanki mutafi abinmu, muje muyi rayuwanmu mubiyun mu koh??"

Share hawayen Umma tayi hade da gyada kai sannan ta tashi.

Tana juyawa tahange Mourad jinjine ajikin kujera ya kurawa waje data fadi ido ko kiftawa bayayi.

Karasawa tayi wajen shi tace" yay Mou dina?"

Ganin bai amsa bane yasa su mai martaba karasowa wajen shi cikin tashin hankalin.

Tsungunawa tayi daidai wajen shi takara Kiran shi amma nan mah shiru            

Hannu tasa adaidai saitin idonshi ko zai kifta amma still

Wani yawu mai daci ta hadiye daidai lokacin da aka taba kafadanta.

"Shikenan balarabe ya mutu adakin  Ramatu"  Zuwaira tafada tana daura hannu akai

"Bangane ya mutu bah??" Tafada afirgice tana kallon Zuwaira

Itama Umma Zuwaira take kallon akidime

"Akawo ruwa" Malam yafada cikin jarumta tareda katse su.

Da sauri Zulfa ta tashi har tana cin tuntube.

Tana dawowa tamika wa Malam ruwan Addua ya tofa  sannan ya watsa wa Mourad amma abin mamaki ko motsawa baiyi bah

Wata irin kara Zulfa tayi tareda zubewa aji....

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 38*

Wata irin kara Zulfa tayi tareda zubewa ajikinshi

Firgit yadawo hankalin shi dalilin faduwar datayi ajikinshi.

Hankali tashe su Umma sukayi kansu,dagota Umma tayi daga jikinshi tace" Zulfa gashi ya tashi ki bude idon ki"

Jin abinda tafada yasa Mourad yayi saurin karban ruwan hannun Malam ya shiga yayyafa mata.

"Wayyo yay Mou dina!" Tafada batareda ta bude idon ta bah.

"Gani nan Zulynah" yafada daidai kunnenta , ahankali tashiga bude idonta.

Sarkewa idonsu yayi takara rufe idon sannan ta bude, ganin bai bace bah yasata sakin sanyayyar murmushi.

Shima din murmushi ya miyar mata ya mikar da ita.

"Alhmdllh"Malam yafada cikin Jin dadi ganin babu abinda yasame su.

"Yaushe zaka koma??" Yatambaye Mourad

"Gobe neh in Allah yakaimu" yafada cikin nutsuwa

"Ohk InshAllah tareda Zulfa dakuma Ummanta zaku taf..."

"Marwa din fah??" Uwar gidan Hindatu ta katse shi

"Nagama magana da Zulfa da Ummanta neh kawai zasuje" yana gama magana yayi ficewar shi batareda yakara jin abinda suke son fada...

Ajiyar zuciya Mourad yasauke jin tareda Zulynshi neh zasu tafi, cikin sanyin jiki su Amarya da Uwar gida suka fita...

Zama Umma tayi akan kujera tareda runtsa idonta.

"Umma na..."

"A'a Zulfa kinji ai koh ni bah Ummanki bane" Umma ta katse ta

"Koda bake kika haife ni bah ni awajena har abada banida wacce tafi ki aduk duniyar nan.."

"Zulfa na..."

"A'a Umma nah zanfi jin dadi in kika cigaba da kirana da yar ki soboda gabadaya Zulfa baiyi dadi abakin ki bah" ta katse Umma

Rungumeta Umma tayi cikin Jin dadi"nagode!nago...."

"Umma nah ai babu godiya tsakanin uwa da y'a , ni yakamata na gode miki bake bah" tasake katse Umma din

Sosai mamaki yacika Mourad ganin ashe ba itace ta haifeta bah sosai ya jinjina wa Umma acikin zuciyar shi kuma girmanta sosai yakaru awajen shi...

"Mun gode Umma" Mourad yafada.

Gyada kai Umma tayi kurum tana jin wani irin dadi na ratsa tah...

```washe gari...```

Daga jiya zuwa da safen nan babu wanda baisan da zancen tafiyansu Zulfa bah.

Wasu sun musu murna while wasu sun nuna rashin jin dadin su akan batun...

Mai martaba Malam da kanshi yamusu rakiya airport soboda yin bankwana da Umma dukda yasan ba magana zata mishi bah...

```AIRPORT```

Tsaye suke suna jiran akira su , Zulfa sai kallekalle takeyi tana yaba wajen azuciyarta.

Mamaki neh yakamashi ganin bata wani nuna kauyancin nan da akeyi bah.

Ba da dadewa bah aka fara kiran su, tashi sukayi suka mawa su Malam Sallama...

Sun fara tafiya kenan Umma ta tsaya cak.

Komawa baya tayi wajen Malam tace" Nagode,kayafe min duk abubuwan dana maka pls.."

"Ba komai Allah ya yafe mana gabaki daya" Malam yafada da murmushi asamar fuskarshi.

Itama murmushin tamiyar mishi tareda juyawa tayi tafiyar ta, sosai zuciyar shi ta mishi dadi dalilin murmushin datayi mai.

Cikeda farinciki yakoma garin Azare tareda musu Adduan sauka lafiya da saduwan Alkheri...

   🛫🛫🛫✈️✈️✈️🛬🛬🛬🛬

```Oxford international airport ,USA```

Saukan su kenan wani bature ya iso wajensu domin  daukan su,kasancewan yasan yaushe zasuyi landing...

Sannu da zuwa yamusu inda ya karbi dan akwati biyun dayake hannun su kasancewan basu taho da tarkace bah.

"Umma agida na zamu fara sauka kafin gobe mun huta sai aje a zabar muku gida" Mourad yafada lokacin da suka shiga cikin motan inda shi yashiga gaba while su Umma na baya

"Toh, Allah yabiya ka Mourad"

"Ameen Umma"yafada yana leken Zulynshi data yi lamo ajikin Umma wanda alamu sun nuna ta gaji neh ta mirror...

Haka suka karaso hadadden gidanshi dake Bell Street acikin Jericho Oxford.

Sosai tsarin gidan ya burge su,sai juye juye sukeyi suna karewa gidan kallo.

Yen aiki neh suka fifito suna mawa ogansu barka da dawowa, sannan suka gaisar da su Umma mah...

Cikin gida suka nufa inda already abinci na jiransu akan dining table, sallah da wanka suka fara yi sannan suka juyo dining don cin abinci.

Abincin dai gashi kaman bazaiyi dadi bah abaki amma abin mamaki ba karamin dadi yayi bah, inda alokacin mah a plate daya suke cin abincin.

Ko kunyan Umma dake wajen mah Mourad baiji itakuwa Zulfa daman bah kunya take dashi bah...

Suna gama cin abinci yace zaije asibiti duba new patient dinda aka kawo nan Zulfa tace saita bishi gashi kallo daya zaka mata kasan tana tareda gajiya amma hakan ta matsa har su fice tare...

"Garin yamiki kuwa Zulynah?"

"Hmm toh gashi nan gashi nan dai bah laifi amma gaskiya ana sanyi"tafada tana gyara khimar dinta

Zaro Ido yayi yace"karki cemin kema kina jin sanyi da wannan zumbuleliyar khimar din ki"

"Allah yay Mou dina wannan khimar bai tare min komai"

"Toh in muna dawowa zamubi boutique musiya cardigan mai tare sanyi"

"Yauwa harma da irin wa'incan kayan"tafada tana nuna wasu baturai masu kananan skirts"

Da dan mamaki take kallonta cos shi azatonshi zata Kira su da yen iska amma saiyaga sabanin hakan

"Ke zaki iya sawa neh??"

"Erh mana zan iya sawa amma in kace karna saka ai bazan sa bah".

"Karki damu zan Siya miki"yafada daidai yayi parking a lott.

Fitowa yayi itama tafito sannan ya riko hannunta suka jero kaman yaya da kanwa...

Gaishe su aka dinga yi harya karaso kofar main office nasu inda neurologists ke haduwa.

Bude kofa yayi yashiga har lokacin hannun su na cikin na juna.

"Welcome back Mr Mourad" suka fada in chorus

"Tnx"yafurta a hankali

"Hey pretty girl" wani bature yafada

Murmushi tasakar mai dukda bata gane miye fada bah amma tasan miye Girl.

"What's your name baby??" Wani yasake magana

Matse hannun Mourad tayi sai ya miyarda hankalin shi kanta cos lokacin har ya fara duba file a hannun wani.

"My name is Zulyn Mourad" tafada ahankali gudun karta kofsa tinda ta lura turancin su sai an lankwasa harshe gashi ita bawai tana jin turancin bane.

Wani sanyayyar murmushi yasake Jin abinda tace,su kuwa sai maimaita Zulyn Mourad sukeyi...

"Is she your sister?" Wani yatambaye shi

"No she's my would be wife" yafada yana sake sakin murmushi.

Zaro Ido sukayi suna nuna ni da mamaki,shikuwa har yanzu blushing  yake nikuma bah baka sai ido ina ta Allah Allah mufita natambaye shi abinda suke cewa cos sosai naji na tsargu...

Muna fita ya bude min mota na shiga zanyi magana ya katse ni da fadin"kina aji nawa neh??

Sanda na girgiza kaina nace" in...

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 39*

Sanda na girgiza kaina nace" ina jss 3 neh  wancan watan mah mukayi BECE din mu"

"Ohk, amma result din yaushe zai fito?"

"Nima bansani bah" tafada tana bude drawer din motan.

"Miye wannan??" Ta tambaye shi tana nuna abinda yake cikin drawer din

Wani irin dariya yayi tareda shafa doguwar suman kanshi jin tambayan data mishi.

"Yanzu ke da miye wannan ya miki kama??"

"Erh dai yayi kaman...

Azaro ido tayi cikin mamaki tace" daman kana shan chocolate neh"

"No lokacin dana je gida ne sister na tasa min a aljihu wai nasha a hanya shine fah namanta sanda nadawo na jefa su acikin nan"

"Toh in sha??"ta tambaye shi

"Erh ki sha" cikin Jin dadi tafito dashi ba bata lokaci ta bude.

Gustiri daya nayi nakai sauran bakin shi, ba shiri ya bude bakinshi nasamai.

Daidai sun gama cinyewa suka iso wani katon boutique.

Sauka sukayi suka shiga cikin boutique din.

Wajen kayan sawa muka nufa inda nadinga kwasa shima na tayani

Kusan guda ishirin muka dauka, danaga yaki karewa nace mai ya isa haka cos nalura baiki ace muyita kwasan Kaya bah.

Bayan ya biya kudi da debit card nashi kasancewan babu kudi a hannun shi,kayan suka kai mana  mota.

Muna isa wajen motan nace ni abaya zan zauna dakanshi ya bude min baya na shiga shirmen da akace na kware ayinshi nadinga zuba mishi shikuma sai biye mun yakeyi.
Chapter 22 · 0% Book details