← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 98

Sashe 94

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rungume ta Fakhiha ta yi itama tana sake fashewa da kuka"kai bana son shashanci fa!"

Ammi ta fad'a cikin zafin rai saboda even she is not herself so ta ke yar mutane ta samu lafiya saboda this crying they are crying(hhhh A.U can relate)  bazai haifar da d'a mai ido ba

"Ke ja dubo Mourad a gida! "Ammi ta fad'a a hankali saboda ta san yan chan gida yana rigzar kuka

Mikewa ya yi ya fita inda Ammi ta miyar da dukkan hankalin ta kan Zuly, hannun ta  ta rik'o ta ce

"Haba ZulynMourad din ta! Ki daina kuka kinji ko ke baki yarda da kaddara bane? Haka fa Allah ya kaddara!  Please ki daina kuka kin dai ji yace zai miki wani cikin? Kar ki damu wani cikin inshaAllah za ki sake haifan wani ukun kinji? " ta fad'a tana share hawayen ta girgiza kai Zuly ta fara yi tare da shagwabe fuskar ta ta ce

"Oho! Ba uku zan haifa ba! "

Murmushin yak'e Ammi ta sake ta ce"Hudu ki keso kenan? "

Girgiza kai ta sake yi ta ce"hudu kuma Ammi? Ni uku sau biyar zan haifa a lokaci daya! "

Zaro idanuwa Ammi ta yi su kuma sauran basu san yaushe suka fashe da dariya ba

"kaiii... Wannan zalama har ina? "Qudsiyah ta tambaya tana share hawayen fuskar ta

"Erh mana guda 15 zan haifo muku lokaci daya ko baku so ne? "Ta tambaye su tana jan hancin ta

"Nikam ban k'i ki haufo mana 50 a lokaci daya ba wallahi waya ga ZulynMourad an tashi a aiki! "Ta fad'a cikin zolaya

Kaman zata fashe da kuka ta ce"Kin gan su ko Ammi"

"Sorry kinji? Yanzu bari na had'a mana abinci sai muci? "Ammi ta fad'a tana kokarin mikewa

"Nikam Ammi da kin bar abincin nan wallahi! "Ta fad'a a hankali hawaye na sake taruwa a idanuwan ta, babu yanda ba'a yi da ita a kan ta ci abinci ba amma tak'i daga karshe ma fashe musu ta yi da kuka babu yanda suka iya haka suka hakura...

A gida kuwa Ammi na koma wa ya shige d'akin Ammi, toilet ya shiga ya je ya dauko towel da ruwa, haka ya dinga goge jinin da ya bushe yana matsawa da hannun sa har san da ya ga wajen ya fita tass kafin ya bari kuma yana goge wa yana hawaye

Bai tashi fashe wa da kuka ba sanda ya gama shanye maganin sa, hoton Zuly ya d'auko yana kallo yana kuma kara volume din kukan sa! Da ba dan sound proof bane kofan da babu wanda bazai ji kukan sa ba acikin gidan

Lokaci daya kammanin sa ya sauya, ya wani rame kaman ba shi ba, idanuwan sa da labban sa sun yi shegen ja, daga karshe ma karfin maganin ya Lula dashi duniyar bacci....

Wani irin tausayin su ne yake tsinkawa Fakhih zuciya, shafa fuskar yayan sa ya yi yana tuna lokacin da ya kira domin sanar da su kyakyawan labari lokacin da Zuly ta yi ciki, tunawa ya yi da d'akin da yayansa ya yi furnishing da kansa saboda babies din su wanda ko maman babies din ba ta san ni yana tuna lokacin da Mourad ya ce

"Dude wallahi ina cikin farin ciki!  Can't believe nan da wasu watanni zan zamo uba! Zan zamo dadyn babies, wallahi ji na ke kaman na jawo sauran watannin da suka rage! "

"Kai yaya wannan zumudin fa? "

"Allah dai ya kaimu kuma insha Allah zan karb'i leave a asibiti in ya saura mata one month ta haihu! "

"Ai ko baka nan mu zamu je da ita! "

"Hmmm bazaka gane bane kasan condition din mine so na ke ta sauk'e nauyin da ke kanta kuma wani sashi na yana cike da fargaba saboda basan ya haihuwan zai zo ma ta ba kasan she's not too well shiyasa na ke son a yi komai a gabana! "Ya fad'a a hankali...... mikewa Fakhih ya yi tare da kashe mai Ac sannan ya fice daga d'akin!...

Fitowar ta kenan daga wanka wanda ya yi daidai da farkawar sa daga bacci, a hankali ta Karaso wajen sa jikin ta d'aure da towel

Zama ya yi tare da had'e ransa tamau kaman bai tab'a dariya ba, murmushin yak'e  ta d'aura a kan fuskar ta saboda a halin yanzu shine abin da zata iya yi

"Idan jinin ya d'auke you will get me pregnant again ko?"ta tambaye sa tana kokarin d'aura hannun ta a kafadarsa

"Don't you dare touch me da wannan hannun na ki! "Ya fad'a babu alaman wasa a muryan sa, turo baki ta yi kaman yanda ta saba sannan ta karasa haurawa kan gadon

Ganin tana son runguman sa ya sa shi hakad'a ta da karfi wanda da ba dan tana kan gado ba to da ta ji ciwo

Arazane ta ke kallon sa sai so take ta yi magana amma ta kasa, cikin rawar murya ta ce"miye na yi maka?  in na maka laifi a rashin sani toh Sorry I love y... "

Bai bari ta karasa ba ya daka ma ta tsawa wanda yasa ta sakin fitsarin da bata shirya saboda kid'ima

"Keep your sorry! Why! Why!! Ban tab'a tunanin haka daga gare ki ba! I thought duk duniyan nan babu wanda ya kai ni sa'an mata! Har nake cewa dama haka Allah ya hallici kowace mace ina Adduan Allah ya bawa kowani mazan kirki irin ki saboda yanda kike to me you're so innocent, so loving, so perfect you're.. You're... Ashe kallon kitse na ke mawa rago ashe da haka duka mata suke da _maza sun fad'i_.... Am highly disappointed in you! "

Cikin kuka ta ke girgiza kan ta sanda taga ya kai aya kafin ta ce"don't judge me haka! Just hear me out I can expla.... "

"Shhhh.. Keep quiet... Ya fad'a yana sa hannun sa a baki, cikin kunan rai ya ce... Explain my foot.. Explanation na ki zai dawo da yaran da kika yi wasting din su ne? Answer me"ya karasa da karfi

"Let forget about  the past we can still make another baby! "Ta fad'a cikin kuka

Wani irin bugu ya kai wa gadon tare da nuna ta da yatsa ya ce"make baby! Ai babu ni babu kara wasting time dina a kan ki! Wato in miki wani cikin ki kara zubarwa? "

Cikin kuka ta ce"Wallahi ba zubarwa na yi ba!  Haka Allah ya kaddara! Already Allah ya riga da ya ce zan samu miscarriage so let move on"

Wani hawayen da suka zubo mai ya share tare da cewa"get lost "

"Babu inda zani, let talk about it please "ta fad'a in a pleading tune

"Babu abinda zanji go! Get lost I say! "Ya fad'a cikin ihu sosai, ganin zai mike ya sata riko kugunsa tana cewa

"Babu inda zani you must hear me out! "

"Kin ci sa'a bana dukan mace da yau sai na miki wanda ko moruwa ba zaki sake yi ba! Ki sake ni ko Kuma yau dinnan na dawo beast din ki! "Ya fad'a babu alaman wasa a muryan sa

Wato in ran Zuly yayi dubu to ya b'aci, sakin sa ta yi cikin fushi tace

"Alright ina cewa kayi na tafi? Fine zan tafi Kuma bazan sake dawowa ba, ana ma maka magana kana nuna kai mai zuciya! To ai ba kai kadai kake da zuciyan ba nima nan Ina da shi! Kama samu Ana ma lallaba ka!"ta fad'a cikin b'acin rai chan ta sausauta muryan ta ce

"Haba pumpkin! Bai kama ta muyi haka da kai ba! We can talk about this please kayi hakuri kar kasa shaitan yaci galaba a kaina! "

"Shaitan!  Kika ce? Kinmanta har kisa kinyi! "

"Shhh kadaina!  Nace maka ma daina ko so ka ke zuciya ta ta buga ne? "Ta tambaya cikin d'acin rai wasu hawaye masu zafi na silalo ma ta

"I don't care!  Ki tafi kawai bana son ganin ki!  Ko mai kama dake bana son ganI ki  tafi kafin ranki ya fi nawa b'aci!"ya fad'a tare da shigewa toilet

Durkusawa ta yi tare da fashewa da kuka mai tsuma rai, azuciye ta mik'e katon khimar din ta ta zura akan towel din jikin ta tare da d'aukan bag din ta, wajen study table din d'akin ta nufa, wani abu ta rubuta a paper

Tana ficewa shikuma na fitowa daga ban d'aki, kaya yasa tare da tada sallah abin sa.....

Washe gari.....

Babu in da ba'a nemi Zuly ba acikin gidan nan amma ko alamar ta babu, Ammi duk ta gama tsurewa gashi number ta baya shiga

Mourad kaman baisan abin da ake yi ba saboda jinyan zuciyan sa da ya keyi gashi ya garkame kofa babu halin a fad'a mai abin da ya ke faruwa bah....

Abu kamar wasa har aka yi wata uku babu alaman Zuly Ammi da sauran mutanen gida har sun rame saboda tunani, kullum sai Ammi ta kira Umma ko zata ji labarin Zuly daga karshe ma Umman ce ta ce ya Zulfa saboda sun kwana biyu basu yi waya saboda gabadaya numbernta baya shiga!

Ammi have to lie akan sunyi tafiya ne da Mourad saboda bata san ya Umma zata d'auki zancen ba barin ma da suka riga suka sanar da ita zubewar cikin Zuly

Gashi Mourad ko alaman damuwan hakan babu tattare da shi amma chan kasan zuciyan sa damuwa ce cikin tipa shi bai ce ta tafi ba shi fa yana nufin Ta fita daga d'akin ne amma shine ta yi fushi ta tafi har da rubuta wa wai kar ya neme ta!  To ta fi ruwa gudu karma ta dawo din

Ganin abun nashi ba na masu hankali bane yasa Ammi bud'e  masa ido akan dole sai ya nemo yar mutane Kuma ya fad'a musu abin da ya faru a tsakanin su

Cikin kunan rai ya fad'a musu komai bai karasa rufe baki a Ammi ta d'auke sa da gigitacciyar Mari wanda ya sa hi hango Zuly a gidan ta na USA(hhhh nace tukunna dai...)

"Ashe baka da hankali ban sani bah! Babu bincike babu komai ma kama ma kori mana yarinyan kirkin nan! "Ammi ta fad'a cikin d'acin rai
Chapter 94 · 0% Book details