← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 114

Sashe 99

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haiydar na isa kofar gidan Ummi yayi Parking ahankali Khausar ta sauƙa tana gyara zaman hijabinta kana atare suka shiga cikin Falon Ummi bakinsu ɗauke da Sallama.
Ummi dake zaune riƙe da carbi ahannunta Asma'u da Bashir na zaune gefenta suka Amsa Sallamar.
Cike da ladabi Haiydar ya gaisheta tare da sake yi mata jaje kana suka gaisa da Bashir tukunna suka fice atare.
Khausar kuwa cike da sanyin tace.
“Ummi ki kwantar da hankalin ki insha Allah yaya Jameel zai bayyana babu abinda zai sameshi da izinin Ubangiji addu'a mu bazai tafi abanza ba".
Jinjina kai Ummi tayi cikin yanayinta kamar mara lafiya tace.
“Ameen ya Allah”.
Cikin sanyin murya Asma'u da Muryanta ya dishe da kuka tace.
“Babbar matsalar mu yau kwana biyu kenan Basu sake kira ba gashi baki ɗaya kuɗin Million Casa'in da biyar aka samu aka haɗa”.
Kallonta Khausar tayi tana cire hijabinta tace.
“Haka dai kika cemin jiya har yanzu kuɗin basu haɗuba”.
Kai Asma'u ta gyaɗa mata kana tace.
“Basu haɗu ba Khausar damuwar dake damunmu kenan wlh, baki ɗaya hankalinmu ya kasa kwanciya sai dai Yah Modibbo yace Abba ya nemi bashin banki amman sunce yau ko gobe zai samu kuɗin”.
Cikin sanyin murya Khausar tace.
“Insha Allah kuɗin zasu haɗu da izinin Ubangiji Allah ya karesa ya tsare lafiyarsa”.
Atare suka amsa da Ameen.
Shiru Khausar tayi tare da tallafe kuncinta kana ta kalli Ummi da Asma'u sai kuma ta fesar da numfashi kana buɗe jakarta tare da kwaso ƴan kunnaye da sarƙa da kuma zobe kala biyu da alamun nata dana Mommy ne, hannun Ummi ta kama tasasu a ciki kana ta rufe hannun Ummin tare da cewa.
“Gashi inji Mommy na, tace Dan girman Allah da Manzonsa kada ki ƙi karba Ummi dan Allah kada kice komai a saidashi a haɗa kuɗin.
Cikin tsananin jin dadi Ummi ta kalli girman Gwal ɗin musamman na Mommy wanda a ƙalla shi kadai zai iya kai one Million da yan ɗori.
Hawaye na tsiyayo mata tace.
“Bazan ƙiba Khausar kicewa Mommynki ngd matuƙa ubanji yayi mata sakayya da gidan al'janna mai girma”.
Cikin sanyi duk suka amsa da Amin.
Cikin sanyi Khausar ta fesar da numfashin kana a hankali tace.
“Amma Ummi Meyesa ba asa Police acikin maganar ba?”.
Cikin raunin murya Ummi tace.
“Sunce muddin Akasa police acikin maganar to abakin ransa”.
Cikin sauri ta dafe ƙirjinta tare da cewa.
“Innalillahi akan ransa kuma?”.
Kai Asma'u ta gyaɗa Tare da cewa.
“Kuma batun kuɗi ma da suka ce da farko Million ɗari biyu sukace yanzu ya zama Million ɗari da hamsin saboda ragin da aka nema to yanzu sunce muddin aka sake neman ragi akan ransa”.
Aruɗe Khausar ta rintse Idanunta tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Sai kuma ta juya tare da kallon Ummi cikin sanyin murya tace.
“Ummi kinsan wani abu?”.
Kai Ummi ta girgiza kana tace.
“A'a”.
Lumshe idanu Khausar tayi tare da cewa.
“Ummi ranan da Yah Jameel ya mai dani gida da muna tafiya munga wata mota tana ta binmu abaya”.
Sai kuma tayi shiru alamar tunani ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.
“Ummi shine fa dama nace da za'a faɗawa hukuma zan iya bada number Motar saboda na zargi motar duk inda mukayi motar na biye damu wataƙil da hukuma zasu shiga za'a iya kama wa anda suka sace Yah Jameel, domin tun fitar mu motar ke bibiyanmu har saida muka kusa gidanmu suka daina binmu”.
Cike da mamaki Asma'u tace.
“Kai Khausar?”.
Kallonta Khausar tayi tare da gyaɗa mata kai kana tace.
“Wallahi kuwa Asma'u amma lokacin bamu kawo komai aranmu ba shima kuma Malam Jameel Bai kawo komai ransa ba”.
Girgiza kai Ummi tayi kana tace.
“Toh ya zamuyi idan an faɗa zai zama matsala zasu kashesa tunda sunce basu yarda afaɗa wa hukuma ba shiyasa dole muyi hakuri”.
Jinjina kai Khausar tayi kana cikin sanyin murya tace.
“Toh shikenan Ummi Insha Allah zamu cigaba da yiwa Yah Jameel Addu'o'i Allah ya bayyana shi”.
Jingina kai Ummu tayi tare da cewa.
“Yawwa shine abinda ya dace Allah yabamu Sa'a”.

Wunin wannan ranan haka Khausar tayi ta rarrashin Asma'u da Ummi kana tana sake basu ƙwarin gwiwa kan cewa da izinin Ubangiji M Jameel zai dawo bayan Sallar sala'sar ta koma gida tana isa gida daga bakin.
Barandarsu ta jiyo sautin kukan Ramadan cikin sauri ta cire takalminta tare da shiga falon bakinta ɗauke da Sallama.
Cike da damuwa ta sauƙe Idanunta akan Ramadan daya kifa kansa kan cinyar Mommy cikin rauni da raɗaɗin ciwo yake jujjuya kansa akan cinyar Mommy kana yana cewa.
“Mommy Kaina ciwo!,Mommy Kaina zai fashe!”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe Cike da damuwa tace.
“Subhanallah Ramadan yau tun safe kake ta cemin kanka na ciwo to meke faruwa ne na baka magani kasha abanza ko dai in kira Abbanka ne akai ka asibiti?”.
Cikin tsanananin ciwo ya Girgiza mata kai yayi kana cikin Muryan kuka yace.
“Mommy ni dai Banason allura aƙara min magani kar kaina ya fashe”.
Khausar kuwa cikin sauri ta cire hijabinta kana ta ƙara sa kusa dashi tare da ɗaura tafin hannunta akan goshinsa lokaci ɗaya zafi ya ratsa tafin hannunta har ƙananan jijiyoyin kansa sun tashi suna harbawa cikin sauri ta kalli idanunsa gani tayi sun kaɗa suyi jawur dasu kana yanayin su ya koma kamar ajuye.

Saurin kallon Mommy dake jera masa sannu tayi kana tace.
“Subhanallah gaskiya Mommy akaishi Asibiti”.
Cikin sanyin murya Mommy ta kalli Ramadan dake ta juyi kana ta kalli Khausar dake cikin damuwa ta fesar da numfashi tare da cewa.
“Nima nace aikai shi asibiti amma yace baya Son allura da zaran nace akaisa saiya sa kuka”.
Girgiza kai Khausar tayi kana ta sake shafa goshinsa da yayi masifar zafi cike da damuwa tace.
“Mommy yaushe za'a biye masa jifa yanda kansa yayi zafi kamar wuta”.
Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.
“Bari akwai maganin da Abbanku yace zai sayo masa yanzu bari idan ya kawo za'a bashi idan Allah yasa ya samu sauƙi shikenan idan kuma abin be lafa ba dole sai mutafi asibitin”.
Jinjina kai Khausar tayi tare da cewa.
“Toh shikenan Allah ya bashi lafiya Allah kuma ya dawo da Abba lafiya”.
Mommy na shafa kan Ramadan tace.
“Ameen”.

Acan ɓangaren Abban Jameel kuwa ahankali ya miƙe tare da kallon wayarsa kana ya sauƙe Ajiyar zuciya tare da nufar toilet domin ya watsa ruwa baki daya baya jin daɗin jikinsa bakinsa ɗauke da addu'a ya shiga toilet din kana ya fara wanka.
Hajiya Karima dake zaune afalon kasancewar itace da girki tayi saurin kallon wayar Abba dake ruri miƙewa tayi tare da isa kan 3sitter ganin number babu suna yasa tayi saurin picking tare da kaiwa kunnenta tace.
“Assalamu Alaikum”.
Ba tare da mutumin ya amsa Sallamar taba yace.
“Ina Mahaifin Jameelu?”.
Da sauri ta gyara zaman wayar akunnenta tare da cewa.
“Me kuke so ku faɗa min nice mahaifiyarsa”.
Cike da gadara Mutumin yayi gyaran murya kana yace.
“Dashi muke son magana, muna son muji shin kuɗin mu sun haɗu ne?.
Zamu faɗa masa inda za'a ajiye kuɗin sannan kuma da inda za'a zo akarɓi Jameel”.
Hajiya Karima kuwa cikin ƙasa da murya tace.
“Haba bayin Allah kuji tsoron Allah mana.
Yanzu fisabilillah ina zamu samu Million ɗari da hamsin wannan aiba rayuwa bane duk da cewa Mahaifinsa mai kuɗi ne ina zai samu wannan uban kuɗin acikin ƙaramin lokaci kawai dai ku temaka ku rage idan ku akayi wa haka ya zakuji? Gwara dai ana rage mugunta”.
Dai-dai lokacin da Abba ya fito daga wankan batare daya gama ba jin alamar muryan Hajiya Karima na magana ƙasa².
Yana fitowa ya Fisge wayar ahannunta tare da mannawa akunnensa dai-dai lokacin da mutumin ke magana cikin tsanananin fushi da gadara yace.
“Ok haka ma kuka ce. Wato wasa da mu ku keyi kun maida mu bamusan abinda muke ba, toh Insha Allah daga yau har gaban Abadan baza mu sake kiran kuba. Alhj Bashir ya maka kyau duk irin halarcin da gargaɗin da muka maka baka jiba har kuna sake neman ragi”.

Cikin tsanananin kaɗuwa, ruɗu, da tashin hankali. Abba ya girgiza kai kana cikin raunin murya yace.
“Dan Allah da m...”.
Kafin ya ƙarasa yaji ɗit-ɗit-ɗit alamar sun kashe kiran.
Cikin wani irin yanayi ya zauna tare da sake kiran layin yaji akashe Aruɗe ya shiga fito da sauran numbers din su yana kira amma baki ɗaya Switch off.
Kansa ya dafe da hannunsa na dama yayin da hannunsa na hagu ke riƙe da wayar.
Cikin wani irin fushi ya miƙe tare da kallon Hajiya Karima dake tsaye azabure ya ɗaga hannunsa tare da kife ta da mari kana ya sake watsa mata wani gigitaccen marin da saida taga gilmawar taurari cikin wani irin fushi ya cigaba da yarfa mata maruka gefen hagunta da damanta.
Muryarsa na rawa yace.
“Karima na saki acikin wannan maganar tunda aka fara. Meyesa zaki ɗauka min waya. Karima kin cuceni. Wallahi Karima duk wani abinda ya faru da Jameelu kece sanadi kece kika ja ke kika cutar min da rayuwar ɗana”.
Da sauri ya dafe ƙirjinsa dake wani irin zafi kana ya ɗago ya kalleta da idanunsa da suka sauya launi zuwa tsantsar tashin hankali kana yace.
“Karima haka nayi dake kina gani ɗazu akan idonki na dawo daga Taraba naje na karamo kuɗi na sake karɓan bashin banki 50 millons yanzu ruwan kuɗi ahannuna Million Ɗari da arba'in da biyar ne Million biyar ne kaɗai ya rage kuma nasan da izinin Ubangiji ba zasu gagara ba zan nemosu amman shine zaki nema min ragi”.
Hajiya Karima kuwa kuncinta ta dafe tare da sun kuyar da kanta ƙasa tana mai cike da taraddadi.
Chapter 99 · 0% Book details