← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 114

Sashe 104

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acan cikin baccin sa kuwa zaune ya hangosa akan wata.
Tattausan shimfiɗa cikin wani masha'hurin falo mai masifar kyau da ƙawa.
Sai dai kima yana ta dariya hartada karketawa, yayinda idanunsa kuma sunyi jawur jikinsa na rawa jin.
A hankali ya fara jujjuya kansa yana mai ci gaba da dariyar ya juyo kansa gabansa, jin alamar tafiya tare da wani ƙamshi daya ratsa hancinsa yasa ya ɗaga manyan idanunsa da sukayi luhu-luhu ya sauƙe ganinsa akan Khausar dake zuwa garesa cikin wata iriyar ƙasaitacciyar shiga, ido ya zira mata ko ƙebtawa bayayi har ta isa garesa, a hankali ta zauna gefensa.
Tare da tsira masa manyan Idanunta masu haske wanda ke ciki da ruwan hawaye kana ta miƙa masa wani hankief fari ƙall mai masifar ƙamshin turare.
Ƙin karba yayi saima lumshe idanunsa da yayi wanda sai lokacin ya samu wasu irin tafasassun hawaye suka samu damar kwaranyowa, hakan yasake kawar da kansa gefe tare da sakin sheshsheƙa.
Ahankali Khausar ta matsa gabansa har suna shaƙan nunfashin juna kana ta sanya hankief ɗin ta shiga share masa hawayen cikin wata Sanyayyar murya mai cike da nutsuwa da kuma rauni tace.
“Yah Jameel Addu'ar mu yake buƙata ba kuka ba idan kai kana kuka.
Toh Ni kuma ya zanyi addu'a za muyi masa kaji ko Abu J”.
Ta ida mgnar da kiransa da sunan da ta raɗa masa, tare da faɗawa jikinsa ta fashe da sassayan kuka dai-dai lokacin kuma ya farka.
Kansa ya dafe tare da miƙewa ya shiga toilet ya ɗaura al,wala kana ya dawo ya shimfiɗa Sallaya ya fara nafillah yana cigaba da yiwa M Jameel addu'a.
Ba tare da yabi ta kan mafarkinba, domin yanzu kam idan da sabo ai yaci ace ya saba da yawan ziyarar kutse da nacin da Khaisar keyi masa cikin rayuwar baccinsa.

Washe gari Ummi ta tattara baki ɗaya Sarkoƙi, ta da ɗan kunnen zobe da awarwon Gwal nata dana Asma'u ta shirya ta tafi Tarata.
Tana isa kai tsaye babbar kasuwar su ta wuce kana tashiga shagon saida gwala-gwalai ta bayar aka gwada cikin sa'a ta samu sunyi farashi sosai kasancewar Manyan Sarƙoƙine nata dana Asma'u wasu nata tun tana gidan Abban Jameel ne, suka haɗa mata kuɗin ta Naira Million biyu da dubu ɗari huɗu da hamsin sukayi mata transfer dinsu.

Daga nan gidan kai tsaye gidan Ƙawarta Hajiya Salma Wanda mijinta ke saida Motoci yawanci awajensa M Jameel ke siyan mota ko kuma can zawa.

Mai A dai-dai-tan na sauƙeta ta miƙa masa kudinsa kana ta shiga cikin tangamenen coumpund ɗin daya tsaru kai tsaye ciki ta nufa tare da Knowking ɗin ƙofar kana ta murɗa handle ɗin tashiga bakinta ɗauke da sallama.
Hajiya Salma dake zaune akan kujera ta miƙe cikin sauri kana tace.
“Hajiya Fatima sannu da zuwa ga wajen zama”.
Kai Mommy ta gyaɗa tare da cewa.
“Yawwa Nagode”.
Sannan ta zauna tare da sakin Ajiyar zuciya.
Bayan sun gaisane.
Cikin sanyin murya Hajiya Salma tace.
“Ayyah Hajiya ashe ga abinda ya faru da ɗana Jameel kuwa?”.
Cikin yanayin sanyin ɗaya zamewa Ummu jiki, ta gyaɗa mata kai tare da cewa.
“Ummm bari ke dai Hajia Salma duniya tayi min zafi”.
Cikin tausayawa Hajia Salma tace.
“Ba komai in sha Allah, kada ki damu Hajia Fatima.
Ubangiji Allah ya bayyanar da Jameel aduk inda yake Ubangiji ya karesa daga sharrin mai sharri”.
Cikin sanyin Murya Ummi tace.
“Ameen ya Allah ameen ya hayyu ya ƙayyum”.
Cike da tausayawa Hajiya Salma tace.
“Wallahi Koda wasa banji ba sai ɗazu da safe Alhj na duba jarida ya gani shine yake sanar min”.
Kai Ummi ta gyaɗa kana tace.
“Allah sarki ai yanzu anshiga kwana na huɗu kenan.
Uhmmm dama nazo kiyiwa Alhj Abdallah magana ne akan ya duba motata ya siya”.
Ajiyar zuciya Hajiya Salma ta sauƙe kana tace.
“Ubangiji Allah ya tsare Malam Jameel aduk inda yake”.
ta faɗa tare da shigewa ciki tsaye ta samu mijin nata yana ƙoƙarin fita Kallonsa tayi kana tace.
“Alhj Hajiya Fatima ce ta zo mahaifiyar Malam Jameel”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Ikon Allah muna shirin zuwa kuma sai gata”.
Ya faɗa tare fitowa a tare, a inda Hajiya Salma ta barta anan suka sameta tayi ta gumi.
Ahankali Ummi ta ɗago jai tare da cewa.
“Alhj Abdallah ina kwana ya gida”.
Zama yayi kana yace.
“Lafiya lau Hajiya ashe kuma ga abinda ya faru da Malam Jameel”.
Kai Ummi ta gyaɗa kana cikin sanyin murya tace.
“Eh”.
Ajiyar zuciya Alh Abdallah ya sauƙe kana yace.
“Wallahi bamu da labari sai ɗazu ina karanta Jarida na gani nake faɗawa Salma tace itama bata da labari dake akwai wani fitar gaggawa daya kamani nace idan nadawo zan kaita da yamma ta gaishe ki”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da gyada kai kana tace.
“Allah sarki dama Motata ce nazo ka tura adauƙa maka ka ga lafiyarta zan saidata in zaka siya”.
Ɗagowa yayi tare da kallonta kana yace.
“Motar da Malam Jameel ya siya miki nan?”.
Kai ta gyaɗa masa tare da cewa.
“Eh shi”.
Zaman hular kansa ya dan gyara kana yace.
“Amma ai motar bata daɗe ba Hajiya Fatima”.
Kai ta gyaɗa Muryanta na rawa tace.
“Eh bata daɗe ba Uzurin gaggawa ne ya kama Ni shiyasa zan siyar”.
Jinjina kai yayi tare da cewa.
“Aikam dama mota ce mai kyau sannan bai daɗe da sayanta ba za tura yaro yaje ya ɗaukota kuma yanzu mugama magana tunda abu na gaggawa ne”.
Cikin sanyin murya tace.
“Tun baka gani ba”.
Girgiza kai yayi tare da faɗin.
“Baki da matsala Indai wannan ne zan baki Million shida”.
Cikin sauri Ummi tace.
“Alhj har Million Shida kuma dama motar yana da tsada kenan?”.
Kai ya gyaɗa mata tare da zaro wayarsa acikin aljihu kana yace.
“Eh dama Million biyar ne haka ya siyeta toh nasiyeta biyar ɗin kamar yanda ya siya sannan Million ɗayan kuma na bada nawa gudunmawar Ubangiji Allah ya bayyana Malam Jameel”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da cewa.
“Ameen ya rabbil izzati, ngd Matuƙa".
Da sauri ta kalleshi jin yana cewa.
“Ki bani account number ki zan miki transfer”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da kiramasa number's ɗin.
Atake ya mata transfer.
Miƙewa tayi tare da yi masa godiya sosai kana ta fito, har ƙofa Hajiya Salma ta rakata kana ta Wuce.

Kai tsaye tashar motar Gembila ta nufa, tana zuwa kuwa tayi sa'a mutun ɗaya ya rage, haka yasa ta shiga motar ta tashi.

Alhamdulillah sun isa Gembila lfy.

A hankali Ummi ke tafiya tana jin wani irin sanyi a ranta tare da Comfedance ga Million ɗaya da dubu ɗari huɗu da dake account ɗinta ga kuma Million biyu da dubu ɗari huɗu da hamsin na Sarkoƙi kana ga Million Shida na mota ya zama tana da tsuran kuɗi ahannunta har Naira Million tara da dubu ɗari takwas kenan.
A hankali ta sauƙe wani zazzafafar ajiyar zuciya kana ta nufi gida.
Acan ɓangaren Moddibo kuwa ya haɗa duk wasu kuɗaɗe dake hannunsa ya samu Million huɗu da dubu ɗari biyu da hamshin kai tsaye gidan Ummi ya nufa yana Parking ɗin motarsa mai A dai-dai-tan sahu na ajiyeta atare suka shiga falonta.
Suna shiga Bayan sun gaisa Ummi tashiga Alart massage tare da miƙawa Moddibo wayarta tare da cewa.
“Babana ka kalli kuɗi sunyi gwaɓi”.
Amsar wayar yayi tare da Kallon Alart massage ɗin kuɗin kana ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.
“Masha Allah kuɗi sunyi gwaɓi bari na haɗa dana wajena”.

Kallonsa Ummi tayi haka nan taji hawaye na ciko mata kwarmin Idanunta.
Cikin sanyin murya Moddibo yace.
“Ummi na wurina na bashi da yawa Million huɗu da dubu ɗari biyu da hamsin ne”.
Cike da tausayinsa tace.
“Toh Allah ya biya. Babana Allah yabamu yanda zamuyi Ubangiji ya saka maka amma ka rage wani abu aciki ka samu na kashewa”.
Girgiza kai yayi cikin raunin murya yace.
“Ummi wani abu zan rage idan ina da abinda yafi wannan zan ɗauka in bayar akarɓo J naje. nayi magana da dillalai gidan mu na sashi akasuwa in dai za'a samu siyansa akan lokaci.
Cikin sauri Ummi ta kallesa tare da cewa.
“Gidan ku kuma Babana!?”.
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Ummi Meye amfanin gidan mai zamuyi da gidan babu wani farin ciki acikisa.
Muddin J baya nan fa wanne farin ciki zamuyi. kuma komai da muka rasa zamu iya samu idan J ya dawo gare mu”.
Jinjina kai Ummi tayi, Account number dake wayarsa ya fito dashi ya mata transfer kuɗin tare da miƙa mata wayar karɓa tayi ta duba Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da kallon kuɗin Naira Million goma sha huɗu kenan cib.
Numfashi ta fesar tare da kallon Moddibo kana tace.
“Alhamdulillah Babana kuɗi sun cika Million goma sha huɗu bari muje gidan Abban sa tare”.

A hankali yace.
“Amma Ummi ki bari sai gobe muje wataƙil yau ba zasu kira ba sai goben, amma ni yanzu idan nafi ta zanje wajen Abba muji nawa aka samu awajensa”.
Kai ta gyaɗa cikin sanyi tace.
“Toh shikenan Babana Allah yasa muji al'khairi”.
Kai ya gyaɗa tare da miƙewa kana yace.
“Amin.
Toh shikenan bari naje yanzu”.
Ya faɗa tare da ficewa.

Kai tsaye gidan Abba ya nufa bayan yayi Parking ya fito tare da shiga Falon bakinsa ɗauke da Sallama.
Abba dake zaune kan 2 sitter ya jingina bayansa da jikin kujera ya amsa masa Sallamar cike da tausayinsa ya zuba masa yana ganin yadda yake tafiya duk ya faɗa acikin kwanaki huɗu ya rame yayi shafal.
Chapter 104 · 0% Book details