← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 114

Sashe 108

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa Khausar tayi tare da bin bayan Hajja Nana jikinta sanye da dogon hijabi har ƙasa yayin da hannunta ke riƙe da wayarta Idanunta sunyi luhu-luhu dasu suna fita coumpund ɗin taga Malam Liman acikin mota amazaunin Driver.
Wara kumburarrun Idanunta tayi kana cikin sanyin murya tace.
“Iyeee lallema tsohon nan ashe ka iya mota?”.
Murmushi malam Liman yayi tare da gyada mata kai kana yace.
“Eyyy sosai ma kuwa dama lokacin da kikaje ai mota ta talalace ne shiyasa ankaita wajen gyara to wata aka sake siya min”.
Murmushi tayi kana tace.
“Ashe kunji daɗi ƙauyenku akwai mota”.
Jinjina kai yayi da murmushi afuskarsa yace.
“Hadda ke ai acikin ƙauyen ya zaki cire kanki?”.
murmushi tayi cikin yanayin sanyin tace.
“ai Lallai dai kam to Allah ya tsare muku hanya”.
Ta faɗa tare da komawa cikin falon Ummi.

Kallon Hajja Nana Malam Liman yayi bayan ya dai-dai-ta motar akan kwalta yace.
“Addah Nana za muje gidan Malam Arɗo wannan ɗaliban nawa”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh ba matsala muje mana”.
Jinina kai Malam Liman.
bayan sun isa gidan malam Arɗo yayi Parking tare da isa falon baƙinsa wanda ke harabar gidan bakinsu ɗauke da Sallama.
Daga ciki malam Arɗo wanda ke zaune tare da Moddibo ya amsa tare da basu Izinin shiga.
Bayan angama gaishe-gaishe Malam Arɗo yace.
“Lafiya Malam Liman yau ziyarar yamma”.
Cikin jimami Malam Liman yace.
“Wallahi ɗan gidan Mai martaba Lamiɗo ne ya rasu shine muka zo Ta'aziyya”.
Jinjina kai Malam Arɗo yayi tare da faɗin.
“Bashakka hakane ai yaron ɗalibin mune, wallahi ni lokacin da akayi jana'izar nasa banji ba amma Insha Allah zanje ta'aziyya da izinin Ubangiji”.
Kai Malam Liman ya gyaɗa tare da gyara zamansa kana yace.
“Wallahi kuwa rasuwa abin tausayi wai ciwo dare ɗaya ya tsananta”.
Girgiza kai Malam Arɗo yayi da alamun damuwa atare dashi yace.
“Ayyah haka fa kwanaki mota ta bigeshi abakin Makarantar mu fa. Yaron ya samu karaya wannan bugewan ba wanda yayi tunanin zai warke Allah sarki ashe ajalin nakusa”.

Kai Hajja Nana ta gyaɗa tare da cewa.
“Haka fa rayuwar take ciwon Ajali lokacin ɗaya zai shige mutum sai dai kaji ance babu shi saidai fatan Allah yasa mu cika da Imani”.
Baki daya suka amsa da Ameen banda Moddibo daya zubawa ƙasan ɗakin Idanu da alama ya zurfafa acikin tunanin da yake.
Ahankali Malam Liman ya juya tare da kallon Moddibo kana ya maida kallonsa kan Malam Arɗo tare da cewa.
“A'a Malam Arɗo wannan jikan namu dashi kaje kwanakin baya ko?”.
Kai Malam Arɗo ya gyaɗa tare da kallon Moddibo da har zuwa lokacin kansa ke ƙasa yace.
“Eh jika nane kuma Malamine Amakaranta na”.
Murmushi Malam Liman yayi tare da faɗin.
“Ayyah Masha Allah Yayi kyau amma lafiya na ganshi haka baki ɗaya ya canza ko bada shine ku kaje Jauro yaya kwana kiba”.
Cikin sanyi malam Arɗo ya gyaɗa kai kana yace.
“Eh da shine mukaje”.
Cike da mamaki Malam Liman yace.
“Amma lafiya kuwa?”.

Numfashi Malam Arɗo ya fesar tare da Girgiza kai kana yace.
“Ina kuwa lafiya wannan zamani da Allah ya kawo ku. Malam Liman kai dai Ubangiji ya rufa mana asiri”.
Anutse Malam Liman ya gyara Alkyabbar dake jikinsa kana yace.
“Amin ya Allah".
Kana ya ɗaura da cewa.
“Amman Meke faruwa?”.
Gyara zama Malam Arɗo yayi tare da fuskantar Malam Liman cikin sanyin murya yace.
“Akwai wani Amininsa Yaron Alhj Bashir mai Dala Jameelu da aka sace baki ɗaya abin ya fitar mana hayyaci mun rasa wani irin tunani zamuyi ma acikin wannan al'amari”.
Cikin sauri Malam Liman yace.
“Sunhanallah”.
Cike da damuwa Malam Arɗo ya gyara zama tare da zayyane musu duk abinda ke tafiya yanda aka sacesa da kuma yanda akanemi kuɗin fansa kana da yanda suka daina jin labarinsa kwata kwata.
Girgiza kai Malam Liman yayi kana yace.
“Subhanallah”.
Ya faɗa tare da maida kallonsa kan Moddibo wanda shima adai-dai lokacin ya ɗago Idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur baki ɗaya fuskarsa tayi fayau ya rame.

Cike da tausayawa Malam Liman yace.
“Amma yanzu baku da labarin sa!?”.
Girgiza kai Moddibo yayi kana cikin raunin murya yace.
“A'a bamu da labarinsa yau kusan kwana goma sha biyu kenan bamu da labarinsa, sannan wayarsa bata shiga suma kuma sun daina kiran mu abinda yafi komai tayar mana da hankali kenan, bamusan Inda J yake ba”.
Malam Liman kuwa Anutse ya fesar da nunfashi cike da tausayinsa kana ya gyara zamansa tare da cewa.
“Bakomai Insha Allah za muyi addu'a da izinin Ubangiji duk inda yake a faɗin duniyar nan Ubangiji zai bayyana shi”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da Gyara zamansa Malam Liman ya cigaba da cewa.
“Da Iznin Ubangiji Allah zaiyi dalilin da za'a ganshi zan baka addu'a'o'in idan har zaku jure kuyita yi da kai da mahaifiyarsa da kuma Mahaifinsa, to za ayi nasara kuma nima zan tayaku”.
Cikin sauri Moddibo ya sauƙe Ajiyar zuciya tare da cewa.
“Munaso Malam ai addu'a'u Saiful mu'uminun ce ita addu'a itace makamin bawa dama ita muke tayi ai”.

Kai Malam Liman ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh shikenan zan baka adduo'i Insha Allah da izinin Ubangiji Allah zai bayyana shi, aduk inda yake afaɗin duniyar nan sai dai walau ko araye ko amace amma Ubangiji zai bayyana shi insha Allah za'a ga walallanilansa”.
Cikin sanyi Moddibo yace.
“Mun gode Malam”.
Cike da nutsuwa da kamala Malam Liman ya fara bashi Adduo'i Moddibo kuwa cikin sauri ya ɗauki jotter da biro ya fara rubutawa wasu da yawa daga cikin Adduo'in Moddibo ya sansu wasu kuma baisan suba sabida shi ilimi kogine faɗi gareshi. sosai ya riƙa faɗa masa adduo'in Moddibo kuwa yana rubuta adduo'in yana bitar su yasan da izinin Ubangiji idan ya zauna na awa biyu yayi research ɗinsu zai haddace su.
Bayan Malam Liman ya gama bawa Moddibo adduo'in Hajja Nana ta saki ajiyar zuciya kana tace.
“Toh Ubangiji Allah ya karesa Allah ya bayyana sa aduk inda yake”.
Cikin sanyi murya suka amsa da Ameen.
Kallon Malam Liman Hajja Nana tayi tare da faɗin.
“Ai wannan Jikanmu ne ka tuna ƙawata Innare?”.
Kai Malam Liman ya gyaɗa mata tare da cewa.
“jikanta ne?”.
Jinjina kai Hajja Nana tayi tace.
“Eh shine”.
Murmushi Malam Liman yayi tare da faɗin.
“A Masha Allah Yayi kyau”.
Ita kuwa maida kallonta kan Moddibo tayi wanda gaba ɗaya ya zubawa takardan adduo'in ido kana tace.
“Idan ka koma ka gaishe min da ita yau kam bazan samu zuwa ba yanzu ma munyi yamma”.
Kai ya gyaɗa kana cikin sanyin murya yace.
“Toh mun gode Allah ya saka da al'khairi Insha Allah zataji”.
Miƙewa Hajja Nana da Malam Liman sukayi tare da yi musu Sallama suka tafi Moddibo kuwa yana fita daga gidan Malam Arɗo kai tsaye gidan Abba ya wuce Bayan sun gaisa Abba yayi shiru tare da tsirawa waje ɗaya ido gabansa da magunguna da alamar bai daɗe da gama shaba.

Ahankali Abba ya maida kallonsa kan Moddibo da yaga yayi mugun rama ya sake zama wani so silent duk da dama can bamai yawan magana bane amma yanzu shirun yayi yawa.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da faɗin.
“Aliyu kaga yanda ka koma kuwa ka dawo kamar wanda yayi shekara yana jinya”.
Kallon Abba Moddibo yayi tare da sakin murmushin da yafi kuka ciwo kana ya sunkuyar da kansa ƙasa tare da cewa.
“Abba”.
Still Idanun Abba na kansa yace.
“Na'am”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe kana yace.
“Insha Allah Abba inaji Ajikina J ɗina ya kusa bayyana”.
Numfashi Abba ya fesar tare da sakin murmushi na alamar jin daɗi kana yace.
“Allah yasa haka Aliyu”.
Ahankali Moddibo ya amsa da Ameen kana yace.
“Abba ya zun nan akwai wani malami da muka haɗu dashi agidan malam Arɗo ko Malam Arɗo da kansa wajensa yake zuwa ɗaukan darasi ya bani adduo'i masu tarin yawa”.
Sai kuma ya lumshe idanunsa tare da cije Lip ɗin sa na ƙasa kana yace.
“Adduo'in da nake ji ajikina insha Allah Ubangiji zai amsa mana, gashi ya bani adduo'i da dama yace mu riƙa yi dani da kai da Ummi. Insha Allah duk inda J yake afaɗin duniya Allah zai bayyana mana shi za muji labarinsa aduk inda yake”.
Murmushi Abba yayi tare da faɗin.
“Mungode ƙwarai Allah yasa adace”.

“Ameen yace kana yaci gaba da cewa.
“Kyansa ma mu ƙara harda Azumi amma dama Ni tuntuni ina Azumin Abba kaima ka gwadayi.
In Sha Allah ni zan shiga itiƙafi na tsawon kwanaki uku Insha Allah”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Toh shikenan Moddibo Allah ya temaka”
Nan Moddibo ya bawa Abba adduo'in kana ya tafi kai tsaye gidan Ummi ya nufa itama ya bata Adduo'in cikin sanyin murya tace.
“Toh Babana Insha Allah zanyi”.
Kai ya gyaɗa kana ya fice kai tsaye gida ya nufa yana isa sashen Innayi ya wuce sannan ya mata bayanin duk abinda ya faru tare da bata Adduo'in da Malam Liman ya bayar kana ya faɗa mata saƙon gaisuwar da ƙawarta ta bata.
Kana ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.
“Toh zan shiga 'itiƙafi a ɗaki”.
Jinjina kai Innayi tayi da faɗin.
“Toh me dame kake bukata?”.
Girgiza kai yayi kana cikin sanyin murya yace.
“Bana buƙatar komai Akwai Friuts a Fridge sannan akwai kayan tea kuma azumi zanyi”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh Allah yatemaka Allah ya bada sa'a.
Ameen ya amsa tare da nufar Bedroom ɗinsa.
Yana shiga yaja ƙofa ya rufe tare da nufar toilet ya ɗaura alawala yana fitowa ya zauna bisa salla ya fuskanci gabas.
Ya fara rera karatun Al'ƙur'ani sai karfi ɗaya ya fara jero Adduo'i yanayi yana kuka.
Sai ƙarfe uku ya kwanta ƙarfe huɗu dai-dai ya farka yasha tea da fruits Washe gari ya tashi da Uzumi haka ya yini da azumi yaita Adduo'i da karatun Alkur'ani idan dare yayi haka zaita nafilfili sai karfe uku zai kwanta ƙarfe huɗu zai tashi yayi Sahur haka ya cigaba da rayuwa har tsawon kwanaki uku aɗaki yana fadawa Ubangiji bukatarsa Aɓangaren Abba ma haka ya ɗauki tsawon kwanaki uku yana bautar Ubangiji haka Ummi ma baki ɗaya ta miƙawa Ubangiji lamuranta.
Chapter 108 · 0% Book details