← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 114

Sashe 93

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da daddare Misalin ƙarfe goma Moddibo ne zaune a falon Abba kansa aƙasa yayinda idanunsa suka kaɗa sukayi ja jawur kana jijiyoyin kansa sun tashi sunyi ruɗu ruɗu rabonsa da bacci tun daren shekaran jiya haka zalika yauma koda runtsawa ne yakasa kana ya sanya duka hannunsa biyu ya dafe kansa dashi zuwa lokacin baki ɗaya ya kasa control ɗin kansa kife kansa yayi ajikin kujera tare da fashewa da kuka mai gunji.
Cikin wata raunan'niyar murya mai cike da karkarwa yace.
“Abba ina J yake? Abba ina J ya tafi ya barni Abba wani hali J yake ciki?”.
Hajiya Karima ce tashigo falon bakinta ɗauke da Sallama tare da kallon Moddibo dake kuka tamkar ƙaramin yaro lumshe Idanunta tayi tare da cewa.
“Haba Aliyu kuka kuma kai da ya kamata ka tausashi Mahaifinsa sannan kuma ka zauna zakuyi ta kuka atare kenan?”.
Karo na farko kenan arayuwar data yi masa magana cikin taushin lafazi.
Ahankali Moddibo ya ɗago kai ya kalleta still yana kuka yace.
“Aunty Karima ina J yake Ina J ɗina yashiga ya barni?”.
Cikin rauni Abba ya ɗago idanunsa da hawaye ke zuba Akuma dai-dai lokacin wayar Abba ta ɗauki ruri yana ɗagawa yaga number ce ba suna sai ya mayar ya ajiye.
Kallonsa Moddibo yayi tare da faɗin.
“Abba waye ne?".
Ciki Sanyin Abba ya kalli wayar kana yace.
“Numbar ce ba suna”.
Cikin muryan kuka Moddibo yace.
“Toh Abba ka ɗaga mana ko za'a faɗa mana anga J ne”.
Cikin sauri Abba yayi Picking call ɗin tare da cewa.
“Assalamu Alaikum”.
Daga ɗaya ɓangaren cikin wata bauɗaɗɗiyar murya aka amsa da.
“Wa'alaikum Salam kaine Alhaji Bashiru Maidala mahaifin Malam Jameelu?”.
Cikin sauri Abba ya gyaɗa kai tare da miƙewa tsaye kana yace.
“Eh nine mahaifin Jameelu”.
Cikin sauri Moddibo ya miƙe tsaye,
itama Hajiya Karima cikin sauri ta miƙe tsaye.
Gyaran murya yayi kana yace.
“Toh Jameelu yana wajen mu”.
Cikin rawan baki Abba yace.
“Jameelu yana wajen ku yana cikin halin lafiya? To a ina kuke?”.
Kai tsaye yace.
“Eh gashi ma kaji muryarsa”.
Ya faɗa tare da miƙawa M Jameel wayar.
Cikin sauri Abba yace.
“Jameelu”.
M Jameel kuwa cikin wata raunan'niyar murya me cike da galabaita da tashin hankali kamar wanda yayi kuka yana sauƙe ajiyar zuciya yace.
“Abbana”.
Cikin rawan jiki da rauni Abba yace.
“Na'am Jameelu Meye sameka?,Aina kake?”.
Ajiyar zuciya mai nauyi M Jameel ya sauƙe cikin rauni da yanayi wahala yace.
“Abba nima ban sani ba bansan inda nake ba Abba ina A.J”.
Cikin muryan kuka Abba ya kalli Moddibo da jikinsa ke rawa kana yace.
“Gashinan".
Ahankali M Jameel dake sakin ajiyar zuciya yace.
“Abba ka bashi wayar”.
Miƙawa Moddibo wayar Abba yayi cikin sauri Moddibo ya amsa tare da mannawa akunnensa kana Yace.
“Jyyyyyy”,yaja sunan cike da taraddadi.
Fesar da numfashi M Jameel Yayi tare da cewa.
“AJ”.
Cikin yanayin rauni da tausayawa ya lumshe idanunsa tare da cewa.
“J ina kake?”.
Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.
“AJ ban sani ba bansan inda nake ba, ban san ida suka kawoni ba”.
Cikin sauri aka Fisge wayar daga hannun M Jameel kana cikin wannan bauɗaɗɗiyar murya akace.
“Ka bawa mahaifinsa waya”.
Ahankali kuma cikin sanyi Moddibo yace.
“Waye kai ina J yake?”.
Cikin wata razananniyar tsawa yace.
“Kabawa mahaifinsa waya ba da kai muke son magana ba?".
Moddibo kuwa Girgiza kai yayi kana yace.
“Toh me kuke so ku faɗa min ko mameye”.
Cikin sauri Abba ya janye wayar daga kunnensa tare da sa wayar a handsfree kana yace.
“Gani mahaifin Jameelu".
Daga ɗaya ɓangaren mutumin yace.
“Jameelu yana hannunmu bawai mun sace sa dan mu kashe sa ko wani abu bane amma idan kuka yi mana taurin kai zamu iya kash”...

*Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa 1k ne kacal ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin wani a kanki 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*

*By*
*GARKUWAR MARUBUTA*
[30/07, 1:40 PM] Halimatu A/rahman Sadeeya: *Littafin SAKAYYAH na kuɗine ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki littafin 1k kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276, sai in saki a Group ɗin*

“Idan har kana son rayuwar ɗanka to.
Kabi sharaɗin mu kabi tsarinmu, sannan kabi dukkan dokokin, muddin kana so Jameel ya rayu idan kuma ka kuskura kayi mana taurin kai kayi mana gardama kan sharuɗan da muka ginda ya maka to zakaga abinda zai biyo bayan gardama”.
Cikin tsanananin kaɗuwa Abba ke girgiza kai yayin da bakinsa ke rawa ya gaza furta komai.
Cikin wannan bauɗaɗɗiyar murya mutumin ya cigaba da cewa.
“Dama kai tsaye mu aikin kashe sa aka bamu. Toj amma saboda nagartansa da mutuncinsa yasa mukaji bama buƙatar kashe Malam Jameelu munfi ɓuƙatar abada kuɗi musakeshi domin shi Jameelu na kowane, kauda irinsu a doron kasa asarace data shafi, dukkan al'umma, dan haka kabi sharuɗanmu mu sakeshi salamun-salaman ya dawo hannunku hankali kwance, idan kuma ka kuskura kayi mana gardama duk da na gartan Jameel zamuyi abinda muma ranmu bai soba!”.
Cikin tsanananin tsoro da tashin hankali Abba ya dafe ƙirjinsa da hannu ɗaya kana yace.
“Innalillahi.
Dan Allah ku faɗa min koma me kukeso zan baku bazan muku gardama ba da Izinin Ubangiji”.
Cikin wata kakkausar murya mutumin yace.
“Bayan kai wanda mu kejin sa agefenka kada ya mana gardama domin shine Amininsa Moddibo”.

Girgiza kai Abba yayi still jikinsa na rawa kana muryarsa cike da rauni yace.
“Ba zaiyi gardama ba”.
Gyaran murya Mutumin yayi kana yace.
“Kasa amsa kuwwa shima Moddibo yaji abinda ake magana akai”.
Kai Abba ya gyaɗa still muryarsa na rawa yace.
“Nasa, nasa, nasa”.
Cikin bada umarni mutumin yace.
“Ku nutsu ku zauna ku jini”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Toh”.
Gyara murya mutumin yayi cike da isa yace.
“Baku zauna ba nasan atsaye kuke”.
Atare Abba, Moddibo da Hajiya Karima suka zauna Araunane Abba yace.
“Toh mun zauna wallahi”.
Kai Mutumin ya gyaɗa tare da faɗin.
“Yayi kyau sharaɗin mu na farko da zamu ƙidanya muku idan ka bishi Jameel ya rayu idan kuwa baka bishi ba Jameel ya mutu wannan shine sharaɗi na farko kuma shine mafi tsauri”.
Ajiyar zuciya kawai Moddibo ke sauƙewa zuciyarsa na cigaba da bugawa da masifar ƙarfi.
Mutumin ya cigaba da cewa.
“Sannan yanzu rayuwar Jameel yana hannunka da kai da Amininsa da kuma mahaifiyarsa da ma sauran Makusantan ku, idan kuka mana gardama kamar kuna wasa da rayuwar Jameel ne”.

Atare Moddibo da Abba suka haɗa baki wajen cewa.
“Meye kuke buƙata menene sharaɗin naku?”.
Kai Mutumin ya gyaɗa kana yace.
“Sharaɗin namu shine wannan maganar kada ku yarda kada ku kuskura koda agigin bacci koda amafarki kusa hukuma acikinta!”.
Moddibo kuwa ƙirjinsa ne ya buga cikin sauri ya dafe kansa da hannunsa biyu tare da kifa fuskarsa ajikin kushin kana ya furta.
“Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n”.
Cikin ƙasa da murya Abba ya runtse Idanunsa tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n La'ilaha Illah anta subhanaka Inni kuntu Minal Zhalimin”.
Cikin tsawa mutumin yace.
“Zaku faɗa kenan!?”.
Da sauri Moddibo ya girgiza masa kai dake kife akan kushin kamar yana gabansa kana yace.
“Ba zamu faɗa ba wa kowa ba, mudai fatan mu J ya kasance cikin ƙoshin lafiya, kada ku cutar dashi”.
Taɓe baki Mutumin yayi kana yace.
“Kada ku yarda kada ku kuskura ku sanya hukuma aciki”.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana yace.
“Ba zamu faɗa ba da izinin Ubangiji zamu bi sharaɗin ku.
Amma sai dai kafin ma ku kiramu mun kaiwa hukuma maganar amatsayin Jameel ya ɓata tunda mun kwana babu shi sannan mun wuni babu shi toh munje wajen hukuma amma bawai munje amatsayin mun kai ƙorafi akan ku bane”.

Jinjina kai Mutumin yayi tare da taɓe baki kana yace.
“Toh wannan sharaɗine Idan hukuma sun dawo dan suna nan kamar Mayu, daga sunji babu mutum idan sun sake kawo kansu kada kuce mun nemi kuɗi awajenku”.
Yarfe hannu Hajiya Karima tayi tare da girgiza kai ta ƙurawa Abba Ido tamkar shike maganar.
Cikin bauɗaɗɗiyar murya Mutumin ya cigaba da cewa.
“Muddin kana son ran Jameel to.
Kayi shiru da bakin ka idan mun kafa maka sharaɗi na biyu ko kuma mun faɗi abinda mukeso kun bayar to Jameel zai dawo amatsayin ɓata yayi sannan ba sace sa akayi ya dawo ba”.
Abba kuwa buɗe idanunsa dake lumshe yayi kana yace.
“Insha Allah zamu bi sharaɗin ku amma yanzu mai kuke so ku faɗa min”.
Cikin sauri ya janyo wayar tare da kallon screen ɗin jin ɗit-ɗit-ɗit alamar an kashe.

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da rintse idanunsa da karfi kana yace.
“Innalilahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin”.
Moddibo kuwa da still hannunsa ke dafe akansa yana taune lip ɗin sa na ƙasa babu abinda ke fita abakinsa face kalmar Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n.
Hajiya Karima kuwa Girgiza kai kawai take tare da yarfe hannu kana tana mai maimaita kalmar Hasbunallahu wani'imal wakin ta juya tare da kallon Abba da idanunsa suka kaɗa suka yi jawur sannan tace.
“Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n wannan wani irin zamani Allah ya kawo mu kenan ƴan Kidnapping ne suka ɗauke Jameelu”.

Lokaci ɗaya Moddibo ya sake dafe kansa da karfin yana cigaba da taune lip ɗin sa na ƙasa.
Girgiza kai Hajiya Karima tayi kana ta cigaba da cewa.
“Amma Alhj wannan sharaɗin nasu zancene na banza ina muke da yaƙinin zasu iya kare Jameelu ba zasu cutar da shiba ba gwara mu faɗawa hukuma ta shiga cikin maganar nan ba”.
Cikin sauri Moddibo ya ɗago kansa daga jikin kushin wanda sai alokacin ya samu damar hakan hannunsa biyu ya haɗe waje ɗaya alamun roƙo kana ya runtse Idanunsa da ƙarfi ya shiga.
Girgiza kansa muryarsa na rawa yace.
“A'a,a'a,a'a Aunty Karima kiyi wa Allah da Manzonsa kada ki sako hukuma acikin maganar nan Wallahi kina sa hukuma zasu iya yiwa J komai kiyiwa Allah kada kisa hukuma aciki kiji abinda suka faɗa mana”.
Chapter 93 · 0% Book details