← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 114

Sashe 109

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yau ya kama kwana na huɗu kenan ahankali Moddibo ya fito daga falonsa tare da tsayawa abakin farandar.
Innayi dake tsaye ta zuba masa ido lokaci ɗaya taji hawaye na zubo mata ganin yanda yayi wani masifar ramewa idanunsa sunyi luhu-luhu dasu yayinda sajensa ya cika fuskarsa kasancewar gashi mai santsi da laushi yasa sai sheƙi yake fuskarsa nan tayi fayau sai sheƙi take alamun a ɗan kumbure take sabida yawan kuka da rashin isasshen bacci.
Lumshe Idanu Innayi tayi hawaye masu zafi suka zubo ganin kamar daga jinya ya tashi.

Moddibo kuwa ahankali ya ɗaga kai ya kalleta jin yandata tsaresa da ido.
Cikin rawan murya tace.
“Moddibo kaga yanda ka dawo kuwa?”.
Murmushi mai ciwo yayi tare da Girgiza kansa cikin sanyin murya yace.
“Innayi bari na tafi wajen Ummi”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh baka tsaya kaci abinci ba”.
Girgiza kai yayi kana yace.
“A'a Innayi na ƙoshi”.

Kallonsa Innayi tayi Idanunta cike da ruwan hawaye tace.
“Dan Allah Moddibo ka tsaya kaci wani abu dubi yanda ka dawo fa”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Toh shikenan Innayi ki bani tea”.
Cikin sauri ta hado masa tea ta kawo masa karɓa yayi yasha bayan yasha ya fita kai tsaye gidan Ummi ya nufa bakinsa ɗauke da Sallama ya shiga falon.
Ummi na ganinsa tayi saurin miƙewa tare da fashewa da kuka mai cike da rauni.
Moddibo kuwa cikin sauri ya ƙarasa kusa da ita tare da riƙe tafin hannunta kana cikin raunin murya yace.
“Ummi meyafaru Ummi kuka kuma?”.
Cikin zubda hawaye ta kallesa tare da cewa.
“Babana abubuwan sun haɗu sunyi min yawa acikin kwanaki Ukun nan Ba Jameelu na sannan kai ɗinma da nake gani inji sanyi na daina ganinka. Babana kaga yanda kadawo fa”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da lumshe idanunsa kana yace.
“Ummi Insha Allahu in Allah ya yarda hawayen mu ya kusa daina zuba inaji Ajikina J yana kusa damu”.
Numfashi ta fesar tare da cewa.
“Allah yasa hakan Babana dubi yanda ka dawo fa kamar wanda aka sallamo daga asibiti kana tafiya Iska na ɗibarka”.
Sai kuma ta maida kallonta kan Asma'u data zabga tagumi tana binsu da kallo baki ɗaya itama ta rame ta sake zama shiru.
Cikin sanyin murya tace.
“Asma'u kawo masa abinci yaci”.
Kai ya Girgiza Asanyaye yace.
“Ummi bana jin yunwa”.
Cikin sauri da sanyi Ummi tace.
“Zafa kaci abinci matuƙar kana son hankalina ya kwanta to kaci abinci Babana”.
Cikin sanyi yace.
“Toh Ummi”.
Ahankali Asma'u ta fito hannunta riƙe da Plate ɗin dambun shinkafa dayaji Vegetables ya na fidda ƙamshi da soyayyan naman kaza akai da kwalin exotic.
Agabansa ta ajiye masa kallon Ummi yayi ganin yanda ta tsare da ido tana zuba masa, ahankali ya fara cin abinci duk da yana jin cikinsa ya cushe yaci ya kai rabi kana yasha lemon Kaɗan.
Ture Plate din yayi kana yace.
“Ummi bari Inje gidan Abba”.
Kai ta gyaɗa da fadin. “Adawo lafiya”.

Moddibo na fita kai tsaye gidan Abba ya nufa yana isa ya shiga falon bakinsa ɗauke da Sallama Atare Abba da Malam Arɗo dake zaune suka amsa masa cikin sanyi Moddibo ya nufi gefen Abba ya zaune tare da Gaishe su.
Kallon Moddibo Malam Arɗo yayi kana yace.
“Moddibo yau kwana uku bakai babu dalilinka sannan wayarka bata shiga shine nace bari inzo tambayi Abban Jameel ko lafiya kaddai wanda suka ɗauki Jameelu ne suka ɗauke mana kai”.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.
“Nima da ban ganshi ba gaba ɗaya hankalina ya tashi duk da cewa nasan yana gida lafiya amma rashin ganinsa ya sake tayar min da hankalin rashin ganin Jameelu na”.
Cikin sanyin murya Malam Arɗo yace.
“Toh Allah ya bayyana shi Alhj Ubangiji Allah ya bayyanar dashi aduk inda yake!”.
Cikin rauni Moddibo ya kalli Abba tare da cewa.
“Abbah basu kira ba atsawon kwana ki ukun nan”.
Girgiza kai Abba yayi da faɗin.
“A'a basu kira ba Aliyu kuma ga wayar Jameelu na ta daina shiga, yanzu sannan suma sun daina kira”.
Moddibo kuwa ahankali yace.
“Bakomai Abba Insha Allah Allah zai bayyana shi akan al'khairi Alfarman Annabi da Alkur'ani”.
Atare suka amsa da Ameen Hajiya Turai ce tashigo bakinta ɗauke da sallama bayan sun gaisa da malam Arɗo ta kalli Moddibo da faɗin.
“Moddibo kwana biyu shiru gashi babu wani labarin Jameelu Ubangiji dai Allah ya bayyana mana shi”.
Cikin sanyin murya suka amsa da Ameen kana ta juya ta fice.

Kallon Moddibo Malam Arɗo yayi kana yace.
“Moddibo muje ka rakani wani waje mana”.
Kallonsa Moddibo yayi da faɗin Ni kuma?”.
Kai Malam Arɗo ya gyaɗa masa kana yace.
“Eh”.
Girgiza kai Moddibo yayi cikin sanyin murya yace.
“A'a kayi haƙuri ni kam babu inda zanje”.
Kallon Moddibo Abba yayi kana yace.
“Aliyu kaje ka rakasa mana”.

Gyara zama Malam Arɗo yayi tare da faɗin.
“Kuma ta'aziyya ne ma zai rakani, gidan Lamiɗo tunda akayi rasuwar yaron nan yau wuni na biyar kenan ban samu naje ba, kuma kaima ya kamata kaje amatsayin ka na Malaminsu”.
Shiru Moddibo yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa.
Ahankali Abba yace.
“Aliyu kuje mana zama waje ɗayan nan ma bashi da daɗi”.
Girgiza kai Moddibo yayi cikin sanyin murya yace.
“Abba ni dai banason zuwa”.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe da faɗin.
“Kuje mana Aliyu Ubangiji Allah yasa zuwan ya zama alkhairi”.
Cikin sanyin murya yace.
“Ameen”.
Sannan ya miƙe Malam Arɗo na biye dashi suka fita.

Acan gidan su Khausar kuwa Lamiɗo ne zaune afalon tare da wasu baƙi guda biyu da suka zo daga Taraba Alhj Ibrahim da Alhj Musa suka zo yi masa ta'aziyya sai kuma Uncle Naseer dake gefe.
Mai gadi ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama kana yace.
“Ranka ya daɗe ga Malam Arɗo da Malam Moddibo Malaman su Ramadan sunzo”.
Kai Lamiɗo ya gyaɗa tare da faɗin.
“A'a kace su shigo harda malam Arɗo da kansa”.
Kai ya gyaɗa sannan ya fice ba dadewa Malam Arɗo suka shigo tare da zama kana suka yi Masa ta'aziyya ahankali Moddibo yace.
“Ashe Ramadan lokaci yayi Allah ya masa rahma”.
Cikin sanyi Lamiɗo yace.
“Ameen Moddibo ya mukaji da taraddadin rashin Jameelu har yanzu shiru ko?”.
Cikin sanyi Moddibo yayi ƙasa da kansa tare da matse yatsun hannunsa batare da yace Uffan ba sai kai da ya gyaɗa masa.
Da-dai lokacin mai gadi ya sake shigowa tare da cewa.
“Ranka ya daɗe ga Ɗan gidan Arɗo Ja'eh yazo yi maka ta'aziyya”.
Kai Lamiɗo ya gyaɗa da fadin kace ya shigo”.
Fita mai gadin yayi tare da sanar da baƙon.

Da Sallama Bararojin Fulanin dajin yashiga falon Lamiɗo cikin shigarsu irin ta Fulani hannunsa riƙe da sanda kusa da ƙafar Lamiɗo ya zauna kana suka gaisa sannan ya musu ta'aziyya.
Juyawa yayi ya kalli Malam, Arɗo, Moddibo, Alhj Musa Alhj Ibrahim ya gaishesu tare da yi musu ta'aziyya.

Kallonsa Lamiɗo yayi kana yace.
“Ori ya Baban naka?”.
Cikin yanayin rashin wadatacciyar Hausa yace.
“Ai bashi da lafiya ne shiyasa bai samu yazo ba, na wakilcesa munji labarin Ramadan ya rasu Allah ya masa rahma”.
Baki ɗaya suka amsa da Ameen.

Ahankali Lamiɗo ya juya tare da kallon Moddibo kana yace.
“Moddibo da gaske wai har yanzu babu labarin Jameelu”.
Ahankali Moddibo ya ɗago kansa dake ƙasa ya kalli Lamiɗo cikin rawan murya.
“Eh har yanzu babu labarinsa, yanzu kam ma sun daina kira, sannan kuma wayarsa ma da ake kira ta daina shiga zuwa yanzu munsa hukuma a cikima sunyi iya bincikensu ba labari”.

Malam Arɗo ne ya gyara zamansa tare da faɗin.
“Ai wannan Zamani da Allah ya kawo mu sai dai Ubangiji ya rufa mana asiri amma an maida satan al'ummar kamar satan ƴaƴan awaki”.
Ido Ori ya zuba masa tare da sakin Ajiyar zuciya.
Malam Arɗo yace.
“Kisan rai kuma ba adaukesa abakin komai ba, ran mutum ya dawo kamar ran kishiya, baki ɗaya duniyar nan ta canza ta burkice ta koma abin tsoro, in ba haka ba kamar Malam Jameelu asace sa bashi babu labarinsa”.
Alhj Musa da Alhj Ibrahim kuwa kai suka jinjina da faɗin.
“Sosai kuwa yanzu idan kana da dukiya hankalin ka ba akwance ba, haka zalika idan kana talaka ma baka da nutsuwa, sai dai Allah ya kawo mana ɗauki amma baki ɗaya jama'ar duniyar ta canza, yanzu ma idan muka fita daga nan zamuje wajen Alhj Bashir ɗin muyi masa jaje”.
Malam Arɗo ya gyaɗa kai tare da cewa.
“Muma yanzu daga can muka fito”.
Jinjina kai Alhji Musa yayi da faɗin.
“Allah sarki Jameelu yaro mai mutunci da karamci, ga sanin darajar manya Ubangiji ya bayyana shi”.

Gyara zama Ori yayi tare da fuskantar Lamiɗo cikin rashin ingantaccen hausarsu yace.
“Hmmm Lamiɗo wato ai wannan duniyar ta zama abin tsoro kwanan nan abinda na gani acikin dajin mu, saman dutsen Membilla aƙasan wata bishiya har zuwa yau hankalina bai gama dawowa jikinaba har zuwa yanzu wanda yasan ni da ya ganni ayanzu yasan ban gama dawowa cikin hayyacinaba”.
Chapter 109 · 0% Book details