← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 114

Sashe 2

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A can side ɗin Moddibo kuwa, kwance yake, harshensa jiƙe da ambaton Allah, duk da cikin bacci yake.
Saidai baccin, ba baccine kamar na kowa ba, domin bacci yake cikin wani irin yanayin daya gaza tantancewa, shi ba bacci ba, kuma ba ido biyu ba, ba kuma mafarkiba ba kuma zahiri ba, ba kuma a sumeba wasu abubuwan da lokuta da dama yana riskarsu cikin bancinsa yake fuskantar su.

Ita kuwa Innayi a hankali ta gyara zamanta, tare da juyowa ta kalli bayanta, da sauri sabida wani irin haske da taga ya gilmawa ganinta, sai kuma tayi saurin juyowa gabanta ta, kalli gabas saitin ɗakin Moddibo domin a zatonta ko an dawo da wutar nepa ne.
Ga mamakinta kuwa, babu alamun hasken wutan nefan sai wani irin sanyi mai ratsa jiki.
Haka nan taji wani yanayi na rufeta,
wanda yafi kama da tsoro abinda bata taɓa fuskarta sa acikin gidanba duk duhun dare.

Hakan yasa tayi saurin sunkuyar da kanta taci, gaba da yin al'wa'ar, hannunta ta wonken, kana ta ciko tafin hannunta na dama da ruwa, zata kai bakinta domin kuskuran baki kenan.
Wani irin saurin ɗago kanta tayi ta kalli gabanta, sabida ganin wani irin masifeffen haske mai firgitarwa da taga ya haska illahirin duniyar har hasken yana haska cikin ruwan dake tafin hannunta.
Cike da tsoro ta zubda ruwan tare, da juyawa ta kalli.
Gabas da yamma Kudu da Arewa.
Babu mutun ba dalilinsa, babu kuma alamun ta inda hasken ke fitowa.
Kana kuma ga kuma hasken dake tsananta.

Da wata sassayan iska mai ratsa jiki da sanyaya zuciya.
Wacce tasa Moddibo gyara kwanciyarsa tare da ci gaba da wani irin bacci mai mayataccen daɗi da yaji ya dannesa da kuma shigo masa da wasu sabbin ababen gani a idanniyansa, yayinda harshensa kuwa ke nanata addu'o'in masu tarin yawa.

Yayinda ita kuwa Innayi, wani irin tsuma jikinta ya farayi lokacin da taga gaba ɗaya duniyar ta ɗauki wani irin mashahurin haske mai kyan gani.
Wanda ta rasa ta ina yake fitowa.
“Innalillahi wa innailaihi raji'un hasbunallahiwani'imanwakil”.
Ta fara maimaita cikin firgici lokacin da ta ɗago kanta, ta kalli sararin samaniya.
Wani irin kerma da makerketa mai cike da tsananin tashin hankali, firgici, tsoro, da karkarwa jikinta ya farayi, sabida yadda taga ubangijin talikai, yana wanzar da ikonsa da buwayarsa a sararin samaniya.
Wasu irin masifaffun hawaye masu zafi wanda irinsu kan tsinkowa ɗan Adam lokacin da yaga tsananin abin tsoro da shiga firgici da ƙudurar Allah.
Kar-kar haka jikinta yake rawa, ganin yadda taurari.
Suke fizgowa sunayin wani irin haske mai kashe idanun ɗan adam, wanda sune take ganin duk sun cika sararin samaniya da haske tamkar rana.
“Ya hayyu ya ƙayyum birahamatika astaƙisu, ya Salam, innalillahi wa innailaihi raji'un, la haulawa ƙuwta illabillahil aliyul azeem”.
Sune tasbihai da furucan da ubangijin ya bata ikon furtawa, lokacin da ta fara ganin taurarin sunayin ƙasa tamkar zasu faɗo, ƙasa domin gani take kamar sai sunzo har ƙasa sosai kamar zasu taɓo rufin kwanon ɗakin Modibbo, sai kuma taga ubangijin ya janyesu sun koma sama da azaban sauri tare da tartsatsin haske mai kyan gani.

Fadin halin tsoro ko tashin hankali ko firgici da ɗimuwar da take ciki ya zarta zaton mai zato, ya wuce tunanin mai tunani ya shallake nazarin mai nazari, wasu irin wahaye ne ke kwaranyo mata.
Yayinda ta koma baya ta jingina bayanta da jikin filan barandar ɗakinta dake bayanta, ta jingina kanta tana kallon sama.
Tare da fara nanata kalmar shahada.
Domin ta gama sallamarwa cewa, lokacin ta yayi, ma'ana mutuwa zatayi.
“La hailahaillahu Muhammadu Rasulullahi sallahu alaihi Wasallama”.
Shi ta fara maimaitawa can ƙasan maƙoshinta domin.
Komai na jikinta ya fara tsayawa, sabida azabebben tsoron daya rufeta da cikekken imanin kaɗaita rabbissamawati wal ardi zuwa yanzu tama fara ɗimautan shin anyama kuwa a raye take?.

A ƙalla 30 minute ubangijin talikai na wanzar da ikonsa! Da kuma, buwayarsa!! Can kuma sai ta fara ganin gaba ɗaya duhu na meye hasken.
Duhu mai cike da sassayan iska.
Wani irin tsorone ya kuma rufeta wanda ya diro mata da zazzafan zazzaɓi mai haɗe da masifeffen ciwon kai.
Wanda ya tilasta mata kife kanta bisa guiwowinta tare da rumtse idanunta tamkar zata liƙesu da juna.

A can cikin masarautar Gembilan kuwa, Gimbiya Dadu ce, ke kwance bisa tsakiyar gadon ta, wani irin masifeffen mafarki mai tada hankali takeyi.
Wanda yasata ihun neman ceto, wanda bata saninba har ya fito fili.
Fitarsan ne, yasa hadimarta saurin shigowa tare, da tadata. Ai kuwa cikin tsananin firgici da tsoro ta farka tana mai karkarwa, lokaci guda kuma zazzafan zazzaɓi ya rufeta.

A nan gidansu Moddibo kuwa.
A hankali ya fara buɗe idanunsa tare da ambaton Allah.
Hannunsa yasa bisa bed side drawer ya jawo wayarsa.
Gefen wayar ya ɗan taɓa da yatsarsa manuniya, wanda hakan yasata kawo haske har ya haska Kekkyawar fuskarsa mai cike da yalwataccen saje mai sulɓi da ɗan madaidaicin gemun da bazai uwace kamu ɗaya ba yayiwa siraran jajjayen leɓɓansa masu sheƙi ƙawanya.

A hankali ya ziro ƙafafunsa ƙasa, sabida ganin, ƙarfe huɗu saura kwata.
Bathroom ɗinsa ya nufa.

Yana shiga yayi brush da wonka tare da yin al'wala, kana ya fito.
Durowarsa ya buɗe yayinda yake amfani da wayar hannunsa wurin haska abin nemansa domin har yanzu babu wuta kasan cewar yanayin garin Gembilan garin mai masifar sanyi mai daɗi, yasa basu cika damuwa da rashin wutar da ƙasartamu ke fama dashi ba.
Wata tattausar jallabiya fara ya zira kan ƙananan kayan dake cikinsa, tare da jawo farin hula taɓa kaji hadis a kansa, turaren Oud bakhur mai masifar ƙamshi ya fesa, tare da sa hannunsa na dama, ya zaro carbinsa kana ya fito, falonsa, tare da sassarfa ya buɗe ƙofar falon ya fito.

Can cikin gidan ya nufa kamar kullum domin tabbatar da cewa kakartasa ta tashi daga bacci duda yasan kullum bisa sallaya zai sameta to amman hakan baya hanasa zuwa.

Ɗan tsayawa yayi tare da kallon inda Innayi ke zaune har yanzu, yadda kanta ke kife bisa guiwarta sai yayi kamar tana sunkuyene irin zata wonke fuskartan nan.
Da ɗan sauri ya juya ya nufi bakin gate nasu yana mai tasbihi.

Ƙarami ƙofar dake manne jikin gate ɗin ya tura ya fita asalin farfajiyar babban gate din nasu,
A hankali yake motsa laɓɓan bakinsa, yana taibihai, tare da shaƙar sassayar iskar,
A hankali ya kuma buɗe ƙaramar kafar kana ya nufi masallacin jumma'a dake layin nasu wanda yana kallo tamfatsetsen gate din gidan tsohon gidan Alhaji Abubakar Mafindi mahaifi ga Amininsa M Jamil kenan.

Ita kuwa Innayi ƙamshin turarensa ne, da kuma motsinsa ya tabbatar mata shine, so take ta ɗago kanta amman ta gaza, sabida wani irin sarawa da kanta yakeyi.
Har yanzu sunan Allah take kira, a ƙalla mintuna 20 da fitarsan kafin Allah ya bata ikon motsawa,
Cikin ƙarfin hali ta ɗago kan nata, lokacin da taji sautin murya Jamil yana kiran assalatu.

Wasu irin zafafan hawaye ne suka tsilalo mata wanda tsananin ciwon kan ne ya jaza mata su,
Cikin ƙarfin hali tayi, al'wala tare da yunƙurawa ta mike tsaye tana mai dafe kanta, ta koma, cikin ɗakinta, dai-dai lokacin kuma aka dawo da wuta, yayinda ko ina ya gauraye da haske, sallaya ta shimfiɗa kana ta zira hijabinta, ta fara nafila, jiki na rawan zazzaɓi da kyarman tsoro tanayi tana mamakin shin wai ashe a raye take?...

Ƙarfe bakwai dai-dai na safe.
Ya shigo gidan, maida ƙofar yayi ya rufe, tare da ɗan tsayawa, tsakiyar gidan, yana mai kallon ƙofar kitchen ɗin, Innayi yana mai nufar cikin gidan.
Agogon hannunsa ya kalla, tare da ɗan jinjina kai sai kuma ya juya, ya nufi, side ɗinsa, yana shiga bathroom ya wuce, ƙofar ya maida, ya rufe, tare dasa hannunsa ya jawo, tattausan towel, ya ɗaurasa a ƙugunsa bayan ya zare, jallabiyar, da vest, yana ɗauke da towel, sassayan numfashin ya fesar kana ya shiga cikin jaccuzie ɗin.

Cikin nitsuwa yayi wonka fes, ya fito.
Yana wani irin masifeffen ƙamshi yayinda gargasan jikinsa ya kwanta lib a tattausar farar fatarsa da damshin ruwa,

Wani towel ɗin ya jawo ya ɗaura, kana ya zare na ƙasan, matseshi yayi tare da shanyasa.
Sannan ya fito yana mai tsane tattausan sumar kansa da ƙaramin towel ɗin.

Gaban dreesin meeror'nsa ya tsaya, ya fara kimtsawa, cikin yanayin nitsuwarsa da rashin yin abu da gaggawa...

Bayan ya gamane ya fito fes yana baza ƙamshi mai masifar daɗin shaƙa, sai wani irin kyalli sajensa keyi, yayinda jajayen lips ɗinsa suke wani irin sheƙi tamkar dai irin yadda lips ɗin jarirai yake sheƙi in sun ɗan laso lips ɗin.
Wata tattausar jallabiya blue color mai ɗan karen taushi da kyau ne, a jikinsa, tayi cib-cib da ɗan madaidaicin jikinsa, sai kuma fararen takalma half cover masu taushi da ya zira tattausan sawayensa da suke farare ƙal, yayinda dun-duniyar sawun nasa ke sarari.
Farin hirami ya naɗa a kansa, irin naɗin nan na zamani wanda matasan larabawa keyi,
Sai wayarshi daya zira a ajihun gaban jallabiyar tasa, wani irin sassayan ƙamshi mai ɗan karen daɗin shaƙa yake zubawa,
Taku yakeyi cike da kamala, yayinda hannunsa na dama ke riƙe da jakar system nasa.

Cikin yanayinsa na nitsuwa ya ƙara so bakin kitchen ɗin.
Siraran Idanunsa ya ɗan jujjuya ya kalli tsakiyar gidan baki ɗaya, sai ya kuma ɗan leƙa cikin kitchen din, nan ma babu alamun Innayi.
Cikin nitsuwa ya kuma juyowa ya nufi ɗakin nata, ganin takalmanta a bakin ƙofar.
“Assalamu alaikum”. Yayi sallama cikin wata iriyar sassayar muryar mai cike da haiba nitsuwa da kamala.
Sai kuma yayi saurin shigowa cikin ɗakin.
Chapter 2 · 0% Book details