← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 114

Sashe 35

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acan sama ajinsu Khausar kuwa wani irin tsarin gini ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali wasu irin windon Glass ne tsala-tsala masu tsayi da kyan tsari sannan ga flowes masu fitar da sanyayyan ƙamshi kana ga Room hita guda biyu gaba da baya daga farkon shiga class ɗin kuwa wani irin Black Board ne mai tsari irin wanda ake amfani dasu a manyan makarantu, kana ga wasu irin kujeru na zaman ɗalibai masu taushi da kyau, agaban ko wani kujeran ɗalibi akwai sunan sa ajiki, hakan yasa duk ɗalibar data shiga baza tasha wahala neman wajen zamanta ba wanda kuma manna sunan ake bisa alamu in an tashi kawai ɓarewa za'ayi a saka sunayen sabbin waɗanda zasu shigo ajin, kujeran Khausar shine na farko acikin jerin kujerun dake gaba da sunanta manne kamar haka _Khausar Usman Abubukar Lelewal._
Samira Sani ce ta ɗan juya Idanunta kan kujerar dake gefenta.
Wanda sunan Khausar dake manne kujerar afarkon.

Wani irin ya mutsa fuska tayi tamkar wacce taga wani abin ƙi cikin taɓe baki da tsanar mamallakiyar sunan tace.
“Ikon Allah wannan shine suna mai buƙatar hadda sunaye huɗu duk masu tsawo!”.
Ta Ida maganar tare da bankawa kujeran harara tamkar Khausar ɗin na kai, kana ta zauna daga baya inda sunan ta ke kai.

Asma'u dake gefe azaune tace.
“Ha'a sunane de ai ba wani abu ba kuma duk sunayene masu inganci da Kekkyawar nasaba naga dai sunanta sunane na ɗiya ga Annabi Muhammad (S.A.W) sannan sunan mahaifinta sune na sahabin Manzon Allah (S.A.W) haka zalika sunan kakanta sune na sahabin Manzon Allah (S.A.W).
Lelewal kuwa naga suna ne da kowa ke fatansa”.

Abeeda Sule ne ta watsa wa Asma'u harara tare da faɗin.
“Ke kuma wayasa bakin ki?”.
Taɓe baki Asma'u tayi kana tace.
“Ai gaskiyane daga kallon sunan baiwar Allah zata fara ƙanan magana”.
Ɗaya daga cikinsu manyan matan ajin nasu ne wacce bata fiye magana Hajia Khadija tace.
“Da wannan hatsaniyar da kukeyi tunda Moddibo ya fita tun ɗazu akan zaije ya dawo bai dawo ba aigwara kuje ku duba ko lafiya mai ya tsaida shi aji ba kowa kuma shine muke da First period?”.

Cikin zumuɗi Samira Sani tace.
“Gaskiya ne kam bari naje na kirasa”.
ta ida maganar tare da ficewa ta sauƙa ƙasa.
Cikin yauƙi ta nufi Office

Tana isa idanunta suka sauƙa akan Khausar dake riƙe da kunnenta, ga kuma Idanunta da suka sauya,
yayin da shi kuwa Moddibo idanunsa ke lumshe yana rera karatun Alkur'ani cikin Sanyayyar sautin muryansa daya haɗu da ɗumin room hita ga ƙamshin daddaɗan tularensa.
Numfashi mai nauyi ta fesar tare da tsirawa yalwataccen sajensa daya ƙawata kyawun fuskarsa idanu sai kuma ta maida kallonta kan zara-zaran yatsun hannunsa dake kan table yana ɗan bubbugasu ahankali cike da shauƙi tace.
“Wowww”.Faɗar hakan da tayi shi ya janyo hankalin M Jameel yayi saurin juyawa ganinta tsaye acikin Office din yasa shi faɗin.
“Lafiya?”.

Sai asannan ta dawo cikin nutsuwarta still Idanunta na kan Moddibo tace.
“Malam Barka da safiya”.

“Barka dai”.

Still idanunta na akan Moddibo tace.
“Malam dama munzo kiran Malam Moddibo ne, shine muke dashi tun ɗazu ya sauƙa, akan cewa zai zo ya ɗauki wani abu sannan kuma bai koma ba”.

Da ido M Jameel ya nuna mata Moddibo da har zuwa lokacin idanunsa ke lumshe yana karatu sai dai ya rage sautin muryansa ya koma fita asaman laɓɓansa.

Shi kuwa Moddibo jin Muryanta yasa ya janye Hiramin dake fuskarsa kana ya buɗe idanunsa da har zuwa yanzu akwai alamun ɓacin rai acikinsu, kallo ɗaya ya mata ya kawar da kansa gefe.
Ita kuwa Samira gefe ta koma ta tsaya.
Khausar kuwa lumshe Idanunta da suka kaɗa sukayi jawur tayi sai kuma ta buɗe su still Hannunta nakan kunnenta tace.
“Ayyah Malam kayi haƙuri”.
Shi kuwa Moddibo juyawa yayi tare da kallon M Jameel yace.
“J ka da keta”.
Da sauri M Jameel ya juya tare da nuna kansa da babban yatsa kana yace.
“Ni!?”.

Cike da tsuke fuska Moddibo ya gyaɗa masa kai kana yace.
“Eh ka daketa!”.
Zare Ido M Jameel yayi tare da cewa
“Meyesa?”.
A kufule Moddibo yace.
“J kadaketa nace!”.
Kallon mamaki M Jameel yake masa tare da cewa.
“Akan me zan daketa?”.
Cike da ɓacin rai Moddibo yace.
“Idan fa ka bari nace ni zan daketa zan sumar da ita fa!, zan karyata fa!!”.
Cikin tsananin fusata ya ida maganar.

Ita kuwa Khausar tuni jikinta ya hau rawa Allah ya sani bata son duka, sannan mari ɗaya daya mata ya mugun gigita mata ƙwaƙwalwa wanda har zuwa yanzu take jin raɗaɗin sa asaman fuskarta.

Fuskarsa babu walwala yace.
“Idan har nace zan daketa zan sumar da ita”.
Ita kuwa Khausar jin azaban mari ɗaya daya mata, aranta tace Ashe Allah ya rufa min asiri da yasa duk lokacin da nayiwa Moddibo laifi baya duka na yake sa Malam Adam display master ke dukana na tabbata dashi yake dukana kullum da tuni ya kasheni!.

Cikin hanzari ta juya tare da kallon M Jameel ta miƙa masa hannu Muryanta na rawa tace.
“Malam ka dakeni!”.
Girgiza kai M Jameel yayi cikin sanyin murya yace.
“Ni dai kam bazan iya ba bazan iya dukanta ba Moddibo, ka dubi fuskarta fa mari ɗaya da ka mata kalli fuskarta fa ai ya wadatar wani hukunci ya rage bayan wannan?”.
Ya kare mgnar a hankali
Moddibo kuwa cikin fushi yace.
“Kada keta in kuma baza ka daketa ba zan daketa da kaina fa”.
Cikin sauri M Jameel ya fara girgiza kai yayi cikin wata Sanyayyar murya me cike da zallar jin ƙai tare da tarin tausayi gami da rauni yace.
“La! La!! La!!! A.J bazan iya ba! Wlh Bazan iyaba ba wannan ba hurumina bane hurumin taɓa ta awajenka yake bani da karsashi ko ƙwarin gwiwar da zan iya taɓa ta!”.
Ya ida maganar cikin wani irin salo na daban, kana dai-dai lokacin Amina tazo Office ɗin domin kiran M Jameel ya shiga ajinsu wani irin sarawa kanta yayi jin yanda yake cewa bazai iya ba.
Da sauri ta dafe ƙofar office ɗin jin jiri na ɗibarta kadde ace dokon soyayyarsa za tayi abanza, kadde Khausar yake so yanda ya ƙarashe maganar na nuni tamkar itace rayuwar sa.

Da sauri Moddibo ya juya ya kalli M Jameel jin yanda yayi magana da kuma yanda ya lanƙwasa harshensa abun ya bashi mamaki.
Azuciye Moddibo yace.
“In daketa kenan?”.

Langwaɓar da kai M Jameel yayi cikin sanyin murya yace.
“Kayi haƙuri ina mai bada haƙuri amada dinta ka nemi wani punishment ɗin ka bata amadadin wannan, amma nikam bazan iya dukan taba sannan kaima banaso ka daketa!”.
Baki ɗayan su kallon Mamaki suka bi M Jameel dashi ganin yanda yake lanƙwasar da murya tare da nemawa Khausar ya fiya, ita kuwa Amina wasu hawaye ne masu zafin gaske ne na tsananin kishi da baƙin ciki, suka zubo mata saurin ta sanya hannu ta share.
Kwantar da Murya M Jameel ya kuma sakeyi ya cigaba da cewa.
“Kallifa A.J mari ɗayan nan da kamata kalli fuskarta fa ka daketa awaje mafi daraja”.

Moddibo kuwa lumshe idanunsa yayi kana ya buɗesu akan M Jameel tare da cewa.
“J kadaketa ni idan nace zan daketa bazai mata daɗi bafa”.
Sake Langwaɓar da kai M Jameel yayi kana yace.
“Kayi haƙuri Moddibo ni bazan iya dukanta ba!”.

Ita kuwa Samari Sani na tsaye agefe ta harɗe hannayenta aƙirji yayin da ta zubawa Moddibo ƙananun Idanunta ko ƙyaftawa ba tayi.
Ita kuwa Amina Idanun ta nakan M Jameel da idanunsa ke kan Khausar zuciyarta nayi mata zafi.

Khausar kuwa kallon M Jameel ta sakeyi akaro na barkatai tace.
“Malam Jameel ni dai ka dakeni”.
Kai ya girgiza mata tare da faɗin.
“Bazan iya dukan ki ba Khausar!”.

Shi kuwa Moddibo cikin tsananin ɓacin rai ya juya ya kalleta a kufule yace.
“Toh inda keta da kaina!?”.
Girgiza kai M Jameel yayi sai kuma yace.
“A'a asassauta mana dan Allah”.
Ƙwafa Moddibo yayi da faɗin.
“Shikenan kije ki kaɗe ɗan kwali sau ashirin”.

Cike da tsoro ta zaro ido domin kaɗe ɗan kwallon da yace yana nufin ta cire ɗan kwalinta tasa abokitin ruwa ta matse kana ta kaɗe har sai ya bushe,
sannan ta sake sakawa cikin ruwa ta matse kana tayi ta kadewa har sai ya bushe.
Tofa jin haka ne yasa a tsorace ta zare Ido Jin hukuncin daya yanke mata ba zata manta lokacin daya sata kaɗewa sau goma ba awannan lokacin ma saida tayi sati biyu gaɓɓanta na ciwo ko abu zata ɗauka da ƙyar take iyawa.

Cikin yanayin neman alfarma M Jameel ya sake langwaɓar da kai kana yace.
“Dan Allah ka sassauta mata karage mata”.
Jin Muryan M Jameel yasa ita ma ta kalli Moddibo cikin wata raunatacciyar murya tace.
“Dan girman Allah Malam kayi haƙuri karage min”.

Shi kuwa Moddibo wani kallo ya watsa mata cikin haɗe girar sama dana ƙasa yace.
“Kada ki sake haɗa ni da girman Allah da kinsan darajar girman Allah da zaki mutunta Malama ki,
kije kiyi shabiyar kinci darajar girman Allah.
idan kika sake cemin dan Allah in rage miki kuwa nida ke bibbiyu!”.
Gyaɗa kai tayi kana tace.
“Toh shikenan”.
Shi kuwa M Jameel kallon Moddibo yayi cikin jujjuya ido yace.
“Ina neman alfarma abarta tashiga aji tayi karatu idan antashi Break sai tayi”.

Shi kuwa Moddibo Ɓata fuska yayi yace.
“Bana son ganinta a aji Idan naganta a aji zan kakkaryata in wurgar ta window”.
Ita kuwa Samira Sani cikin lanƙawasa harshe tace.
“Malam Moddibo mu tafi”.
Sake tamke fuska yayi tare da juyawa ya watsa mata wani bayyane harara sai kuma ya nuna mata ƙofa alamar ta ɓace masa da gani.

Sum sum ta juya da sauri ta fice.
Da harara yabi bayanta Aransa yace.
Shegiyar yarinya mai kama da Mayya,
sai shegen kallon jaraba tasani gaba zakiyi dan rashin kunya.
Chapter 35 · 0% Book details