Sashe 55
Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.
“Toh shikenan Allah ya kaimu goben”.
M Jameel kuwa kallon Asma'u yayi fuskarsa ɗauke da murmushi ya ajiye Plate ɗin hannunsa kana yace.
“Tafff lallai Asma'u ke ta musamman ce kinyi babban sa'a babu yanda ba muyi da ita ba muja mata wuta taƙi”.
Murmushi Moddibo yayi kana yace.
“Ai Asma'u ta hannun daman Innayi ce”.
Murmushi Asma'u tayi tare da ficewa ta koma falon Innayi suka kwana Misalin biyu da rabi Innayi ta farka kana ta tashi Asma'u suka fita alwala sukayi suka gabatar da nafilla tare da adduo'i ƙarfe uku dai-dai Innayi da Asma'u suka shiga kichen Innayi tayi musu ɗumanen tuwan jiya tare da tafasa ruwan shayi daya ji kayan ƙamshi sai kuma ta ɗumama perpesoup ɗin kazan ita kuwa Asma'u attaruhu da albasa ta jajjaga tare da ɗauraye tukunya ta sanya akan gas wanda zuwan Asma'u ne Moddibo suka kawo mai ta zuba kana ta zuba jajjegen tare da zuba spices da Maggi da kuma Curry ta zuba kana ta zuba sanwa Bushesh-shen kifi dake gyare ta zuba sannan ta ɗauƙi carrots,da grean beans,da kuma cabbage ta shiga gyarawa jin ruwan na tafasa ta tsaya ta zuba Spaghetti leda ɗaya sannan ta cigaba da gyarawa sai daya kusa tsotsewa sannan ta zuba cabbage,grean beans,Carrot,aciki Nan da nan gidan ya kaure da ƙamshi Warmers ta ɗauka ta juye sannan ta zuba sauran a plate ta haɗa kayan duka a babban faranti ta ɗauka bakinta ɗauke da Sallama tashiga falon.
Moddibo dake zaune riƙe da Alkur'ani ya ɗago kansa tare da amsa Sallamar bayan ya kai ƙarshen ayan Moddibo kuwa idanunsa ya ɗauke daga kan system ɗin tare da kallon Warmers din sai kuma ya Kalli Asma'u dake ajiyewa akan center table ya shafa sajensa tare da cewa.
“Asmeey ya naga kuloli da yawa haka?”.
Murmushi tayi kana tace.
“Wannan ɗumame ne Innayi tayi muku ɗayan kuma ɗumamen perpesoup ɗin jiya ne wannan kuma jollof nayi muku na Spaghetti”.
Jinjina kai M Jameel yayi kana yace.
“Ni dai kamar nafi son ɗumamen Amma bari naga jollof ɗin naki”.
Ya ida maganar tare da buɗe Kulan cikin sauri ya lumshe idanunsa jin ƙamshin daya ratsa hancinsa.
Kallonta yayi kana yace.
“A'a bazan ci ɗumame ba”.
Juyawa Moddibo yayi tare da kallon M Jameel kana yace.
“Ai kuwa baka Isa ba ɗumame zaka ci, Asma'u Allah ya miki albarka”.
Sai kuma ya sake kallon M Jameel dake murmushi kana yace.
“Ai dolenka ɗumame zaka ci dan kaine Innayi ke yin ɗumame ko wani shekara sai ka ishemu da ɗumame saboda kai ake liƙa mana”.
Murmushi M Jameel yayi kana yace.
“Ai ɗumamenta yana da daɗi kai kan ka in faɗa maka zakayi missing ɗumanenta idan baka kusa yanzu ma dan kana tare dashi ne”.
Murmushin gefen baki Moddibo yayi kana yace.
“Um naji amma dai yau shi zaka ci”.
Dariya M Jameel yayi tare da cewa.
“Ba matsala ai ɗumamen Innayi nace”.
Miƙewa Asma'u tayi tare da ficewa Moddibo da M Jameel kuwa Matsawa sukayi tare da fara cin ɗumamen kaɗan suka ci sannan suka ci jollof ɗin taliya suka sha tea perpesoup din kazar kuwa ko buɗewa basuyi ba bayan sun gama suka miƙe suka tafi masallaci tare da idar da sallah saida sukayi Azkhar kafin suka dawo gida suka kwanta bacci kafin wani lokaci su tashi su tafi Tafseer acikin makarantar su.
Ƙarfe Goma da rabi dai-dai suka farka atare Moddibo ya miƙe bakinsa ɗauke da addu'a kana yashiga toilet yayi wanka tare da daura al'wala zama yayi tare da shafa lotion mai ƙamshi sannan ya sanya Jallabiya Marron colour tare da ɗaura baƙin Alkyabba akai kana ya naɗa hirami akansa sosai yayi kyau tamkar balarabe kana ya feshe jikinsa da turarukansa masu daɗin ƙamshi sallah walha ya gabatar tare da zama ya fara ƙira'a cikin Suratul Maryam.
Sha daya da rabi dai-dai M Jameel ya fito daga ɗaya Bedroom din cikin shiri da alama ya gabatar da sallar walhar shima kallon hadaɗɗen agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa yayi kana ya maida kallonsa kan Moddibo tare da cewa.
“A.J sha biyu ta kusa fa mutafi kasan ana jiranmu”.
Dai-dai lokacin da wayar Moddibo yayi ruri kallon screen ɗin yayi tare da kallon M Jameel kana yace.
“Gashi ma malam Arɗo ke kirana da alama zai ce mu ake jira masallaci ya cika”.
Jinjina kai M Jameel yayi kana yace.
“Mu tafi”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da ɗaukar mukullin motar suka fice.
Kai tsaye masallacin dake cikin makarantarsu suka nufa wanda yake cike da maza da mata ko wanne na ɓangaren su sai dai mata sunfi yawa ƙarfe 12:00 ya musu acikin masallacin.
Gyaran Murya M Jameel yayi cikin nutsuwa da kuma yanayin zafin jinjinsa ya gyara zamansa tare da cewa.
_“Innalhamdulillah Nahmaduhu Wanastainuhu wanastaghfiru wa'nazubillahi billahi min shuriri anfusna wamin sayyi ati a'amalina manyah dillahu fala hadiyala waman mudillah fala hadiyala Wa'ash hadu Allah ilahalillahu Wa'ash hadu anna Muhammadu Abduhu warasulu amma ba'ad faya Ikhwatul musulmi Assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuhu”_.
Suka amsa da.
“Wa'alaikum Salam warahmatullah wabarkatuhu”.
Ya numfasa tare da kallon Moddibo da idanunsa ke lumshe sai kuma ya gyara zamansa kana yace.
“Duk kan yabo da godiya su tabbata ga Allah subhanahu wata'ala mai kowa mai komai daya sake nuna mana wannan wata mai cike da falala da kuma rahma Allah ya nuna mana ƙarshen sa lafiya kamar yanda ya nuna mana farkon sa Awancan shekarar mun tsaya aƙarshen Suratul Jinni insha Allah yau zamu ɗaura acikin Suratul Muzammil Aramma jeka cikin suran muji mai Allah yace”.
Gyaɗa kai Moddibo yayi tare da gyara zamansa cikin nutsuwa da sanyin Muryansa tare da kamala kana yayi A'uziyya tare da basmala ya fara kamar haka;.
_“1-Ya Ayyuhal Muzammil,2-Ƙumullaila illa ƙaliliah 3-Nisfshu awinƙus minhu ƙalila”_
Atake masallacin yayi tsit tamkar babu mahalukin dake numfashi yayin da karatun ke ratsasu.
Shikuwa M Jameel Kai ya gyaɗa da faɗin.
“Yawwa Aramma ci gaba mai Allah yake cewa acikin aya ta gaba”.
Jinjina kai Moddibo yayi tare da manna bayansa da jikin kujera ya cigaba da cewa.
_“4-Auzidhu alaihi warartilill ƙur'ana tartila5-Inna sanulƙi alaika ƙaulan sakila”_.
Numfashi M Jameel yayi kana yace.
“Suratul Muzammil Makiyya ce tana da ayoyi guda ashirin.
Ya numfasa tare da lumshe idanunsa kana ya cigaba da cewa.
“Suratul Muzammil tana karantar da tarbiya da juriya ga Muslimi,domin susami damar tsayuwar da umarnin Allah”.
Still wajen yayi tamkar babu mahalukin dake numfashi jama'ar dake wajen su tattara duk kan nutsuwarsu suna sauraron abinda Allah yace Moddibo kuwa System ɗin gabansa ya zubawa Idanu tare da lumshe idanunsa.
M Jameel ya numfasa tare da cewa.
_“Ya Ayyuhal Muzammil,Ma'ana ya kai wanda ka lulluɓa da mayafi”_
Atake masallacin ya kaure da kabbara suna faɗin.
“Allahu akbar, Allahu akbar Allah yakareka Malam”.
Zama M Jameel ya gyara tare da kallon jama'ar bayan sunyi shiru ya ɗaura da cewa.
_“ƙumillayla illa ƙalila,katsaya domin yin Sallah acikin dare(suka) face kaɗan”._
Nanma kabbara suka sake kaurewa dashi.
Shi kuwa M Jameel numfashi ya sauƙe kana ya cigaba da fadin.
_“Nisfshu awin minƙushu ƙalila,Rabinsa ,ko ka rage Abu kaɗan daga gareshi._
Haka suka cigaba da tafsirin ayoyin.
Ƙarfe ɗaya dai-dai suka tashi ɗaya da kwata sukayi Sallar azahar zama sukayi acikin masallacin suka fara Muraja'a tun daga suratul tauba zuwa Nahal jin kiran la'asar yasa suka dakata kana suka tashi Moddibo ne yaja Sallar M Jameel kuwa shi yayi ladanci bayan sun idar ne suka fita kai tsaye masallacin dake Unguwar su Moddibo suka nufa ƙarfe biyar suka fara gabatar da tafsirin acikin suratul hujurat wannan kuma na maza ne zalla ƙarfe shida dai-dai suka tashi.
Bayan sun tashi M Jameel yashiga mazaunin Driver Moddibo kuwa gefen mai zaman banza ya zauna tare da lumshe idanunsa yana sakin numfashi Kallonsa M Jameel yayi tare da murmushi kana yayiwa motar key.
Wayar Moddibo ne ya hau ruri Anutse ya sanya hannu ya ɗauka ganin sunan Ummi yasa ya gyara zamansa cike da nutsuwa yayi Picking tare da Sallama kana yace.
“Ummi ina yini”.
Daga ɗaya ɓangare cike da so da kulawa Ummi tayi murmushi kana tace.
“Babana".
Moddibo ya amsa da.
“Na'am Ummina”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Babana sannuku da ƙoƙari nasan yanzu baki da hutu Ramadan ya shigo”.
Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.
“Ga munan dai kam Ummi muna fama”.
Cike da kulawa da kuma ƙaunar su tace.
“Allah sarki Allah ya biya ku Allah yaƙara rufa asiri”.
Ya amsa da.
“Ameen”.
Ummi ta gyara wayar akunnenta kana tace.
“Babana nashirya muku abin buɗa baki kuzo kusha ruwa”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.
“Toh Ummi mun gode muna nan tafe yanzu ma Insha Allah zamu zo”.
Kasancewar M Jameel na Jin Komai saboda wayar a handsfree yake yasa ya juya akalar motar zuwa hanyar gidan Ummi adai-dai ƙofar gidan Ummi M Jameel yayi hong mai gadi ya buɗe musu suka shiga...!
Yau dai ba editing. Dan muna cikin hidiman bikine
By
*GARKUWAN MARUBUTA*
[19/07, 7:44 PM] Halimatu A/rahman Sadeeya: 📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇
*SAKAYYAH*
_Page 15_
_NA_
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*Saura ƙiris FREE PAGE dai yazo ƙarshe in sha Allah mun kusa gamawa. Yar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci domin littafin SAKAYYAH na kuɗine 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP. 09097853276. Kana in saki a Groups ɗin da zamuci gaba da posting.*
*GARKUWAR* taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*