← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 114

Sashe 84

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acan ɓangaren su M Jameel kuwa suna isa Hospital ɗin aka karɓi Ramadan tare da kaisa Emergency Room.
Atake aka fara bashi temakon Gaggawa kasancewar akwai ƙwararrun Likitoci cikin ikon Allah beji wani rauni ba sai karaya daya samu aƙafarsa na hagu.
Cikin mintunan da baza su gaza talatin ba ya farfaɗo tare da fashewa da kuka kana ya buɗe Idanunsa tare da cewa.
“Wayyo ƙafata Addah Khausi Ƙafata, Wayyo Addah Khausi Ƙafata”.
Ahankali Moddibo dake gefensa ya matsa tare da riƙe hannunsa kana yace.
“Sorry Ramadan kayi haƙuri kayi shiru kaji”.
Cikin kuka sosai Ramadan ya kallesa tare da cewa.
“Mommy na Malam akaini wajen Addah Khausi.
Ina Addah Khausi na Ƙafata ciwo yake min zafi?”.
Ya ida maganar yana jujjuya kai yayin da gaba ɗaya zufa ya wanke masa ilahirin jikinsa Musamman saman goshin sa amma babu hawaye a Idanunsa yayinda ƙafansa ya sake kamar roba ya langwaɓe.
Cike da rarrashi da kuma tausayawa Moddibo yace.
“Kayi haƙuri zai daina insha Allah”.
M Jameel kuwa magunguna da abubuwan da za'ayi ɗauri Dr ya rubuta masa kana ya ya fice tsaye ya samu malam Arɗo maƙale da waya akunnen da alama da Lamiɗo yake magana.

Cikin yanayin jimami ya gyara zaman wayar akunnensa tare da cewa.
“Wallahi kuwa akwai yaron wajenka da mota ta ɗan kuskuresa yanzu haka ma muna asibiti”.
M Jameel ne ya gyara tsayuwar sa tare da harɗe hannunsa aƙirji kana ya lumshe idanunsa.
Cikin sauri Malam Arɗo yace.
“A'a ka kwantar da hankalin ka Mai Martaba baiji wani ciwo ba.
Dan Allah dan Annabi ka kwantar da hankalin ka”.
Ganin Malam Arɗo ya katse kiran yasa M Jameel cewa.
“Malam wai batun ɗauri ne ƙafarsa ta karye to yanzu ance za'a yi masa ɗauri”.
Jinjina kai Malam Arɗo yayi kana suka fita da M Jameel.

A can Gidan Lamiɗo kuwa tun bayan tafiyarsu Ramadan Makaranta Mommy ta kasa miƙewa taje ta gyara ɗakin mijin nata.
Duk da kuwa cewa itace da girki baki ɗaya jikinta Asanyaye yake bata da wani kuzarin kirki yayin da Khausar ke kwance gefenta har zuwa lokacin hannunta na dafe da maranta.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da furzar da iska mai zafi daga bakinta kana ta yunƙura da niyyar miƙewa dai-dai lokacin Lamiɗo ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.

Yana shiga idanunsa akan Mommy tare da cewa.
“Aysha!, Aysha”.
Cikin sanyin murya da mutuwar jiki Mommy tace.
“Na'am”.
Sai da yayi ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa tare da cewa.
“Zo muje ki rakani?”.
Kallon Mamaki Mommy tayi masa tare da faɗin.
“Ina zamu je?”.
ƙasa yayi da kansa kana yace.
“Ke kam zoki rakani wani waje mana”.

Atake zuciyarta ya tsinke ƙirjinta ya buga da masifar ƙarfi kana tace.
“Rakiya kuma ina kuma zamuje. Mai Martaba ka faɗa min?”.
Ta ƙara sa maganar tare da kallon ƙwayar idanunsa da take iya hango tsantsar tashin hankali da damuwa.
Cikin rawan murya tace.
“Meyesa mu Ramadan”.
Jin abinda tace yasa Khausar dake kwance tayi saurin miƙewa Atake Idanunta suka cika da ruwan hawaye lokaci ɗaya tsoro ya rufeta!.

Cikin dakiya Lamiɗo yace.
“Babu Abinda Ya samu Ramadan ke kam zoki rakani”.
Cikin yanayin sadaukar wa Mommy ta kallesa kana tace.
“Dan Allah ka faɗa min Meya samu Ramadan ɗina!”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“Kizo mu tafi mana”.
Miƙewa Khausar tayi cikin rawan murya dan tuni hawaye suka wanke mata fuska kana tace.
“Dan Allah Abba inzo mu tafi”.
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Eh”.
Cikin sauri ta sanya dogon hijabinta dake fitar da sanyayyan ƙamshin ta fita, shima Lamiɗo fita yayi sashen Hajiya Bunayya ya nufa yana kirata kasancewar shi kansa be san waya samu hatsari acikin ƴaƴan nasa ba Haiydar, Aminu, ko Ramadan.

Mota suka shiga Khausar na gaba Lamiɗo Gimbiya Bunayya da Mommy suna baya.
Lokaci ɗaya hankalin Mommy ya sake tashi ganin sun nufi hanyar asibiti cikin tsanananin tashin hankali tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n dan Allah Mai Martaba ka faɗa min me yasamu Ramadan ɗina?”.
Girgiza kai yayi tare da kallonta kana yace.
“Nima kaina ban sani ba Aysha babu yanda muka iya da hukuncin Ubangiji”.
Hajiya Bunayya kuwa ƙasa tayi da kanta cikin tsananin farin ciki da jin daɗi ta saki murmushi aranta tace Alhamdulillah burina ya cika in. Allah ya yarda yau ankawar min da Haiydar da Ramadan na huta dole inƙara musu kuɗi me tsoka yanda zasuji farin ciki na kawar min da ƴaƴa biyu maza ɗin nan shikenan Mai martaba bashida wani ɗa Namiji sai Aminu dole Aminuna shi zai gaji sarauta.

Ahankali ta ɗago kanta Idanunta cike taf da ruwan hawaye ta kalli Lamiɗo tare da cewa.
“Innalillahi Wa'inna ilahi rajiu'n. Mai martaba mai yafaru?”.
Cikin yanayin damuwa yace.
“Ni kaina ban sani ba ance min dai ɗana Namiji ne amma ban sani ba Aminu ne...”.
Aruɗe Hajiya Bunayya tasa hannu ta dafe ƙirjinta tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n ɗaya-ɗayan nawa”.
A hankali ya fesar da iska daga bakinsa kana yace.
“Kuma ban sani ba ko Haiydar, ko Ramadan ne ban sani ba sai mun shiga”.
Mommy kuwa lumshe Idanunta tayi tare da faɗin.
_“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan min ha”_.
Suna isa suka fito bayan Driver Yayi parking Malam Arɗo na ganin Lamiɗo yayi saurin miƙewa tare da isa inda suke kana yace.
“Sannunku da zuwa Mai Martaba”.
Khausar kuwa tun da suka fito take kuka baki ɗaya jikinta ya gama bata Ramadan ne kuma ya rasune.

Batare da Lamiɗo ya amsa Barka da zuwan da yake masa ba yace.
“Acikin ƴaƴana waye ne yasamu hatsarin?”.
Malam Arɗo ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.
“Ƙaramin ne”.
Ƙasa daure wa Khausar tayi kuka ta fashe dashi tare da faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Mommy Ramadan ne,
sai da yace kada yaje makaranta yau kawai abarshi kada yaje kamar yasan me zai faru dashi na nace dole na muka turashi”.
Mommy kuwa kasa daure wa tayi hawaye masu zafi suka shiga zubo mata.

Dai dai lokacin M Jameel ya dawo daga sayo magungunan a Pharmacy dake cikin Hospital ɗin.
Kallon Malam Arɗo Lamiɗo yayi kana yace.
“Ku kaimu ciki”.
Kai M Jameel ya gyaɗa tare dayi musu Jagora kasancewar Mai matarba ne da iyalansa yasa aka barsu suka shiga.

Suna Shiga idanun Khausar ya sauƙa akan Moddibo dake Rungumeta da Ramadan yana lallashinsa.
Ramadan na kallonta ya fashe da sabon kuka tare da cewa.
“Adda Khausi ƙafata Addah Khausi zoki riƙe min ƙafata”.
Kallonsa ya mayar kan Mommy tare da cewa.
“Mommy ancire min ƙafata ko? Bana jinta a jikina”.
Sai kuma ya kalli Lamiɗo daya zuba masa Idanu cikin matsanancin kuka yace.
“Abbah Ƙafata, Ƙafata”.
Kallonsa ya mayar kan Hajiya Bunayya ya langwaɓar da kai amma baice komai ba.

Hajiya Bunayya kuwa kallon Moddibo tayi jikinta na tsuma tace.
“Ina Haiydar kadde shi yana mutuware?, Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Ido Moddibo ya zuba mata tare da tsaida idanunsa acikin nata abinda ba ɗabi'arsa bace ba kuma al'adarsa bace haɗa ido da mutum amma haka nan ya tsinci kansa da tsaida idanunsa akan matar yana kuma nazartan ta.
Cikin yanayin ɓacin rai M Jameel ya juya ya kalleta tare da cewa.
“Haba Hajiya wannan wani irin kalma ne ya za ayi kice yana mutuware?”.
Hannu tasa tare da share hawayen fuskarta kana tace.
“To ina yake? Ina Haiydar Allah sarki babban ɗan mu wanda zai gaji Mahaifinsa a sarauta Wayyo Haiydar”.

Malam Arɗo da shigowarsa kenan ya kalleta tare da cewa.
“Haiydar na nan lafiya yana makaranta yana karatu kana suna cikin kulawa!”.
Da sauri Ta haɗiye wani abu mai masifar ɗaci tare da cewa.
“Toh Ina Aminuna?”.
Cike da kulawa malam Arɗo yace.
“Shima yana cikin ƙoshin lafiya wannan ne kaɗai Accident ɗin ya faru dashi”.
Lokaci ɗaya wani masifaffen ɓacin rai da baƙin ciki ya mamaye zuciyarta cikin ranta tace Haiydar bai mutu ba sannan shima wannan karayane ka ɗai?”.
Tsaban zancen zuci dake cinta saida kalmar Karaye ne kaɗai ya fito fili.

Atare Khausar da Moddibo suka kalleta jin abinda tace wannan ɗin ma Karaye ne kaɗai Moddibo ya maimaita kalmar Aransa.
Khausar kuwa kwallon ta tayi tare da tsareta da ido tana sake maimaita kalmar aranta.
Malam Arɗo ya kalli Lamiɗo tare da cewa.
“Mai Martaba karaya yasamu dama akan za'a yi masa ɗauri ne saboda Andu basa gaba ɗaya baiji wani ciwo ba Karayane da Allah ya ƙadarta toh insha Allah yanzu za'a yi masa ɗauri”.

Jinjina Kai Lamiɗo yayi tare da cewa.
“Mun gode Allah ya saka da alkhairi”.
Cike da damuwa Malam Arɗo yace.
“Dan Allah kayi haƙuri akasani ne, tsautsayi aka samu wanda baya wuce ranan sa mai motar kamar da gayya yayi ko tsayawa bai yiba ya gudu baki ɗaya abin yazo da akasani ne bamu taɓa samun irin wannan akasin abakin makarantar ba”.
Girgiza kai Lamiɗo yayi tare da cewa.
“Bakomai Malam Arɗo ai babu yanda muka iya da ƙaddara ko agadon Mahaifiyarsa yake idan Allah ya ƙadarta zai karye dole ya karye Waman Ƙadarallahu Haƙƙa ƙadrihi”.
Kai Malam Arɗo ya gyaɗa tare da cewa.
“Haka ne kam”.
Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauƙe tare da faɗin.
“Amma bana son ɗaurin asibiti zamu koma dashi gida ayi masa na Gargajiya”.
Jingina kai Malam Arɗo yayi tare da cewa.
“Toh shikenan Babu matsala”.
M Jameel ya Kalli Ramadan cike da tausayawa kana yace.
“Toh Mai Martaba Allah ya ƙara sauƙi”.
Kana ya miƙa masa ledan maganin daya sayo yace.
“Gashi magunguna ne na rage zugi da zafin ciwo koda ɗaurin gidan za'ayi masa za ayi amfani dasu”.
Karɓa Lamiɗo yayi tare da faɗin.
“Toh angode”.
Kana ya sanya hannu acikin aljihu ya ciro wayarsa tare da kiran number Malam Bala mai ɗauri.
Katse wayar yayi bayan sun gama mga, juyawa yayi ya kalli Hajiya Bunayya da Mommy kana yace.
“Mutafi to”.
Sai kuma ya juya ya kalli Khausar dake kuka hadda sheshsheƙa yace.
“Haba Addah Khausi kiyi haƙuri mana ai sai ki ƙara tayar masa da hankali shi yana kuka yana kiran ki sannan kema kina kuka ki bashi ƙarfin gwiwa mana”.
Chapter 84 · 0% Book details