← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 114

Sashe 27

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Moddibo ta hango zaune a gefen gabas yana fuskantar tata, bima'ana yana kallon yamma, zaune yake akan wani dutse mai masifar sheƙi kana wasu mutane biyu na tsaye gefen hagu da damansa,
Sannan da buta gabansa bisa alama Al'wala yayi domin farin yashin daya mamaye wajen daga gabansa a jiƙe yake, kana yana mai fidda wani irin ni'imtaccen ƙamshi maisa ɗan Adam lumshe ido. Baki ɗaya haske ya mamaye ilahirin filin wajen hakan yasa itada Moddibo suna fuskantar juna yayin da M Jameel da Adda Adama matar Baffan Umaru suma ke fuskantar juna.
Kana lambu dake can bayanta kuwa yake feso musu iskar yammaci dana lambun suka haɗu waje ɗaya daga sama kuma rana ne yayi Ja yana shirin faɗuwa.
A hankali ta sauƙe numfashi mai nauyi tare da lumshe idanunta.
Da sauri ta buɗe idanun nata, jin wani irin sassayan sautin dariya mai cike da shauƙi da Moddibo yakeyi.
Cike da mamaki duk suka zuba mishi idanu.
Yayinda Adda Adama ma tuni ta fara dariya mai sauti.
Ita kuwa Khausar haka nan taji jikinta yana tsuma tare da sakewa, da sauri ta juya ta kalli M Jameel ga mamakinta shima ita yake kallo, da idonshi ya nuna mata Moddibo yana mai yin lallausan Murmushi, da sauri ta maida kallonta kan Kekkyawar fuskar Moddibo, wacce tunda take a rayuwarta dashi bata taɓa ganin yayi dariyar da har haƙoransa na gaba zasu baiyana ba.
“Fatabarakallahu fih hasanil khaliƙeen”.
Ta furga a saman lips ɗinta, lokacin da ta sauƙe ƙwayar idanunta kan fuskar Moddibo, da sauri ta kuma lumshe manyan Idanunta sabida wani irin masifeffen sheƙi da ta hango sajenshi dake kwance lip-lip yanayi,
Sautin dariyarsa da har yanzu yake ne yasata saurin buɗe idanun.
“Subahanallah, tsarki ya tabbata ga Ubangiji da ya halicci wannan bawa ya kuma bashi waɗan nan haƙoran”.
Ta faɗa a fili lokacin da taga ƙyellin da haƙoransa keyi har yana ɗauke mata idanunta,
Lobgoɓar da kanta tayi bisa kafaɗarta.
Wani irin sassayan numfashi ta fesar tare da tsaida idanunta a kanshi.

Shi kuwa Moddibo dariya yakeyi mai sayyan sauti wanda yake da daɗin ji, har maƙolloton wuyanshi yana ɗan haurawa yayi sama kana ya dawo ƙasa.
Yayinda ya ɗaura tafin hannunsa kan ƙirjinsa.
Cikin tsananin dariyar ya samu ya ɗan tsagaita tare da furta.
“Astagfurillah watubu ilaik”.
Sai kuma ya ɗago ya kalli M Jameel lokaci ɗaya kuma ya sake sakin dariya mai sauti yana cewa.
“Astagafitillah Wayyo cikina”.

Cikin rage girman idanunta take kallon gashin girarsa dake kwance lip.

Jameel kuwa sai Murmushi yakeyi tare da girgiza kansa.
Yayinda Adda Adama ma dariyar takeyi harda riƙe ciki.
Ita kuwa Khausar gaba ɗaya ta kasa ɗauke idonta daga kansa.
A haka har rana tayi mudun kuyanƙi alamun yana gab da faɗuwa.

amma kafin ya faɗi saiya rabu kashi biyu.
Yayinda Khausar kuwa ke zaune tana fuskantar yamma hakan yasata ganin abin.
Atake hankalin ta ya tashi ganin yanda ranan ya rabu kashi biyu.

Ita kuwa Adda Adama hannu tasa ta dafe ƙirjinta tare da faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n yau mun shiga ukun mu ku dubi yanda ranar tayi fa!”.
Tana faɗin haka duk dariya da murmushin da sukeyi ya tsaya.

Moddibo kuwa daga inda yake zaune ya ɗaga kansa sama tare da juyawa bayanshi kana a hankali yace.
“Ya Salam ya ilahi ya mujabat da'awati meke Shirin faruwa”.
Cikin tsananin gigita da tashin hankali da firgici Khausar ɗin ta saki kuka mai cike da rauni tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi raji'un, hasbunallahiwani'imanwakil, mun shiga uku”.
Sai kuma ta juyo ta kalli Moddibo da ya gyara zamanshi kana a hankali yace.
“Babu abinda zai faru wanda Allah bai sani ba, Insha Allah Ubangiji zai mana maganin duk kan abinda yayi tsanani”.

M Jameel kuwa kasa furta komai yayi sai hawaye dake kwaranya daga idanunsa.
ita kuwa Khausar ganin M Jameel na Hawaye kawai sai itama tashiga yin kuka amma ba mai sauti ba.
Cikin wani irin yanayin da bazai misaltuba Moddibo ya dubesa kafin yace.
“Haba J. Kamar ba namiji ba addu'a ya kamata muyi duk kan tsanani yana tare da sauƙi”.
Still dai M Jameel baice komai ba.
Shi kuwa Moddibo cikin sanyin jiki ya fuskanci Khausar cikin wata iriyar murya yace.
“Khausar tausayi na kike ji ne?”.
Cikin kwaranyar hawaye ta gyaɗa mishi kai tare da sakin raunataccen kuka mai cushe numfashi, lokaci ɗaya numfashin ta ya fara cushewa yana ɗauke wa, cikin yanayi wahalar neman numfashi taga Moddibo ya...!
Dai-dai lokacin kuwa ta farka daga baccin da takeyi ciki razana tare da kaɗuwa ta dafe kanta da takeji yana jujjuyawa.
Kana duk da sanyi da ake tsulawa a garin wani irin zufane ke tsastsafo mata ta ko ina.
Cikin sauƙe ajiyar zuciya, ta juya gefen hagunta ta karanta A'uziyya ƙafa uku kana ta canza hannun kwanciyar ta zuwa dama.
Sai dai sam baccin yaƙi zuwa mata, sai ta kama karatun Alqur'ani cikin sassayan sauti,
Cikin ikon Allah ta samu bacci ya kuma yin awon gaba da ita.

Baki ɗaya Wunin wannan ranan akasalance tayi koda abinci ta kasa ci haka zalika koda yawan surutu sai ta rage sosai mafarkin ya tsaya mata arai da zaran ta tuna irin mafarkin da tayi sai taji zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske.

Da daddare cikin ikon Allah data karanta Alkur'ani mai girma tare da bin haddarta da Malam Liman ya bata sai taji sauƙin abin aranta duk da kuwa bawai ta daina jin tsinkewar zuciyar bane amma ya ragu sosai.
Da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare Khausar suna zaune a farfajiya gidan Hajja Nana su uku ita Yaya Abba da kuma Dije suna hira jefi-jefi take sanya musu baki aciki daga ƙarshe ma ta miƙe tace zata je ta kwanta sai Dije ma ta miƙe ganin haka yasa Yaya Abba ya musu rakiya har gida.

Washe gari:Da safe still haka Khausar ta tashi bata da wani ku zari koda abinci ne ta kasa ci iyakacinta tasha Tea ko ruwan kunu sannan ta kasa faɗawa kowa irin mafarkin da tayi domin jikinta ya mutu sosai da mafarkin.
Da daddare ba kinta ɗauke da Sallama tashiga gidan Hajja Nana.
Asaman laɓɓa Hajja Nana ta amsa mata Sallamar tana binta da harara dan tunda taƙi markaɗa mata wake take jin haushi ta.
Ita kuwa khausar bata masan Hajja Nana nayi ba ta nemi waje ta zauna tare da kallon Hajja Nana tace.
“Yunwa nakeji ki bani abinci zanci”.
ta faɗa tana kallon ƙorenta dake jere guda goma sha Uku.

Harara Hajja Nana ta wurga mata tace.
“Gashi ki ɗauka ki ci”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da Matsawa jikin ƙoren tashiga buɗewa ɗaya bayan ɗaya tana dubawa saboda taga gidan Malam Liman anyanka kaji cikin Sa'a kuwa tana buɗe ɗayan taga Jan miyar dage-dage da kuma tuƙeƙƙen tuwon shinkafa.
Ta gyara zamanta tare da wanke hannunta ta fara cin tuwon cikin Mintuna kaɗan ta cinye tass sannan ta kuma janyo wani Ƙoren dan sosai take jin yunwa sannan bata wasa da cikinta dan ita dai ko ciwo bai cika hanata cin abinciba karo na forko kenan a rayuwarta da abu ya tsaya mata a rai har ya hanata cin abinci na kwana biyu son ta Tara yunwar shiyasa.
ta cinye ƙore biyun tas dan dama tuwon ba wani mai yawa ake samata ba tunda akwai yawan kanukan.

Hajja Nana kuwa juyawa tayi da mamaki ta kalleta kafin tace.
“Yanzu har kin cinye tuwon nan”.
Kai Khausar ta gyaɗa mata tace.
“Na cinye mana kuma yanzu ma ƙarawa zanyi dan yunwa nakeji rabo na da abinci tun shekaran jiya da daddare fa sai dai in ta Shan abu mai ruwa-ruwa”.

Taɓe baki Hajja Nana ta kuma yi tace.
“Toh bubbuga rumbu ga shican ki ƙara ki cinye duka ma in Kinga dama”.
Ta Faɗa tare da tura mata wani akoshin.

Ɗauka Khausar tayi kamar wasa ta cinye dake abincin ba wani da yawa ake sawa aƙoron ba dake sun san cewa ƙorenta da yawa mafi yawan lokuta ma loma ɗaɗɗaya takeyi ako wani ƙoren idan tayi loma sha uku ya wadatar mata a dai cikin tsohuwa ta kuma tsinci nama ta cinye to shiyasa ba'asa mai yawa.

Ita kuwa Hajja Nana ganin yanda Khausar ke cin abinci yasa tayi zaton gatse take mata ta harareta da faɗin.
“Mutum kamar jaki wannan ci haka ki cinye wannan ƙoren ki cinye wancan”.
Ta ida maganar tare da sake tura mata wani ƙoren.

Ita kuwa khausar ta ƙoshi amma saboda ta ƙular da ita yasa ta janyo ta buɗe naman kan abincin ta cinye sannan ta gutsiri kamar loma biyar ta zuba akwanan dake empty.
Wani kwanon Hajja Nana ta kuma tura mata still ta cinye naman ta kuma gutsura ta zuba a sauran kwanon.

Hajja Nana ta dube ta cikin tsareta da ido tace.
“Wai har yanzu baki ƙoshi ba?”.

Khausar cikin yamutsa fuska ta gyaɗa kai kana tace.
“Eyyy ban ƙoshi ba”.
Wani akoshin Hajja Nana ta sake tura mata, Khausar kuwa laluma ta cigaba dayi idan taji da nama ta cinye ta gutsits-tsira tuwon ta bari.

Ita kuwa Hajja Nana kamar wacce akace ta leƙa taga aika-aikan da Khausar keyi da tuwon ta miƙe cikin fushi tace.
“Shegiyar yarinya gantalelliya ni kike nunawa barikanci, 'yar banza kinje kin zauna gidan Mayu kema kin koma kamar Mayya, sai cin nama kamar kura, wato ma duk naman kike lalubewa dan mayta ai dai na sani in dai ba cikin zanine da keba ai yaci ki ƙoshi”.
Ya mutsa fuska Khausar tayi tare da riƙe ƙugunta tace.
“Naci ɗin idan ni Mayya ce kinsan inda na samu maita, tunda nazo saboda shegen maƙo ko zabuwa ɗaya kin kasa yanka min gaki da Zabbi kamar zasu kashe ki ga shanu kuma aina Babana ne”.

Salati Hajja Nana tayi tare da fashewa da kuka.
Kasancewar duk dare aƙofar gidan ta suke zama yasa Baffa Umaru daya ji sautin kukan ta ya miƙe kasancewar Allah ya bashi kunne komai ƙanƙantar sautin abu ya kan iya ji.

Ganin Hajja Nana na kuka yasa Baffa Umaru nufarta tare da cewa.
“Addah Nana Meya faru?”.
Nuna Khausar tayi da hannu kana tace.
“Wannan ‘yar Usmanu har zata min gori wai gadon Ubanta na riƙe kaji shegiyar gantalalla yarinya dan ma Allah yayi dan ke macece!”
Chapter 27 · 0% Book details