← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 114

Sashe 10

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Riƙe cup ɗin tayi ba tare da tasha ba,
Ido Khausar ta ɗan zuba mata kana tace.
“Ya dai Giɗaɗo lfy kuwa?".
Numfashi mai nauyi Asma'u ta fesar kana cikin sanyi tace.
“Kamar zan biya ɗazu ki rakani”.
Ajiye cup ɗin hannunta tayi tare da cewa.
“Ina?”.
Murmushin Asma'u tayi tare da cewa.
“Gidan su Moddibo”.
Fuska ta kwaɓe tare da cewa.
“Allah ya kiyasheni, me zai kaini gidansu wannan mugun, mutumin da duk duniya bana da maƙiyi sama dashi, duk abin da nai laifine, ni zanje gidansu yace na kai musu fitsara ya dakani a banza”.
Murmushin Asma'u tayi tare da cewa.
“Yoh ai shiyasa ma ban biyaba dan nasan bazaki taɓa yarda kijeba, kuma dai don shine sarkin masifa da mugunta kawai daga zuwa gidansu sai ya kama dukanki”.
Baki ta taɓe tare da cewa.
“Yoh ai bazanma jeba ma”.
Kai Asma'u ta jinjina a ranta tana raya wata rana zatayiwa Khausar tsiya, ta kwasheta ta kaita.

Ajiye kofin tea ɗin tayi tare da cewa.
“A'a dubiyar mara lfy cefa Innayinsa ce ba".
“Can musu”.
Ta faɗa tana kwaɓe fuska
Murmushin Asma'u tayi tare da cewa.
“Toh naji”.

Daga nan sukaci gaba da hira.

Washe gari ranar jumma'a, misalin ƙarfe biyar dai-dai Khausar da ta shigo cikin gidan riƙe da hannun Raudat da alamun kitso ta kaita.
A bakin mashigar gidan nasu tayi kiciɓis da Amina da Samira sani,

Sun iso bakin ƙofar a tare, dole sai ɗaya ya kaucewa ɗaya kafin a samu wurin wuce.
Wani masiyacin kallo Samira ta cillawa Khausar tare da jan tsaki.
Ita kuwa Khausar tsuke fuska tayi cikin rashin shakka ko tsoro ta goga kafaɗarta da na Samira duk da kuwa Samira ta girmeta ainun.
Cikin izza Samira tace.
“Ke karere ki nitsu kisan da waye kikeyi”.
Ba tare da ta cire idanunta cikin nataba tace.
“Toh dodon gori”.
Cikin fahimtar caguben baƙar mgnar da Khausar ɗin ta yaɓa mata wanda yafi abinda ta gaya mata ciwo, tace.
“Ke nifa uwarki zanci”.
Wani bauɗeɗɗen harara da dogon tsaki Khausar taja tare da cewa.
“Raudat mu tafi, kada mu tsaya muji, kukan tsuntsaye marasa tushe da gurbatacciyar tarbiya”.
Daga nan, ta juya tayi gaba.

Samira sani kuwa wani irin masifeffen kallo mai cike da tsana take Binta dashi.
Cikin takaici tace.
“Wallahi na tsani wannan yarinyar sam bana son ganinta, domin ta zame min madakatar nasarata".
Kwaffa Amina tayi tare da cewa.
“Bar shegiyar yarinya zanyi mgninta”.

Cikin tarin tsana Samira tace.
“Kune ma kuka bata dama ai, tana agola sai iyayi take muku, an wani dai-dai ta komai naku da nata, wai hatta makarantarku ɗaya da ita, ni wlh da nice ke sai na zuga Umma ta zuga Lamido tasa an cireta a wannan makarantar, shegiyar yarinya mai kama da ƴan ruwa.”
Kwaffa Amina tayi tare da cewa.
“Bar hegiyar yarinya, zanyi maganinta”.

Ita kuwa Khausar a falo suka samu Mamynsu kishingiɗe bisa carpet saƙale da wayarta a kunne, da alamu waya takeyi, ido ta zuba mata jin tana cewa.
“Eh Hajja Nana in Sha Allah, zata zo, don dama cikin azumi suna hutu to kuma rashin lfyar ne ya hanata zuwa, amman yau suka koma makaranta, kuma an ƙara musu hutun mako uku guda, sabida gyaran da akeyi a makarantar in Sha Allah zata zo, a satin nan,".
Sai kuma ta ɗan yi shiru, na wasu ƴan daƙiƙu, cikin sanyi da girmamawa tace.
“Eh gata nan ma”.
Tayi mgnar tana miƙawa Khausar wayar, cikin kwaɓe fuska kamar zatayi kuka ta amshi wayar tare da karawa a kunne murya ciki-ciki tace.
“Njam ɓanɗu.
Ina yini?".
Daga can kuwa cikin irin isa da kasaita ta tsofi masu iko Hajia Nana tace.
“Lafiyata lau, ki shirya kuna gama jarrabawar jarabar taku ta bokoko a wutan zakizo nan Jauro yaya inada buƙatar ganinki”.
Cikin sauri da alamun akwai zaunanniyar tsama a tsakaninsu tace.
“Toh ai muna da hadda yanzuma da aka ƙara mana hutun, kuma zamuna zuwa leson”.
A faɗace tace.
“Leso mato nace leso mato, ita haddar mu nan ɗin ce miki akayi garin kafuraine, kizo liman Sadu zai baki duk ilimin da kikeso in dai na addinine, na kafurcine dai bamu dashi”.
Cikin takaici tace.
“Nifa ki dena kafurta mana ilimin mu".
Cike da mamaki da al'ajabi Hajja Nana tayi wani dogon salati, tare da sanar da Ubangiji wai itace tana mgn ana bata amsa, ita da mgnar ta take tamkar wahayi a cikin rugarsu kasancewarta itace babba.
Da sauri ta katse kiran tare dasa wayar a Airplane mode, ta kifeta gefenta sabida kada Mamynta ta gane.

Cikin yin rau-rau da ido tace.
“Mamy dan Allah kice mata tayi haƙuri sai ran babban sallah zanje muyi kwana biyu kafin a koma makaranta”.

Da sauri Momy ta fara jujjuya mata kai tare da cewa.
“Ban isaba Khausar ni dai kam bani da bakin yin taƙaddama da umarni Hajja Nana, ki kwana da sanin can zakije kiyi hutun nan, da kika samu ma bakije kinyi azumi a canba, tun tsawon shekaru takebi tana son hakan kuma bai samuba sabida uzurin da ita kanta ke fadarsa na zuwan ta Umara, bana kuma tace, saboda ke, bazata je Umrar ba, saboda tana so kije ki daɗe kisan yan uwanki su sanki.”
Cikin jan dogon numfashi tace.
“Mamy ni dai kin san ba shiri nakeyi da ita ba, ko zuwa nan tayi a wuni ɗaya sai tayi min masifa da sharri sama da sau biyar”.
Cikin haɗe fuska Mamy tace.
“Kuma dole kan umarnin ta da izininta mizanin muhallin zamanki yake, ki fara shiri kawai ma in Allah ya kaimu gobe zan gayawa Abbanku, zuwa ranar jumma'a mai zuwa sai ki bisu in sunzo cin kasuwa kije RUGAR JAURO YAYAH tabbas d....!

Littafin SAKAYYAH na kuɗine biya ki karanta cikin Salamah yar uwa.

By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[19/07, 7:44 PM] Halimatu A/rahman Sadeeya: 📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

*SAKAYYAH*
_Page 3_

_NA_
_AYSHA ALIYU GARKUWA_

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*FREE PAGE*

*Littafin SAKAYYAH na kuɗine 1k ne kacal ƴar ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin wani a kanki 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*

*GARKUWAR* taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran su dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk jihar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida. Set ɗina akwai manya akwai ƙananan set akwai kuma na tsakiya, ƙananan set ɗin daga 40k 35k 30k 25k 20k 15k 10k shine ƙara ɗan cukulan haɗiba bana haɗin kasa da 10k sai kuma haɗin kwanon ƙasaitacciyar mace shi 8k set ɗin tsakiyan su da 50k 60k 70k 80k 90k ne manyan kuma daga 100k ne zuwa yadda zaki iya Hajia ta*

GARKUWAR MA'AURATA

Cikin sanyin jiki Khausar ta miƙe tsaye tare da juyawa a hankali ta bar falon Mommy ta wuce ɗakinsu.

Ɗakin mai girmane wanda ke ɗauke da matsakaici gado ƙiran Italian bed sai durowarsa dake gefe wanda ke ɗauke da ƙofa shida, daga kusurwan gabas babban TV plasma ne da DStv sai tattausan canis carpet pinch color dake shimfiɗe Atsakiyar ɗakin wanda shi ke ɗan rage musu masifeffen sayin tayis ɗin,
komai na ɗakin pinch colour ne sai ɗan ratsin fari.

Cikin jagulewar zuciya ta kwanta bisa gadon tare da lumshe manyan Idanunta dake cike da ruwan hawaye.
Allah ya sani sam bata ƙaunar zuwa Jauro Yaya ko kaɗan, ya zame mata dole ta newa kanta mafita.
Ɗan gajeren tsaki taja tare da mirginawa ta juya tsakiyar gadon, kana ta lumshe idanunta, da wannan tunani bacci ya ɗauke ta...
Chapter 10 · 0% Book details