Sashe 23
Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.
🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA)*
Cike da mamaki Sadik ke kallon yanda take ta tsar Nonon cike da tsantsar ƙwarewa da rashin tsoro.
Fuskarsa ɗauke da murmushi ya juya ya kalli Baffa Jauro kafin yace.
“Ikon Allah Baffa kalli yanda take tatsan”.
Murmushi Baffa Jauro yayi yace.
“Ai ‘yar na gadana tafi ‘yar na koya gadonta ne fa abune da ajinin mu yake in Bata iya ba ai sai muce ba tsatson mu bace”.
Ita kuwa khausar murmushi tayi ita da kanta tana mamakin yanda ta riƙe bakin Nonon shanun tana tatsa Shar-shar kawai Nono mai ɗumi yana zubowa.
Ƙwayar dake cinyarta ne ya cika Dije ta janye ta sake sanya mata wani cike da shauƙi da kuma jin daɗi take cigaba da ta tsar Nonon kamar wacce tunda canma ta iya.
Baffa Jauro na murmushi ya janye ƙwarya ta biyu ya sake saka mata wani yana murmushi yace.
“Zan kaiwa Addah Hajja Nonon da kika tatsa da hannunki”.
Murmushi kawai tayi yayin da Sadik da Dije ke cigaba da mamakin ƙwarewarta.
Bayan ta tatso na ƙarshe ne Baffa Jauro yace.
“Kusha toh”.
Ita kuwa khausar ɗaga ƙwaryan tayi ta kai bakinta sai kuma ta cire kana ta mayar da kallonta kan Baffa Jauro tace.
“Nikam bazan iya sha ba suga ba”.
Murmushi Baffa Jauro yayi tare da buɗe tandu duma dake hannunsa wanda ke ɗauke da zuma ya zuba mata aciki kana yace.
“Toh kusha”.
Kai Khausar ta gyaɗa masa sannan takai ƙwaryar ɗanyen madaran mai ɗumi bakinta tasha sosai tana lumshe Idanunta kafin ta miƙawa Sadik yasha kana ya bawa Dije sauran.
Bayan sun shanye suka ɗauko hanyar komawa gida.
Khausar ta ɗaga Kaita kalli gefen damanta inda taji muryar Yaya Abba, ta hango Yaya Abba da Sule yayan Dije da take bi zaune acikin shagon caji da kuma kati wanda duk lokacin da Yaya Abba ya koma makaranta Sule ke zama ashagon kallon Sadik da Dije Khausar tayi tace.
“Ayyah mu biya ta wajen Yaya Abba mu gaisa”.
“Toh”
Suka ce sannan suka nufi shagon kana suka gaisa.
Kallon Khausar Yaya Abba yayi yace.
“Khausar kisan yanda zaki zauna da Goggon mu kar kinayi mata gautsin baki ba daɗi gsky”.
Khausar kuwa jin abinda Yaya Abba yace yasa ta taɓe baki kafin tace.
“Ni gaba ɗaya haushin matar nan nakeji idan ita bata sani ba ita tasa na tsani zuwa Rugar nan ba abinda yake ban haushi da Rugar nan kamar rashin wuta,Jiya duhu kamar zai kashe mutane sannan gashi ta ajiye Kuliya aɗakinta baki ɗaya garin ba daɗi wallahi”.
Ta ƙarashe tana mai ya mutse fuska.
Murmushi Abba yayi yace.
“Shine kenan matsalar duhu na damunki!?”.
Kai ta gyaɗa masa kai da faɗin.
“Eh”.
Yace.
“Shikenan toh za'a haɗa wutan Gen.ɗin nan dana ɗakinta shikenan ko?, Saboda kar kuna samun matsala atsakaninku bakisan yanda take son Babanki ba kema kullum zakiji tana maganarki amma ta shedeki cewa kina da gautsin baki ke ba irin Nanne data raina bace kinga su suna mata biyayya duk abinda take so”.
Kallon sa Khausar tayi kafin tace.
“Toh sude sunga zasu iya ne wannan ai mulkin mallaka takeyi mutum bashi da ‘yancin yin abu saida izininta, kuma batun wuta nifa ba kwana zanyi a gidanta ba tunda naga kuliyoyi take kiwatawa”.
Kusan a tare Sadik da Dije suka haɗa baki wajen cewa.
“Ki daure ki riƙa yin abinda takeso zaku shirya”.
Shiru kawai ta musu amma bata tunanin yin haka hira suka sake taɓawa kana daga bisani sukayi wa Yaya Abba sallama sannan suka shiga cikin gida...
Akwana atashi ba wuya yau kwanakin Khausar Biyar acikin Rugar Jauro Yaya ta fara sabawa da mutanen garin Sosai Musamman ma Dije ta sun zama ƙawaye dan agidansu take kwana ita da zuwa gidan Hajja Nana sai da safe take zuwa tayi mata shara sannan duk lokacin da sukaje sukayi tatsa zasu kai mata Nono.
Kasancewar duk gidajen ƙannenta taran ne ko yaushe sukayi tatsa zasu kai mata madara Shiyasa koda duk Rugar za'a rasa Madara da zuma ba'a rasawa a wurinta.
Kullum da rana gidan Hajja Nana Khausar ke zuwa cin abinci saboda anan ne zata zaɓi wanda ranta keso duk sanda ta zata buɗe kwanikan ta zaɓi wanda ranta keso Hajja Nana za tace ba tasa son ƙaƙale duk wanda ta fara buɗewa shi zata ci ita kuwa khausar tace bataji abunta haka ba domin Hajja Nana ta kasance irin tsofi nan masu sa ido bata gani sai ta tanka to kullum cikin faɗa suke ko yaushe Dije na maƙale da Khausar sosai Shaƙuwa ya sake shiga tsakaninsu sai kuma Ma'u yar bappa Garga sai dai ita bata karisasu girmaba,
sannan sosai take walwala domin garin ya mata daɗi sai dai kullum cikin kewar Mahaifiyarta da kuma ƙannenta take .
Washe gari, da safe Khausar na zaune gefen Hajja Nana tana matsa mata ƙafa.
Hajja Nana tayi saurin janye ƙafarta azabure tana watsawa Khausar kallon banza azafafe tace.
“Idan ba zaki matsa min ƙafarba aise ki bari bawai kizo kina min mugunta ba”.
Sheƙeƙe Khausar ke Kallonta da mamaki.
Ta janye hannunta daga kan ƙafar Hajja Nana tace.
“Ashe abin arziƙi yana zama na tsiya daga temako sai kiyi min ƙazafi”.
Kallon Banza Hajja Nana ta warsa mata kafin tace.
“Saboda baki da kunya nice zanyi miki ƙazafin?”.
Khausar data buɗe baki da niyyar magana ta fasa jin Sallamar Yaya Abba zama yayi tare da gaishe da Hajja Nana cike da ladabi Amsawa tayi tana sanya masa albarka.
Kallonsa Khausar tayi tace.
“Good Morning Yaya Abba”.
Da murmushi afuskarsa yace.
“Morning Khausar how was your night?”.
“Fine”. Tace tana ɗan murmushin tsokana tasan kwanan zance,
Ai kuwa taɓe baki Hajja Nana tayi tace.
“Wato Abba ƙafara koyon munafurci irin na baƙaƙen kafuran nan ko kazo har gaba kana zagina?”.
Kai Yaya Abba ya girgiza yace.
“Wallahi ba munafurci ko zagi muke ba Goggo Hajja kawai gaisawa muke”.
Ta gyaɗa kai tace.
“Toh adai dinga magana da yaren da zanji dan Manzon Allah (S.A.W)Yayi Hani da idan mutane na zaune wasu daga ciki su sauya harshe zuwa wanda sauran basaji koda ba zaginsu zasuyi ba amma wanda baijin Yaren zai tsargu dan haka ku kula hegiya gantalelliya mai kaɗifiri”.
Kai Yaya Abba ya gyaɗa cike da ladabi yace.
“Insha Allah zamu kiyaye”.
Ita kuwa khausar baki ta taɓe aranta tace wannan tsohuwa ta fiye mita da takalan magana. Ta fara da fadin Manzon Allah a karshe kuma ta buge da masifa da cemin gantalelliya.
Azahiri kuwa sai ta saki fursakarta ta matsa kusa da yaya Abba tace.
“Ayyah Yaya Abba ka sammin wayarka zan kira Mommy na mugaisa”.
Juyowa yayi ya kalleta tare da cewa.
“Ok ba matsala anjima zan baki sai Khadijah ta rakaki bishiyar ƙare zancen ka kuyi magana”.
Cikin jin dadi tace.
“Toh shikenan Nagode”.
Sallama yayi musu kana ya tafi.
Da yammaci Khausar na zaune adakali Dije kuma na shara suna hira sai da ta kammala sharan Khausar ta dube tace.
“Dije muje ki rakini wajen Yaya Abba in karɓi wayarsa”.
Kai Dije ta gyaɗa da faɗin.
“Toh”,sannan suka fice suna hira har suka isa.
Yaya Abba kuwa yana ganinsu ya miƙe tare da zuwa kusa dasu Idanunsa akan Khausar yace.
“Kinzo”.
Kai ta gyaɗa alamar eh.
Yace.
“Ok mutafi nima zanje taya ƙanina Ibrahim ɗiban ƙwai”.
Ɗan murmushi tayi tare da faɗin.
“Yaya Abba kaima kana aikin?”.
“Sosai ma aikin gado ne ai duk da cewa ina shirin kammala degree na acikin Ɓadamaya bazai hana nayi aikin gadona ba”.
Cewar Abba
Kai ta jinjina kana tace.
“Allah yataimaka”.
Ya amsa da.
“Ameen”.
Suna isa Gindin bishiyar Khausar ta juya ta kalli Dije tace.
“Dole sai na hau bishiyar network zai zo”.
Dije ta girgiza kai tace.
“A'a ko kan duwatsun nan kika zauna zaki samu network inde ba'a cika ba abinda yasa wasu ke hawa bishiyar saboda kafin su zo duk an cika saman duwatsun idan kasamu ancika dole sai kan bishiyar”.
Kai ta gyaɗa kafin ta ƙarasa ainihin inda ƙarƙashin bishiyar yake Sadik ta gani zaune yana waya.
Murmushi ta sakar masa tare da zama gefensa sannan ta sanya number Mommy. ringing ɗaya ana biyu Mommy tayi picking.
Ita kuwa khausar cike da zumuɗin jin Mommy tayi picking call ɗin tace.
“Mommy na”.
Aɓangaren Mommy kuwa jin Muryar Khausar yasa ta saki murmushi mai sanyi kafin tace.
“Khausar”.
Murmushi mai nuni da zallan farin ciki Khausar tayi tace.
“Na'am Mommy na nayi missing ɗinki”.
“Nima nayi missing ɗinki Mamana”.
Dariya Khausar tayi tace.
”Mommy Ina Raudat?,Ina Haiydar?, Ina Ramadan??”.
Murmushi Mommy tayi tace.
“Duk suna lafiya”.
Haiydar dake gefen Mommy yace.
“Gani nan Maman Fitina nayi missing ɗinki tunda kika tafi babu mai min faɗa babu wanda zai ce na renasa sannan babu mai nuna min iko da mulkin mallaka”.
Dariya Khausar tayi tace.
“Hmmm ai nagane ɗan uwa ko ina nuna maka iko da mulkin mallaka gada nayi in faɗa maka na samu wacce ta cuna Ni komai da ƙa'ida akeyi ko kallo zakayi sai an maka tsarin kallon da zaka yiwa mutum shi”.
Murmushi Haiydar yayi yace.
“Allah Hajja Nana ko?”.
Dariya tayi tace.
“Ita dai fitinanniyar tsohuwa, tsohuwa sai Bala'i ba'a zaman lafiya da ita".
Mommy dake gefe ta amshi wayar da faɗin.
“Um,Um Khausar karfa ta jiki”.
Murmushi Khausar tayi tace.
“Toh idan ta jini ma ya ta iya dani bare ma tana can gida mun barta tana gyaɗa kai muku ma munzo wajen bishiyar ƙare zancenka ne ko surutunka ne ohon musu!”.
Haiydar ne yayi Dariya kasancewar wayar a speaker yake yana jin komai yace.
“Wani irin bishiya ne kuma ƙare zencen ka”.
Ita kuwa khausar cewa tayi.
“Hmm garin fa basu da network sai wajen bishiya ɗaya suke zuwa yanzu ma haka wurin bishiyar nake”.