← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 114

Sashe 13

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da dare.
Mamy ce tsaye cikin ƙasaitacciyar shiga, tana zuwa wani irin ƙamshin kulaccar sirri da ta saya wurin Aysha Aliyu Garkuwa.
Baki ta ɗan taɓe tana kallon yada Khausar ke shishita sabida uban yajin da ta zambadawa indomei wanda yaji nama da.
Kai kawai ta jijjiga sannan tayi musu sallama ta wuce turakar mijinta.
Tanaci tana kurɓar ruwan sanyi, tana bawa Raudat har suka gama ɗaukar Raudat tayi suka shiga ɗaki kai tsaye toilet suka wuce brush tayi sannan tayiwa Raudat kana suka ɗaura alwala suka fito.
Jikin window Khausar ta nufa da niyyan rufewa Idanunta suka sauka akan Haiydar dake ɗauke da Ramadan zasu shiga sashen Hajiya Bunayya,
fasa rufe window tayi cikin ɗan ɗaga murya tace.
“Haiydar ina zakuje?”. shima cikin ɗaga murya yanda zataji yace.
“inda kika aikemu”.
Cikin takaici ta rumtse idonta kafin tace.
“Wai Haiydar meyesa karai nani ba dama in maka magana, ko in baka umarni saika riƙa bani amsa kai tsaye”.

Bakinshi ya taɓe tare sa fadin.
“Acikin gida ma saiki riƙa tambayar ina zanje! Me zanyi? Me zanci? fisabilillah ni bani da ikon da zanyi abu da kaina koda Mamy bata Matsamin irin yanda kike min gsky na gaji”.
Bai jira jin amsartaba ya wuce yashiga sashen Hajiya Bunayya,
Aseeya yayar Amina na ganinsa ta saki murmushi tace.
“Umma ga babanki yazo”.
Cikin sauri Hajiya Bunayya ta fito hannunta ɗauke da glass cup na madara tana jujjugawa fuskarta da murmushi tace.
“Gashi babana madaran shanu ne mai ɗumi”.
Amsa yayi yana murmushi saboda yanayin sanyin dake garin yace.
“Nagode Umma”.
Jujjuya Glass Cup ɗin yayi kafin ya kai bakinsa da faɗin
"Bismillahi”.

Khausar kuwa jingina bayanta da jikin bango tayi kafin ta ɗaga hannunta sama cikin raunin murya tace.
"(Ya wadud³,Ya zul'arshil makin,ya fa'alillima yurid,As'aluka bi izzatil lati la yura,wa mulki kallazi la yuda)ya Allah katsare min ɗan uwana kada Hajiya Bunayya taci galaba wajen cutar dashi”.
Kafin ta shafa ta kwanta lamo agado....

A can side din kuma cikin mugun sauri Hajiya Bunayya ta riƙe hannunsa domin bokan daya basu maganin ya tabbatar musu da zaran anyi Bismillah laƙanin maganin ya karye,ta anshi Glass Cup ɗin da faɗin.
“Bari mugani kode da zafi ne kada ka ƙone bakinka”.
Kai ya girgizi tare da faɗin.
“Ba zafi Umma”.
miƙa masa ta sake yi amsa yayi ya sake kaiwa bakinsa da faɗin.
“Bismillah”, saurin karɓa ta kuma yi tare da cewa.
“Mugani kode sugar bai jibane”.
Kai ya girgizi yace.
“Kin san ba damu da zaƙiba Umma”.
yaƙe tayi da faɗin.
“bari dai na ƙaro maka sugar”.
Ta faɗa tare da shigewa Bedroom duk aƙoƙarinta na ganin ta mantar dashi Bismillah ba jimawa ta fito ta sake miƙa masa tana jujjuyawa aranta tana addu'ar Allah yasa ya manta da Bismillah. Aseeya kuwa ikon Allah kawai take gani wajen mahaifiyarta ita kuwa Amina tasan komai domin ita ta karɓo maganin wurin boka Karƙuzu.
Karɓan Glass Cup ɗin yayi yakai bakinsa kana yayi Bismillah yasha kallon Ramadan yayi yace.
“Zaka sha?”.
Kai Ramadan ya girgiza alamar a'a...
Hajiya Bunayya kam ji tayi kamar ta haɗiye zuciya ta mutu ganin maganin data kashe maƙudan kuɗi wajen amsarsu aranta tace.
“Shegen yaro mai ta ammalli da addu'a duk uwarsu ta koya musu yin addu'a akan ko wani irin abu afili kuwa murmushi tayi tace.
“Babana sugan yayi?”.
Kai ya gyaɗa mata sannan ya shanye bayan sun sake taɓa hirane ya mata seda safe ya fice...

Washe gari da safe Ummi ta nufi gidansu Moddibo domin duba jikin Innayi bakinta ɗauke da sallama tashiga cikin gidan atsakar gida taci karo da Innayi dake faman gasa nama irin wanda ake yiwa masu jegon.
Cikin sakin fuska Innayi ta mata sannu da zuwa, Murmushi Ummi tayi tare da zama ta gaisheta cike da ladabi tare da tambayarta ya jiki kana ta kama mata aikin suka gama.
Bayan sun gama ne Moddibo da M Jameel suka dawo zama sukayi tare da gaisawa Ashagwaɓe M Jameel ya dubi Ummi yace.
“Ummi bacci nakeji”.
bai jira cewarta ba ya zame ya kwanta tare da ɗaura akansa a cinyarta
Moddibo kuwa Hararansa yayi yace.
“Kaidai ba zaka taɓa girma”.
Tura baki M Jameel yayi amma baice komaiba saboda baccin dake cinsa kwanciyarsa ba jimawa bacci ya ɗaukesa ganin lokaci na tafiya yasa Ummi tace. “Moddibo bani filo ka gani”.
miƙewa yayi ba daɗewa ya fito hannunsa riƙe da pillow Ummi ta karɓa ta ɗaura kan M Jameel akai sannan ta yiwa innayi Sallama.
Moddibo ya tafi mai data bayan sun hau kwalta Moddibo ya dubi Ummi cikin sanyin murya yace.
"Dan Allah Ummi ki riƙa yiwa Asma'u faɗa ta daina ƙawance da wannan yarinyar sam bata da nutsuwa zata ɓata Asma'u da halayyarta na rashin nutsuwa yarinya nada naci in ba da gaske mukayi ba bazamu ci nasara ba da na lura ta shiga ranta koda na yiwa Asma'u magana kan tarabu da ita.
Kuma naga kamar ba zata yiba anma idan ya zamana mu biyune muke mata faɗa zata ɗauka”.
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
“Insha Allahu zan riƙa yi mata”.
Ahaka suka isa gida ya ajiyeta sannan ya koma...

Washe gari. Ya kama Juma'a misalin ƙarfe uku Khausar na zune kan 2sitter Raudat na gefenta tana yanke mata ƙumba yayin da Mamy ke riƙe da hisnul Muslim tana Azkhar Asma'u tashigo bakinta ɗauke da sallama miƙewa Khausar tayi tare da rungumeta tace.
"Oyoyo Ƙawar arziƙi”, Murmushi Asma'u tayi cikin sigar zolaya tace.
“Fattanah kina son karya ni ko?”.
Saketa Khausar tayi tare da tura ƙaramin bakinta tace.
“Kina so mu ɓata ko?”, Murmushi Asma'u tayi tare da tsugunnawa har ƙasa ta gaisheda Momy cikin sakin fuska Momy ta amsa tana tambayarta Umminta ta bata amsa da.
“Tana lafiya, Momy tace ma in gaidaki”.
Cikin sakin fuska Momy tace.
“Ina amsawa”.
Ita kuwa Asma'u cikin girmamawa tace.
“Ayyah Momy in ba abinda Khausar zatayi miki ta rakani mana Ummi ta aikeni kuma banason zuwa ni kaɗai”.
Sanin Asma'u yarinya ce me tarbiya da nutsuwa uwa uba kamun kai yasa Momy amincewa.
Kai ta gyada mata tare da cewa.
“Toh kada dai ku daɗe ku kuma kula da kanku banda kula maza”.
Cikin jin dadi Asma'u tace.
“In sha Allah kuwa Momy”.
Ita kuwa Khausar murmushi tayi tare da cewa.
“To ni baki nemi izinina ba”.
Ta ƙare mgnar tana
Shiga Bedroom ɗin ta, murmushin Asma'u tayi tare da bin bayanta kana ta langwaɓar da kai tace.
“Ayimin afuwa ƙawar arziƙi”.
Hira suka ɗan fara taɓa sannan Asma'u ke sanarwa mata zata raka unguwar Teku ta kai saƙo Ummi ta aiko cikin zumuɗi da son fita ta miƙe tare da ɗaukan dogon hijab maroon colour tasa akan riga da wondon dake jikinta ba tare data tambayi inda zata jeba tace su tafi dan kawai tana masifar son unguwar Teku...

Aɓangaren Moddibo kuwa bayan ya dawo daga sallar la''asar,
Side ɗinsa ya wuce,
Ruwa ya watsa tare da sauya kayan jikinsa, wani tattausan riga da wondo nevy blue mai taushi ya zira, tare da fesa turarensa oud jannah mai masifar ƙamshi,
System ɗinsa da wayarsa ya ɗauka kana ya fito, a hankali ya lumshe idanunsa jin yadda sassanyar iskar ke ratsa cikin tattausan sumar kansa da yana iya kwana biyu bai cire hulaba.
A hankali yake taka steps din yana sauƙowa ƙasa wani irin masifeffen kyau yayi collor kayan jikinsa yayi matuƙar amsarsa farar fatarsa ta ƙara bayyana, yayinda tattausan sajensa yayi lib-lib gwanin burgewa jajayen lips ɗinsa dake cikin zagayen sajensa da kota million ɗinsa sai sheƙi sukeyi, a hankali yake taka tattausan silifas dake sawunsa.
ya nufi can gefen yamma inda wasu kyawawan bukoki na zamani da yake wajen hutuwansa,
Wurine mai kyau da ban sha'awa a hankali ya zauna bisa ɗaya daga kujerin dake cikin bukkar da tafi sauran ƙawayuwa da flawers.
A hankali yake motsa lips ɗinsa alamun yana tasbihi yalwataccen sumar kansa kamar na larabawa na sheƙi da ɗaukar ido idanunsa na lumshe yana motsa bakinsa a hankali.

Cikin nutsuwa Asma'u da Khausar suka fito duk da rawan kai irin na Khausar komai nata anitse takeyi cikin nutsuwa suke tafiya yayinda hijabansu yarufe har takalmansu adedeta suka tara tare da sanar dasu inda ze kaisu.
Tafiyar Mintuna ashirin da biyar sukayi suka isa aƙofar gidan.
A gaban gate ɗin adedeta ya ajiyesu.

Asma'u ce agaba tasa hannunta da babu komai ta tura ƙofan gate ɗin yayin da ɗaya hannu ke riƙe da Kula wanda Ummi ta yiwa Innayi dambun naman kaza.
Cikin wani irin shauƙi Khausar ke bin ilahirin gidan da kallo ganin yanda flowes da shuke shuken kayan marmari suka zagaye gidan tamkar garden,
Da sauri ta juyo da kallonta kan Asma'u tare da cewa.
“Wooow masha Allah.
Kai Asma'u wannan gidan waye haka? gaskiya yayi kyau sosai”.
ta ƙare mgnar tana lumshe idanunta tare da shaƙar sassayan iskar dake haɗe da ƙamshi flawers da kuma turare jikin Moddibo.
Kana ta riƙa bin fulawowin tana shafa duk wanda hannunta ya sauƙa akai saita tsinke takai hancinta kana taja dogon numfashi tare da lumshe ido.

Shi kuwa Moddibo tun ƙarar buɗe gate ɗin da yayi ya ɗago kansa yana kallon wajen.
Cikin mamaki yace
“Khausar Usman Lelelwal a gidan nan”.
Hannunsa yasa ya tallabe habarsa tare tsuke fuskarsa.
Ita kuwa Khausar cike da shauki ta buɗe hannunta tare da jujjuyawa har hijabinta na buɗuwa cikin ɗan ɗaga sauti tace.

“Agaski Asma'u gidan nan ya min komai na ciki sun burgeni gawani irin ƙamshi da suke, ji yanda ilahirin gidan ke fitar da wani ni'imantaccen ƙamshi.
Gaskiya gidan nan shine aljannar duniya da alamu kuma mutanen ciki maƙurane wajen tsabta ina son komai na gidan nan”.
Asma'u Kam dariyar dake cinta take ƙunshewa ta tabbata da Khausar tasan cewa gidansu Moddibo ne babu dalilin dazai kawota sannan ta tabbata yau juma'a ya irin wannan lokacin Moddibo na gida babu inda zeje.

Ita kuwa Khausar juyi ta cigaba da yi tare da sauri ta nufi side din Moddibo steps din ta fara tattaunawa tana shafa furannin dake jere a kan.
Saida ta hau har tsakiyar barandar kana ta juyo ta fuskanci yama.
“Wooww Masha Allah Asma'u zo ki hau ki gani wlh ina hango bakin Teku kinga yadda ruwa da tsuntsaye keyi!".
Chapter 13 · 0% Book details