← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 114

Sashe 15

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Moddibo kuwa cikin yanayin nutsuwarsa da kuma sanyinsa ya kira sunanta da faɗin.
“Asma'u”.
Saidai akwai alamun ɓacin rai acikin sautin Muryansa.

Atsorace Asma'u ta juya Idanunta cike da tsoro tace.
“Na'am Yah Moddibo”.
Tsayuwarsa ya gyara tare da lumshe idanunsa masu ƙwarjini da haiba kana ya buɗe su ya dubi Asma'u da har yanzu take tsaye da tsoro a idanunta yace.
“Meyesa zaki ɗauko Biri ki kawo mana gida!?”.
Ya ƙare mgnar da bin Khausar da ido wacce tuni ta kai bakin gate.

Asma'u kuwa saurin ɗagowa tayi ta dubesa jin ya kira Khausar da Biri saidai bata yarda sun haɗa ido ba.
Shi kuwa cike da takaici
ya cigaba da cewa.
“Koda wasa kada ki sake zuwa da wannan yarinyar gidan nan, tunda ita bata da hankali da kuma nutsuwa da kamun kai”.
Ya ƙarashe mgnar yana mai lumshe idanunsa dake cike da ƙwarjini har zuwa sannan yatsun ƙafar na masa rawa tamkar alokacin ta buga masa yatsunsa.

Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe ganin tuni Khausar ta fice kanta a ƙasa tace.
“Dan Allah kayi haƙuri Insha Allah hakan bazai sake faruwa ba”.
Moddibo kuwa baice da ita Komai ba saima lumshe idanunsa da yayi yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi yaci gaba da yi.

Ita kuwa Asma'u jin baice komai ba yasa ta juya cikin sassarfa ta nufi gate dan bin bayan Khausar...

M Jameel dake zaune cikin falon Moddibo kuwa wanda ya tsirawa window idanu yana ganin duk abinda ya faru ya saki lallausan murmushi tare da miƙewa yana gyara zaman Farin t-shirt da blue jeans dake jikinsa kana ya sanya hannu ya buɗe ƙofan falon ya fito fuskarsa ɗauke da ƙayataccen murmushi cikin yanayin sa na ƙaunar Amininsa yace.
“Ba sa ido ba?,ka fita sabgar yarinya ka ƙi yanzu inba sa'a ba kasa taji ciwo dan naga lokacin da take gudu tana ɗin gishi”.
Moddibo kuwa buɗe idanunsa dake lumshe yayi tare da zab gawa M Jameel Harara cikin yanayin nutsuwarsa daya zame masa jiki yace.
“Dama karyewa tayi da shi yafi yarinya bataji bata da hankali ko kaɗan”.

Da gudu Asma'u ke bin Khausar tana cewa.
“Khausar ki jira ni mana”.
Ƙin tanka mata Khausar tayi tana cigaba da sassarfa yayin da ko wani gaɓa na jikinta ke rawa kana tana cigaba da ɗaure gashinta daya baje kasancewar unguwa ce da babu hayaniyar mutane yayin da take yarfe hannunta dake masifar zugi kana tana me ɗingisa ƙafarta.
Ganin da gaske Khausar ba zata tsaya ba yasa Asma'u ta ƙara gudunta har ta isa inda take tana sauƙe numfashi saboda gudun da tayi tace.
“Ayyah Khausar ki tsaya mana ga hijabinki saka”.
Hannunta tasa ta amshi hijabin nata tare da zirashi a jikinta kana taci gaba da tafi.
“Ayyah Khausar ki tsaya mana”.
Asma'u ta kuma faɗa tare da shan gabanta,
a raunane tace.

“Bazan tsaya ba Asma'u meyesa zaki min haka Asma'u? banyi tsammanin zaki yimin haka ba gidansu Moddibo kika kawoni mutumin da kin san baya ko son ganina.
Gashi yanzu kinsa na buga masa yatsuna masu zobe aƙafa naji masa ciwo,yanzu bansan wani irin hukunci zai ɗauka akaina ba”.

Tsoron Khausar ɗaya kada Moddibo yace zai zaneta duk irin rashin ji da ƙiriniyarta tana matuƙar tsoron bulala kana tasan duk hukuncin da Moddibo zai ɗauka bazai wuce yasa Malam Bello ya zaneta idan taje Hadda.

Cikin sanyin murya Asma'u tace.
“Ayyah Khausar kiyi haƙuri, amman kuma ai da kinji mgnata da haka bai faruba. kece bakya ji sannan ba kyaso ataɓa lafiyar jikinki”.
Kallonta Khausar tayi da Idanunta dake cike da tsoro da kuma fargaba tace.
“Meyesa zaki ce haka Asma'u kawai naga Appel da inabin ne ya ban sha'awa shiyasa na cira”.

Kai Asma'u ta girgiza tace.
“Inabi Khausar? na tabbata duk wannan abubuwan da kika gani akwai su a gidanku ku fiye ma da hakan”.

Sake Marerece fuska Khausar tayi tace.
“Na ganine ya bani sha'awa laifi ne dan na cire!?”.
Murmushi Asma'u tayi ganin har zuwa lokacin Atsorace Khausar take sai kuma tace.
“Kema dai baki jira kanki ba daga zuwa gidan mutane sai ki fara cire musu abu batare da neman izini ba”.

Ita kuwa khausar jin abinda Asma'u tace yasa ta watsa mata Harara cike da tsiwa tace
“Tun da kinsan gidan masu baƙin hali zaki je Meyesa zaki ɗaukeni ki kaini?, Kisa aranki daga yau babu inda zan sake rakaki tunda haka kikayi min”.

Wara ido Asma'u tayi sai kuma ta langwaɓar da kai tace.
“Kiyi haƙuri Khausar bansan haka zai faru ba ni kawai da niyyar mu gaida Innayi nace ki raka ni amma kada kice baza ki sake raka niba na tuba”.

Kallonta kawai Khausar tayi amma ba tace komai ba, sake langwaɓar da kai Asma'u tayi cike da tausayinta tace.
“Ki zauna awancan dakalin se inja miki ƙafar!”

Kai Khausar ta girgiza tana rintse Idanunta tace.
“Basai kin ja minba kawai sama mana adedeta mu hau”.
Kai Asma'u ta jinjina tare da riƙe hannunta suka ɗan tsaya bakin titi cikin sa'a tsayuwar su babu daɗewa suka samu adedeta hawa sukayi tare da yimasa kwatancen inda ze kaisu...

Aƙofar gida me Adedeta ya sauƙe su bayan sun isa Asma'u ce ta ciro kuɗi ta basa kana ta riƙe hannun Khausar suka nufi gate Khausar ce tasa hannu ta tura gate ɗin cikin rashin sani suka buge juna da Samira Sani wacce ke ƙoƙarin fita Amina na biye da ita.

Saurin ɗago kai Khausar tayi jin Samira Sani na cewa.
Ke 'yar uban waye da zaki haɗa kafaɗa dani shin dame kike taƙama!?”.
Kamar Khausar za tace wani abu sai kuma ta fasa taja siririn tsaki tare da jan hannu Asma'u suka bar wajen tana me cigaba da ɗingisa ƙafarta.
Ƙwafa Samira Sani tayi cikin kumfar baki tare da tsanan Khausar aranta tace da Amina.
“Wallahi na tsani wannan shegiyar yarinyar me kama da sadaka yalla Idan ban sabautata ba bazan taɓa samun nutsuwa ba!”.
Tsaki Amina taja tana kallon Samira tace.
“Allah ne kaɗai yasan irin abinda zan mata”.

Kafin su ƙarasa shiga falon Khausar ta janye hannunta dake cikin na Asma'u kana ta gyara tsayuwar tare da dai-dai ta tafiyarta tana me rintse Idanunta sam bataso Momy ta fahimci abinda ya sameta.
Asma'u kuwa kallon ta tayi cike da tausayinta amma batace komai ba Ƙofan falon suka tura
suka shiga tare da haɗa baki wajen cewa.

“Assalamu Alaikum”.
Momy dake zaune kan kujera ta ɗaura ɗaya kan ɗaya ce ta faɗaɗa Murmushin fuskarta tace.
“Wa'alaikum salam har kun dawo?”.
Zama suka yi daga gefen ƙafarta aƙasan chanis capet Asma'u tace.
“Eh Momy”.

“Masha Allah ya jikin Innayin?”.
Cewar Mommy.
Khausar na ƙoƙarin miƙewa tace.
“Da sauƙi Momy” Sannan ta nufi Bedroom ɗin ta da sauri Asma'u ta miƙe tabi bayanta.

Bakinta ɗauke da sallama tashiga ɗakin nata kana tayi saurin ɗin gisa ƙafarta se kuma ta kwanta agefen gadonta dake shimfiɗe da white bedsheet tana sakin ajiyar zuciya akai-akai alamar har yanzu akwai tsoro atare da ita.
Zama Asma'u tayi agefenta ganin yanda ƙafan Khausar ke rawa yasa tace.
“Bari na ɗebo ruwan ɗumi na matsa miki”.
Kai Khausar ta girgiza da faɗin.
“A'a ga can man zafi agaban mirrow ki ɗauka min na shafa”.

Kai Asma'u ta gyaɗa kana ta miƙe ta ɗauko man zafin ta ɓude kana ta kama ƙafar Khausar tana mulka mata.
Khausar kuwa rintse Idanunta tayi tanajin zafin man na ratsa jikinta yayin da aƙasan zuciyarta tsakanin tsoro da firgicin hukuncin da Moddibo ze ɗauka akan tane.
Asma'u kuwa hira ta riƙa yiwa Khausar na ɗebe kewa kana daga bisani ta miƙe ganin yamma tayi seda ta biya ta kichen ta sake yiwa Momy Sallama kana ta tafi.

Khausar kuwa yanayin zogin da ƙafarta da kuma hannunta ke mata yasa bayan tafiyar Asma'u ba jimawa bacci ya ɗauke ta...

Ita kuwa Momy ganin har maghariba tayi bata jiyo motsin Khausar kuma bata nemi Raudat suyi salla ba se abin ya bata mamaki bayan ta idar da Sallah ta fito daga Bedroom ɗinta Kai tsaye Bedroom ɗin Khausar ta nufa,
bakinta ɗauke da sallama ganin Khausar na bacci yasa ta ƙarasa bakin gadon tare da taɓa fuskarta da hannunta dake da damshin ruwa ruwa tana kiran sunanta da faɗin.

“Khausar! Khausar!! Khausar tashi kiyi Sallah maghariba tayi”.
Momy ke faɗa tana me sake shafa fuskarta da hannunta dake da damshin ruwa.
jin muryan Momy da kuma damshin hannunta da take shafa fuskarta yasa ta buɗe Idanunta ahankali tace.
“Na tashi Momy”.
Juyawa Momy tayi ta fita ita kuwa khausar miƙewa tayi tare da furta.
“Alhamdulillah”,Jin babu ciwo da Zugin da ƙafar ke mata se kuma hannun data ji ya sake baki ɗaya tamkar ba ajikinta yake ba.

Ta lumshe lumsassun idanunta kana ta miƙe ta nufi toilet tana me furta.
“Allahumma Inni Auzubika Minal khubsi wal khaba'is”.
Kana tashiga cikin toilet ɗin da komai ke akimtse yana fitar da wani irin ƙamshi Anutse tashiga yin alwalan har ta ida kana ta fito bayan ta furta.
“Gufra naka”.
Bayan ta gabatar da Salla tayi adduo'i ta miƙe tare da naɗe darduman se kuma ta juya ta fice tana me buɗe hannunta da rufewa koda ze dawo dai-dai...

Zaune ta samu Momy kan kujera hannunta riƙe da hisnul Muslim tana Azkharul Masa,Yayin da Raudat ke gefenta daga ƙasa tana bin bakinta zama Khausar tayi daga gefen Raudat kanta aƙasa tace.
“Momy gobe zan tafi JAURO YAYAH”.
Da mamaki Momy ta zuba mata ido jin mgnar a bakatatam cike da mmki tace.
“Zaki tafi Jauro yaya kuma Khausar?”.
Ataƙaice Khausar tace.
“Eh”.
tana mai cigaba da jan yatsun hannunta.

Momy ta sake duban ta da mamaki akaro na biyu tace.
“Anma babu yanda banyi dake ba jiya kan cewa kishirya yau kutafi tunda mutanen garinsu na zuwa sallan jumma'a sosai ku tafi tare, kika ce ba zaki tafi dasu ba kuna hadda, sannan kun kusa zuwa ƙarshen surar idan kika tafi karatun ki ze koma baya sannan na yarda na barki kan cewa se sati me zuwa yanzu kuma kice zaki tafi gobe”.
Chapter 15 · 0% Book details