Sashe 64
Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Alhamdulillah su Moddibo sun sauƙa lfy a ƙasa Mai Tsarki cikin ikon Allah Mabuwayi gagara Misali sunyi Umarah sun samu goma shabiyar na watan acan cike da ɗumbin farin ciki.
Yau yakasance ranace ta Sallah angama azumi lfya. Al'ummar Musulmai na duniya sun cika da farin ciki kowa kagani fuskarsa ɗauke da yalwataccen farin ciki, kana kowa yayi shiga ta haiba da kamala.
Alhamdulillah bayan an saƙƙo daga sallar idi ko wani gida kashiga zaka samesu cikin farin ciki da shiga ta kamala kana da Lafiyayyan abinci.
Kamar yanda ko ina na faɗin duniya ya cika da farin cikin wannan ranan haka yakasance Agidan Lamiɗo.
Acan falon Mommy kuwa hallare suka gaba ɗayan su Khausar ce tsaye riƙe da waya ahanununta cikin shiga ta alfarma da kamala wani rantsatstsen less ne Blue da ratsin fari ne ajikinta ɗinkin riga da skirt yayin da skirt ɗin ya fitar mata da shape din ƙugunta rigan kuwa tayi ɗass ajikinta ma dai-dai-tan dukiyar fulaninta sun cika fam yayin da tayi ɗaurin ƴar Minister ta zubo yalwataccen sumar kanta zuwa baya daga gaban goshin kuwa ya kwanta luf-luf wuyanta maƙale da sarƙan Gwal da ɗan kunnensa kana fuskarta ɗauke da simple make up daya sake ƙawata kyawun fuskarta.
Yayin da Raudat ma ke sanye cikin irin shigar dake jikin Khausar sai dai nata ɗinkin dogon riga ne.
Haiydar kuwa sanye yake cikin wata Bugaggiyar shadda Sky blue anyi masa ɗinkin samarin zamani rigar ta tsaya iya gwiwarsa, kansa sanye da hula yalwataccen sumar irin na fulanin Usul yana kwance lib aƙeyarsa haka ma Ramadan sanye yake cikin irin shigar Haiydar Yayin da Mommy ke sanye cikin Atanfa mai Golden mai masifar kyau anyi mata ɗinkin riga da zani fuskarta ɗauke da simple make da Khausar tayi mata.
Baki ɗaya falon wani sanyayyan ƙamshi yake fitarwa wanda ya haɗu da ƙamshin jikinsu.
Cike da tsantsar farin ciki Khausar dake ɗaukar su hoto ta juya ta kalli Mommy kana tace .
“Kuce Chesss”.
Dariya suka fashe dashi kana suka ce.
“Cheeessss”, Akuma dai-dai lokacin ta ɗauki hoton.
Sosai hoton yayi kyau kallo ɗaya zaka musu ka tabbatar da cewa suna cikin tsantsar farin ciki da annushawa tare da nutsuwa.
Suna cikin hoton Hajiya Bunayya tashigo cikin shiga ta alfarma da kamala sosai tayi kyau.
Zama tayi bayan tayi Sallama Idanun ta akan Mommy tace.
“Barka da Sallah ƙanwata fatan anyi Sallah lafiya?”.
Murmushi Mommy tayi kana ta zauna kusa da ita tare da cewa.
“Ayyah Yaya ina shirin zuwa wajenki ma”.
Murmushi Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Ayyah babu komai nima cewa nayi bari na rigaki zuwa in samu ladan gaisuwar. Fatan munyi Sallah lafiya?”.
Jinjina Kai Mommy tayi kana tace.
“Lafiya Lau Alhamdulillah Yaya Ubangiji Allah ya amshi ibadun da ayyukanmu na Al'khairai Allah ya nuna mana na baɗin baɗaɗa da rai da lafiya”.
Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa kana tace.
“Ameen ya Allah Ƙanwata”.
Khausar kuwa kallo ɗaya tayi mata ta kawar da kai gefe.
Hajiya Bunayya kuwa kallonta ta mayar kan Khausar dake ɗaukar Haiydar, Ramadan, da Raudat hoto, cike da makirci tayi wani murmushi kana tace.
“Khausar Barka da Sallah”.
Anutse Khausar ta juya ta kalleta babu walwala afuskarta muryarta ta saisaita kana tace.
“Yawwa Barka dai Ummah”.
Hajiya Bunayya ta mayar da kallonta kan Haiydar dake tsaye gefenta hannunsa ta kama tare da damƙa masa key da murmushi afuskarta tace.
“Ga Barka da Sallah ka Babana”.
Zare ido Haiydar yayi tare da buɗe hannunsa ya kalli sabon key ɗin mashin dake cikin tafin hannunsa,
cike da tsananim farin ciki mara misaltuwa ya faɗa jikin Hajiya Bunayya tare da rungumeta cike happy ya saƙi ƙara kana yace.
“Wayyo Ummah na Nagode. Allah ya saka da al'khairi. Allah yaƙara miki nisan kwana mai amfani. Allah yarabaki da sharrin Mutum da Aljan, gaskiya nayi farin ciki kinyi surprise ɗina da kince sai bayan Sallah da kwana biyu.
Cike da farin ciki tayi murmushin gefen baki kana tace.
“Ameen,Ameen Babana, Eyyyy dama sunce sai bayan Sallah da kwana biyu sai kuma suka kawo jiya da daddare”.
Khausar kuwa cike da takaicin halayyar matar ta riƙa watsa mata harara wani irin haushin ta takeji, aƙasan ranta kam cewa take shegiya muguwa aniyar ki ta biki da izinin Allah babu abinda zai samesa.
Mommy kuwa kallon Khausar dake bin Hajiya Bunayya da harara tayi kai ta girgiza tare da cewa.
“Khausar jeki ɗauko mana abinci a kichen ki kawo kin tsaya kin tsare mutane da ido baza ki iya taya ɗan uwanki samun abin farin cikin da yayi ba”.
Zumɓura baki Khausar tayi tare da miƙewa batare da tace Komai ba tashiga kichen.
Haiydar kam Kallon Mommy Yayi kana yace.
“Mommy Ummah ku tashi nayi muku hoto”.
Miƙewa sukayi da murmushi afuskarsu Haiydar yashiga ɗaukar su.
Khausar kuwa fitowa tayi hannunta riƙe da Warmers dake ɗauke da soyayyun kaji ta ajiye a dining kana ta koma ta sake ɗauko wasu Warmers ta ajiye.
Dai-dai lokacin da Mommy ke cewa.
“Yaya mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi Agaskiya nayi farin ciki”.
Fuskar Khausar ta ɓata kana tace.
“Haba Mommy irin wannan godiyar sai kace wacce aka biyawa Kujeran Hajji”.
Kallonta Mommy tayi kana tace.
“Ai kujeran hajjin ne Khausar, mutumin daya so ɗan ka arayuwa har yayi masa alkhairi ai babu kamarsa ”.
Kai Khausar ta girgiza kawai aranta tace Mommy har yanzu baki san wacece wannan makirar matarba, shiyasa kike yabonta wannan matar da kike gani tafi kwalba sharri afili kuwa cewa tayi.
“Hmmmm Allah ya kyauta”.
Murmushin da be wuce saman laɓɓaba Hajiya Bunayya tayi kana ta miƙe tare da cewa.
“Nikam zan wuce”.
Miƙewa Mommy tayi tare da cewa toh mungode Yaya Allah yaƙara girma da ɗaukaka”.
Ita kuwa Hajiya Bunayya ficewa tayi Yayin da Haiydar yabi bayanta zuwa sashen Lamiɗo.
yana shiga yace.
“Abba gashi Ummah ta siya min Mashin zan hau?”.
Kai Lamiɗo ya gyaɗa kana yace.
“Babu damuwa tun da kana son hakan, amma kafin nan sai an sake koya maka mashin ɗin na tsawon wata biyu kafin ka fara hawa kai ɗaya kaga ai ka sake koya”.
Jinjina kai Haiydar yayi kana yace.
“Toh shikenan Abba babu Matsala ”.
Bayan sallah da kwana biyu jirginsu Moddibo ya sauƙa a Nigeria cike da farin ciki Moddibo, Innayi da M Jameel Ummi suka dawo gida yayin da Hajja Nana ma ta sauƙa ta Ɓadamaye cike da farin ciki da kuma murna.
**********
Ahaka rayuwa ta cigaba da tafiya komai yana tafiya dai-dai cikin ikon Allah Akwana atashi asaran mai rai, sekonni na juyawa izuwa Mintuna, Mintuna na tafiya izuwa awanni.
Yayin da awanni ke juyawa izuwa kwanaki, kwanaki na tafiya izuwa Makonni.
Yayin da Mokonni ke juyawa izuwa Watanni. A hankali kuma watanni ke tafiya Izuwa shakara ko shekaru...
Alhamdulillah su Khausar sunyi nisa kiwo aski yazo gaban goshi, yanzu suna shirye shiryen zana jarabawar Ƙarshe na kammala secondary School WEAC and NECO baki ɗaya kansu ya ɗauki zafi basu da wani lokaci saina karatu sosai suka maida hankalin su suna karatu tuƙuru domin fitowa da kyakkyawan sakamako Inda yanzu ya rage saura Exam biyar ya rage su kammala Neco.
Khausar ce tsaye gaban Dressing mirror jikinta ɗaure da towel da tsawon sa ya kai gwiwarta,
Zuwa yanzu ko ina na jikinta ya cika fam, dukkan ƙirar girma maƙerin budurci ya ƙenƙesa matashi, musamman Dukiyar fulaninta da kuma hips dinta da suka cika ƙugunta, yalwataccen sumar kanta irin na Fulanin Usul ya sake tsawo da sansti.
Manyan Idanunta sun sake girma tare da lumshewa siririn dogon hancinta ya sake tsawo yayin da madaidaicin bakinta ya sake tattarewa izuwa pich collor, yana yin ƙiranta kamar kolbar Coca cola Yayin da Tsananin kamanninta da Kajol ya sake bayyana ayanzu tana da shekara goma sha tara a duniya.
Cikin sauri ta shafa Lotion ɗin ta tare da shafa powder sama-sama sai kuma ta shafa kwalli amanyan Idanunta lipstick kaɗan ta shafa asaman laɓɓannta cikin sauri sauri ta sanya Uniform ɗin ta daya sha guga tulin sumar kanta tayi acuci dashi kana ta feshe jikinta da turarukanta masu masifar daɗin ƙamshi da sanya nutsuwa.
Cikin Sassarfa ta fito falo harara Mommy ta maka mata kana tace.
“Ke dai Khausar ba zaki canza ba kin girma amma kullum shiririta kike ƙarawa tun yaushe Ake jiranki, ga Amina ma can tanata jira amma sai ɓata musu lokaci kike”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da riƙe kunnenta kana tace.
“Sorry Mommy”.
Fuska ta tsuke tare da ce wa. “Kin dai san Amina in ta gaji da jiran ki”.
Cikin ɗan sauƙe numfashi tace.
“Uhumm ai yaseen in ta gaya min mgn ramawa zanyi in banda asarama tun tuni yaci ace ta gama, amman kullum taba cikin dakon aji har wai sai yanzu zamu gama tare”.
Mommy na juya zata fita tace.
“A'a ni bana son fitina”.
Ta ida mgnar tana fita,