← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 114

Sashe 70

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rawan jiki ta sanya hannunta dake ta karkarwa ta janye Hijabinta kana ta kalli Mommyn Muryanta na rawa tace.
“Yah Jameel ne ya kawo ni”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe kana tace.
“Kai Ubangiji Allah yayi masa albarka. Allah ya saka masa da mafi kyawun sakamakon”.
Kai Khausar ta gyaɗa still jikinta na tsuma tace.
“Ameen Mommy bari in cire kayana”.
Ta ida mgnar tare da wucewa Bedroom ɗin ta tana shiga ta kalli hannunta lokaci ɗaya ta sake shiga sabon tashin hankali, cike da damuwa ta yarfe hannunta kana tace.
“Nashiga uku Ni Faɗimatuzzahara ina nasanya hannu na! Ni Batula?”.
Duk da cewa tana cikin tsoro amma tana sane da inda ya zaro hannunta kai tsaye toilet ta Wuce tare da cire kayan jikinta ta sakarwa kanta ruwan ɗumi sabulu ta ɗauka ta mulke hannunta dashi kana ta shiga gogawa ajikin tiles dake jikin bangon tana Girgiza Kai kana tana mai Furta.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Astagfirullah wa'atubu ilaik Subhanallah ya Salam Allah na tuba”.
Da ƙyar ta iya yin wankan ta fito bayan ta ɗaura alawalan tare da buɗe Siff ta ɗauki dogon riga na roba baƙi ta sanya har zuwa lokacin jikinta na ƙamshin tularensa Sallaya ta shimfiɗa ta gabatar da Sallah kana ta riƙe carbi tana hawaye da Istigfari.

Acan ɓangaren Moddibo kuwa bayan ya gama wanka al'wala ya ɗaura tare da fitowa har zuwa lokacin zuciyar sa na tsaye alamar zai samu nitsuwa Siff ya buɗe tare da ɗaukar Boxes ya sa sai kuma ya tsaya yana kallon kansa, ya tabbata idan yasa Jallabiya mutane zasu iya fahimtar halin da yake ciki wani dogon tsaki yaja.
“Mitsssssssss!!! Yar iskar yarinya”.
tare da sanya hannunsa ya matse muhallinsa da ƙarfi wai ko zai masa biyayya cikin yanayin tashin hankali ya kalli kuma sunkuyar da kansa tare da faɗin.
“Wai wannan wacce iriyar Masifa ce!?”.
Sake buɗe sabbin boxers ɗin sa dake cikin leda yayi ya ciro wani ƙarami wanda yake zaton zai masa kaɗan shiyasa ma bai taba sakasu ba,
Cikin yamutsa fuska ya sanyashi,
sosai ya matsesa sai dai har zuwa lokacin al'amarin azimunne.

Wani boyel baƙi mai kyau ya ɗauka ya sanya kana ya feshe jikinsa da turarukansa cikin sanyin jiki ya fita zuwa Masallaci ya gabatar da sallah Azahar.
A wunin wannan ranan dai baki ɗaya haka yayita agigice.

Acan gidan Lamiɗo kuwa Hajiya Bunayya ce zaune akan 3sitter yayin da Amina ke gefenta riƙe da kofin shayi yana tururi.
Anutse Hajiya Bunayya ta juya tare da kallon Amina data kai kofin shayin bakinta kana tace.
“Amina yanzu ya kuke da Malam Jameel ne? nifa nagaji da wannan al'amarin kullum sai munga Abu kamar yaci sai kuma kiga abu ya sake ta ɓarɓarewa!”.
Gyara zama Amina tayi tare da ajiye Cup ɗin tea kana tace.
“Hmmm ba gwara ma muba akan Samira Sani, sufa duk abinda suke kamar anshuka dusa shi Moddibo na nan kamar Waliyyi baya fahimtar karatunta shu'umanci bare ya ratsasa kamar kurma baya ma sauraronta bare kuma ya sake mata fuska”.
Ta gumi Hajiya Bunayya tayi tana cigaba da sauraren Amina.
Amina ta cigaba da cewa.
“Amma kinga gwara Ni dama Malam Jameel Yana da sauƙin kai sannan yanzu ya daina shash-shareni idan na gaishesa yana Amsawa cikin sakin fuska da mutunci mun koma kamar da duk da dai dama haka halinsa yake ga kowa”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.
“Kawai dai abinda nake gani Ummah kawai Abbah ya masa magana idan Abba ya masa magana kan cewa Ina son sa bazai ƙini ba, saboda yana da kirki yana da mutunci da kawaici ko ba komai kuma gidan dala yake domin nifa kuɗin mahaifinsa nafiso, badon kuɗin da suke da shiba, nafi son miji irin Modibbo mishkili, ba sake fuska dan sunfi iya soyayya”.

Ajiyar zuciya Hajiya Bunayya ta sauke tare da gyara riƙon wayarta kana tace.
“Anya Amina za'ayi hana kuwa? Ai gwara dai mujawo hankalinsa zaifi, kuma batun kuɗi yoh dama ai shi mukewa bauta domin duk abinda nake kashewa a wurin boka ina lissafawa kina shiga daga ciki zaku biyani”.
Kwaɓe Fuska Amina tayi kana tace.
“Kayya Ummah tun yaushe mukeyi amma abin baya wani kamasu gwara ma Malam Jameel Idan munyi munga Abu ya kama kwana biyu sai kuma ya dawo baya kula har kata! anata ƙara lissafin kuɗin da zan biya”.
Kai Ummah ta gyaɗa kana tace.
“Gaskiya dai kam in dai hakan zaiyi sai in faɗawa Mafaifinku yafi min kwanciyar hankali ma amma ko. Abbanku baza mu fuskance sa kai tsaye haka ba dole sai anja hankalinsa akan maganar”.
Ta gumi Amina tayi tare da cewa.
“Toh Ummah acanza wani boka mana?”.
Saurin Kallonta Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Wani boka muke dashi da yafi wannan?,Duk aikin sai yace ana wasa dashi sannan aikin kuɗi yake buƙata sosai kuma kinga Yanzu bani da kuɗi sosai Amina, kuma ai tunda muka canza boka Zurau wannan duk aikin da yake min yana ci”.
Taɓe baki tayi tare da cewa.
“Gaskiya Ummah asamu ayi aikin nan idan muka samu nashiga gidansu zamu fanshe duk kuɗin da muka kashe!”.
Jinjina kai Ummah tayi kana tace.
“Zanyi ƙoƙarin hakan in Allah ya yarda”.

Acan ɓangaren su M Jameel kuwa bayan ya shiga gida ya sauya kayansa zuwa blue jeans da farin t-shirt mai dogon hannu kana ya gabatar da Sallah Azahar Yana idarwa ya nufi sashen Mahaifinsa zuwa lokacin ruwa ya tsaya bakinsa ɗauke da sallama ya shiga kana ya zauna kusa da Abbansa.
Kallonsa Abba yayi bayan sun gaisa yayi gyaran murya tare da cewa.
“Dama batun Company Adamawa ne acikin kayayyakin da aka kawo muga ya yanayin ingancinsu akwai atomfofi,
Gyaleluwa da kuma sauran kayayyakin ya kamata kaje”.
Jinjina kai M Jameel Yayi kana yace.
“Toh shikenan Abba yaushe ne tafiyar”.
Kallonsa Abbah yayi kana yace.
“Insha Allah tafiyar zai kasance idan kun gama jarrabawar ɗaliban ku da zasu gama makarantar bana nasan zuwa lokacin hankalinka ya kwanta Asma'u da Bashir sun kammala Secondary School”.
M Jameel kuwa jingina kansa da jikin kujeran yayi tare da lumshe idanunsa kana yace.
“Hakane kam Alhamdulillah yanzu kam na gama sun gullarsu Asma'u”.
Dai-dai lokacin da Hajiya Karima ta shigo falon Abba na cewa.
“Kaga yanzu shikenan tun da kagama da wannan shungullan gaba ɗaya duk abinda ya shafi shungullana da kuma harƙoƙina, kasuwancina duk zan danƙasu ahannunka Babana.
Domin ni girma ya fara zuwa Inason hutu”.
Murmushi M Jameel Yayi kana yace.
“Toh shikenan Abba babu damuwa duk abinda kace shi za ayi da izinin Ubangiji”.
Murmushi Abba yayi har cikin ransa yake jin ƙaunar ɗan nasa saboda yanda yake masa biyayya ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Toh Nagode Allah yayi maka Albarka”.
Duk abinda suka tattauna Hajiya Karima na rakuɓe tana jin tattaunawar su Amaryan Abban Jameel Hajia Turai ta shigo ganin Hajiya Karima atsaye yasa ta faɗin.
“A'a Lafiya kike tsaye anan Hajiya Karima?”.
Cikin sauri ta juya, sai asannan Abba da M Jameel suka juya suka ganta tsaye.
Murmushin da bai wuce saman laɓɓabanta ba tayi kana tace.
“Yanzu na iso ina gyara labule nai”.
Ita dai Hajiya Turai batace komai ba ta ƙarasa shiga falon kana Hajiya Karima tabi yo bayan suka cigaba da hira.

Washe gari.
Cikin sanyin jiki da damuwa Khausar ta shirya cikin Uniform ɗin ta dake haska fatarta baki daya ta kasa sakewa da zaran ta tuna inda ta sanya hannunta sai taji tashiga matsanancin tashin hankali.
Cikin sanyin jiki ta fita tare da nufar inda motarsu ke fake Amina ce tafito hannunta riƙe da lunchbox ɗin Aminu dai-dai lokacin da Lamiɗo ya fito daga sashen Gimbiya Dadu da fuska a tsuke ya kalli Amina tare da cewa.
“Banaso Amina kada ki sake yi min abinda kikayi jiya banaso haka ki kiyayeni! Ki kiyayeni!”.
Ƙasa tayi da kanta kana tace.
“Toh Abba kayi haƙuri”.
Sannan ta juya ta shiga, kana su Khausar ma suka shiga mota ko acikin mota Khausar jingina bayanta da jikin kujera tayi tare da damƙe hannunta ahaka har suka isa makarantar.

Anutse ta fito ta tashiga hall da suke Exam kai tsaye bencin da number ta ke kai ta nufa tare da zama kana ta dafe kanta ba jimawa Malam Isa ya shigo ya fara raba musu Booklet da questions na Economics.
Kallon Khausar data dafe kanta da hannu biyu yayi kana yace.
“Lelewal meke damunki?".
Da sauri ta ɗago kanta ta kallesa sai kuma ta girgiza kanta cikin sanyin murya tace.
“Ba komai Malam”.
Question peper ya ajiye mata kana ya cigaba da rabawa sauran.
Cikin mutuwar jiki Khausar ta riƙa yin amsarin Questions ɗin tun kafin a miƙa wa wasu Questions pepar tuni ta gama Amsawa kwantar da kanta akan deks ɗin tayi tana godewa Allah daya sa basu da Exam din Moddibo da batasan da idon da zata iya kallon sa ba.

Moddibo kuwa tunda yashigo makarantar ya wuce office ɗin su ya zauna cikin zullumi da damuwa.
Ahankali M Jameel ya fito daga class da yake teaching hannunsa riƙe da booklet ya nufi Office ɗinsu bakinsa ɗauke da Sallama yashiga zaune ya samu Moddibo idanunsa na rufe kana lips ɗin sa na rawan sanyi ahankali.
Booklet ɗin ya ajiye tare da zama gefensa kana yace.
“A.J meke damunka?”.
A hankali Moddibon Ya jujjuya idanunsa dake lunshe yayi kana ya Girgiza masa kai tare da cewa.
“Bakomai”.
Kallonsa M Jameel Yayi kana yace.
“Ya zaka ce min bakomai A.J ke faɗa min meke damunka ko dai baka da lafiya ne?”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da gyaɗa masa kai.
Chapter 70 · 0% Book details