← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 114

Sashe 42

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuska Khausar ta ɓata cike da damuwa tace.
“Wallahi nikam ba zanci ba Mommy kema Meyesa zakici, kema daga ganin abu saiki hau ci, batare da kin duba ingancin sa ba Allah ma dai yasa kinyi Bismillah”.
Dafe kai Mommy tayi tace.
“Aikuwa de Wallahi kwaɗayin sa yasa na shafa banyi Bismillah ba, Anma bari nayi.
Bismillahi feh Auwalihi Wa'ahirihi”.
Ta faɗa tare da cigaba da shan perpesoup ɗin.
Wani banzan kallo me cike da tsana Hajiya Bunayya ta watsa wa Khausar aranta tace, shegiyar yarinya, wannan yarinyar saina bi takan ta tukunna zata gane kurenta, bari dai ingama da matsalolin dake gabana”.
Ita kuwa Khausar kallon mahaifiyarta da har zuwa yanzu take shan perpesoup ɗin tayi tace.
“Wai Mommy ba zaki haƙura dasha haka ba?".
Girgiza Kai Mommy tayi kana tace.
“Kema Idan zaki ci ga shican akula Khausar ban hana kiba, amma wannan tambayoyin naki sun fara isata”.

Ƙwafa Hajiya Bunayya tayi tace.
“Ƙyaleta bare ma ni bazan bar mata ba ina kedai ya isheki?”.
Cikin sakin fuska Mommy ta gyaɗa kai tare da faɗin.
“Eh Alhamdulillah ya isheni”.

“Aiko buƙatar maje haji salla, ba zan bar matashi ba, tunda dai ke kinsha ai hikenan, idan tanaso ta biyoni ɗakina”.
Ta ida maganar tare da ɗaukan kularta ta fice bayan ta yiwa Mommy sai anjima.

Zama Khausar tayi agaban mahaifiyarta cikin raunin murya da yanayin damuwa tace.
“Mommy meyesa!?, Rayuwar nan fa ba yanda kika ɗauke ta da yanda zuciyarki take ace haka na kowa yake da munji daɗin duniyar nan fa, amma Mommy meyesa daga kawo miki abu zaki ɗauka kici yanzu kuma idan abin cutarwa ne fa?”.

Kallonta Mommy tayi cikin tsukr fuska kana cikin fushi tace.
“Khausar ki kiyayeni fa, bana son wannan baƙin halin da kike ɗaurawa rayuwarki fa. Ni bakiga ina nunawa matar nan baƙin hali ba haka zalika itama da zuciya ɗaya take zaune damu, zaman lafiya mukeyi babu kishi bare tsangoma ko hassada, amma meyesa zaki sawa ranki rashin yarda akan n
Me kike zaton zata cutar dani, babu abinda zata yimin dan haka ki kiyaye”.
Ita kuwa khausar hawaye da ya cika mata Idanunta tashiga ƙoƙarin mayarwa sabida takaici, mahaifiyarta ta ɗauki duk kan yarda da amana ta basu, amma sukuma da wannan damar suke amfani ganin sun cutar da rayuwarta.
Ƙasa Tayi da kanta kana tace.
“Shikenan Mommy Komai na faɗa miki ba zaki yarda dani ba, amma babu komai Ubangiji Allah yatsareki ya kuma kareki".
“Ameen”Mommy ta amsa a kufule.
Ita kuwa Khausar cikin mutuwar jiki ta miƙe tare da wucewa Bedroom ɗinta tana maijin wani irin zafi azuciyarta.
Da kallo Mommy tabi bayanta tana ayyana abubuwa da yawa akanta, tarasa ina Khausar ta ɗauko wannan halin baki ɗaya bata da yarda muddin Hajiya Bunayya zata kawo mata abu ko Haiydar saita tsaya tana musu tambayoyi akai, da faɗin kada suci kada suyi kaza da kaza.
Jin ƙiran sallah magriba yasa ta miƙe tashiga Bedroom ɗin ta dan gabatar da Sallah.

Aɓangaren Khausar kuwa tana shiga ɗaki ta lumshe Idanunta tare da manna bayanta da jikin ƙofa.
Hawaye masu ɗumi suka zubo mata jikinta na bata da wani makircin da Hajiya Bunayya ta shiryawa mahaifiyarta sam bata yarda da wannan perpesoup ɗin da takowo mata ba,
shin wai ma ta wani hanya zatabi ta fahimtar da mahaifiyar?.
Sosai ta zurfafa acikin tunanin da take har aka shiga Masallaci sai, asannan ta sauƙe gauron numfashi tare da nufar toilet cikin nutsuwa ta ɗaura alwala kana ta fito, tare da shimfiɗa darduma duk da yanayin zullumi da take ciki bai hanata tattara nutsuwarta zuwa ga Ubangiji mabuwayi gagara Misali ba,
bayan ta sallame ta ɗaga hannayenta biyu zuwa sama kana tace.
“Ya Allah baka zalinci sannan kai ka hana zalunci atsakaninmu ya Allah baka gyan-gyaɗi bare bacci ya Allah kada ka bawa wannan baiwar taka daman cutar damu ya Allah ka kare mahaifiyata al'farma Annabi da al'ƙur'ani”.
Kana ta shafa addu'ar tana mai zubar da hawaye har aka idar da Isha'i bata fita ba saima miƙewa da tayi ta kwanta agado lamo cike da tunanin rayuwa da haka bacci mara daɗi ya ɗauke ta.

Cikin ikon Allah haka Mommy ta kwana lafiya lau batare da wani mugun abu ba, tun Khausar na jira taji Mommy tace wani wajen nayi mata ciwo ko kuma taga zubewan cikin Mommy kamar yanda Hajiya Bunayya ta faɗa taji shiru,
hakan yasa ta watsar da abin aranta yayin da Aɓangaren Hajiya Bunayya baki ɗaya kunnenta ke sauraron jin wani labari daga bakin Mommy sai dai shiru amma tace bari ta kara jira kaɗan ta gani.

Yau kwanan Mommy uku da cin perpesoup ɗin da Hajiya Bunayya ta kawo mata tana zaune a Bedroom ɗin ta cike da kasala.
Cikin rumtse idonta ta zabura tare da dafe ƙasan maranta da yayi wani masifan murɗawa ahankali ta furta.
“Wash! Allah na”.
Sai kuma ta koma ta zauna tare da lumshe Idanunta yayin da hannunta na dama ke dafe asaman maranta sai ka ta miƙe tare da fitowa falon tana takawa ahankali.
Khausar dake zaune a asaman 3sitter Jikinta sanye da half gownt na bacci yayin da ta tura tulin sumar kanta acikin hular Net Idanunta na kan takardan Geography dake riƙe ahannunta yayin da Nahawu ke ajiye gefe ta ɗago manyan Idanunta ta zubasu akan Mommy dake ya mutse fuska alamar bata jin daɗin jikinta, zama tayi akan 1 sitter kana a hankali tace.
“Khausar har yanzu baki shiga ba?”.
ta ida mgnar tana mai cije lips ɗinta.

Ita kuwa Khausar kai ta gyaɗa mata tace.
“Eh Mommy karatu nakeyi, gobe Idan Allah ya kaimu zamu fara Exam ɗin First term, lokacin ai ya tafi amma Mommy lafiya na ganki haka?”.
Ta ƙare mgnar tana kafe mata ido.
Ya mutse fuska Mommy tayi tare da lumshe Idanunta still cikin na damƙarta tace.
“Wallahi cikina ke ɗan min ciwo Khausar”.

Cike da tausayawa Khausar tace.
“Cikin ki kuma Mommy?”.
Kai Mommy ta gyaɗa tace”.
“Eh”.
Ita kuwa Khausar ajiye takardan hannunta tayi tare da tsirawa mahaifiyarta ta Ido cikin tausayawa tace.
“Mommy kodai in faɗawa Abba Azo atafi Asibiti ne?".
Kai Mommy ta girgiza kana tace.
“A'a ai beyi tsanani har haka ba”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da sauƙe numfashi tace.
“Toh Allah ya sawwaƙe”.
Mommy da hannunta ke dafe asaman cikinta still Idanunta na lumshe tace.
“Ameen”
Miƙewa Mommy tayi ta koma kan 3sitter ta kwanta kamar minti biyu da kwanciyarta ta sai kuma sake miƙewa ta zauna tana yamutse fuska.

Ita kuwa khausar cikin yanayin damuwa tace.
“Sannu Mommy kode in Kira Abba ne?”.
Girgiza kai Mommy ta kumayi sannan tace.
“A'a tashi ki koma ɗaki nima yanzu zan shiga na kwanta”.
Girgiza kai Khausar tayi tace.
“A'a Mommy Zan zauna dake”.
Lumshe idanu tayi tare da cije laɓɓanta na ƙasa tace.
“Kada ki damu kije ki kwanta na faɗa miki naji sauƙi kuma nima yanzu zan shiga na kwanta”.

Cikin sanyin jiki ta mike kana tace.
“Saida safe Allah yaƙara sauki”.
Mommy ta amsa da “Ameen”.

Ita kuwa Khausar tana shiga ɗaki ta zube akan gadonta tare da faɗa wa duniyar tunanu, a haka bacci ya ɗauke ta kasancewar dare yaja batayi bacci ba ga kuma gajiya.

A ɓangaren Mommy kuwa haka ta kwana cikin mawuyacin hali tare da murƙusoso cikin matsanancin ciwon ciki.
Washe gari.
Da safe bayan Khausar na idar da Sallah tayi Azkhar ta nufi ɗakin Mommy bakinta ɗauke da sallama.
Mommy dake kishingiɗe kan darduma ta ɗago kanta tare da amsa sallamar Khausar.

Kusa da ita Khausar ta tsugunna tare da riƙe hannunta tace.
“Mommy ina kwana ya cikin naki?”.
“Murmushin Ƙarfin hali Mommy tayi kana tace.
“Naji sauƙi Khausar kije ki haɗa muku abin Breakfast kada lokaci ya ƙure”.
Kai Khausar ta gyaɗa kana tace.
“Amma da sauki Mommy kodai daurewa kike yi?”.
Murmushi Mommy tayi tace.
“Eh jeki shirya muku”.
Kai ta gyaɗa sannan ta fice kai tsaye kichen ta nufa.

Tana shiga tasa ruwa kadan atukunya yanda zai wadatar mata bayan ya tafasa ta ɗan zuba mai kana ta zuba Couscous kamar minti goma ta buɗe taga ya dahu yayi sar gwanin kyau, amfanin ɗiga man kenan.
Sauƙewa tayi sannan ta buɗe fridge ta ɗauko miyan stwe da yaji naman kaza ta ɗumama sai kuma ta dauko lunch box din Raudat, Ramadan da Haiydar da kuma nata ta zuba musu, sai kuma ta koma ɗaki tashiga toilet tayi wanka Agurguje ta fito ɗaure da towel mai ɗan girma sannan ta cirewa Raudat kayanta tayi mata wanka bayan sun fito tashafa mata mai kana ta sanya mata Uniform sannan itama ta shirya cikin Uniform da yayi matukar amsar jikinta hannu Raudat taja suka fita dai-dai lokacin da Haiydar suka fito da Ramadan cikin shiri ko wannensu ya nufi inda lunch box ɗin da yake ya ɗauka kana suka fice harabar gidan suka shiga mota.

Kamar ko yaushe motar na parking Khausar ta fito riƙe da hannun Raudat,
Sai da ta kaita ajinsu sannan cikin sauri ta juya ta kama hanyar koma ajinsu daga baya taji ankira sunan ta da faɗin.
“Lelewal ke kullum sai kowa ya riga ki shiga cikin aji ko?”.
Ahankali ta juya tare da sauƙe manyan Idanunta akan Malam Isa dake tsayi murmushi tayi da faɗin.
“Ba haka bane Malam na tsaya kai Raudat ajinsu ne shiyasa”.
Kai ya gyaɗa still Idanunsa akanta hakanan yarinyar ke burgesa ahankali yace.
“To ki tafi kar araba musu questions paper ba kyanan”.
Kai ta gyaɗa tare da juyawa cikin sassarfa da sanin darajar kanta take tafiya har ta isa cikin ajin.

Aɓangaren Amina kuwa koda M Jameel yashiga class da niyyar raba musu questions paper ƙasa tayi da kanta ta amsa batare data kalli fuskarsa ba domin koda gaishesa ne ta dena tunda ta lura da baya buƙata kallon fuskanta, to shima M Jameel Sosai yaji daɗi da yarinyar ta daina gaishesa, dan ko kaɗan baya ƙaunar kallon fuskarta, bare kuma wata magana ta haɗa su.
Chapter 42 · 0% Book details