← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 114

Sashe 39

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asma'u ta katse shirun tare da buɗe Handbag ɗin ta ta ciro takardan Economics da Mi'atu Hadith da sauran darasin da sukayi ta miƙa mata tace.
“Gashi ki kwafa sannan kiyi karatu akai”.
Amsa Khausar tayi tare da budewa tace.
“Toh shikenan ba matsala zan duba”.
Bayan sun sake taɓa hira Asma'u tace.
“Zan tafi”.
Khausar tace.
“Tun yanzu?”.
Hararanta Asma'u tayi tayi tace.
“Eyyyyy lalle kam aigwara ni dakeke sai ki kusan shekara bakije gidanmu ba”.
Tana gama Fadar haka ta Miƙe ta fita.
Dariya Khausar tayi tare da sanya Blue Black ɗin hijabinta ta fice afalon ta samu Asma'u nayiwa Mommy Sallama bayanta tabi suka fice.

Washe gari ta kama ranar.
Asabar Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ce acikin mota, suka nufi unguwar shamaƙi, yayin da Hajiya Bunayya ke tuƙi suna sauraron wakar Nazeer Sarkin Waƙa mai taken Bamu babu ku,kuma baku babu mu.
Cike da nishaɗi Hajiya Lami tace.
“Hajiya Bunayya Matsalar mu tazo ƙarshe da zaran munje wajen wannan mutumin komai yazo ƙarshe dan ina da tabbacin aikinsa”.
Dariya Hajiya Bunayya ta sheƙe dashi tare da buga stairing motar tace.
“Kedai bari nayi al'ƙawari saina tarwatsa wannan matar”.
Da wannan hiran suka isa unguwar daga can bakin hanya sukayi parking motarsu.

Kana suka ɗanyi tafiyar ƙafa kaɗan suka tsallaka titin, suka nufi wani ƙaton kango mai zagaye da dogon katanga da duhuwar bishiyoyi,
da baya-baya suka fara shiga cikin wajen da manyan bishiyoyin Tsamiya dana kuka suka masa ƙawanya sai kuma wasu manyan bishiyoyi irin na Ceɗiya masu masifar tsawo da duhu kana sai wani ƙaramin bukka daya kasance Atsakiyar bishiyoyin,
jikin bukkar ke waye yake da jajayen ƙyalle da wasu irin ƙwarya masu masifar munin gani ajikin ƙwaryan akwai kuratandu sai kuma wasu baƙaƙen ƙaho masu siffar fuskan bil Adam.
Daga nesa suka ajiye takalmansu kana suka cigaba da tafiya da baya har suka shiga cikin gidan da ƙafar hagu yayinda wani masifaffen ɗoyi ya cika gidan baki daya ya mamaye ilahirin gidan.

Cikin ɗaga sautin murya suka haɗa baki wajen faɗin".
“An gaida Boka Kar'uzu uban bokaye angaida la'anannen Uban la'anannu mugu uban mugaye
Hatsabibi uban hatsabibai”.
Daga ciki kuwa wata daskararriyar murya mai firgitarwa mara daɗin saurara yace.
“Kushigo da baya-baya kana ku tabbata ƙafar hagu zaku riƙa takawa har ku iso gareni”.

Cikin tsinkewar zuciya da matsanancin tsoron kada su saɓa masa doka cike da biyayya suka gyaɗa masa kai tare da ƙara sawa kusa dashi suka zauna suna maida numfashi.
Cikin daskararriyar muryarsa mara daɗin sauraro yace.
“Ku tashi anan suna zaune zaku danne ɗan ƙundalo mai ido agoshi! Maza ku koma ta gefen hagu bana ƙaunar ganin ku.
A dama saboda ba aikin dama zamu yiba”.

Tsaban tsoro saidai Hajiya Bunayya ta dungura tare da kurje hannunta kana jikinsu na rawa suka koma gefen hagunsa.
Kallon Hajiya Bunayya yayi ya kece da wata mahaukaciyar dariya me tsananin razanarwa, ya nunata da wani mummunan yatsansa da farce yayi tsawo kana yace.
“Kin makara cikinta har ya kusa wata uku amma zamu jijjigesa da ƙarfin ikon mu zamu fito dashi!”.
Ita kuwa Hajiya Bunayya Atake taji tsoron ta ya tafi ta washe baki da faɗin.
“Laaa Malam kasan abinda ke tafe dani?”.

Cikin fushi yace.
“Sunana ba Malam ba Kur'ani kika gani agabana ko hadisai da za ki kirani da Malam ki kirani da Boka Kar'uzu uban bokaye La'anannen uban la'anannu Mugu Uban Mugaye”.

Ƙasa da kai tayi tana cewa.
“Tuba nake Boka Kar'uzu bazan sake ba”.
Kai ya gyaɗa mata yace.
“Sai kuma batun Jameel da ’yarki Amina”
Cikin rawan jiki tace.
“Eh boka Kar'uzu”.

Ya kece da wata mahaukaciyar dariya yace.
“Ai ƙaddarar abai-bai take,Ai ƙaddarar abai-bai take, ƙaddarar abai-bai take!”.
Ita kuwa Hajiya Lami cikin zaƙuwa take gyaɗa kai.
Hajiya Bunayya tace.
“Boka kamar ya ƙaddara abai-bai take ban fahimta ba”.
Yace.
“Babu damuwa za'ayi Miki aiki”.
Hajiya Lami ta gyara zama sosai tace.
“Toh Boka Kar'uzu ni ya batun ‘yata?”.

Ya sake kecewa da wata mahaukaciyar dariya yace.
“Aike batun ki mai sauƙi ne shi wannan babu wata Aransa shi wannan dakike gani yana nan kamar Waliyi ne, koko ince katako, sai dai fa akwai ganye bishiya da yake tsirowa ajikinsa har ta fara jijiya ajikinsa tana gab da zuba rassuna”.

Hajiya Lami tace.
“Boka koma wani irin ganye ne Indai bana Samira bace atun ɓukesa”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Angama angama”.
Cikin jin dadi ta juya ta kalli Hajiya Bunayya tana sakar mata da murmushi alamar da akwai Nasara.
Sai kuma ta juya ta kalli Boka Kar'uzu tace.
“Ya batun abubuwan aiki?”.

A tsawace boka Kar'uzu yace.
“Zaku kawo Fararen Bunsuraye guda uku, Da baƙaken karnuka guda biyu da baƙar kaza mai bungi-bungi guda ɗaya na batun aikin zubar da ciki.
Batun Jameel kuwa zaki kawo gurguwar jaka mace sannan ki samu makauniyar tinkiya me watanni bakwai sai kuma agwagwa fara mai ƙafa ɗaya”.
Zare Idanu sukayi Atsorace jin abubuwan da ake buƙata.
Ya cigaba da cewa.
“Batun aikin Moddibo kuwa zaku kawo Gurguwar shanu ja mai Ido ɗaya da kuma namijin doki fari soll wanda aka haifesa acikin gida sai kuma ku samo Alade guda biyu mace dana miji”.

Cikin tashin hankali da damuwa Hajiya Lami tace.
“Boka a ina zamu iya samo wa'annan abubuwan aise kai saidai mu bayar asamo”.
Yace.
“Toh ku ajiye kuɗin masu tarin yawa”.
Cikin rawan jiki Hajiya Bunayya tasa hannu a jakarta ta ciro kuɗi wanda batasan adadin suba ta ajiye masa”.
Kallon kuɗin yayi yace.
“Kuje bayan sati biyu kuzo ku karɓi kayan aikinku sha yanzu magani yanzu”.
Godiya suka masa kana suka tashi suka fita kamar yanda suka shigo.

Acan ɓangaren su Khausar kuwa karatu suke sosai babu kama ƙafar yaro sabbin Malamai da aka kawo musu sun zage damtse wajen koyar da ɗalibai ga kuma sabbin ɗalibai da ake shigowa dasu saboda yanda aka tsara Makarantar sosai makarantar ya sake samun ɗaukaka fiye da farko ga kuma shirye-shiryen musabaƙa da akeyi na Jahar Taraba baki ɗaya Khausar da Asma'u sun sake dagewa.

Bayan sati biyu Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ce zaune agaban Boka Kar'uzu.
Wani ƙullin magani ya ɗauka tare da kallon Hajiya Bunayya ya miƙa mata kana yace.
“Wannan ki dafa shi da farfesun kayan ciki ki bawa Hajiya Aysha tana ciki, sunan cikinta anyi angama saide wani cikin bashi ba!.
Sannan idan kin shirya kizo za'a zazzage mata mahaifa asa mata ajiya yanda baza ta sake ɗaukar wani cikin ba, sannan kuma mijinta zai tsaneta ba zai sake sha'awar kusantar taba!”.
Murmushin samun nasara Hajiya Bunayya tayi tace.
“Boka Indai cikin nan ya zube zan dawo akan aikin amma yanzu burina cikin ya zube sannan ajawo hankalin Jameel kan Amina”.

Wata mahaukaciyar dariya Boka Kar'uzu ya sheƙe dashi yace.
“Ga wannan”.
Hannu bibbiyu Hajiya Bunayya tasa amshi ƙullin maganin tana jujjuyawa yace.
“Ki bawa ‘Yarki Amina tayi wanka dashi sannan tayi hayaƙi idan zatayi hayaƙin ta ɗago kaskon ta kawo bakinta ta riƙa kiran Jameel!, Jameel!!, Jameel!!! na tsawon kwanaki uku sannan ta tsallake kwana uku ta sake na kwana uku na sannan ta sake kwana uku ta tsallake kwana uku sannan ta sake kwana uku kuma ko wanne idan tazo hayaƙin sai takai kaskon bakinta ta kira sunansa kada ku yarda asamu kuskure dan in an fa samu kuskure abun bazaiyi kyau ba”.

Kallon Hajiya Lami Hajiya Bunayya tayi tare da jinjina mata hannu tana murmushi cikin ƙasa da murya tace.
“Alhamdulillah nakusa ganin ƙarshen wannan matsiyatan”.
Martanin Murmushin Hajiya Lami ta mata itama ranta fess burinsu ya kusa cika.
Tunda Boka Kar'uzu yace.
“Muddin tayi na tsawon wannan kwanakin shida kansa zai kawo kansa gareta idan kuma wannan baiyi ba akwai wanda zamu sakeyi saidai shi wannan kankat ne amma shi sai farkon damuna tukunna zamu samu ayishi”.
Cike da farin ciki Hajiya Bunayya tace.
“Boka Kar'uzu Uban bokaye Insha Allahu ma nasan wannan aikin zaici”.
Cikin wata razananniyar tsawa yace.
“Oho Ni dai nace kada ki sake kiramin sunan Allah anan domin da kina jin tsoronsa ba zaki zo nanba bare har kinemi aikata mugun abu akan wani idan kuma kina son aikin ki ya ɓaci ki sake kiran Allah anan”.

Cikin rawan baki da tsoron kada aikinta yaƙi ci tace.
“Tuba nake Boka Kar'uzu Uban bokaye La'anannen Uban La'anannu Mugu Uban mugaye da ikon ka wannan aiki zaici”.

Ya sheƙe da wata mahaukaciyar dariya mai kama da sautin ƙaran lalataccen Injin Markaɗe yace.
“Yanzu ne aikin ki zaiyi yanzu ne kika yi magana mai ma'ana”.
Ta saki ajiyar zuciya cike da farin ciki.

Hajiya Lami ta matso kusa tare da gyara zama sosai tana fuskantar Boka tace.
“Ni kuma ya maganar ’yata?”.
Wani irin kallo ya mata kana yace.
“Na ‘yarki sai anyi babban shiri domin wannan da kike gani shida saƙago basu da banbanci baya kallon mace ako wani irin mataki daya wuce ɗaliba ya karantar da ita ya kuma bata ilimi da tarbiyya shi koda mace zata wuce tsirara agabansa babu abinda zai damesa da ita tamkar zuciyar dutse ne aƙirjinsa!”.

Ta gumi Hajiya Lami tayi tare da faɗin.
“Ikon Allah aƙasan ranta”.
Boka Kar'uzu ya cigaba da cewa.
“Sai munyi mata shiri sosai yanda lokaci ɗaya zata jawo hankalin sa gareta sai bayan wata biyu zaki zo ki karɓi haɗin da muke tsuma shi sannan tayi kokari ta bashi yaci daya ci aiki ya gama”.
Ajiyar zuciya Hajiya Lami ta saki tace.
“Da ƙarfin ikon ka zamuyi hakan boka”.
Ya kece da wata mahaukaciyar dare yace.
“Na gama daku zaku iya tafiya”.
Miƙewa sukayi suka ce. “Godiya muke Boka Kar'uzu Uban bokaye La'anannen Uban La'anannu Mugu Uban mugaye”.
Shikuwa Dariya ya kece dashi yana jin daɗin kirarin da ake masa kamar yanda suka saba shiga haka suka fita da baya.
Chapter 39 · 0% Book details