Sashe 73
Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Gyaran murya yayi tare da fuskantar Gimbiya Dadu kana yace.
“Yafendo na gama karatuna yanzu na dawo sannan na dawo da burin yin Aure. Ya maganar mu da khausar tana nan dai ko?”.
Ajiyar zuciya mai nauyi Gimbiya Dadu ta sauke tare da lumshe Idanunta kana ta saki wani shu'umin murmushi tare da kallonsa kana tace.
“Sosai ma kuwa maganar ku tana nan mai zai hanata da izinin Ubangiji maganar ku tana nan baka da matar data wuce Khausar yau ɗin nan zan yiwa Abbansu maganar”.
Cike da farin ciki ya saki sanyayyar ajiyar zuciya kana yace.
“Kai Alhamdulillah Yafendo na naji daɗi”.
Murmushi kawai tayi shi kuwa miƙewa yayi bayan sun sake taɓa hira ya tafi.
Bayan kwana uku.
Ahankali Khausar ta sauƙa daga motar dake kaisu makaranta hannun riƙe da Raudat ta nufi ajinsu ta kaita kana ta dawo tashiga ajinsu Lokacin har an fara raba booklet kallonta Malam Isma'il dake raba Booklet ɗin yayi kana yace.
“Lelewal mai yasa kike son zuwa letti ne Exam ɗin ma baza ki fito da wuri ba?”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da cewa.
“Ayyah Malam ayimin afuwa”.
Harara Samira Sani dake bayan ta ta watsa mata cike da tsanar ta Asma'u dake gefen ta ta girgiza kai domin ita dai ta rasa me. Khausar ta tsare musu suka tsaneta.
Khausar kuwa zama tayi Malam Isma'il ya bata Booklet da kuma Quatons peper Na Arabic da zasuyi yau ma kamar kullum tun kafin a gama rabawa Khausar tashiga answering Questions ɗin cikin mintunan da baza su gaza ashirin ba ta kammala.
Acan office ɗin Moddibo kuwa zaune yake ya jingina bayansa da jikin kujera yayin da ya ɗaura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya akan deks ɗin Idanunsa na lumshe.
Cikin sauri ya buɗe Idanunsa tare da jan dogon tsaki.
Domin da zaran ya rufe idanunsa babu abinda yake gani sai moment da suka kasance da yarinyar cike da damuwa ya sauƙe numfashi kana aƙasan ransa yace.
“Na godewa Allah da yasa karatun yaran nan yazo ƙarshe kana naji daɗi da cewa sun gama Exam ɗina, bazan sake shiga ajinsu ba”.
Da sauri ya runtse Idanunsa haka nan yake jin kunyar kansa da kansa ya rasa ta yanda zai fassara al'amarin yasan tun farko yarinyar bata da kunya bare kuma wannan abu ya faru shin taya zai iya haɗa ido da ita?.
Anan sashin su kuwa.
Atare Khausar da Asma'u suka fito daga Area class ɗinsu har zasu wuce suka hango M Jameel tsaye.
Abakin Office ɗin su Moddibo.
M Jameel ne tsaye ya jingina bayansa da jikin ƙofar yayin da Amina ke tsaye gefensa cikin iyayi da yauƙi ta kashe murya tare da cewa.
“Malam sai gobe idan Allah ya kaimu zan dawo ko Principal ya dawo na amshi result ɗina”.
Anutse M Jameel ya juya ya kalleta tare da cewa.
“Ok Allah ya kaimu ki gaida gida”.
Sake karya murya tayi cikin tsaresa da ido tace.
“Toh gida zaiji Malam kaima ka gaida gida”.
Jinjina kai yayi batare daya sake kallonta ba yace.
“Gida zaiji”,Juyawa tayi tabar wajen.
Dai-dai lokacin da Asma'u da Khausar suka iso a tare Kallonsa Khausar tayi tare da cewa.
“Barka da rana Yah Jameel”.
Murmushi ya sakar mata kana yace.
“Yawwa Khausi bar ka dai yanzu kam an zama manyan ƴan mata ankusa agama Secondary school a huta a shiga babin girma ko?”.
Jinjina kai tayi cikin jin daɗi ta kalli Asma'u kana tace
“Ai lallai dai kam bari kawai Yah Jameel jinmu nake tamkar ansaki tsuntsuwa daga sheƙarta.
Wani irin daɗi mukeji mun kusa mu rabu da rayuwar bauta rayuwar duka cin zali, kaɗe ɗan kwali, harara, tsawa, hantara,”.
Kallon ta M Jameel Yayi tare da juya idanunsa zuwa office ɗin ya mata alamar Moddibo na ciki.
Cikin sauri ta sanya hannunta ta rufe bakinta tare da barin wajen bayanta Asma'u tabi tana ƙyalƙyala dariya tare da cewa.
“Khausar ga Moddibo na miki magana wai kije”.
Dariya M Jameel yayi ganin
Cikin sassarfa Khausar ta fice daga wajen batare data yadda ta juya ba.
Moddibo kuwa na zaune a office duk Maganar da sukayi akunnensa da zaran sautin muryanta ya ratsa kunnensa zaiji tsikar jikinsa ya tashi tamkar ana stikaresa da allura hakan yasa ya runtse Idanunsa da ƙarfi kana yayi shiru.
Allah ne kaɗai yasan yana yin da yake ciki.
Khausar kuwa na fita wajen motarsu ta nufa ta samu duk su Amina su shiga ita kadai ake jira tana zama Driver yaja suka tafi.
Asma'u kuwa na fita ita da Bashir mai Napep ɗin su ya iso ya ɗauke su suka tafi.
Washe gari da yamma bayan Khausar sun dawo makaranta misalin ƙarfe Uku ta fito cikin wata Bugaggiyar shadda milk color anyi masa ɗinkin dogon riga da kuma zubi da akayi sa da Coffee zare fuskarta ɗauke da light Make-up yayin da tayi ɗaurin Aysha Buhari ta zuba jelar gashinta ta gefen dama dake fitar da sanyayyan ƙamshi kana ta yafa milk colour gyale akafaɗarta Hannunta riƙe da jaka Coffee haka ma takalmin Half cover coffee color jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin tularen Balila da kuma Sedection.
Kai tsaye Bedroom din Mommy ta nufa bakinta ɗauke da sallama tashiga ganin Mommy Bata ciki yasa ta fito tare da nufar kichen.
Tsaye ta samu Mommy tana yanka albasa.
Mommy na ganinta tace.
“Har kin gama shiryawa?”
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Eh Mommy na gama shiryawa”.
Jinjina kai Mommy tayi tana cigaba da yanka albarsar tace.
“Idan kinje ki Gaishe da Ummin Asma'u”.
Kai ta gyaɗa tare da gyara rikon Handbag din ta kana tace.
“Insha Allah zata ji Mommy”.
Dai-dai nan suka jiyo Sallamar Naseer afalo, cikin sauri ta kalli Mommy sai kuma ta ɓata fuska lokaci ɗaya ta nemi fara'ar dake fuskanta ta rasa.
Kallon mamaki Mommy tayi mata kana tace.
“Ya dai haka daga jin muryan sa kin wani tsuke fuska sai kace wanda yazo miki da wani mugun abu”.
Girgiza kai tayi tare da cewa.
“Babu komai Mommy”.
Girgiza kai Mommy tayi tare da fita tana cewa.
“A'a wa nakeji kamar Naseer mutan India”.
Yana zaune kan kujera ya gyaɗa kai tare da cewa.
“Eh Mommy nine”.
Dai-dai lokacin da Khausar ta fito miƙewa yayi idanunsa akanta yace.
“Wooow Masha Allah”.
Sam ya mance da Mommy dake tsaye a wurin.
Gaba ɗaya imaninsa ya tafi gareta cike da zalama ya nufi Khausar tamkar zai rungumeta yana faɗin.
“Wowww my dear Wife you look so georoures, Fantastic, beautiful you look so Pretty”.
Khausar kuwa ganin yanda yake matsota zai Rungumeta yasa taja baya da sauri tare da cewa.
“Nagode.
Mommy kuwa kallon ikon Allah take ganin yanda baki ɗaya hankalinsa ya tafi kan Khausar da alama ya mance da tana wajen.
Gyaran murya tayi tare da cewa.
“A'a Naseer ka zauna mana akawo maka abin taɓawa mana”.
Girgiza kai yayi da faɗin.
“A'a Mommy Nagode”.
Itako Khausar ɓata fuska tayi babu walwala atare da ita tace.
“Mommy na tafi".
Cikin sauri ya mike tare da bin bayanta kana yace.
“My dear Wife Ina Zakije?”.
Ataƙaice tace.
“Unguwa”,
Cikin yanayin zumuɗinsa yace.
“Bari in sauƙe ki”.
Mommy kuwa ita kanta rawan kansa ya bata tsoro ganin yanda yake nuna zalamarsa afili kamar kura yaga ɗanyen Nama!”.
Da sauri Mommy ta kallesa tare da cewa.
“A'a Naseer ka bari basai ka kaita ba ai zata shiga Napep”.
Zare ido yayi tare da cewa.
“A'a Mommy na isa kamar ni ace Matata tashiga Napep no, impossible kamar Matar Naseer Ibrahim ɗancanji amma ace Matata na hawa Napep Ina bai yiba bai yiba”.
Ita kuwa Mommy aranta tace Ohhh wannan yaro dai Allah yamasa kurari bawai basu da arziƙinba mahaifinsa nadashi amman kurarinsa yafi kuɗin nasu yawa bashi da aiki sai cika baki.
Khausar kuwa tuni ta fice cike da takaicin zumuɗinsa.
Da sauri yabi bayanta yana cewa.
“My dear Wife ki tsaya mana let me drop you”.
Banza Khausar tayi masa tayi ficewar ta.
Kashe murya yayi tare da cewa.
“Dan Allah ki tsaya mai yasa kike yin haka?”.
Ba tare data juya ba kana cikin ɗaure fuska tace.
“A'a Uncle Naseer ka bari kawai zanje da kaina gidansu Asma'u nefa Napep ma zan shiga”.
Murmushi yayi kana yace.
“Yawwa muje kinga nima sai ingaishe da Umminta kinga dama na daɗe banga Asma'u ba yau ya kamata mu gaisa”.
Khausar kam sake ɗaure fuska tayi tare da cewa.
“Yaya Naseer Allah da kabari kada in saka wahala nasan baza ka rasa abinyi ba”.
Langwaɓar da kai yayi tare da marairaice fuska kana ya karyar da murya tare da cewa.
“Please My dear Wife allow me to escort you kinsan dai Ina ƙaunarki sannan ina son kasancewa da ke banaso kidinga nesanta kanki daga gareni”.
Siririn tsaki taja aranta kana tayi gaba abinta domin har ga Allah zalamarsa na bata tsoro.
Shi kuwa da sauri ya nufi Parking space tare da ɗaukar motarsa yazo ta gefenta tare da buɗe mata kana ya karyar da murya tare da cewa.
“Please Wife to be kishigo mana”.
Dai dai lokacin da gate man ya buɗewa Lamiɗo da Gimbiya Dadu suka shigo bisa duk kan alamu daga asibiti suke anje duba lafiyar Idonta dan bayan ta fito hannunta na riƙe da ledan magunguna da kuma tambarin asibiti.