← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 114

Sashe 103

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kallonsa Ummi tayi cikin muryan kuka tace.
“Babana ka faɗa min gaskiya tsakanin ka da Allah yau kunyi magana dashi?”.
Girgiza mata kai Moddibo yayi tare da faɗin.
“Ummi ba muyi magana dashi ba, amma naji muryan J ƙasa-ƙasa yana cewa Abba abasu duk abinda suke so”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da rintse idanunsa kana tace.
“Babana ka tabbatar gaskiya kake faɗa min?”
Jinjina kai Moddibo yayi kana cikin sanyin murya yace.
“Wallahi Wa rabbul Khaba Ummi naji muryan J ƙasa. yana magana bawai sun bashi bane amma naji yana magana”.
Kuka Asma'u da Bashir suka fashe da shi atare kana lokaci ɗaya suka haɗa baki wajen cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n ya Allah ka kuɓutar da Yah Jameel Ubangiji kada ka basu ikon cutar dashi ya Allah kaine gatanmu Yah Jameel shine ka wakilta da isar mana gatanmu ya Allah ka karesa da karewaka”.

Numfashi Malam Ahmad ya fesar kana cike da tausayawa yace.
“Asma'u ba kuka ya kamata kuyi ba addu'ar mu Jameelu ke buƙata idan kuna kuka ya kuke so Ummin ku tayi?”.
Cikin sheshsheƙan Kuka Asma'u tace.
“Abba Yah Jameel fa Yah Jameel yana cikin mawuyacin hali Abba kaji fa maƙudan kuɗin da suke buƙata Abba ya za'ayi mu samu irin wannan kuɗin mu karɓo Yah Jameel Abba Ina tsoron kada su cutar mana dashi”.

Girgiza kai Malam Ahmad yayi cikin sanyin murya yace.
“Insha Allah da izinin Ubangiji babu abinda zai samu Jameelu, ko wani bawa da kalar tashi ƙaddaran tun kafin a haifi Jameelu Ubangiji ya zana masa ƙaddaransa muyi masa addu'ar Allah ya sauƙaƙa mana zafin ƙaddararsa”.
Jinjina kai Moddibo yayi yana jin wani irin azabebben zafi aƙirjinsa.
Kallon Moddibo Malam Ahmad yayi kana yace.
“Moddibo mai Yakamata ayi acikin wannan al'amarin!?”.
Moddibo da kansa ke ƙasa ya ɗago ya kallon Malam Ahmad a hankali yace.
“Malam abinda yakamata kawai afara cuku-cukun neman kuɗin nan sai muga abinda zai kasance”.

Girgiza kai Ummi tayi still tana jingine da jikin kujera tace.
“Babana ina zamu samu kuɗin nan Million ɗari biyu fa da ace Million biyu suka ce koni kaina ma zan bada su”.
Ta faɗa tare da ɗaukar wayarta tayi checking balance kana tace.
“Gashi yanzu anan ina da Million ɗaya da dubu ɗari huɗu da hamsin da ɗaya sannan kuma ba matsala gobe in Allah ya kaimu zan tafi cikin.
Taraba zan kai gwala-gwalaina”.
Sai kuma ta ɗan tsaya, jin numfashin ta na yankewa, da ƙarfi ta fizgo numfashin tare da cije labɓanta na ƙasa hawaye cike da Idanunta murya na cike da rauni ta cigaba da cewa.
“Zan saida su inga nawa zan samu ajikinsu zan haɗa harda na Asma'u sannan, motata itama zan saidawa muga nawa zan samu awurina”.
Jingina kai Malam Ahmad yayi kana cikin sanyin Murya yace.
“Har gidan nan ma asashi a. Kasuwa asayar dashi”.
Kallonsa Moddibo yayi tare da girgiza kai kana yace.
“A Malam ayi haka”.

Kai Malam Ahmad ya gyaɗa kana yace.
“Asiyar Moddibo menene Jameelu baiyi mana ba aduniyar na, kasancewar sa atare damu shiyafi mana komai”.
Ahankali Ummi ta ɗago kanta tare da tsira masa ido hawaye na bin kuncinta ta sani fili dai filinsa ne halalinsa mallakinsa, amma baki ɗaya ginin dake ciki Jameel ne ya musu bayan yasa an buge tsohon ginin taɓon.
Girgiza kai tayi cikin rauni tace.
“A'a ba sai anyi haka ba bari muga abinda Mahaifinsa zai samu”.
Girgiza kai Malam Ahmad yayi tare da kallon Asma'u da Bashir da har zuwa lokacin suke kuka a hankali ya fesar da numfashi tare da cewa.
“Ni dai na sadaukar da wannan gida ga.
Jameelu wallahi na yafe masa shi duniya da lahira na amince asa shi akasuwa muddin za a samu masu siya, to asa shi akasuwa mu samu muga aƙalla dai awajen mu ace an samu Million goma kuɗin zaifi gwaɓi”.
Sun kuyar da kai ƙasa Ummi tayi hawaye masu masifar zafi suka zubo mata.
Hannunta Moddibo ya riƙe cikin sanyin murya yace.
“Ummi dan Allah ki daina wannan kukan idan kina kuka muku ma ya zamuyi Ummi babu abinda J ke buƙata awajen mu face addu'a ganin ki awannan yanayin naya sake raunatamana zuciya”.
Kai Malam Ahmad ya gyaɗa kana yace.
“Sosai ma wannan kukan da kike Fatima saidai ya haddasa miki wani ciwon amma babu amfanin da zaiyi dan Allah ki daina ki cigaba da yi masa addu'a. shi kansa ba zaiso ace kina masa kuka ba”.
Kai ta gyaɗa tare da share hawayen ta kamar yarinya kana tace.
“Na daina Insha Allah zan cigaba da yimasa addu'a Ako da yaushe”.

Saida Moddibo ya tabbata ta daina kukan kafin ya mata sallama ya fice cike da tausayinsu Driving yake ahankali har ya isa gida yayi Parking kana ya fito ya rufe gate din tare da wucewa sashen Innayi bakinsa ɗauke da sallama.
Kwance ya samu Innayi cikin Yanayin damuwa gefenta da Radio tana sauraro wanda ɓatan M Jameel ake sanarwa.
Miƙewa tayi ta zauna tare da amsa Sallamar sa kana tace.
“Moddibo ya labarin Jameelu?”.
Cikin sanyin murya yace.
“Innayi sun sake kira ɗazu”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“Toh kunyi magana dashi yana cikin ƙoshin lafiya?”.
Girgiza mata kai yayi kana yace.
“A'a Innayi bamuyi waya dashi ba amma bisa duk kan Alamu J baya jin daɗin zaman wajen can”.
Ahankali Innayi ta jingina bayanta da jikin bango kana ta matsar da Radio gefe tare da cewa.
“Dama Moddibo ya za ayi yaji daɗin zaman wannan wajen. kasan yanayin da yake ciki ai dole bazai ji daɗin zaman wannan wajen ba amma me suke buƙata?”.

“Innayi kuɗi suka nema”.

“Kuɗi suka nema to aisai abasu aje a karɓe shi”.

“Innayi kuɗin da suka nema na fitar hayyacine!”.

“Kuɗi har nawa suka nema? Da zai zama na fitar hankali”.
Dafe goshinsa yayi kana yace.
“Innayi Million ɗari biyu suka nema kuma cikin ƙanƙanin lokacin fa”.
Ita kam Innayi baki ɗaya lissafin ta sincewa yayi jin maƙudan kuɗin tama rasa nawane, kallon Moddibo tayi tare da cewa.
“Dubu ɗari biyu?”.
Kai Moddibo ya Girgiza tare da cewa.
“A'a ba dubu ɗari biyu bafa Million fa Million ɗari biyu”.
Daga kanta sama tayi alamar tunani sai kuma ta kallesa tare da cewa.
“Million biyu?”.
Still girgiza mata kai Moddibo yayi kana yace.
“A'a Million ɗin goma, ashirin, hamsin, ɗari, ɗari da hamshin har ɗari biyu”.
Dafe kirji tayi kana tace.
“Million ɗari biyu?”.
Jinjina mata kai Moddibo yayi.
Girgiza kai tayi tare da cewa.
“Ban gane lissafin ba Aliyu”.

Lips ɗinsa duka biyu ya cije a lokaci guda kana yace.
“Ba zaki gane lissafin ba Innayi kuɗi ne masu tarin yawa suke nema”.
Cikin sanyin murya Innayi ta jujjuya kanta kana tace.
_“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin Layukalliful nafsi illa wusɗaha_
Toh yanzu mai Baban nasa yace?”.

“Innayi Abbansa bashi da wannan kuɗin a ƙasa kwanan nan dama ya gama yi mana ƙorafi bashi da kuɗi”.
Lumshe idanu Innayi tayi kana tace.
“Ya Salam ya Ubangiji Allah ka dube mu da idon rahama, ya Allah ka yayemana ya Allah ka sauƙaƙa mana ya Allah ka tsare Jameel ka kare mana shi, Allah ka tseratar da wannan bawan naka”.
Cikin sanyin murya Moddibo yace.
“Ameen”.

Kallon second biyar zuwa bakwai Innayi ta yiwa Moddibo kana tace.
“To amma kai Moddibo mai kake ganin zakayi akai?”.
Still hannunsa na dafe akansa yace.
“Innayi akwai kuɗi awajena zan tattara su in haɗa su muga nawa za'a samu awajena”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Yafi kam”.
Bayan sun sake tattauna ne Moddibo ya miƙe tare da yi mata Sallama kana ya nufi Sashen sa ahankali ya tura Murfin Kofar shiga tare da mayarwa ya rufe.

Kana ya jingina bayansa da jikin da kofar tare da rintse idanunsa sautin murya M Jameel ya farayi masa kai-komo AJ bansan idan nakeba,
Lumshe danunsa yayu zuciyarsa na bugawa da masifar ƙarfi yana bada sautin dif-dif-dif cikin sauri ya buɗe Idanunsa jin muryan M Jameel na yawo a kansa yana cewa A.J A.J Kallon kan 3sitrer kurui ji yake kamar zaiga J dinsa a wurin, cikin raunin murya yace.
“J Why are you?, Zuciyata zata fashe ya Allah kaji ƙaina ya rabbil Izzati ka dawo da J garemu cikin aminci da salama ya Allah kada ka bawa waɗɗanan azzaluman daman cutar dashi”.
Ya kai 15 minutes yana mai jero Addu'o'in cike da rauni, kafin ya miƙe kamar wanda aka mitsina ya nufi Bedroom ɗin sa kai tsaye toilet ya shiga ya watsa ruwa kana ya ɗaura alwala ya fito ya kwanta bisa gadonsa yayi rigingine duk da yasan cewa da wuya bacci ya ɗauke sa amman ya lumshe idonsa domin yau kwana uku rabon da ya samu wani wadataccen bacci sai wani irin azabebben ciwon kai da yakeji tamkar kansa zai rabe da ga wani irin sarawa da yakeyi yana bada wani irin sauti mara daɗi gau-gau-gau!.
A hankali ya bude idon sai kuma yayi saurin
Lumshe Idanun sabida sarawa da kan yayi masa.
Cikin zazzaƙan muryansa mai cike da rauni ya fara raira ƙira'ar Suratul Yusuf hawaye masu ɗumi suka riƙa fita daga idanunsa suna shiga kunnensa cikin wannan yanayin da cikar Sa'adatu da karatun Alqur'ani mai girma ya samar masa, wani irin kiɗimemmen baccin da bai shirya masa ba ya sace sa.
Chapter 103 · 0% Book details