← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 114

Sashe 113

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin tausayinta ya ratsa baki ɗaya jama'ar dake falon ahankali Malam Ahmad da Lamiɗo suka sanya hannu tare da share hawayen da suka saƙƙo musu.
Cike da rauni Ummi ta cigaba da cewa.
“Babana zan ƙare baki ɗaya sauran rayuwata ina maka addu'ar Ubangiji ya karbi shahadarka Allah ya maka SAKAYYAH tun daga nan duniya akan wa anda suka zalince ka har zuwa ranar tashin Alkiyama. Allah Ubangiji yajiƙan ka da rahma Allah ya gafarta maka yasa kahuta”.
Cikin sauri Hajiya Turai ta ƙarasa kusa da ita tare da Rungumeta ajikinta kana cikin Muryan kuka tace.
“Kiyi haƙuri Hajiya Fatima kiyi shiru”.
Kallonta Ummi tayi still Muryanta adake tace.
“Idan banyi haƙuri ba Hajiya Turai ya zanyi. Ubangijin daya ɗauke Jameelu shi yabani shi kuma shi ya ɗauke sa kana ya fini sanin wanene Jameelu agareni, sannan ya fini sanin Jameelu Allah ya masa rahma”.
Ta ida maganar tare da janye Jikinta daga na Hajiya Turai tare da juyawa ta kalli Abba kana tace.
“Ina Moddibo!?”.
Tana gama fadar haka tayi baya tare da sumewa.

Cikin sauri Hajiya Karima ta mike tare da ɗauko ruwa ta yayyafa mata dogon numfashi Ummi taja tare da buɗe Idanunta kana tace.
“Ina Moddibo yake?”.
Cike da tausayawa Abba yace.
“Moddibo yana asibiti asume tunda abin ya faru daya farfaɗo idan ya kira sunan Jameel zai sake sumewa, yanzu ne da aka samu ya farfaɗo aka masa Alluran bacci”.
Araunane tace.
“Ku kaini inga Moddibo sannan kada aje abinne Jameelu abari sai Moddibo ya farfaɗo yaga J ɗinsa na ƙarshe ya tabbatar cewa J dinsa tafi ya barsa bari na har abada, idan yaga haka zai dangana ya sawa ransa haƙuri amma yanzu dan Allah ku kaini wajen Moddibo”.
Abba ne yace.
“Yanzu zaki tafi can?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh ku kaini wajensa”.
Ahankali Malam Ahmad ya miƙe tare da riƙe hannunta suka tafi.

Asma'u da Bashir kuwa kuka suka sake fashewa dashi har muryarsu baya fita saboda tsananin tashin hankali.
Rintse Idanu Abba yayi cike da tausayawa ya kallesu kana yace.
“Ku daina kukan nan kuyi masa addu'a babu abinda Jameelu ke buƙata awajenmu yanzu kamar addu'a.

Acan asibiti kuwa Ummi da Malam Ahmad na isa a reception suka samu Malam Arɗo tsaye ganinsu yasa ya ƙara sa kusa dasu kana yace.
“Maman Jameelu kiyi haƙuri. Ubangiji Allah ya jikansa da rahma Allah ya gafarta masa Ubangiji ya amshi shahadarsa”.
Cikin sanyin murya tace.
“Ameen Malam Arɗo ina Moddibo?”.
Ahankali ya gyara tsayuwar sa kana yace.
“Gashi can yana ciki”.Ya faɗa tare da shiga gaba Ummi da Malam Ahmad na biye dashi.
Suna shiga ɗakin Ummi ta zubawa Moddibo idanu dake kwance plat Fuskarsa tayi fayau duk da bacci yake amma tashin hankali da fargaba ne kwance asaman fuskarsa.
Ahankali ta riƙe hannunsa acikin nata kana tace.
“Moddibo munyi rashi, rashin da baza mu maimaita gurbinsa ba, munyi rashi rashin da har abada ba zamu mance shiba, munyi rashi rashin da saidai namu mutuwar ne zai mantar mana dashi”.
Moddibo kuwa duk da Alluran baccin dake jikinsa hakan bai hana shi jiyo sautin muryan Ummi ba. So yake ya farka domin kunnuwansa na sauraronta haka zalika yana iya motsa gaɓɓansa sai dai koda ya buɗe idanunsa baya ganin komai cikin wani irin yanayi ya damƙe hannun Ummi acikin nasa, yayinda zuciyarsa ke cigaba da bugawa da masifar ƙarfi.
Kallon Malam Ahmad Malam Arɗo yayi kana yace.
“Toh tunda kunzo bari na wuce na faɗawa Kakarsa halin da ake ciki”.
Jinjina kai Malam Ahmad yayi tare da cewa.
“Ya kamata kam aje afaɗa mata sannan itama ataho da ita”.

Kai Malam Arɗo ya gyaɗa kana ya juya ya fita kai tsaye gidan su Moddibo ya nufa yana isa yayi Parking ɗin motarsa kana ya shiga gate din farko ya daga sautin muryarsa tare da yin sallama.
Cikin sauri Innayi ta fito ganinsa yasa ta saki Ajiyar zuciya tare da cewa.
“Alhamdulillah dama yanzu nake tunanin in kira ka dan. Moddibo tun safe daya fita bai dawo ba, duk da cewa dama yanzu bai cika dawowa da wuri ba”.
Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe kana yace.
“Ki zo mutafi”.
Saurin Kallonsa tayi kana tace.
“Ina zamuje”.
Cikin sanyin Murya Malam Arɗo yace.
“Wajen Moddibo zamuje yana asibiti”.
Da sauri ta dafe ƙirjinta sai kuma ta juya ta nufi cikin gida hijabinta ta ɗauko ta sanya kana ta rurrufe kofofin gidan kafin ta fita.
Bayan sun fara tafiya acikin motar Malam Arɗo ya kalli Innayi kana yace.
“An samo gawar Jameelu fa!”.
Cikin tsanananin ruɗu da tashin hankali ta dafe ƙirjinta tare da faɗin.
“Gawar Jameelu kuma?”.
Kai Malam Arɗo ya gyaɗa kana yace.
“Eh gawar Jameelu aka samu sun kashe sa”.
Atake hawaye suka shiga zubowa Innayi cikin tashin hankali da jimami ta saki sassayan kuka tare da addu'o'i.

A dai daren wannan ranar haka kowa ya kwana cikin ƙunci da raɗaɗi azuciya.
Asp da tawagarsa sun koma gida bayan sun gama dukkan abinda ya dace na bincikensu, haka zalika Lamiɗo ma ya koma gida Abba kuwa kwana yayi da gawar Jameelun sa agabansa batare daya rintsa ba.

Asma'u kuwa Hajiya Turai ta jata zuwa ɗakinta Anan ta kwana duk da cewa ba tayi bacci ba.
Bashir kuwa aɗakin ƙannen M Jameel ya kwana tare dasu Aɓangaren Moddibo kuwa haka ya kwana cikin wani irin yanayi shi ba bacci ba kuma kuma shiba Ido biyu ba ba kuma a sumeba.
Ana kiran Assalatun Farko acikin kunnen Moddibo sannu Ahankali ya fara bude idanunsa da yaji sunyi masifar nauyi har ya sauƙesu akan Ummi dake riƙe da hannunsa Idanunta abushe alamar ko rintsawa ba tayi ba bare kuma bacci.
Cikin wata murya mai cike da karaya da kuma rauni yace.
“Ummi”.
Kallonsa Ummi tayi tare da faɗin.
“Na'am Aliyu”.
Girgiza kai yayi yayinda zuciyarsa ke cigaba da bugawa da masifar ƙarfi yace.
“Ummi J ɗina”.
Cike da tausayawa ta rintse Idanunta kana tace.
“Aliyu kayi haƙuri”.
Cije Lips ɗinsa yayi tare da damƙe hannunta acikin nasa kana yace.
“Ummi J ɗina”.
Jinjina kai tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya tace.
“Kayi haƙuri kaje kayi sallah duk abinda kake ji Aranka kana so ka faɗa min ka faɗawa Ubangiji”.

Cikin sauri Malam Ahmad dake tsaye ya ƙara so bakin gadon tare da riƙe hannun Moddibo cikin sanyin murya yace.
“Kayi haƙuri kaje kayi alwala”.
Kallon Malam Ahmad Ummi tayi kana tace.
“Toh ni yanzu zan tafi gida”.
Girgiza kai Malam Ahmad yayi tare da cewa.
“A'a ki bari mu tafi gidan Alhj Bashir yanzu”.
Girgiza kai tayi kana tace.
“A'a mu tafi gidanmu dai”.
Girgiza mata kai yayi kana yace.
“A'a gidan Alhj Bashir zamu je acan fa za ayi jana'izar mu tafi can ɗin!”.

Shiru kawai Ummi tayi ahankali.
Moddibo da har yanzu hannunsa ke cikin nata yace.
“A'a Ummi dan Allah muje gidan Abba”.
Kai ta gyaɗa masa cikin sanyi tace.
“Toh shikenan”.
Batare da an sallamesu ba suka fita Moddibo da Malam Ahmad suka shiga gaba Ummi tashiga baya Anutse Malam Ahmad yayiwa motar key kana yaja suka bar Asibitin kai tsaye gidan Abba suka nufa suna isa Malam Ahmad ya danna hong ta cikin ƙaramin ɓulin. Mai gadi ya leƙa jin ana ta danna hong ganin motar da tazo jiya da safe ne yasa ya koma cikin gida tare da sanarwar Abba yaga motar da jiya tazo yauma ta dawo.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Eh kaje ka buɗe musu Maman Jameel ne yanzu aka sallame su daga asibiti kaje ka buɗe musu”.
Kai ya gyaɗa sannan ya buɗe musu gate din suka shiga bayan Malam Ahmad yayi Parking suka fito kai tsaye falon Abba suka shiga.
Zaune suka samesa shi kaɗai a falon hannunsa riƙe da Carbi ya tsirawa kwalin Gawar Jameel Ido.
Ahankali Ummi ta ƙarasa tare da zama agefen kwalin shima Moddibo zama yayi agefen kwalin Malam Ahmad ma ya zauna agefen kwalin sai ya zamana sun saka kwalin Atsakiyar su.
Moddibo kuwa kallon kwalin yayi kana ya kalli Ummi cikin raunin murya yace.
“Ummi yanzu J ɗinane aciki?.
Ummi da gaske J ɗina ne ya rasu!?”.
Kai Ummi ta jinjina kana tace.
“Da gaskene Moddibo, tabbas Jameelu ne yarasu Jameelu ya tafi yabar mu bari na har abada, ba zamu sake ganinsa ko jin sautin muryarsa ba sai dai ahoto”.
Girgiza kai Moddibo yayi tare da ɗaura kansa akan kwalin ya fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya cikin sheshsheƙan Kuka yace.
“Yanzu shikenan J ɗina mun rabu har abada bayan yana burin yin Aure ya zauna gida ɗaya da Ummi da ƙannensa yanzu shikenan wannan burin ya tafi”.
Ya sake Rungume Kwalin tare da cewa.
“Yanzu shikenan J ya tafi ya barni shin dawa zan rayu duk wani farin ciki ne da walwala na J ɗina ne shin waye zai fahimcini a duniya? J ɗina ne kaɗai yake iya fuskarta halin da nake ciki shikenan sun rabani da aminina kuma farin cikina!”.
Wani irin tausayinsa ne ke ratsasu Abba kam kasa daure wa yayi ya sunkuyar da kansa ƙasa hawaye na zuba.

Cikin sheshsheƙa Moddibo ya ɗago kansa tare da kallon Ummi idanunsa cike da ruwan hawaye yace.
“Shikenan Ummu sunyi mai kisan gillah, sun hanashi shan ruwa, ya mutu da kishi da begenmu, yana ganin muna kiransa amma bashida damar ɗauka, Ummi ashe duk kiran da mukewa J yana kallon kiran mu!”.
Sai kuma ya kife kansa akan kwalin hawayen sa na sauka akai yace.
“Ummi J yana ganin kiran mu amma bazai iya ɗagawa ba Ummi sun azabtar da J ya mutu da tsananin begenmu da muradin son kasancewa damu Ummi sun cutar da J mutumin da koda ƙwaro baya iya cutarwa bare bil adam shin wani irin zunubi suka aikata!”.

Jin ankira assalatu yasa Malam Ahmad sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.
“Moddibo kayi haƙuri ku tashi muyi alwala mu tafi masallaci”.
Ahankali Moddibo ya ɗago kansa akan kwalin daya jiƙe da hawayensa cikin ransa yace shikenan J ya tafi yabarni bari na har abada shikenan ni kaɗai zan rayu.
Hajiya Turai ce ta shigo falon tare da jan Ummi suka tafi ɗakinta Anan sukayi sallah.
Chapter 113 · 0% Book details