← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 114

Sashe 74

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gimbiya Dadu kuwa tun da ta sauƙa daga mota Idanunta nakan Khausar ta wani kafeta da Ido tare da sake laɓenta na ƙasa.
Khausar kuwa cikin rawan jiki da tsinkewar zuciya tayi saurin koma wa bayan Naseer zuciyarta na bugawa da mugun ƙarfi cike da tsoro take karanta duk wata addu'a da tazo bakinta.
Murmushi Lamiɗo yayi tare da cewa.
“A'a Nasiru ya dai ina zakuje kaida Mutuniyar taka?”.
Cikin yanayin zumuɗinsa da rawan kai ya shafa ƙeyarsa tare da cewa.
“Abbah zan kaita gidansu Asma'u ne dan banaso ta hau Napep”.
Jinjina kai Abba yayi kana yace.
“Yayi kyau Allah ya kiyaye hanya, Khausar sai kun dawo”.
Kasa cewa komai Khausar tayi still tana tsaye bayan Naseer zuciyarta na cigaba da tsinkewa ganin har zuwa lokacin Gimbiya Dadu na Binta da ido burinta su haɗa Ido.
Gyaran Murya Lamiɗo yayi kana yace.
“Khausar shiga mota ku tafi”.
Cikin sauri tace.
“Toh Abba”.
Kana ta fito daga bayan Naseer tashiga gaban motar.
Kallon Gimbiya Dadu Naseer yayi kana yace.
“Yafendo sai mun dawo”.
Ya ida maganar tare da buɗe mazaunin Driver ya shiga kana yaja motar suka fice ahankali ya dai-dai ta hancin motarsa suka hau kwalta.

Sai asannan ya juya ya kalli Khausar da fuskarta babu annuri kona misƙala zarratin zaman blutooth dake kunnensa ya gyara ajiyar zuciya ya saki yana bin ilahirin jikinta da kallo hannunsa ya kai tare da ranƙwafawa kanta zai riƙe yalwataccen sumar dake gefen wuyanta zai shinshina.
Cikin sauri Khausar ta kauce tare da watsa masa wani kallo.
Tsuke fuska yayi tare da marairaice murya kana yace.
“Haba My Wife mai yasa zaki min haka kibari mana in sinsina gashinki naji wannan Sanyayyar ƙamshin da yake fita”.
Sake tsuke fuska Khausar tayi tare da tura ƙaramin bakinta kana tace.
“A'a nidai Yaya Naseer ka bari bana so”.
Langwaɓar da kai yayi kana cikin wata murya mai ɗauke da zallan shauƙi da sha'awa yace.
“Toh na bari ai yanda kike so haka za ayi hope dai kina sona?”.
Ƙasa tayi da kanta tana wasa da zara-zaran yatsun hannunta amma ba tace komai”.
Sake narkar da muryarsa mai ɗauke da zallan sha'awa kana yace.
“Dan Allah kice kina ƙaunata ko zanji daɗi kinsan na daɗe ina dakon soyayyarki azuciyata, Khausar kece rayuwata bazan iya rayuwa idan babu keba kece muradin raina, kece fitilar dake haskaka rayuwata ina miki sahihiyar ƙauna wanda bana yiwa kaina”.
Lumshe idanunsa yayi tare da kallon fuskarta zuwa ƙirjinta kana yace.
“Kece wacce zuciyata keda burin kasancewa da ita, kece farin cikina muddin ban mallakeki amatsayin matata ba bazan taɓa samun nutsuwa ba, My Khausi saboda ke nadawo Nigeria ba dan keba wlh bazan dawo ba.
Duk yawan kyakkyawawan matan dake India babu wacce ta burgeni ta kuma kwanta min arai sai ke duk kyawunsu kallon maza nake musu!”.

Ita dai Khausar batace komai ba sai wasa da take da yatsun hannunta.
Naseer kuwa karyar da murya yayi tare da lashe lips ɗin sa kana yana binta da wani shu'umin kallo ya lumshe Idanunsa tare da cewa.
“Khausar inada burin mallakar ki ke kaɗai ce zaki iya sarrafani, akan shimfiɗata sannan ke kaɗai ce zaki iya bani farin ciki akan shimfiɗa ta”.
Lokaci ɗaya Khausar ta sake haɗe fuska cike da takaici tarasa Meyesa Naseer yake mata wasu irin maganganu marasa kan gado.
Al'amarin Naseer yafi kama da irin mayaudaran mazan nan na zamani.
Shirune ya ratsa motar har suka isa ƙofar gidansu Ummi yayi Parking daga waje, Ahankali Khausar ta ziro ƙafanta da suka sha jan lalle.
Dai-dai lokacin Asma'u ta iso.
Ganin Khausar yasa ta faɗaɗa fara'ar fuskarta kana tace.
“A'a Khausisi, Lelewal tawa”.
Murmushi Khausar ta sakar mata tare da gyara zaman gyalenta kana tace.
“A'a ina kika je?”.
Asma'u na gyara wuyan hijabinta ta kalli Khausar tare da cewa.
“Wallahi kitso naje”.
Jinjina kai Khausar tayi kana tace.
“A lallai dai kam”.
Juyawa tayi ɓangaren da Naseer ke tsaye ya zuba mata ido ɗauke kanta daga garesa tayi kana ta mayar da kanta kan Asma'u tare da cewa.
“Asmeey ga Uncle Naseer”.
Sai alokacin Asma'u ta ganesa da murmushi afuskarta tace.
“Laa Uncle Naseer Mutanen India fatan kazo lafiya. Khausar tace min kadawo toh Allah yatemaka”.
Kai ya jinjina cike da Iyayi kana yace.
“Wallahi na dawo amma fa saboda My Khausi nazo, ana ɗaura mana aure kuma zan ɗauki abata mukoma can”.

Murmushi Asma'u tayi tare da kallon Khausar da ta tsuke fuska kana tace.
“Toh Allah ya tabbatar mana da alkhairi”.
Da sauri ya amsa da.
“Ameen”.
Khausar kuwa hannun Asma'u ta riƙe zasu shiga gida.
Da sauri yace.
“Ya dai haka My Khausar ba zaki tsaya mu ɗanyi hira ba?”.
Ataƙaice ta girgiza masa kai tare da cewa.
“A'a”.

Shafa kansa yayi tare da lumshe idanunsa kana yace.
“Toh ƙarfe nawa zaki koma gida sai inzo in ɗauke ki”.
Babu walwala atare da ita tace.
“A'a ba sai kazo ba Uncle Naseer zan koma”.
Wani irin zare ido yayi tare da girgiza kai kana yace.
“A'a My Khausi kar ki min haka.
Ni dai ki faɗa min ƙarfe nawa zanzo ɗaukarki”.
Ƙaramin tsaki taja aranta tare da cewa wannan mutumin ya fiye naci afili kuma juyawa tayi ta kallesa tare da cewa.
“Toh ka dawo ƙarfe shida na Yamma”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh shikenan My Wife sai nazo”.
Ya ida maganar tare da shigewa motarsa yaja.

Bayan sun shiga cikin gida Khausar ta juya tare da kallon Asma'u kana tace.
“Ya dai naga kamar Ummi bata nan?”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh Ummi ta tafi gidan Innayi. Ni kaɗai ce sai Bashir dana bari yana mana gadin gidan shiyasa ma ana gama min kitson na dawo.
Jinjina kai Khausar tayi kana tace.
“Ayyah yayi kyau”.
Kai tsaye Bedroom din Asmau suka shiga fridge Asma'u ta buɗe ta kawo mata drinks da Fruit.
Kallon Friut ɗin Khausar tayi tare da zabga ta gumi.
Zama Asma'u tayi daga gefenta cike da kulawa tace.
“Ya dai Khausar tunanin me kike?”.
Ajiyar zuciya Khausar ta saki tare cire gyalenta ta ajiye kana ta kalli Asma'u tare da cewa.
“Ni wallahi lamarin Uncle Naseer ya fara damuna”.
Asma'u na ninke hijabin data cire ta kalli Khausar tare da faɗin.
“Mai yafaru?”.
Ajiyar zuciya Khausar ta saki tare da lumshe Idanunta kana tashiga zayyanewa Asma'u abubuwan daya yima tun daga zuwansa har yanzu daya kawota kana ta ɗaura da cewa.
“Asma'u Uncle Naseer yana bani tsoro abubuwan da yake gwada min sun fi kama dana mayaudara idan yana wani abun tamkar yana da wani nufi akaina, sannan yana yawan nuna zalamarsa akaina, ya rinƙa wani abu kamar maye!”.

Dariya Asma'u tayi tare da cewa.
“Wataƙil tsanananin son da yake miki ne kike ganin kamar haka, kinga tun kina ƙarama kamar da wasa ya fara ce Miki matarsa har gashi girma yazo wataƙil tsananin soyayya ne sannan kinga ya zauna a ƙasar da al'adun mu ba ɗaya dana suba kinga ƙasashen India wannan sai ahankali runguma da sumbata basu ɗauke shi abakin komai ba may be shiyasa kike ganin yake miki haka kuma kinga ai ya riƙa dole zaiso mace”.
Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tare da furzar da iska mai zafi kana tace.
“Anya kuwa Asma'u abin nasa is too hight ɗazun fa agaban Mommy saura kaɗan ya rungumeni saida na kauce”.
Dafe kunci Asma'u tayi tare da kallon Khausar da fuskarta ke ɗauke da alamun damuwa kana tace.
“Toh tunda har haka ne ki kiyaye al'amarin sa”.
Ajiyar zuciya Khausar ta saki tare da lumshe Idanunta kana tace.
“Zan kiyaye insha Allah amma gaskiya ya fara bani tsoro baki ɗaya al'amarin sa azalamance yake”.
Jinjina kai Asma'u tayi tare da cewa.
“Amma duk da haka yana sonki”.
Kai Khausar ta gyaɗa kana ta buɗe Idanunta dake lumshe tace.
“Na sani Uncle Naseer na ƙaunata, amma kuma wani lokaci soyayyar tafi kama da Sha'awa”.
Girgiza kai Asma'u tayi tare da cewa.
“No Khausar kada ki fassara shi da haka, sannan kinga yanzu lokaci yayi da zaki bawa Uncle Naseer dama kinga dama ga Maganar da Hajja Nana tazo da ita cewa kina gama Secondary school za ayi batun Aurenki kinga yanzu munzo gangara koma ince mungama kawai”.
Shiru Khausar tayi tare da lumshe Idanunta tana jin wani iri azuciyar ta.
Chapter 74 · 0% Book details