← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 114

Sashe 95

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka zalika ɓangaren Abba ma ya kwana ba tare daya rintsa ba acikin kwana ɗaya da yini duk ya canza yayi zuru-zuru dashi.

Washe gari da safe:Misalin ƙarfe 8:00am Abba ne zaune afalonsa ya ƙurawa wayoyinsa Idanu koda motsin kirki ya gagara baki daya hankalin sa nakan wayarsa.
Cike da ladabi mai gadi yayi Sallama ɗagowa Abba yayi ya kallesa kana ya amsa masa Sallamar.
Cike da tausayawa mai gadin yace.
“Alhj ga baƙi awaje”.
Numfashi Abba ya fesar kana yace.
“Su waye ne?”.
Tsayuwa mai gadin ya gyara kana yace.
“Hukumar ƴan sanda ne wai daga Taraba suka zo”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh ka shigo dasu”.
Kai mai gadin ya gyaɗa kana ya fice yace su shiga.
Dai-dai lokacin Moddibo yazo Parking motarsa Yayi kusan atare suka shiga ƴan sandan mutum biyar na gaba shi Kuma yana bayansu.
Bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga wajen zama Abba ya nuna musu bayan ya amsa Sallamar su.
Moddibo kuwa gefensa ya nufa ya zauna cikin mutuwar jiki da damuwa.

Gyaran murya ɗaya daga cikin ƴan sanda yayi kana Idanunsa akan Abba yace.
“Sunana Asp Mahmud Adam Shani daga rundunar ƴan sandan jahan Taraba masu bincike akan abinda ya shafi ɓatan mutane da kuma kisan kai kana da fashi da makami ina fatan zaku bamu haɗin kai.
Mun samu kirane daga nan ƙaramin Headquarter din mu”,'.
Sai kuma ya sauƙe numfashi tare da kallon Moddibo da yayi ƙasa da kansa kana yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi yake.
Kana ya cigaba da cewa.
“Mun samu masaniya Kan cewa Jameel ɗan Alhj Bashiru Maidala ya ɓata shiyasa nazo da kaina inji ba'asin maganar sannan muga ta inda ya kamata mu fara da taimakon Allah da kuma baya nan da zaku bamu zamuyi nasara wajen gano inda yake”.
Jinjina kai Abba yayi tare da rintse idanunsa kana ya fesar da numfashi tare da sunkuyar da kansa ƙasa hawaye masu zafi suka zubo masa.
Cike da tausayawa Asp Mahmud Adam Shani yace.
“Alhj ka kwantar da hankalin ka kayi min duk kan bayanin da zan gane saboda yanda zamu kula da aikin da kuma abinda ya kamata ayi akai”.
Jinjina kai Abba yayi tare da ƙoƙarin hana hawayensa zuba kana ya daure yace.
“Jameelu nine mutum na ƙarshe da yayi sallama dani ya fita ina tsaye ajikin window har ya fita bayan fitarsa na kai kimanin awa ɗaya da rabi ina tsaye ajikin window, Bayan nan kuma duk cikin mu babu wanda yayi magana da Jameelu domin ya fita akan zaije wajen Abokinsa amma bai isa ba”.
A hankali ya fesar da zazzafan iska tare da taune lip ɗin sa na ƙasa tare da kallon Asp Mahmud Adam Shani kana yace.
“Adaren Abokinsa yazo domin rashin samun layinsa da bai yiba”.
Jinjina kai Asp Yayi kana yace.
“Eh anyi min wannan bayanin daga Headquarter din mu na Nan Inspector Ayuba Garba kumo ya sanar dani komai to amma daga ɓatansa zuwa yanzu babu wanda ya kira ka!?”.
Cikin sauri Abba ya Girgiza masa kai kana yace.
“A'a babu".
Ido Asp ya zuba masa kana yace.
“A'a Alhj Bashir dan Allah kada kuce zaku bi sharuddan ire-iren mutane masu garkuwa da mutane, idan har akwai wanda ya kira ka ya maka barazana ko kuma ya nemi wani abu ka faɗa mana ko kuma ka bami number da suka kira Insha Allahu Jameelu zai kuɓuta sannan zai rayu da izinin Ubangiji zamu tsera tar dashi”.
Moddibo kuwa cikin sauri ya kalli Asp zuciyarsa na bugawa da masifar ƙarfi ya Girgiza kai tare da cewa.
“Babu wanda ya kira ai da akwai wanda ya kira zamu sanar daku sannan mu ma da hankalin mu zaifi kwanciya ma, mun san cewa yana raye”.
Ido Asp ya tsira musu kana yace.
“Anya kuwa anya babu wanda ya kira ku!?”.
Cikin sauri Moddibo ya gyaɗa kai kana cikin ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa yace.
“Babu wanda ya kira tashin hankalin mu kenan”.
Abba ya karɓi maganar da cewa.
“Da har ankira Asp Mahmud da ace ankira kamar yanda kake zaton ƴan Kidnapping ne kuma sun buƙaci kuɗin ai da tuntuni nayi muku bayani sannan idan yakama da in basu kuɗi zasu dawo min da Jameelu na da tuni na bayar an dawo min da Jameelu na!”.

Anutse Asp ya gyara zamansa kana cikin sauri yace.
“Alhj na roƙe ka dan Allah koda ankira ance kuɗi ake buƙata kada ka basu, kawai ka bamu Number sannan kayi mana bayani shine abinda muke bukata amma ana temakamu sune sannan ana ƙara basu ƙarfin gwiwa dayi musu abinda suke so shiyasa suke ƙara yin abinda suke su ɗin”.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da jingina bayansa da jikin kujeran kana yace.
“Insha Allahu zanyi ƙoƙari duk abinda ake ciki zan sanar muku Nagode sosai musamman tattakin da kayi daga Taraba zuwa nan”.
Dai-dai lokacin Hajiya Karima tazo Idanunta akan Asp Mahmud Adam Shani da sauran Folisawan Kallonta ta mayar kan Abba kana tace.
“A baƙi mukayi ne sannun ku da zuwa”.
Asp dake rubutu awata ƙaramar takarda yace.
“Yawwa”.
Kana ya cigaba da rubuce-rubucen sa.

Kallon Abba Hajiya Karima tayi tare da kallon Moddibo da idanunsa ke lumshe haƙoransa uku na sama na kan laɓɓansa na ƙasa numfashi ta fesar kana ta ƙara sa kusa da Abba da har zuwa lokacin bayansa ke jingine ajikin kujera tace.
“Alh ga Hajiya Fatima mahaifiyar Jameel ta iso”.
Ahankali Abba ya ɗago kansa kana cikin sanyin murya yace.
“Kice ta iso”.
Kai ta gyaɗa tare da juyawa ta fita ba jimawa ta shigo Ummi na biye da ita Ahankali Ummi ta ƙara sa kusa da Moddibo ta zauna Hajiya Karima ta juya ta fice cike da tausayawa Moddibo da Abba ke kallonta ganin yanda Idanunta suka kumbura sukayi jawur sun ƙanƙance.

Anutse Asp ya ɗago kansa tare da kallon Ummi kana yace.
“Wannan ce mahaifiyarsa?”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da faɗin.
“Eh itace”.
Atausashe Asp ya gyara zamansa tare da cewa.
“Sannu Mmn Jameel Ubangiji Allah ya bayyana sa ya kuma tsaresa aduk inda yake, ki kwantar da hankalinki in sha Allah zamuyi iyakar iyawarmu zamu samoshi a duk inda yake”.
Kai ta gyaɗa cikin muryanta daya dishe da kuka tace.
“Ameen ya Allah”.
Miƙewa Asp Yayi kana yace.
“Alhj to bari mu tafi amma dan Allah duk abinda ake ciki a faɗa mana”.
Kai Abba ya jinjina tare da cewa.
“Toh Insha Allah”.
Bayan tafiyarsu Ummi ta juya tare da kallon Abba cikin raunin murya tace.
“Alhj har yanzu basu sake kira ba!?”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Fatima har yanzu basu kira ba”.
A raunace ta sanya gefen hijabinta tare da share hawayen da suka zubo mata kana tace.
“To idan sun sake kira duk abinda suke so dan girman Allah kataima keni kaceci rayuwar Jameel kayi musu”.

Girgiza kai Abba yayi idanunsa na tara ƙwalla yace.
“Fatima ba sai kin roƙeni kin haɗa Ni da Allah ba, idan har banyi musu abinda suke so andawo min da Jameel ba menene amfanin dukiyata?”.
Sai kuma ya runtse Idanunsa kana ya cigaba da cewa.
“Jameel yafi min komai aduniyar nan zan iya sadaukar da duk dukiyata domin ceton rayuwar Jameel insha Allah zanyi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin ya dawo”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.
“Toh shikenan Nagode Ubangiji Allah ya kuɓutar dashi Allah yasa su faɗi abu mai sauƙi kada su faɗi abinda yafi ƙarfin mu Allah ya tsaresa Allah yasa yana cikin ƙoshin lafiya”.
Atare Moddibo da Abba ke Amsawa da Ameen cike da tausayawa.
Kallon Abba tayi kana tace.
“Bari na tafi gida”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Toh shikenan”.
Cikin sanyin murya Moddibo yace.
“Ummi muje in kaiki gida”.
Kai ta gyaɗa kana ta miƙe.
Suka fita da kallo Abba ya bisu cike da tausayawa.

Moddibo kuwa yana ajiye Ummi agida kai tsaye makarantar Malam Arɗo ya nufa yana isa yayi Parking tare da fita ya nufi harabar makarantar iska na kaɗa shi kai tsaye Office din malam Arɗo ya Murɗa handle din ya shiga bakinsa ɗauke da Sallama.

Anutse Malam Arɗo dake duba wani littafi ya ɗago kansa tare da sauƙe Idanunsa akan Moddibo ganinsa cikin wani irin yanayi yasa yayi saurin miƙewa tare da riƙe hannun sa kana yace.
“Moddibo ya dai?”.
Kai Moddibo ya Girgiza cikin sanyin murya yace.
“Bakomai”.
Kujera Malam Arɗo yaja masa ya zauna kana shima ya koma mazauninsa.

Cike da kulawa Malam Arɗo yace.
“To ina ƴan biyun naka?”.
ƙasa yayi da kansa tare da runtse Idanunsa kasancewar sa ba mai saurin kuka ba ya tabbata da ace yana da saurin kuka da zaran an ambaci sunan J ɗin sa zaiyi kuka ko hakan zaisa ya samu sassaucin abinda yake ji Aransa ya sake damƙe lip ɗin sa da ƙarfi wanda zuwa lokacin ya sake kumbura kana yayi ja sai sheƙi yake.

Ido Malam Arɗo ya tsira masa kana yace.
“Ya dai Aliyu mai yake faruwa da Jameelu tun jiya da yamma naji ana raɗe-raɗin wai ba agansa ba nayi ta kiran wayarka baka ɗauka sannan shi kuma idan na kirasa akashe ina Jameelu da gaske ne babu shi!??”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗago kansa still yana taune da lip ɗinsa kana cikin raunin murya yace.
“Babu J”.
Kai Malam Arɗo ya gyaɗa kana yace.
“Na sani Aliyu ka nutsu ka dawo hayyacinka Aliyu na sani babu Jameelu sannan na gaskata tunda har naga kai kaɗai kazo nan na tabbata do min idan anganka tamkar anga wata ne dole za'aga zara”.
Ya faɗa tare da miƙewa ya dafa kafaɗar sa.
Runtse Idanu Moddibo yayi

“Yanzu ya ake ciki?”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da shafa ƙirjinsa dake bugawa da ƙarfi kana yace.
“Nima kaina ya kulle a duniya bansan me zanyi ba bansan ya zanyi na ganni da J ba?”.
Dafa kafaɗar sa Malam Arɗo yayi cike da tausayawa yace.
“Toh yanzu wani mataki aka ɗauka akan lamarin!?”.
Chapter 95 · 0% Book details