← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 114

Sashe 60

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*In sha Allah daga gobe zan gama free page, ƴar uwa baki makara ba ki biya ki karanta cikin Aminci littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 daga wannan page ɗin sai na gobe mun gama free page, ki biya yafi sauƙi tsira ba haƙƙin kowa kanki.*

*GARKUWAR* taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.

GARKUWAR MA'AURATA

Shiko M Jameel Wani irin tsuma ilahirin jikinsa keyi sakamakon tuni da ayoyin sukayi mishi na jin azabar da Ubangiji ya tanadar wa da duk wanda ya kashe ran mumini da gangan ba tare da wani haƙiba.
Cikin raunin murya me cike da tsananin tsoron Ubangiji M jameel ɗin ya kawo fassarar aya na 90 da kuma 91, tsit gaba ɗaya masallacin yayi babu abinda ke tashi sai sautin kukan M Jameel daya kasa ci gaba, yayinda kukansa yasa da dama cikin mutanen yin kuka.
Middibo kuwa kife tafukan hannunsa yayi kan fuskarsa yana maiyin wani irin sassayan kuka mai masifar sa rawan jiki, gaba ɗaya fuskarsa tayi jazir.
Cikin ƙarfin hali M Jameel ya fara mgn cikin rawan murya yace.
“A cikin suratul Nisa, Aya ta 92 Allah ma ɗaukakin sarki na cewa, 92:
-:Baya halasta ga mutum da ya kashe ran mumini, sai dai idan ya kasance kuskure ne.”.
Sai kuma ya tsagaita tare da sayan tafin hannunsa ya share hawyen daketa kwaranyowa da idanunsa, cikin rawan murya yaci gaba da cewa.
“Duk wanda kuma ya kashe! Mumini da kuskure toh, zai ƴanta wuyan Muminin, sannan ya bada Diyya ga iyalan wanda ya kashe”.
Sai kuma ya dire ayar mgnar tare da rushewa da zazzafan kuka mai cike da tashin hankalin da raunata zukata aya ta 93.
Cikin rauni yasa hannu ya karɓi hankicif ɗin da ɗan agajin dake bayansa ya miƙa masa, sharce hawayensa yayi tare da juyowa ya kalli Moddibo da gaba ɗaya jikinsa rawa yake sai sheshsheƙan kuka mai fuzge numfashin da yakeyi, bazai iya hana kansa kuka ba, bare ya samu iko da damar hana aminin nasa.
Cikin sheshsheƙan kuka M Jameel ya gyara zamanshi tare da cewa.
“Huymmmm, a kuma cikin suratul Nisa ɗin ayata 93, Allah madaukakin sarki nacewa-:
(Duk wanda ya kashe Mumini bisa ganganci, ko Mugunta da zalumci. Toh Sakamakonsa shine wutar Jahannama”.
Sai kuma ya sake sakin wani irin raunataccen kuka mai cike da tsoro kana yaci gaba da cewa.
“Allah madaukakin sarki cewa yayi-:
Duk wanda ya kashe ran mumini zai dawwamane cikin jahannama, kuma Allah yayi fushi dashi, sannan kuma ya tsine masa”.
Kawai sai ya kife kansa bisa Table ɗin dake gabansa, shar-shar haka hawayensa ke kwaranyar babu ƙaƙƙautawa.
Modibbo kuwa cire tafukan hannunsa yayi bisa fuskarsa tare da dafa kafaɗar M Jameel ɗin kawai saka sufashe da kuka a tare, cikin kukan murya na rawa M Jameel ya buɗe baki da nufin zaiyi mgn amman ina ya kasa.
Haka yasa Moddibo rumtse idanunsa kana murya na rawa yace.
“Bayan fushi da tsinuwar ubangiji Allah Mabuwayi da komai baya ɓuyar masa yace.
-:Wa ahdalahun Azaban Azeeymah).
Ma'ana ya tandarwa duk wanda ya kashe ran mumini da ganganci Azaba mai girma!!!!.”
Zuwa lokacin wasu daga mutanen cikin masallacin kuka sukeyi da sheshsheƙan mafi akasari kuma duk jikinsu yayi sanyi.
Shi kuwa Moddibo cikin rauni da sanyi yace.
“Duk waɗannan ugubobin sun ta'allaƙane ga wanda ya kashe ran mumini da ganganci, sakamakonshi Jahannama, kuma a cikinta zai tabbata, sannan Allah yayi fushi dashi, kana ya tsine masa, kuma ya ƙara masa da azaba mai girma.
Wannan masifa har ina ɗan adam zai kaishi koda iyayenka ne sukayi fushi da kai taɓewa kakeyi bare Ubangijin talikai, koda iyayenka ne suka tsine maka lalacewa kakeyi bare tsinuwar Allah, sannan azaba koda ta tururin tea ne tsoronsa muke bare kuma tabbata ta jahannama sannan da tanadin azaba mai girma”.
Kawai sai lips inshi suka fara rawa kar-kar shima ɗin ya kasa ci gaba.
Ganin hakane yasa M Jameel sharce hawayensa tare da cewa.
“Aramma kawo mana dukkan wata Ayar Al,qura'ani da Ubangiji yayi magana akan duk wanda ya kashe ran mumini”.
Cikin tsumar jiki tare da wata raunatacciyar murya mai cike da tsananin tsoron Ubangiji da kuma sanin hukuncin wanda ya saɓa masa Moddibo yayi gyaran murya dai-dai zai fara karanta Ayar manyan Malaman dake wajen suka nuna musu agogon dake liƙe a can bayansu a jikin gini.
Wanda hakan ke musu nuni da alamar lokaci yayi.

Nan-nauyan ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe tare da share ƙwallan da suka zuba masa kana cikin raunin murya yace.
“Lokaci yayi sai dai idan Allah ya kaimu gobe zamu ɗaura daga inda muka tsaya”.
Ya sauƙe nannuyar Ajiyar zuciya tare da cewa.
“Ya Allah Ubangiji yabamu zaman lafiya ya Allah karabamu da sharrin ƴan bindiga daɗi Ubangiji ya tsare mu da sharrin kidnappers Ubangiji ya bamu zaman lafiya Allah yajiƙan iyayen mu da duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya.
Wa subhanakallahumma wabi hamdika ash shahadula'ilahu. nastagfirka wanatuubu Ilaik”.
Tunda ya fara addu'ar suke Amsawa da Ameeen har aka shafa.
Mata ne suka fara fita kafin maza.

Acan ɓangaren Khausar kuwa, bayan ta koma gida kai tsaye Bedroom ɗinta ta wuce batare data shiga wajen Mommy ba, tana shiga ta kwanta lamo akan gado hawaye na tsiyaya daga kyawawan Idanunta sosai.
Tafseer ɗin da M Jameel Yayi ya riƙa ratsa jikinta har ƙwaƙwalwar kanta Muryar Modibbo kuwa har yanzu yana ratsa kunnuwanta, da haka bacci ya ɗauketa batare data shirya ba.
Washe gari Da safe still haka Khausar ta tashi cikin mutuwar jiki Anutse ta fito daga Bedroom ɗin ta zauna agefen Mommy dake falo.
Lumshe Idanunta tayi kana cikin sanyin murya tace.
“Mommy ina kwana”.
Anutse Mommy ta maida kallonta gareta tare da na zartan yanayin ta batare data amsa gaisuwar data mata ba ta jefo mata tambya tare da cewa.
“Meke damunki Khausar na lura tun jiya jikin ki Asanyaye”.
Ɗago Kai Khausar tayi Idanunta cike da ruwan hawaye kana cikin sanyi murya tace.
“Wallahi Mommy tun jiya da muka je wajen tafsir ɗin da Malam M Jameel yayi jikina ya mutu hankalina ya tashi gaba ɗaya na rasa mai yasa tsoro ya kamani”.
Miƙewa Mommy tayi tare da matsowa kusa da Khausar ta shafa kanta kana tace.
“Babu komai wannan masiface-masiface ne da Allah ya jarabci Al'umma wannan ƙarnin saidai mu dage da addu'a Allah ya yaye mana ya kuma tsaremu da faɗa wa mummunar ƙaddara Allah ya rufa mana asiri ya karemu da zamewa sanadin mutuwar koda kadagare ne”.
Jinjina kai Khausar tayi tare da cewa.
“Ameen”.

Acan gidansu Moddibo kuwa Innayi ce zaune atsakar gida ta zabga tagumin tunda taji tafsirin da M Jameel sukayi jikinta yayi masifar sanyi wani irin tsoron Allah mara misaltuwa tashiga hakan fargaba ya rufeta.
Washe gari.
Da hantsi A hankali Moddibo da M Jameel suka fito, Moddibo na sanye cikin Shigarsa as Usual Jallabiya Sky blue mai yauƙi da santsi kansa ɗaure da farin Hirami kana takalmamsa farare jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi turaren Oud Khareem na tashi.
Shima M Jameel sanye yake cikin irin shigar Modibbo jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi kai tsaye sashen Innayi suka nufa,Innayi dake zaune gaban barandar akan kujera ƴar tsugunno ta ɗago kai ta kalli Moddibo da M Jameel kawai sai taji Idanunta na tsats-tsafowa da ruwan hawaye.
Tsayuwa Moddibo ya gyara kana yace.
“Ya dai Innayi”.
Idanu ta zuba masa batare data iya furta komaiba kawai sai hawaye suka shiga kwaranya daga idanunta.
Chapter 60 · 0% Book details