← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 114

Sashe 54

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da jingina bayansa ajikin kujera kana ya lumshe Idanunsa tare da gyara system dake gabansa ya cigaba.
_“4-Wa'atunnisa'a saduƙatihinnah Nihylah,Fa'in ɗibna lakum anshay'in minhu nafsa fakuluhu hani'am mariyya.5-Wala tu'utussahafa'u Amwa lakumallati ja'alallahu lakum ƙiyama warzuƙuhum fihaa warkusuhum waƙulu lahum ƙaulan ma'arufah”_.
Ya ƙarashe jan ayar cikin zazzaƙar muryarsa.
Shiko M Jameel gyara zaman Microphone dake gabansa yayi kana yace.
“Masha Allah Aramma”.
Atake masallacin ya kaure da kabbara wasu na buri da fatan Allah ya azurtasu da baiwan murya irin na Moddibo da yawa daga masu zuwa Tafseer ɗin suna zuwa ne Saboda zaƙin muryan ƙira'ar Moddibo da kuma nutsuwarsa musamman yanda Laudspeaker ke fitar da zazzaƙan murya Moddibo tare da sanya nutsuwa,
M Jameel da Moddibo sun iya Tafseer domin shi M Jameel mutum nai mai zafin jini Moddibo kuma ya kasance mutum mai sanyi komai nasa cikin nutsuwa yake hakan yasa mutane ke matukar ƙaunar Tafseer ɗin su mutane kan tsallake unguwar su suzo su saurari nasu.

M Jameel kuwa cike da tsantsar ƙwarewa da kuma sanin abinda yake yi ya fara tafsirin ayoyin bayan yayi muƙaddima ya fara fassarar kamar haka :
_”Aya ta(2) Allah madaukakin sarki nacewa
(Kuma ku baiwa marayu dukiyoyinsu kuma kada ku musanya mummuna da mai kyau.kuma kada kuci dukiyoyinsu zuwa ga duniyoyin ku, Lalle shiya kasance zunubi ne mai girma”_
Mafiya yawan mutanen dake wajen jikinsu ne yayi sanyi domin ji sukayi Ayar tamkar dasu take magana cike da nutsuwa suke sauraren.
M Jameel ya numfasa kana ya cigaba da cewa.
_“Aya ta (3) Allah yana cewa.
_Kuma idan kunji tsoron ba za kuyi adalci ba acikin marayu to(akwai yadda za'a yi)ku auri abinda yayi muku dai-dai daga mata biyu-biyu,Uku-uku ko huɗu-huɗu sa annan idan kunji tsoron baza kuyi adalci ba to ku auri guda ɗaya ko kuwa abinda hannayenku na dama suka mallaka.wannan shine mafi kusantar zama baku wuce haddi ba”._
Numfashi wasu daga cikin mata masu kishi suka saki jin Allah da kansa ya bawa maza ikon su ƙara aure yi shin to wai menene abin kishin hauka duk da cewa dole ne ayi kishi amma ya kamata su rika sassauta.

M Jameel kuwa juyawa yayi tare da kallon Moddibo daya zubawa system ɗin sa idanu numfashi ya sauƙe cikin yanayin zafin jinjinsa ya cigaba da cewa.
_“Acikin aya ta (4). Allah Mabuwayi gagara Misali cewa yayi.
Kuma ku baiwa mata sadakin su sauƙin bayarwa sannan idan suka yafe muku wani abu daga gareshi a daɗin rai to kuci shi da jin daɗi da saukar da hadiya”._
Ya ɗago kansa tare da kallon jama'ar dake masallacin cikin ɗaga sautin murya ya gyara zaman hular dake kansa kana yace.
“Kai Kuce Allahu Akbar”.
Atake masallacin ya ɗauki kabbara da faɗin Allahu Akbar Allah ya ƙara maka nisan kwana.
Murmushi yayi tare dasa hankie ya goge gaban goshinsa kana ya cigaba da cewa.

_“Kada ku baiwa wawaye dukiyar ku Wanda Allah ya sanya ta agareku kuna tsayuwa (ga gyaranta)kuma ku ciyar dasu cikinta,kuma ku tufar dasu kuma ku gaya musu magana sanyayya ta alkhairi”_.
Atake masallacin ya jure da kabbara cike da jin daɗin tafsirin.

Agefen ɓangaren mata Asma'u ce zauna tare da Innayi sai Khausar dake can gabansu Matsawa Asma'u tayi tare da taɓa bayan Khausar,juyawa Khausar tayi ganin Asma'u yasa tayi murmushi tare da miƙewa daga inda take ta dawo kusa da Asma'u.
Tana murmushi ta gyara zamanta tare da cewa.
“Asma'u ya Ummi amma ɗazun da mukayi waya baki ce min zaki zo Tafseer ba”.
Murmushi Asma'u tayi kana tace.
“Ai nadawo gidan Innayi da zama zan riƙa taya ta aiki sai Azumi ya ƙare zan koma gida”.
Bata jira jin Abinda Khausar zata ceba ta juya tare da kallon Innayi data tattara nutsuwarta zuwa ga tafsirin da jikokin ta keyi hannunta Asma'u ta riƙe kana tace.
“Innayi ga Khausar ƙawata”.

Murmushi Innayi tayi tare da kallon Khausar,Ita kuwa khausar ƙasa tayi da kanta cike da nutsuwa ta gyara zaman hijabinta kana tace.
“In wuni ya ibada?”.
Murmushi Innayi tayi tare da cewa.
“Lafiya lau Alhamdulillah".
Haka nan Khausar taji tsohuwar ta burgeta Kallon Asma'u tayi cikin ƙasa da murya ta kalli Asma'u tare da cewa.
“Wacece?”.
Asma'u na murmushi ta juya ta kalli Khausar kana tace.
“Kakar Moddibo ce”.
Taɓe baki Khausar tayi kana tace.
“Itakam tana da kyawawan hali ba iri jikanta ba ko ina ya gado baƙin zuciya ohon mishi mugu”.
Dariya Asma'u tayi amma batace Komai ba.

Bayan M Jameel yayi tafsirin Ayoyi guda goma,ya duba lokaci ganin ƙarfe goma saura minti takwas ya numfasa tare da faɗin.
“Wasubhanakal Lahumma wabi hamdi Nash'hadu Allah'ila ha Illah anta nastagfirka wanstubu Ilaik”.
Ya rufe system ɗin sa tare da cewa.
“Dan Allah kamar yanda aka saba maza suyi haƙuri mata su fara fita”.

Sai da duk matan suka gama fita kafin maza acan mota Innayi da Asma'u suka jira M Jameel da Moddibo har gida aka kaisu bayan sun isa gidansu Moddibo kasancewar duk Ramadan agidansu Moddibo M Jameel keyi saboda yawan hidimarsu.
Suna isa kai tsaye sashen Moddibo M Jameel suka nufa Asma'u da Innayi kuwa sashen ta suka nufa suna shiga ciki Innayi ta cire dogon hijabin dake jikinta tare da kallon Asma'u tana ajiye hijabin ta sauƙe ajiyar zuciya da faɗin.
“Asma'u ɗauki abinci ki kaiwa Yayunki tun da akayi buɗa baki ƴaƴan itatuwa da kunu kaɗai suka sha basu ci wani abu ba”.
Jinjina kai Asma'u tayi kana tace.
“Toh”,Sannan ta ɗauki Faranti Perpesoup ɗin kaza,da Couscous da miyan ƙwai sai perper cheking sai juice ɗin Abarba da kwakwa sai kuma fruit salad.
Bakinta ɗauke da Sallama tashiga zaune ta same su M Jameel na kan 2sitter yayin da Moddibo ke kan 3sitter Idanunsa alumshe ajiye wa tayi tare da juyawa zata fita.

M Jameel ya ɗago kansa tare da kallon Asma'u dake shirin fita yace.
“Asma'u zo ki zuba mana yunwa nakeji wallahi kinsan Magana ba wasa ne dashi ba”.
Murmushi tayi kana tace.
“Hakane”.
Kam sannan ta tsugunna ta buɗe Warmers din Atake ƙamshi ya bugi hancinsu da sauri M Jameel ya Kalli Asma'u tare da cewa.
“Asmeey wayayi wannan girkin?”.
Tana zuba musu miyar ƙwoyin akan Couscous ɗin ta ta ajiye kana tace.
“Ya Jameel nice Nayi”.

Ware ido M Jameel yayi.
“Kai Asmeey ki faɗi gaskiya dai”.
Murmushi tayi da faɗin.
“Allah da gaske ni nayi yaya Jameel”.
Abincin ya ɗiba ya kai bakinsa tare da lumshe idanunsa kana yace.
“Waya koya Miki wanna girkin?”.
Dariya tayi kana tace.
“Khausar ce ta koya min Allah yaya Jameel yawanci idan naje gidan take koya min”.
Moddibo dake kwance ya harareta kana yace.
“Ke dai Arayuwarki komai baki iya ba sai dai wata ce ta koya miki, ki bari mana akoya mikin kawai akayi ba magana ta ƙare ba ba sai kince ga wacce ta koya miki ba”.
Ya ƙare maganar kamar bashi yayi ba.
Murmushi Asma'u tayi kana tace.
“Allah Yaya Moddibo Khausar ta iya girki sosai saboda kullum tare suke shiga kichen da Mommy ta”.
Baki ya taɓe da faɗin.
“Naji jeki ki gaida Innayi”.

Kai ta gyaɗa tare da yin murmushi har ta kai ƙofa zata fita sai ta kuma ta sake juyawa tare da komawa ciki kana tace.
“Yaya Jameel ƙofan Innayi babu wata gashi kuma naga nan akwai wuta”.
Moddibo dake kwance ya shafa sajensa kana yace.
“Itace tace bata so gashi har cikin kicin ɗinta taƙi a kaishi ɗakinta”.

Baki Asma'u ta tura tare da Marerece fuska kana tace.
“Nikam gaskiya zama ba wutan nan baimin ba”.
M Jameel dake cin Chicken Peper ya kalleta tare da cewa.
“Toh kije ki faɗa mata wata ƙil wala Allah idan ke kin faɗa ta yarda asa mata”.

Kai Asma'u ta jinjina kana ta miƙe tare da faɗin.
“Toh”,Sannan ta fice ta nufi sashen Innayi.
Bakinta ɗauke da Sallama tashiga ɗakin Innayi zaune ta samu Innayi da lantarta azaune hannunta riƙe da carbi tana ja.
Zama tayi daga gefen Innayi kana tace.
“Innayi naga an kawo wuta a sashen su Yaya Moddibo Nan kuma babu wallahi rashin wutar nan beyi ba”.
Anutse Innayi ta juya ta kalleta kana tace.
“Ayyah Asma'u am ni tsoron wutan nan nake ji bana son irin wannan abubuwan ke kuma kina so ko?”.
Jinjina Kai Asma'u tayi tare da faɗin.
“Allah Ni dai inaso”.
Innayi ta kalleta kana tace.
“Zafi kike jine?”.

Girgiza kai Asma'u tayi tare da cewa.
“Ba zafi ba haske dai Innayi ɗan tv nan dai idan alasa zamu riƙa kallon sunna Tv”.
Jinjina kai Innayi tare kana tace.
“Shikenan sai asaka tunda haka kike so insha Allah gobe zan faɗa musu asaka mana”.
Da sauri Asma'u ta miƙe kana tace.
“Bari Inje in faɗa musu yanzu”,Ta ida maganar tare da ficewa.

Kai tsaye sashen ta koma bakinta ɗauke da Sallama tashiga Idanunta akan Moddibo dake kurɓan Juice ɗin fuskarta ɗauke da murmushi kana tace.
“Yaya Moddibo Wallahi Innayi ta yarda aja mata wuta kuma dan Allah asamar mana Tv zamu riƙa kallon Tafseer kaga ita yanzu sai dai tayi ta rungumar Radio komai sai dai taji ta Radio”.
Chapter 54 · 0% Book details