← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 114

Sashe 94

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba kuwa jujjuya kai ya shiga yi kana idanunsa akan Hajiya Karima yace.
“Karima ban yarda ba ban yafe ba wannan maganar ya fita muddin kinaso Jameelu na ya dawo kada ki faɗawa hukuma wannan maganar”.
Kai ta gyaɗa cike da damuwa.
Kallon wayarsa Abba yayi tare da cewa.
“Yanzu bari na sake kiransu naji me suke buƙata”.
Ya faɗa tare da dearling number amma swich off”.

Ɗagowa Abba yayi tare da kallon Moddibo kana yace.
“Aliyu Wayar akashe”.
Cikin sauri Hajiya Karima tace.
“Ai dama zaiyi wuya yashiga ya za ayi ya shiga ai ba zai taɓa shiga ba”.
Daga Abba har Moddibo babu wanda yace komai Allah ne kaɗai yasan abinda suke ji aransu.

Dai-dai lokacin Hajiya Turai ta shigo bakinta ɗauke da Sallama kusa da Hajiya Karima ta zauna Idanunta sun kaɗa sunyi jawur har sun kumbura alamar tayi kuka ta gaji Idanunta akan Abba tace.
“Alhj har yanzu babu labarin Jameelu”.
Kafin Abba yace wani abu Hajiya Karima tayi saurin cewa.
“Yan zun nan ƴan Kidnapping sun Kira su suka ɗauke sa!”.
Cikin sauri Hajiya Turai ta dafe ƙirjinta tare da cewa.
“Hasbunallahu wa niimal wakil Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n,Ƴan Kidnapping kuma Alhj!?”.
Girgiza kai Abba yayi sai kuma ya riƙe tafin hannunta kana yace.
“Ki zauna”.
Ba musu ta tazauna jikinta na rawa saboda tashin hankali da take ciki.

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana ya maida kallonsa kan Hajiya Karima tare da cewa.
“Wannan maganar daga mu sai mu iya mu nan kada ku kuskura maganar nan ta fita iya mu nan ban amince ba kuma ban yafe ba daga ke har Karima ban amince ku kai maganar nan kunnen hukuma ba, duk wacce takai abakin igiyoyin auren ta duka saboda sun sa sharaɗin idan na yarda hukuma ta shiga zasu kashe min Jameelu”.
Ya ida maganar cikin raunin murya.

Kai Hajiya Turai ta girgiza cikin Muryan kuka tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n in sha Allah ba zamu faɗa ba Alhj yama za ayi mu faɗa ai wannan ba abin faɗa bane!”.
Hajiya Karima ma cikin sauri ta girgiza kai kana tace.
“Insha Allah ba zamu faɗa ba, zamu kiyaye”.
Moddibo kuwa har zuwa yanzu yana dafe da kansa da hannu biyu still Idanunsa aruntse.
Ahankali Abba ya kira sunan sa tare da cewa.
“Aliyu”.
Araunane Moddibo ya ɗago idanunsa da sukayi Jawur kana sun kumbura ga lip ɗin sa na ƙasa sunyi ja kana ya ɗan kumbura.
Cikin rauni ya kalli Abba tare da cewa.
“Na'am Abba”.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.
“Aliyu ya zamuyi?”.
Zazzafafar ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da cewa.
“Abba sai dai mu jira kiran su na biyu muji mai suke buƙata magana ce dai na kuɗi atanadi abinda suke bukata a ajiye tun wuri”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh Aliyu amma yanzu ya zamuyi da mahaifiyarsa inaga kada ka faɗa mata halin da ake ciki”.
Moddibo kuwa kallon Abba yayi kana ya girgiza kansa tare da cewa.
“Abba kar afaɗa mata kuma? Ai gwara tasan cewa J yana raye, domin zuciyar Ummi zata iya bugawa da idan ba afaɗa mata ba gwara in Faɗa mata tasan cewa J yana raye tasan cewa munyi magana da shi naji muryansa, kaima kaji muryan J fa yanda muka yi magana dashi ƙilan sun dake shi!”.
Ya faɗa cikin raunin murya.

Runtse Idanu Abba yayi da ƙarfi hawaye masu zafin gaske suka shiga bin kuncinsa Shar-shar-shar.
Moddibo kuwa still Idanunsa na runtse ya gagara buɗewa har zuwa yanzu yana jin muryan M Jameel na cewa A.J bansan inda nake ba ban san ina nake ba.
Cikin rauni ya ɗago kansa muryarsa na rawa yace.
“Abba kaji fa J cewa yake baisan inda yake ba Abba ina suka kaisa ina suka cusa sa”.
Dafa kansa Abba yayi kana yace.
“Aliyu duk yanda za ayi idan ka faɗawa Fatima kada ta faɗawa kowa, sannan ka kiyaye yanda zaka faɗa mata kada hankalinta ya tashi!”.
Girgiza kai Moddibo yayi kana yace.
“Abba ba zata faɗawa kowa ba idan na faɗa mata halin da ake ciki”.
Jinjina kai Abba yayi tare da cewa.
“Toh shikenan Aliyu ka kula”.
Kai Moddibo ya gyaɗa dai-dai lokacin kiran Ummi ya shigo wayar Moddibo kallon Abba yayi kana yace.
“Abba ka gani ko kirana ma take yi yanzu kafin na wuce gida ma saina biya wajenta”.
Cike da rauni Abba yace.
“Toh shikenan tashi kaje Aliyu gashi kaima har ƙarfe goma na dare yayi tsoro nakeji, jiya a irin ya wannan lokacin suka ɗauki Jameelu”.
Runtse Idanu Moddibo yayi tare da miƙewa kana ya yiwa su Hajiya Turai sallama ya fita har kofar gida Abba ya rakasa sai da yaga tashin motarsa kafin ya koma cikin gida zuciyarsa na zafi.

Cikin sanyin jiki yayi parking kana ya fita ƙaramin ƙofar ya tura ya shiga A baranda ya hango Ummi, Asma'u da Bashir Idanun Ummi da Asma'u sun kaɗa sunyi Jawur dasu kana sun kumbura.
Bashir kuwa cikin dauriya kasancewar sa namiji yasa ya riƙe hannun Asma'u dake kuka tare da cewa.
“Ummi ki kwantar da hankalin ki da izinin Ubangiji ba abinda zai samu Yah Jameel Allah zai tsaresa aduk inda yake Asmey ki daina kuka dan Allah”.
Girgiza kai Asma'u tayi cikin Muryan kuka tace.
“Bashir taya zamu iya tsaida hawayen mu bayan bamu san halin da Yah Jameel ke ciki ba!?”.
Cikin rauni Ummi ta ɗago kanta Idanunta ya sauƙa akan Moddibo dake shigowa Iska na kaɗa sa duk yayi sauya cikin sauri Ummi ta miƙe jikinta na rawa ta nufesa tare da cewa.
“Babana”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana ya zuba mata Ido cike da tausayawa ganin kamar bata cikin nutsuwarta ƙarasawa kusa da ita yayi tare riƙe hannunta kana suka zauna agefen barandar cikin sanyin yace.
“Ummi”.
Kallonsa tayi tare da cewa.
“Na'am Babana ya labarin Jameelu na”.
Sunkuyar da kansa yayi tare da cije labɓansa na ƙasa wanda zuwa lokacin sunyi masifar ja kana sun kumbura yayin da Idanunsa ke tsats-tsafo da ruwan hawaye sai dai sun gagara zubo wa.
Ahankali ya ɗago kansa tare da damƙe hannun Ummi na dama acikin nasa kana yace.
“Ummi munyi waya da J”.
Cikin sauri Ummi ta zaro Idanunta duka waje kana tace.
“Kayi waya da Jameelu”.
Kai ya gyaɗa mata hawaye masu zafi suka zubo akuncinsa.
Kallonsa Ummi tayi tare da faɗin.
“Kayi waya da Jameelu Babana kuma kana kuka!?”.
Moddibo kuwa kallonta yayi cikin ƙoƙarin tsaida hawayen sa yace.
“Ummi anyi Garkuwa Da shine”.

Cikin matsanancin tashin hankali Asma'u ta ɗaura hannunta akai tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Ta dire addu'ar tare da komawa ta zaun.
Ita kuwa Ummu wani irin zazzafan numfashi ta fesar tare runtse idanu kana ta buɗe su akan Moddibo cikin dan sassaucin tashin hankali da take ciki tace.
“Toh ai ba komai Babana kawai Abbansa yayi ƙoƙarin haɗa kuɗi da suke buƙata a basu, su sako mana shi.
Alhamdulillah tunda yana raye, domin ai wannan abune da ya zama ruwan dare, tunda su dai in an basu abinda suke so basa kisa.”
Sai kuma ta lumshe idanunta wasu sirran hawaye suka gangaro mata cikin raunatacciyar murya tace.
“Waya sace min Jameelu na!? Waya sacemin farin ciki na!?
Waya ɗauke min jin daɗina!?
Waya ɗauke min Garkuwana da gatana!?
Wayake son yimin shamaƙi da bangona majinginata!?”.
Moddibo kuwa hannunta ya riƙe acikin nasa kana yace.
“Ummi dan Allah ki daina kuka addu'a zakiyi masa kamar yadda kikace abinda suke so kawai za'ayi musu, sun kuma gargaɗemu kada asa hukuma a cikin mgnar, sai muyi ƙoƙarin kiyayewa”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da share hawayen ta amma still wasu na zubowa.

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da zayyane mata duk yanda sukayi.
Atare Asma'u, Ummi,da Bashir suka sauƙe nannauyan numfashi.
Kallon Moddibo Ummi tayi kana tace.
“Babana basu faɗi nawa suke so bane?”.
Kai ya girgiza tare da cewa.
“Ummi basu faɗa ba tukunna sharaɗin su na farko suka bamu kada ayarda a faɗawa hukuma”.
Ajiyar zuciya mai haɗe da jan zuciya Ummi ta sauƙe still tana hawaye tace.
“Ba zan faɗa ba Insha Allah bazan faɗa ba Babana.
Ba zan faɗa ba”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da cewa.
“Ummi ki cigaba da addu'a Insha Allah babu abinda ya gagari Ubangiji kuma Insha Allah tunda suka fara kira zasu sake kira su faɗi abinda suke so sai ayi ƙoƙari amusu abinda suke so”.
Jinjina kai tayi kana tace.
“Insha Allah gobe zanje gidan su muyi magana da Abbansa idan Malam ya bari”.
Dai-dai lokacin Malam Ahmad ya shigo cike da tausayawa yake Kallonsu kana yace.
“Nama bari Fatima na bari Allah ya tsaresa ya kuma bayyana sa aduk inda yake”.
Atare suka amsa da Ameen.
Miƙewa Moddibo yayi kana yace.
“Ummi zan tafi gida”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Toh Babana Allah ya kiyaye”.
Ameen ya amsa sannan ya juya ya fice cikin mutuwar jiki.

Yana isa gida yayi Parking tare da fitowa ya rufe ƙofar kana ya shiga falon baki ɗaya abubuwan sun ca kuɗe masa ga rashin bacci rabonsa da bacci tun daren shekaran jiya ga tashin hankali da damuwa baki ɗaya zulumi sun mishi rubdugu ya fita hayyacinsa sai alokacin ya tuna baki ɗaya wayewar garin yau baiyi wanka ba cikin kasala ya nufi toilet din sai dai baya tunanin zai iya yin wanka, al'wala ya ɗaura kana ya fito tare da shimfiɗa darduma ya fuskanci alƙibla cike da nutsuwa ya shiga gabatar da nafillah aduk lokacin da ya kai goshinsa kasa (Sujjada)Sai ambaci J dinsa, raka'a huɗu yayi bayan ya idar ya ɗauki Alkur'ani mai girma kana ya fara karantawa Acikin Suratul An-Nisa'i har Misalin ƙarfe 2:00am yana karatun idan ya karanta wani aya sai M Jameel ya faɗo Masa arai kana ya tuna da wasu lokutan idan yana karatu yazo wajen Ayar azaba saiya rufe Kur'anin ya Rungume kana yaita kuka idan kuma yazo wajen Ayar Rahma sai yaita sakin murmushi kana yana cigaba da karatun.
Ahankali Moddibo ya runtse Idanunsa tare da Rungume Kur'anin aƙirjinsa idanunsa sun kaɗa sunyi jawur dasu kana sun kumbura saboda tashin hankali da yake ciki har aka kira Assalatu Moddibo bai rintsa ba.
Chapter 94 · 0% Book details