← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 114

Sashe 12

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aɓangaren Moddibo kuwa.
Zaune suke da Alh Bashir bayan sun gama gaisawa shiru na wasu daƙiƙu ya wanzu atsakaninsu kafin.
Cikin kulawa Moddibo ya ɗan juyo ya kalli Alh Bashir cikin kulawa yace.
“Alh ya akayi?”.
Numfashin mai nauyi Alh Bashir ya sauƙe kana a hankali yace.
“Mitsss Moddibo Agaskiya al'amarin Babanmu yana matuƙar ɗaure mana kai?”.
Lumshe idanunsa yayi kafin yace.
“Meya faru!?”.
Kai ya girgiza cikin yanayin damuwa yace.
“Modobbo wallahi Mahaifiyata bata da lafiya, ance sai anfitar da ita waje, gashi duk cikin mu babu wanda yake da halin biya afita da itan.
Kasan halin Babanmu kuma, duk iyakar iyawata yaƙi amincewa.
Ni kuma bani dashi”.
Cikin sanyi Moddibo yace.
“Alh baka dashi kuma”.
Kwaffa Alh Bashir yayi tare da cewa.
“Wallahi Allah Moddibo wasu lokuta idan akace min Alh Bashir ba ƙaramin ɓaci raina yake ba domin bafa mahaifina ne yabiya min Makka ba.
Sannan ba nine na biyawa kaina ba dukiyata bace yasa naje ba.
Dalilin Surukina naje wato mahaifin Matata fa ya biya min na samu naje duk wani abu da nake buƙata sai dai Inje wajensa wanda kuma hakan da kunya da kuma zubar da girma.
amma mahaifina Allah ya hore masa fiye dana surkina amman bazai taimaka manaba ayanzu ga jinyar mahaifiyarmu dole sai anfitar da ita waje an mata dashen ƙoda.
shi kansa yana ɓuƙatar canjin mota lokuta da dama yana tafiya Atsakiyar titi zakaga ta lalace, idan shi baya damuwa da zaginsa da akeyi a gari da rayuwarsa to mu muna buƙatarsa ba mason wani abu ya sameshi kuma bama jin dadin habaice-habaicen da akeyi mana.
Shiyasa nazo wajen ka.
Dan Allah da Manzonsa kayi masa magana ya kai mahaifiyarmu asibiti. Sannan ya canza motarsa bayan wannan akwai kannen mu mata da suka gama secondary akwai buƙatar su tafi jami'a amma yaƙi sasu domin aganinsa za'a cajesa kuɗi masu yawo dan Allah katemaka kayi masa magana akan waɗan nan abuvuwan”.
Ya dire ayar mgnar da haɗe tafin hannunsa alamun roƙo da neman al'farma.
Moddibo kuwa ajiyar zuciya ya sauƙe tare da buɗe idanunsa dake lumshe kana a hankali yace.
"Insha Allah zanyi masa magana, amma ayanzu da ƙyar zai amince domin da mun zauna zance ɗaya yake nanata min wai na sashi kashe kuɗi amakaranta wai zan talautashi”.
Murmushi mai ciwo Alh Bashir yayi tare da cewa.
“Muma ko agida haka muke shan complain Koda kudin cefene da sauran abubuwa aka tambayesa zaice Ni bani da kudi wannan yaron Moddibo duk yasa na kashe kuɗaɗenna aginin makaranta”.
Murmushin gefen baki Moddibo yayi wanda ke ƙara fitar da ainihin kyawunsa cikin sanyi yace.
“Uhufm Malam Arɗo kenan.
Ba matsala Insha Allah zanyi magana dashi duk yadda mukayi dashi zakaji”.
Ya kare mgnar yana shafa tattausan sajensa.

Godiya Alh Bashir ya masa sannan su kayi sallama Moddibo yashiga cikin gida.

Shi kuma ya juya ya tafi.

Tattausan murmushi Ummi tayi ganin Moddibo cikin kulawa tace.
“Babana na kaina sannu da zuwa”.
Kasancewar sunan mahaifinta garesa.
Cike da ladabi ya zauna yana cewa.
“Ummi fatan mun same ku lafiya ya yara?”.
Da murmushi afuskarta tace.
“Duk muna lafiya ya jikin Innayi?”.
“Alhamdulillah Ummi jiki kam da sauƙi sosai ma".
Ya kare mgnar yana mayar da kallonsa ga Asma'u data fito daga Bedroom da alama muryarsa taji ta fito, har ƙasa ta tsugunna tare da cewa.
“Yah Moddibo ina yini”.

“Lafiya Asma'u ya karatu da hadda?”.

“Alhamdulillah”.
Kai Ya jinjina tare da faɗin.
“Meyesa yau bakije hadda ba?”.
Kanta aƙasa tace.
“Yah Moddibo bani da lafiya ne zazzaɓi ke damuna”.
Kallonta yayi na daƙiƙu uku, kana yace.
“Asmau kadafa ki biyewa wannan mashiririciyar ƙawar taki, ki dena harƙa da ita sam banason alaƙarta dake tsakaninku.
Domin yarinyar bata ji kona misƙala zarratin, bana son ganinki tare da ita dan gaba ɗaya sunanta ya zagaye makarantar saboda rashinjinta sam bata da nutsuwar da za'ayi abota da ita.”
Ita dai Asma'u kai take jinjina mishi.
M Jameel kuwa ido ya zuba mishi yayinda Ummu kuwa ke murmushi.
Shi kuwa Moddibo gyara zamansa yayi tare daci gaba da cewa.
“Domin shin abota anaso ayi da na gari, bi ma'ana idan za kayi abota kayi da mutum na gari domin kamar dai misalin:
meyin abota da me saida turarene koda ba azata masa ƙamshi ba to baza azata masa wari ba, sannan misalin: mai abota dame zuga-zugi koda yana da haske to ba za'ayi masa zaton haske ba".
Ɗan kishingiɗan M Jameel yayu tare da lumshe idanunsa.
Shi kuwa Moddibo cikin nitsuwa yaci gaba da cewa.
“Manzon Allah (S.A.W) ya kwaɗaitar damu da yin abota da mutanen ƙwarai domin abokin ƙwarai yana daga cikin wanda Allah yayi alƙawarin zai sasu acikin inuwar alarshinsa ranar tashin ƙiyama, amma kuma duk abotar da ba'agina sa saboda Allah da manzo ba to ƙarshensa nadama ce sam wannan FATTANAH bata dace da zama abokiya a garekiba”.
Itade Asma'u kanta na ƙasa batare data ɗago ba tace.
“Toh Yah Moddibo”.

M Jameel dake kishin giɗe idanunsa lumshe kuwa a hankali ya miƙe tare da buɗe idanunsa akan Moddibo dake cigaba da yiwa Asma'u nasiyya akan tarabu da Khausar cikin tsareshi da ido yace.
“Wai dan Allah A.S meye haka? kana tayiwa Asma'u huɗubar watsar da aminiyarta shin ita Khausar ɗin sheɗan ka ɗauketa ko kuwa dujjal?”.
Ɗago kai Moddibo yayi tare da tsuke fuska yana kallon M Jameel yace.
“Kusan haka domin sam yarinyar bata da ɗabi'un kirki”.
Kai M Jameel ya girgizi kana yace.
“Haba Moddibo yarinyar nan tana fahimtar karatu duk wasu abubuwa da ake koyarwa tana ganewa fiye da duk yan ajinka,
kawai rawan kai da ƙuruciya ke damunta, da zaran ta mallaki hankalinta zata dena, amma ka zauna kana ƙoƙarin cusa ƙiyayyarta azuciyar Aminiyarta sam hakan ba dai-dai bane yoh ba ita cema ke taimakawa ƙanwar taka da kake zugawarba ita me take ganewa ma tana nan kai kamar na kifi”.
Itade Asma'u kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

Wani kallo mai cike da manufofi Moddibo yayiwa M Jameel tare da taɓe baki kana yace.
“Ina ruwanka? bansa bakinka ba da Asma'u ƙanwata nake magana”
Kana ya juyo ya kalli Asma'u da har zuwa lokacin kanta ke sunkuye yace.
“Maganata kika ɗauka zakiyi amfani dashi ko nasa?”.
Da sauri tace.
“Naka Yah Moddibo”.
Murmushi yayi da faɗin.
“Ɗayyit Allah ya miki albarka”.
Ɗago kai M Jameel yayi dai-dai lokacin Asma'u ta ɗago kanta,
ido yakashe mata ita kuma murmushi ta sakar masa.
Ummi dake sauraronsu kuwa sai yanzu tace.
“Yawwa Moddibo ka cigaba da samun Ido akan yaran nan dan yaran saida sa ido”.
Moddibo kuwa ido ya lumshe tare da gyaɗa kai kana yace.
“Insha Allah Ummi na lura J da wannan fitinanniyar yarinyar kusan halinsu ɗaya shima kullum fama nake dashi ya nutsu yaƙi nitsuwa”.
Wara ido M Jameel yayi tare da cewa.
“Nine bani da nutsuwar A.S?”.
duk dariya suka sanya banda Moddibo da yayi murmushi.

Abinci Ummi ta bawa Asma'u umarnin ta kawo musu fita tayi ba daɗewa ta dawo hannunta ɗauke da warmers ta ajiye musu M Jameel ne ya buɗe murmushi Moddibo ya saki yana kallon yanda dambun yayi kyau sai tashin ƙamshi albasa da kuma ƙamshin man shanu.
Ummi da kanta ta zuba musu tare da mimmiƙa musu plate ɗin.

Bismillah sukaui kafin suka fara ci suna kammala ci sukayi wa Ummi sallama sannan suka tafi.

Washe gari. Tun wuri Khausar ta tashi amma taƙi shiryawa da wuri seda kowa ya gama shiri ya rage saura ita kaɗai, dan Allah ya sani ita ta tsani ta gama shiri ta tsaya jiran wasu.
Ahankali take shan comflakes dake hannunta kamar ba jiranta akeyi ba yayin da Raudat ke zaune gefenta, Cikin fushi Amina ta banko labulen ɗakin cikin kumfar baki tace.
“Wallahi Khausar zamu tafi in banda raini da samun waje tuntuni muke jiranki amma kin tsaya feleƙe dan kin san in mun tafi mun barki Abba zaiyi faɗa”.
Anutse ta ɗago manyan Idanunta dake lumshe ta watsawa Amina wani kallo kafin ta taɓe bakinta kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa ta miƙe ta riƙo hannu Raudat suka fita bayan ta gama shanye Comflakes ɗin.
Ajiyar zuciya Amina ta sauƙe cike da takaici tabi bayan Khausar da haramta, duk sanda tazo da niyyan ciwa yarinyar mutunci da zaran sun haɗa ido zata nemi duk wani karsashinta ta rasa koda suka shiga motar Amina bata tanka taba ita da Raudat keta faman surutu har suka isa cikin sa'a Moddibo beshiga ba zamansu ba daɗewa yashigo as usual cikin shigar jallabiya Onion color da yasha guga kansa sanye da hula malam taɓani kaji ruwan hadith yayin da ya naɗe da hirami jikinsa na fitar da ƙamashin daddaɗan tularensa,
cike da ladabi suka shiga gaishesa Amsawa yayi kamar ko yaushe a saman laɓɓan sa.

Taɓe baki Khausar tayi aranta tace.
“Akwi madaran ƙasaita ana mutun kamar sarki”.
Batare daya kallesu ba yace.
“Su kawo hadda wiƙiƙi da ido Amina tashiga yi kasancewar itace afarko kuma bata iya ba ya dubi Samira sani yace ta karanta hadda still itama bata iyaba kallon Abeeda Sa'idu yayi yace ta karanta wacce ƙawar Samira Sani ce da ƙyar ta karanta aya biyar aciki sumunin da zasu karanta koda yazo kan Khausar cikin nutsuwa da ƙwarewa ta karato sumuni ɗaya na farkon Suratul Taubah.
Kanshi ya jinjina tare da juyowa ya kalli Asma'u Ahmad.
Cikin yanayin tsoro ta kawo suminin amman yayi mata gyara biyu.

Da ɓacin rai Moddibo ya fitar da wanda basu karanta ba ya basu punishment.
Khausar kuwa tasa su gaba ta riƙa dariya baƙin ciki ya cika musu zuciya kamar su mutu ahaka Malam Ahmad dake malamin Tajweed ne shima ya zuwa wurin addar.
Har yayi ya gama basu dawo ba seda aka tashi kafin aka ƙyalesu akan punishment ɗin...
Chapter 12 · 0% Book details