← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 114

Sashe 32

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan fitowarsu daga gidan Hajja Nana Moddibo ya ciro wayarsa da niyyar kira sai yaga ba network kallon Yaya Abba yayi yace.
“Baku da network ne?”.
Kai Yaya Abba ya gyaɗa yace.
“Eh bamu dashi amma akwai inda zaka samu idan kana da buƙata sai muje in kaika wajen akwai service ta nan nede babu”.

Kai Moddibo ya gyaɗa yace.
“Eh inada buƙata gaskiya muje”.
Sai kuma ya juya ya kalli Malam Arɗo da Baffa Liman yace.
“Bari zamuje ya rakani in sami network ina so zanyi kira”.

Baffa Liman yayi Murmushi yace.
“Yau ka shigo Rugar Fulanin da basu da network sai anje annema ko?”.
Dan murmushin Moddibo yayi tare da shafa sajensa zuwa gyamunsa daya ƙawata kyawun fuskarsa.
Malam Liman ne yace.
“Abba in kunje ku karasa cikin Rafi Modibbo yayiwa Jauron garin nan ta'aziyya sannan kuce yazo munada boƙo ne”.
Jinjina kai Abba yayi sannan suka fita shi kuma Malam Arɗo da Baffa Liman suka wuce can gida domin ƙara karatu.

Suna fita Moddibo ya kalli Yaya Abba yace.
“Kai sanyin garin kun nan yayi yawa bari na ɗauki Jacket nasa”.
Ya faɗa tare da nufar motar ya buɗe ya ɗauki farin Jacket ya ɗaura akan Army green ɗin jallabiyarsa da yayi masifar yi masa kyau.

Murmushi Yaya Abba yayi Aransa yana yaba baiwar kyawunsa da kuma iya Dressing ɗin sa.
Ta cikin wata siririyar hanya dake ɗauke da korayen ciyayi masu kyau da ƙamshi suka ratsa.
Sai wani lumshe ido Moddibo keyi yana jin kamar ya tabbata awajen saboda yanda garin ya tsaru komai nasu mai kyaune.
Ta Cikin wannan Hanyar suka ɓulla har Rafi Yaya Abba nata yi masa hira shi dai daga Uhm sai Um-um saiko Masha Allah.
kasancewar sa ba mutum nai me surutu ba.

Suna shiga cikin Rafin Moddibo ya dunƙule hannunsa waje ɗaya jin sanyin wajen yafi na cikin garin juyawa yayi ya kalli Yaya Abba kana yace.
“Muma muna da sanyi amma sanyin ku yafi namu sosai”.

Kai Yaya Abba ya gyaɗa yace.
“Sosai ma ai tanan kam munfi sanyi”.
Jinjina kai Moddibo yayi yace.
“To ku riƙa rage Bishiyoyi mana sanyin be damun ku?”.

Yaya Abba yace.
“Aikuwa mu munajin daɗin sanyin”.
Moddibo yace.
“Masha Allah”.
Acan cikin rafi kuwa Sadik riƙe yake da ƙwan Zabbi mai yawa yayin da Khausar ke riƙe da ma daidaicin kwando ahannunta wanda ke ɗauke da,Inabi,Tuffa, Mangoro,Abarba,Kwakwa, Lemo,da sauran kayan itatuwa yayin da ɗaya hannunta ke riƙe da wayar Yaya Abba tana dannawa Sadik ya juya ya kalleta yace.
“Khausar da kin haƙura da danna wayar nan sai mun tsallake wannan ruwan dake gudu kinga akwai duwatsu aciki”.
Still hankalinta na kan wayar tace.
“Kada ka damu ai ina kallo”.
Kai ya gyaɗa mata sannan suka cigaba da tafiya.

Yaya Abba kuwa yana ƙoƙarin karya kwanar da zai sadasu da Bishiyar ƙare zancenka ya hango Baffa Jauro acikin Rafi juyawa yayi ya kalli Moddibo yace.
Gacan Baffa na Jauron garin nan da Malam yace mubiya kamasa ta'aziyya”.

Kai Moddibo ya gyaɗa yace.
“Toh mu ƙara sa".
Kai Yaya Abba ya gyaɗa sannan suka nufi wajen Moddibo kuwa wayarsa ya ciro a aljihu yana duba ko akwai network ata wajen Dai-dai lokacin da Khausar ta iso wajen baki ɗaya hankalinta da nutsuwar ta nakan wayar tana saka number Mommy.

Kallon Dije Yaya Abba yayi wacce tuni ta tsallake ƙoramar ruwan yace.
“Dije har kun ɗebo ƙwoyin?”.
Kai Dije ta gyaɗa masa kana tace.
“Eh Ya Abba".
Moddibo kuwa sam bai lura da mutum agabansa ba, ya ɗago ƙafarsa na dama zai tsallaka yashiga rafin kenan, ita kuma Khausar ta ɗago ƙafarta na hagu zata tsallaka tafita a rafin ji kake gub suka bugi juna da ƙafafunsu.
Tagal-tagal Khausar tayi baya zata fadi yayin da shikuma Moddibo da ƙyar ya tsaida kansa daga faduwar da zai yi.
Ita kuwa khausar Atsorace ta saki kwandon kayan Marmarin dake hannunta tare da kai hannu ta riƙe rigarsa da hannu ɗaya yayin da ɗaya hannun ke riƙe gam da wayar Yaya Abba.
A kuma lokaci guda ta rumtse idanunta tare da sakin kara.
Shi kuwa Moddibo cikin hanzari yakai hannu ya riƙota sai alokacin idanunsa suka sauƙa akan fuskarta ita.
Ita kuwa Khausar sassayan numfashi ta fesar jin an riƙeta bata faɗiba yasa ta ɗago kan Idanunta ne suka sauƙa akan fuskar Moddibo.

Lokaci ɗaya jikinta ya ɗauki rawa na tsananin tsoro da firgicin ganinsa kawai sai ta sake hannunsa tare da rintse Idanunta tayi baya zata faɗa cikin ruwan,Cikin zafin nama yasanya Lallausan tafin hannunsa ya riƙo hannunta tare da fisgota ta tsallaka sai yayi wucewarsa batare daya juya ya kalleta ba.
Ita kuwa khausar banda rawa babu abinda jikinta keyi cikin rawan murya tace.
Ka-ka-kayi ha-ƙuri ban gankaba shiyasa, shi kuwa Moddibo ko juyawa baiyi ba bare yaji abinda take faɗa yabar wajen.
Sai alokacin Yaya Abba ya lura da yayan itatuwan ta data zubar yace.
“Ya haka Khausar mai yasa bakya kallon gabanki in kina tafiya?”.
Cikin rawan murya tace.
“Tsautsayine”.
Tafaɗa tare da barin wajen aranta kuwa tunani take yau kuna Moddibo Arugar mu me ya kawo sa? kuma mai ya haɗa sa da yaya Abba? to me ya zoyi? da wannan tunanin ta isa Bishiyar ƙare zancenka tana isa ta hau kan dutse. dake farko ta zauna tare da sa hannunta ta riƙe reshen, kana ta kiran number Mommy.

Shi kuwa Moddibo bayan sun karasa wajen Baffa Jauro.
yace.
“Ina yini Baffa fatan mun same ku lafiya ya kuma ƙarin haƙuri?”.
Baffa Jauro kuwa cikin yanayin sauƙin kansa da kuma dattako ya amsa da.
“Haƙuri Alhamdulillah fatan kunzo lafiya?”.
Moddibo ya amsa da. “Lafiya Ubangij Allah yajiƙan sa da rahma idan kuma tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani”.

Baffa Jauro ya amsa da.
“Ameen”.

Yaya Abba ya kalli Baffa Jauro da faɗin.
“Bari muje na rakasa Bishiyar ƙare zencen ka kuma Baba Yace kaje tare suke da Malam Arɗo".
Kai Baffa Jauro ya gyaɗa kana yace.
“Adawo lafiya”.
Miƙewa sukayi suka nufi Bishiyar ƙare zancenka tun kafin su isa Moddibo ke jiyo suturatai da dariyar mutane Aransa yace to lafiya dai.

Suna ƙarasawa yaga tsoffi,Matasa,maza,da mata kowa maƙale da waya akunnensa ahankali kunnuwansu ke jiyo masa kamar sautin Muryan Khausar da mamaki ya ɗaga kansa gefen yamma idanunsa suka sauƙa akanta saman dutse kana kanta na bisa reshen Bishiyar.
Aransa yace to ashe ga inda ta samo ɗabi'ar hawa bishiya wato garin ne dole sai akan bishiya ake waya wannan shine gado.

Ya juya tare da kallon yaya Abba yace.
“Dole sai na hau kan Bishiya zanyi wayar?”.
Girgiza kai Yaya Abba yayi yace.
“A'a ko akan dutsen ma zaka samu network”.

Jinjina kai Moddibo yayi yace.
“To ku maida ƙa'ida mana mata su hau kan duwatsu maza su hau kan Bishiya idan ya kama dole ne sai an hau kan Bishiya ko kuma ku maida lokacin yin wayar mata daban lokacin yi. Wayar maza da ban kusa tsari da ƙa'idar musulunci ku dena gwamutsuwa haka”.
Jinjina kai Yaya Abba yayi yace.
“Gaskiya ne kabamu shawarar data dace Insha Allah za'ayi haka zan faɗawa Baffa Jauro ayi haka”.

Moddibo kuwa cewa yayi.
“Ai ya kamata ayi haka yanzu Meye amfanin ga mata asama sannan ga maza aƙasa ko kuma duk suna gwamutse maza da mata ko da duk kan ku 'yan uwane ai yakamata ayi abu duka bisa tsarin Addini ko ba haka ba bai dace ba duk da cewa yawancin ku ’yan uwane amma akwai auratayya atsakanin wasu”.

Cikin jin daɗin Nasiyyar da ya masa da gamsuwa Yaya Abba yace.
“Hakane Insha Allah za'a gyara malam”.
Ita kuwa khausar sam batasan Moddibo sun zo wajen ba.
Bayan sun gama gaisawa da Mommy.
Mommy tace.
“Khausar kwana biyu baki kira ba kuma kinsan ba zai yiwu na kira kiba”.
Araunane Khausar da mutuwar Baffa Umaru ya dawo mata sabo tace.
“Mommy ankashe Baffa Umaru har gida aka kashesa Mommy agaban idanuna aka kashesa!”.
Shi kuwa Moddibo hankalinsa na kan yiwa Yaya Abba magana bai san mai take faɗa ba juyawar da zai yi yaji tana cewa.
“Mommy har anyi sadakan bakwai hankalina ne bai kwanta ba”.
ta faɗa hawaye na zuba daga idanunta.
Shi kuwa Moddibo ido ya zuba mata ganin yanda hawaye ke kwaranya daga idanunta.
Khausar tace.
“Mommy ai zakizo kiyi mana ta'aziyya ko?”.

Mommy da mutuwar ya kashe mata jiki tace.
“Insha Allahu zamu zo, nasan idan na faɗawa Abbanki ba zai hana ba, ki shirya idan nazo zamu taho tare, dan Asma'u tazo tayi min magana batun zaku koma makaranta, kishirya kayanki idan muka zo zamu tafi tare idan Hajja Nana ta yarda”.

lumshe Idanunta tayi tace.
“Baza ma ta hana ba Insha Allah idan kunzo zamu tafi tare dan dama tace zanje Ɓadamaye wajen Baffa na nacan kuma sunzo ta'aziyya mun haɗu dasu, sannan ma Addata Ikki tazo mun haɗu da ita sai wani lokaci zanje Ɓadamaye nama karɓi number su, suma sunce dan suna sauri ne kuma mun haɗu amma da zasu je su duba ni anma munyi canjin number”.

Cikin sanyi Mommy tace.
“Toh shikenan babu damuwa ki shirya idan nazo zamu taho Insha Allah gobe zamu zo ta'aziyya”.
Sallama Mommy ta mata.
Juyawar da zatayi Idanunta suka sauƙa akan Moddibo daya tsareta da ido saida ta kusa faɗuwa saboda tsoron ganinsa.
Da ido ya mata alamar ta saƙƙo kafin ƙiftawa da Bismillah kuwa ta diro ƙasa.
Kallon Dije dake jiranta tayi tace.
“Mu tafi”
Yaya Abba ya miƙa mata kwandon kayan Marmarin ta data zubar yace.
“Gashi kin zubar dasu na ɗebo miki”.

Kamar wacce aka fisgo maganar daga bakinta tace.
“Banaso ka bashi na bashi”.
Sai da ta rufe bakinta asannan ta tuna mai ta faɗa hannu Dije ta fusga tace.
“Mutafi".
Shi kuwa Yaya Abba gyara riƙon kondon yayi.
Chapter 32 · 0% Book details