← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 114

Sashe 9

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kam Khausar cike da mmki take kallon yadda mahaifiyar ke sakin wani murmushi mai cike da yarda da jin daɗin kawaici da ihsanin uwar gidan tata,
Yayinda ita kuwa Khausar take kallon abun da idanun basira, tana tuna kalaman da taji ɗazu da wanda Umman keyi a yanzu, a sanyaye tace.
“Marching kuma?”.
Daga ciki kuwa sai suka tsinkayo muryar Asiya na cewa.
“Ehye Haiydar ɗan gatan Umma da Lamido, yaron nan kunaji dashi,”.
Murmushin mai cike da manufa tayi tare da kallon inuwar Khausar da Mami ta jikin window nata, cikin ɗan daga sauti tace.
“Kema ai ɗan lelenki ne,”.
Miƙewa tsaye Asiya tayi tare da cewa.
“Yauwa dan Allah Umma ni zanyi masa albishir”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Amman ba yauba sai marching ɗin ya iso”.

Numfashi mai sanyi Momy ta fesar tare da kamo hannun Khausar suka juya suka tafi.

Ganin tafiyar sune yasa Hajia Bunayya yin kwaffa tare da cewa.
“Uhum zanyi mgnin kine, shegiyar yarinya mai masifar wayon tsiya da sa ido, tama fi mahaifiyar tata wayo da fahimtar manufar mutum”.

Su kuwa, suna shiga falon Khausar ta juyo a hankali tace.
“Dan Allah Momy kada ku bari Haiydar yaja marching yayi ƙarami dudu du fa shekarunsa sha 13 ne kawai dan yanada saurin girma”.
Da sauri ta juyo ta kalli Haiydar da yanzu shigowarsa, kanshi ya nuna da yatsarsa manuniya tare da cewa.
“Ni ne ma yaron? To da shekaru nawa kika fini dabino uwar tsufa, ba shekara ɗaya rak kike bani”.
Yes tabbas kam shekarunsa 13 ne, amman in ka ganshi zakayi zaton yaje 16, domin yanada girman jiki, kuma irin masu wayo da halin girman nanne shiyasa sam bazaka tantance shekarunsa ba, ya fita jiki da tsawo sosai.
Dan in ka gansu zakayi zaton shine babban irin ya bata shekara ukun nannan ne”.
Kai ta jujjuya tare da rumtse tafin hannunta, kana cikin sanyi tace.
“Dan Allah Momy kada ki bari dan Allah a wannan karon dai ki yarda dani”.
Kai Hajia Aysha ta gyaɗa mata tare da cewa.
“Zan duba."
Cikin kwaɓe fuska Haiydar ya turo baki gaba tare da cewa.
“Plesse Momy kada kibi ta kan mgnar ta”.
Still kai ta gyaɗa masa shima tare da cewa.
“Toh zan duba”.
Cirko-cirko sukayi a gabanta.
Dan dama da haka take yanke musu taƙaddama.
Idanu ta ɗan lumshe jin an kira sallan magrib cikin fesar da sassayan numfashi tace.
“Lokacin salla yayi, maza muje muyi salla”.
Ba musu duk suka juya, shi Haiydar waje ya fita yana cewa.
“Ramadan zomu tafi masallaci”.
Ita kuwa Khausar ɗakinsu ta nufa tana cewa.
“Raudat zomuje muyi salla."
Da sauri kuwa sukabi bayansu.

A can gidansu Moddibo kuwa,
M Jamil ne, ya kalli dun-duniyar sawun Moddibo lokacin da suka fito kan barandar da alamun al'wala sukayi.
A hankali yake taku cikin nitsuwa, yayinda yake motsa laɓɓan bakinsa yana taibihi.

Sai kuma ya maida kallonsa kan sumar ƙeyarsa dake kwance lip-lip tayi irin naɗin nan mai kamar taburma.
Kusan a tare suka sauƙo,
Hango Ummi da Innayi zaune bisa sallayunsu, da kaskon rushi a tsakiyar su ne, ya sasu juyawa suka nufi waje, sabida tafiya masallaci.

A hankali Moddibo ya zira tafukan hannunsa cikin aljuhun jallabiyar jikinsa, sabida wani irin masifeffen sanyi dake fesowa, duk da rigunan sanyin da suka ɗaura kan jallabiyoyin bai tsare musu sanyi irin na garin Gembila ba, musamman ma, a lokacin da magrib ta ƙarato, wanda lokacin sanire ke sauƙa.

Kasan cewar masallaci babu nisa da gidan ne, yasa suka, tafi da sawu.

A hankali M Jamil ya lumshe idanunsa sabida yadda yake jiyo sautin muryar Moddibo can ƙasa yana zikirin tafiya masallaci.

Shi kuwa Moddibo cikin yanayin sanyin da yakeji yake motsa laɓɓan sa a hankali cikin dadɗan sauti can ƙasa-ƙasa yake cewa.
اللَّهُـمَّ اجْعَـلْ فِي قَلْبِـي نُوراً، وَفِي لِسَـانِي نُوراً، وَفِي سَمْعِي نُوراً، وَفِي بَصَرِيِ نُورًا، وَمِنْ فََوْقِي نُوراً، وَ مِنْ تَحْتِي نُوراً، وَ عَنْ يَمِينِي نُوراَ، وعَنْ شِمَالِي نُوراً، وَمِنْ أَماَمِي نُوراً،,وَمِنْ خَلْفِي نُوراً، وَاجْعَلْ فِي نَفْسِي نُوراً، وأََعْظِمْ لِي نُوراً، وَعَظِِّمْ لِي نُوراً، وَاجْعَلْ لِي نُوراً، واجْعَلْنِي نُوراً، ألَلَّهُمَّ أَعْطِنِي نُوراً، وَاجْعَلْ فِي عَصَبِي نُوراً، وَفِي لَحْمِي نُوراً، وَفِي دَمِي نُوراً، وَفِي شَعْرِي نُوراً، وفِي بَشَرِي نُوراً، أَللَّهُمَّ اجِعَلْ لِي نُوراً فِي قَّبْرِي... وَ نُوراَ فِي عِظاَمِي، وَزِدْنِي نُوراً، وَزِدْنِي نُوراَ، وَزِدْنِي نُوراً، وَهَبْ لِي نُوراً عَلَى نُوراً
Dai-dai lokacin da yazo ƙarshen addu'ar suka isa bakin masallacin.
Kusan a tare suka haɗa baki wurin yin addu'ar shiga Masallaci.
”أَعوذُ بِاللّهِ العَظِيـمِ، وَبِوَجْهِـهِ الكَرِيـمِ وَسُلْطـَانِه القَدِيـمِ، مِنَ الشَّيْـطَانِ الرَّجِـيمِ، بِسْـمِ اللّهِ وَالصَّلَاةُ وَالسَّلامُ عَلَى رَسُولِ اللّهِ، اَللَّهُـمَّ افْتَـحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتـِكَ“
Kana a nitse suka shiga cikin masallacin.
Shi Moddibo gefen daman sahun forko ya zauna, yayinda shi kuma M Jamil ya nufi wurin kiran salla...

Kasan cewar M Jamil ke ladancin masallacin Moddibo kuma limancin...

Bayan an idar da sallane, Khausar ta juyo ta kalli Raudat tare, da miƙa mata littafin Dua azkar, amsa tayi kana ta buɗe daga shafin forko ta fara cikin sassayan sautin yarinta.

Ita kuwa Khausar Alqur'anin ta, ta ɗauka tare da fara, rero karatun Alqur'ani cikin zazzaƙar muryarta take biya suratul Nisa'i.

A haka har aka kira isha sukayi kana, suka fito.
A falon suka zauna baki ɗayansu suna cin abinci.

Misalin ƙarfe tara da rabi, Ummi ce zaune gefen Innayi da hijabi a hannunta alamun ta gama shirin tafiya.
Cikin kulawa da martabawa tace.
“Toh Innayi Allah Ubangijin talikai ya baki lfy yasa zakkan jikine, in Sha Allah gobe koda dare zan zo in kuma dubaki da jiki”.
Kai ta gyaɗa cike da jin daɗin kulawar Ummin Jamil cikin ƙarfin guiwar da ta ɗan samu tace.
“Amin ya rabbil izzati Fatima ngd matuƙa Allah ya raya miki ahlinki yasa suyi miki fiye da abinda kikeyi min”.
Cike da jin daɗin addu'ar tace.
“Amin ya Allah”.
Moddibo kuwa, kai ya tankwara gefe yana kallon kakartasa, sosai ta rame a dare ɗaya da wuni ɗaya.

Haka dai sukayi sallama Jamil ya ɗauke ta suka tafi.

Har bakin gate Modibbo ya rakasu.
Kai ya ɗan juya ya kalli wata motar dake gefen damansa ƙirar BMW irin dai wacca M Jamil yaja sukaje makaranta, sai dai wacce baƙace wannan kuma farace ƙal mai masifar kyau.
Murmushin M Jamil yayi sabida ya fahimci kallon da yayiwa motar ma magana ce.
kanshi ya juya tare da cewa.
“Lafiyarta ƙalau kawai na barta a nanne sabida nan ya dace da ita, tunda ba gida ɗaya mukeba, Allah ya kiyaye wani uzurin zai iya tashi da dare, kaga kamar jiya da kasan Innayi ba lafiya kawai ɗaukarta zakayi ku tafi hospital ko Ummi?”.
Ya dire ayar mgnar yana kallon Umminsa da shima Moddibo ita yake kallon.
Cikin gamsuwa Ummin tace.
“Sosai ma kuwa”.
Cikin yin ƙasa da kai Moddibo yace.
“Ummi har kema haka zakice, kamar baki san me ake faɗi a cikin gariba, ba cikin gari, bama har cikin gidansu fa, ganin kaskas akemin wasuma ɗaukar abotarmu ta tun yarinta sukeyi a matsayin na maida J saniyar tatsa."
Cikin sanyi Ummin tace.
“To Moddibo ai shi ɗan adam ba'a biye masa”.
Da sauri Jamil yace.
“Yauwa Ummi gaya masa dai kam”.
Cikin tsare M Jamil din da ido yace.
“Motace dai ta hannunka ta ishemu, kuma ga waccar ma, kasan in bawai baka nanba always muna tare”.
Da sauri Jamil ya jujjuya mishi kai tare da jan motar ya tafi.

Sashin Innayin ya nufa, cike da zurfin nazari.
Tv ya kunnamata tashar Sunna, inda aka sa sautin karatun Alqur'ani mai girma.
Ido Innayi ta lumshe jin nitsuwa da salama na diro mata,
Saida safe yayi mata kana juya ya fita zuwa Part ɗin sa.

Washe gari ranar Alhamis ne, yau babu makaranta ko yan haddan bazasu jeba, shiyasa su Khausar suna gida,
Bayan sallan la'asar Asma'u Ahmad ta shigo falon Momy cikin sakin fuska tayi sallama.
Da sauri Khausar ta fito daga ɗakin Momy tana cewa.
“Wa alaikissalam Giɗaɗo".
Murmushin Asma'u Ahmad Giɗaɗo tayi, ƙanwar M Jamil kenan da suka haɗa uwa.
Cikin sakin fuska tace.
“Jauro”.
Fuska Khausar ta kwaɓe tare da cewa.
“Wai jauro gsky ni an cuceni”.
Murmushin sukayi baki ɗaya sabida daƙuwar da Mamy tayi musu.
Cikin kunya Asma'u ta ɗan rusuna, tare da cewa.
“Barka da yamma Mamy”.

“Barka dai Asma'u ya Umminki?”.

“Tana lfy tace in gaidaki”.

“Masha Allah Ina amsawa”.

Da sauri ta miƙe tsaye jin Khausar ta kamo hannunta.
Ɗakinta suka nufa, suna shiga suka zauna bisa gado.
Raudat dake kwance kan gadon riƙe da wayan Mamy tana game ne ta miƙe da sauri ta faɗa kan Asma'u.
Ruggumi yarinyar tayi tare da cewa.
“Autan Mamy tsifa ake yi ne”.
Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.
“Eh kuma gashi har yanzu Adda Khausi bata gama minba, tsifanta zafi”.
Hararanta kausar ta ɗanyi tare da cewa.
“Da Allah tashi daga nan, nawama da yaya nake tsifan, kin samu ma inayi miki”.
Ta ƙare mgnar tana fita daga ɗakin.
Jim kaɗan ta shigo riƙe da filas da kofuna guda biyu bisa tray da kuma kayan tea, kan bed side drower ta ajiye tiran kana ta haɗa musu tea mai zafi, sabida rage sanyin da suke rayuwa cikinsa, yasa tea ya zame musu tamkar ruwa, madadin in kaje baƙunta a baka abin sha mai ɗan sanyi, sai a tarbeka da zazzafan shayi.

“Gidado bar tsifan nan ga tea".
Khausar ta faɗa tana zama gefenta tare da miƙa mata, kofin.
Amsa tayi tare da kallon Raudat da ta fice da gudu sabida jin Abbansu ya shigo yana kiranta.
Chapter 9 · 0% Book details